Showing 90001 words to 93000 words out of 144990 words
ta ya kara a kunnensa.
"Eh nine, ni ne wanda ya kira ka yanzun nan... Dan Allah ka taimaka in samu ticket din nan... Eh,
na Lagos... To shikenan ina son na Lokojan... Nagode ka samar min shi
ɗ
in kawai, gani nan yanzu zan karaso."
Ta fadi dukkan wannan bayanin, zuciyarsa na rawa tare da amon muryarsa, burinsa da ma fatansa ya ta'allaka ne a tanzu kawai kan barin garin nan, b
abu iya kokarin da baiyi ba wajen kokarin fahintar da Hajiya Salamatu iya gaskiyarsa don ta yarda da dukkan bayanin da yayi mata, amma bata saurare shi ba sam! Hasali ma ta gaya masa ne cewar zata yi masa alfarmar rufe sirrinsa a wajen Kilishi don niyyar t
aimakon da yayi mata, kuma bata ko sake
ɗ
auko shi motar ta ba ita da direbanta suka juya suka tafi suka barshi tsaye a ƙofar gidan Bunun nan.
Haka ya fito daga cikin ƙauyen nan ya samu ya isa tasha sannan ya
ɗ
auki shatar mota guda saboda tun akan hanya zuc
iyarsa ta gaya masa cewa bashi da isasshen lokaci da kuma kwanciyar hankali daga yanzu, gobe ne... gobe ne ranar da Kilishi ta gama tsarinta akansa, gobe ne dukkan wannan bayanan da yaji su a matsayin labari zasu tabbata idan har bai samarwa kansa mafita b
a.
Don haka a yanzu zai dauki dukkan wasu abubuwansa masi muhimmanci ne ya var garin nan, idan yaso daga baya,zaiyi magana da dillalin da zai sayar da gidan ya kuma
ɗ
aukar masa sauran kayansa... Burinsa da fatansa kawai shine ya bar cikin Kano a yau, yayi
nisa daga inda Kilishi zata iya samunsa kafin yayi nisa daga gare ta gabadaya, nisan da ba zata taba iya samunsa ba, don idan har shi baiyi nasara akanta ba, to kuwa ba zai taba bari ita tayi akansa ba.
Bayan ya ajiye wayar ya zaro wallet dinsa ya kalli ad
adin kudin ciki da kuma tarin cards
ɗ
insa na banki, ya tabbatar komai yana nan daidai sannan ya sake mayar da ita aljihunsa.
A hannayensa duka biyun ya
ɗ
auko jakar ya kuma riƙo akwatin da guda
ɗ
aya, ƙafafunsa na sassarfa ya fito daga
ɗ
akin ya sake biyowa t
a cikin falon ya nufo hanyar fita waje inda motarsa da ya bude ke jira, sai dai da taku biyu ka
ɗ
ai ya rage tsakaninsa da kofa lokacin da abin ya faru...
Kofar falon ta bu
ɗ
e da wani irin ƙarfin da yafi na hankali, kuma a cikin sakanni biyun da suka biyo bay
a, idanun Awwalu suka
ɗ
aukar masa hoton mutanen da suka fado ciki...
Ya san su, ya gane shigarsu, kayan jikinsu da kuma yanayin yadda suke rufe ba tun yau ba, ba kwanan nan ba, a shekaru masu yawa da suka wuce, shekaru goma da suka wuce.... Sai dai kafin k
wakwalwarsa ta tariyo masa inda ya san su da kuma a ranar da ya gansu
ɗ
aya daga cikinsu ya karaso da saurin da suka fa
ɗ
o gidan dashi ya buga masa wani dogon abu da yake riƙe dashi.
Wata tsawa tare da wani farin haske suka ratsa kunnuwa da kuma idanun Awwal
u a lokaci guda! Yaji kamar ruwa na bi ta bayansa, kamar yana sulalewa zuwa wata duniyar daban, taji sanda kafafunsa suka yi rawa suna durkushewa a wajen, kuma kafin idanunsa su tafi su rufe gaba
ɗ
aya, yaga sanda da yawansu ke shigowa cikin gidan suna yanya
me shi.
****
"Kun gama?"
Ma'aruf ya tambaya a cikin wayar dake kare a kunnensa yayin da yake zaune cikin daga office din Faruk.
Amina dake tsaye ya gaban mudubin dakinta ta daga kai kafin tace.
"Eh yanzu ta fita, ta gaya min duk abinda zan dan kiyaye ne ku
ma tace babu wani abu tunda anui scanning a asibitin babu wata matsala, kuma nace mata babu abinda nake ji."
Ma'aruf yayi shiru yana kallon tarin takardun dake gabansa da kuma Faruk
ɗ
in dake can jikin windon office
ɗ
in yana waya, an kammala dukkan wani bin
ciken da gidan waya je yi akan lambar da suka samu ta Awwalu, sun sami tarin bayanin da tun dazu ake turowa Faruk
ɗ
in yana printing dinsu daga computersa, a yanzu abu
ɗ
aya kawai suke jira, so suke yi a turo musu da address din inda yake wanda aka samu daga
cikin wayarsa tare da wani shekaru uku da suka wuce yana bayanin canja gidan da yayi.
Yaron da zai turo musu da report
ɗ
in hakan ne ya tafi wani meeting tare da sauran shuwagabannin su, don haka tun
ɗ
azu Faruk
ɗ
in ke rike da kan waya yana jiran dawowarsa
tare da kuma samun wasu bayanan daga sauran ma'aikatan wajen.
A gabansa kuma tarin takardu ne na meeting din da zasu shiga da kamfanin Rotel&co gobe, kwangilarsu ta gaba... Babu yadda Faruk bai yi dashi akan su daga ranar zaman nasu ba amma yace masa A'a d
ole zasu ajiye komai a gefe su yi hakan, don baya son bawa Baffa kowacce irin dama da zaiyi tunanin cewa suna kasawa a wani abu, sannan su kansu kamfanin sun samu kwangilarsu ne da kyar, akwai tarin kamfaninnika da yawa da suke neman samun yin aiki dasu do
n tabbas kowa shaida ne cewar biyansu ya banbanta da na wasu kamfanikan da yawa.
Don haka ko yaya suka basu wata dama, kai tsaye zasu iya tuntubar wasu su manta da zancensu, fon haka ya dage cewar dole su tsaya kan alkawarinsu, amma kuma duk da
Wadannan
tarin ayyukan dake gabansa tunaninsa ya kasa mantawa da matarsa da kuma sabon al'amarin da suke ciki, gani yake kamar ba haka bane, kamar abinda ita da kuma asibitin nan suka gaya musu ba gaskiya bane, ba don komai ba sai don yadda abin yake iya tsakaninsu
kawai har yanzu.
Lokacin da yana tare da Rukayya, lokacin da ta sami ciki, zai iya cewa shi da Malam sani direba sune na ƙarshe a sani, don yayi tafiya a lokacin har aka kwantar da ita a asibiti ta kwana babu wanda ya kira shi a cikin ƴanuwanta tunda ita
tana bacci a lokacin, sai da safe da Mami zata je asibiti wajenta sannan ta kira shi tana gaya masa, a lokacin suka ji tare da Malam Sanin da zai kaita.
Kuma Allah ya sani a wancan lokacin da zuciyarsa ta riga ta gama sarewa da al'amarin Rukayya, don baya
jin ko sau daya ya ta
ɓ
a nuna damuwa da abinda ke cikin nata, ya san dai ya bata dukkan kulawar da zai iya, bayan haka bai damu ba da dawainiyar cikin ba kamar ita, kamar itama da a lokacin bata
ɗ
auke shi a komai ba.
Sai a ranar da Hamida tazo duniya, ranar
da ya riƙe ta a hannunsa sannan wannan ƙaunar da iyaye ke ji a lokacin da suka kalli gudan jininsu ta mamaye komai, ta rufe wasu abubuwan ta kuma bude tarin wasu a zuciyarsa, tarin wasun da duk karfin da suka yi basu iya saita rayuwarsa daidai a lokacin b
a, don ƙaunar da yake bukata, zuciyar da yake bukata ta fahimce shi tafi tafi karfin ƴar karamar dake bugawa a kirjinta.
Amma wannan karon, haka kawai yake jin kamar komai daban ne, tunda rayuwarsa ta canja, yana cikin nutsuwa da kuma kwanciyar hankalin da
yake ji hannayensa zasu iya bu
ɗ
ewa su riƙe wani abun fiye da wanda yake iya kokarinsa wajen kula dasu a yanzu, shi yasa haka kurum bayan yazo office
ɗ
in ya kira wata likita dake aiki a asibitinsa na can Abuja, ya kira ta yace taje gidan ta sake duba ta tu
nda sunyi magana tace masa tazo Kano ita da Familyn ta hutu.
Saboda haka ya sake gyara zamansa yana zura hannunsa cikin gashin kansa kafin yace.
"BabyDoll kin tabbata babu abinda kike ji?"
Amina ta girgiza kanta a hankali tana neman wajen zama daga bakin g
adonta.
"Ba abinda nake ji da gaske, kawai kamshin wasu abubuwan ne suke damuna ka sani..."
Ya gya
ɗ
a kansa yana kallon Faruk
ɗ
in da a yanzu ya tafi can gaban teburinsa yana karanto wasu lambobi daga cikin wayar tasa zuwa cikin wayar dake kare a kunnensa.
"Kiyi list dinsu gaba
ɗ
aya ko menene we are getting them out of the house da zarar na dawo... Kinji."
Ta cije lebbenta taba murmushi, don list
ɗ
in farko da ta fara hangowa kusan rabi na turarukan da yake amfani dasu ne, sai kawai ta gya
ɗ
a kanta sannan tace.
"Insha Allah Sugar."
Yayi shiru na wani lokaci, itama tayi shiru bata ce komai ba, tana jin muryar Farouk din dake magana daga cikin wayar.
"Kina son wani abu?"
Ya tambaya a hankali yana katse shirun, sai ta girgiza kanta kamar yana kallonta kafin tace.
"A'a."
"Ni ina son wani abu..."
"Wani abu me?" Ta tambaya tana cije lebbenta sanin halinsa, amma sai taji yace.
"Dan Allah ki min tuwo yau..."
Tuwo. Kalmar ta dira akanta duk da yadda ya fade ta a hankali, ba wani jin da
ɗ
in jikinta take ba, kawai daurewa t
ake tana gaya masa babu komai tunda ta san tarin ayyukan dake gabansa da kuma abinda yake fuskanta. Bata tunanin ma zata so kamshin kowacce miya da zai ce yana so.
Amma ya zata yi? Ba kullum ne zata fyskanci abinda take so a cikin auren ba ma ta sani, ta s
ani a cikin kanta cewa wannan matakin da suke ciki mai wucewa ne ma, yau da gobe tafi ƙarfin komai, rayuwar ba tatsuniya ba ce ba, ko a tatsuniyar ma akwai lokacin da abubuwa basa tafiya daidai, tana lissafi da ranar da zata zo Ma'aruf zaiyi mata abinda za
i ƙona ranta, tana lissafi da ranar da zata fara fuskantar irin hakurin da kowacce mace ke yi a gidan aurenta, saboda hakan shine auren shi yake mikewa ya cigaba da haifar da fahimtar juna da kuma shaƙuwa a tsakani, idan har babu hakuri a ginshikin aure, d
a tabbas duk wani nau'i na jin dadin duniya ya ƙare.
Saboda haka sai kawai ta gya
ɗ
a kanta a hankali sannan tace.
"Insha Allah Sugar, kayi aikinka ka dawo, muna nan muna jiranka da tuwonmu a ƙofa..."
Tana jiyo murmushin da yayi mai kama da dariya.
"I love y
ou so much Noor..."
"Love u too."
"Ki saka min wannan rigar kafin in dawo."
"Wacce?"
Ta tambaya girarta biyu na gadewa waje guda alamun bata gane ba.
"Wadda ba sai na sha wuya ba..."
Dariyar da ta kyalkyale da ita ta katse sauran maganganunsa, yayi shiru y
ana juya biron hannunsada nasa guntun murmushin shima.
"Da gaske nake."
Sai ta girgiza kanta sannan tace.
"Kar ka damu, zaka so wadda zan saka fiye da wadda kake tunani ma..."
Ya girgiza kansa a lokaci guda
"The day is rough Babydoll, and you are making me
go crazy..."
(Ranar yau sai a hankali Babydoll, kuma kina kara rikita ni....)
Amina ta cije le
ɓɓ
enta a hankali tana murmushi, kuma sanin halinsa da abinda zai iya fa
ɗ
a a ga
ɓ
a, yasa tayi saurin yi masa sallama, wayar tasu ta ƙare da hakan.
A daidai lokacin
da Ma'aruf ya sauke wayar daga kunnensa daidai lokacin da Faruk ya tsaya a gabansa yana miƙo masa takardar dake hannunsa, kuma murmushin dake kan fuskarsa shine abu na farko da ya fara shaidawa Ma'aruf abinda bai furta ba.
"Mun same shi Ma'aruf, ga addres
s dinsa nan, ka shirya mu tafi... ko waye wannan Awwalun yau dubunsa ta cika!"
***
_Su wa kuke tunanin sun kama Awwalu?_
_A wane lokaci kuke tunanin su Ma'aruf zasu isa gidansa?_
_Tare da mutanen nan?_
_Ko bayan sun tafi da Awwalun?_
_Ina Kilishi?_
_Kuna t
unanin Hajiya Salamatu ta hakura da zancen dan ta?_
_Ta yaya Jawad zai gano mahaifiyarsa?_
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha s
hafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
°°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*18*
~~~~~~
*Assalamu alaikum barkanmu da warhaka, ina mika ta'aziyyata da kuma jaje ga dimbin al'ummar musulmi da ma jama'ar Kano game da tashin hankalin da muka fu
skanta a cikin satin nan na kisan gilar da aka yiwa ƴar ƙaramar yarinyar da bata da laifin komai a duniyar nan, ina rokan Allah ya bawa iyayenta haƙurin rashi, Allah ya ƙara kare mu da iyalanmu, Allah kuma ya kawo mana karshen dukkan tashin hankalin da muk
e ciki lafiya. Ameen.*
***
Motoci guda hu
ɗ
u zaka fara gani a ƙofar gidan kafin idanunka su lura da cewar kofar motar guda
ɗ
aya a bude take hade da mukullinta a jiki.
Don a lokacin da suka tsaya, tunanin Ma'aruf da kuma duk wata nutsuwarsa tayi kaura daga c
ikin kansa, fatansa kawai shine su sami mutumin da suka zo nema a cikin gidan nan, Awwalu!
"Nan ma baya nan...!"
Ƴ
an sanda na ƙarshe da suka dawo daga bayan gidan suka fada suna shivowa cikin falon inda dukkaninsu ke tsaye, sun duba koina a gidan sun duba
koina, kuma hasashen Ma'aruf na cewar babu mutum a cikin gidan tun sanda ya tako ƙafarsa ciki shine ya tabbata.
Babu kowa, babu kowa a cikin gidan banda shatin tayoyin motar da suka tarar a jikin kasar waje ta compound
ɗ
in gidan, shatin da ƴan sandan suka
tabbatar da cewar bai da
ɗ
e ba, babu da
ɗ
ewa da fitar mota a gidan.
Bai san lokacin da yayi baya ya zauna kan wata kujera dake cikin falon ba yayin da hayaniyar ƴan sanda da kuma sauran tanen da suka zo dasu ta tafi kan wata jaka da suka tsinta a cikin falon
, wata jaka da babu komai sai tarin wadu CD's da kuma computer guda daya.
Yana jin abinda suke fada, yana jin suna fadin cewa kayan ba karamar kadara bace da zata iya kaisu ga abinda suka zo nema, amma shi ba wannan ne a ransa ba, ba hakan yake do ba, ba k
uma hakan yayi fata
ba. Burinsa yaga ko waye wannan Awwalun, burinsa yaga fuskarsa yaga WAYE SHI, ya ga waye wanda ya da
ɗ
e yana cutar dasu a duniyar nan ya kuma san dalilinsa.
So yake ya tambaye shi me suka yi masa? Me suka yi masa shi da mahaifinsa da dau
ki aniyar tarwatsa su? Wane irin laifi duka yi ko kuma ta ta yaya suka cutar da rayuwarsa da yake bata lokacinsa yana kuma sadaukar da dukiyarsa da fasaharsa don ganin karshensu? Abinda yake so a wannan lokacin kenan, so yake ya riƙe wuyansa a cikin hannay
ensa ya tambaye shi me suka yi masa... So yake ya dake shi, ya mare shi, ya naushe shi har sai yaga haƙoransa suna biyo jini suna fitowa....
"Kusan duka Cd's
ɗ
in are write-protected, sai mun je office zan iya aiki akansu."
Cewar wani a cikin ƴan sandan nan
yana ƙoƙarin danne-danne a cikin computer dake hannunsa bayan ya gwada CD guda
ɗ
aya a ciki, kuma bayan hakan yana ji mutum biyu da suka bu
ɗ
e computer hannunsu suna fa
ɗ
in itama a ƙulle take da password.
Wayarsa tayi kara a lokacin, hannunsa ya zaro ta a ha
nkali daga aljihunsa, Ishaq ne.
"B kana ina? Tun dazu nake kiran wayarka taƙi shiga, gani har nazo Airpot daukan Abdurrahim, ka manta ko?"
Sai kawai ya cusa hannusa gaba
ɗ
aya cikin gashin kansa.
"Wallahi na manta Ishaq, ina nan ina wajen aikin nan ne, amma
bari mu gani, may be kafin jirgin nasu ya sauka I'll be there."
Ishaq dake zaune a cikin motarsa a harabar filin airpot din ya gyada kansa.
"Kayi kokari Dan Allah Ma'aruf, don kafin in fito Baffa yayi fadan me yasa baka gida bayan ka sani."
Ya sake gyada k
ansa a lokacin da Faruk dake tsaye tare da wani
ɗ
an sanda ya matso daidai inda yake zaune.
"Zan zo yanzu insha Allah, bari mu kammala."
Kuma da haka wayar tasu ta kare, ya sauke ta san da Faruk din ke cewa.
"Kar ka damu Ma'aruf, zamu sami wani abu a cikin
wa
ɗ
annan kayan insha Allah, kuma zasu saka security daga yanzu za'a saka ido akan gidan nan 24/7, we are close to finding them Insha Allah."
Abinda dukkaninsu basu sani ba shine, amsar da suke nema a yanzu tare da mabu
ɗ
in da zai bude komai ya kuma kawo kar
shen komai
ɗ
in yana dab da taka kasar Nigeria!
***
"Naira miliyan tara!"
Muryar mutumin ta furta a hankali yana kallon wanda ke gabansa, a zaune yake akan doguwar kujera da ta cika kusan rabi na dakin, don bayan ta miƙe ta zagayo ta bari
ɗ
aya cikin wani sh
ape mai kama da C,
kalarta milk ce kamar yadda tattausan carpet
ɗ
in da aka baje a
ɗ
akin yake, akwai labulaye da suke kalar brown, kalar da ta dace da fentin
ɗ
akin da kuma sauran kayan furnitures
ɗ
in da kyawunsu ke ƙara haska haduwar
ɗ
akin.
Mutumin na zaune
ne daga shi sai gajeren wando da kuma wata yaloluwar T-Shirt yayin da teburin gabansa ke cike da wasu kwalabe da kuma kule-ƙullen da ba sai an tona ba kowanne mai hankali zai san cewa abubuwa ne da ya kamata a liƙa musu ayar tambaya.
"Naira miliyan tara b
a wasa bane..."
Mutumin ya sake fa
ɗ
a yana
ɗ
ora kafafunsa duka biyu akan teburin dake gaban nasa wanda hakan yasa wasu abubuwa dake kan teburin suka fa
ɗ
i. Awwalu dake zaune daga can ƙarshen