Showing 102001 words to 105000 words out of 144990 words
cinch. Yard by yard. Life is hard._ _—John Updike, Rabbit Redux_
~~~~~~
*Tariyar Baya.( Flashback)*
"Hajiya akwai matsala fa, motocin ƴansanda ne gasu nan zagaye da gidan, na tsaya daga gefe ba zan iya karasawa ba...."
Muryar Sadik
din ta fa
ɗ
i kalaman da a lokaci guda suka dako zuciyar Hajiya Kilishi da wani irin tasirin da tunda take a rayuwarta bata ta
ɓ
a jinsa ba.
Bugun zuciyar tata ya cika kunnuwanta a lokaci guda da sauran bayanin Sadik din ya
ɓ
ace daga cikin kunnuwanta, ba shiri
dukkan jikinta ya shiga rawa yayin da ta nemi gefen gadon nata ta zauna, hannunta daya da baya rike da wayar ya kamo zanin gadon don neman tallafi.
"Kana ina yanzu Sadik, ka bar wajen?"
Ta tambaya da sautin da taji kamar ba nata ba saboda ƙarar buguwar za
ciyar tata da shi ka
ɗ
ai take iya ji har a yanzu. Tun da rana da ta daga labulen dakinta ta kula da gajimaren da ya baibaye sararin sama, ya rufe ta kusan bakidaya saboda haka babu kadawar iska sosai, amma bata tabbatar da hakan ba sai a yanzu da take jin
gumi ko tawanne
ɓ
angare na lullu
ɓ
e ilahirin jikinta.
"Ina daga gefe Hajiya, na leƙa layin ne sai na dawo daga baya nake kiranki."
Wannan karon, muryar Sadik
ɗ
in ta amsa tar a cikin kanta.
Sai ta mayar da wani abu dake shirin tasowa daga makogwaronta kafin
tace.
"Motocin ƴansanda ne ka
ɗ
ai a wajen Sadik?"
Ya girgiza kansa.
"A'a akwai wata karamar mota kirar Accord."
Accord. Accord... Kalmar ta ranga
ɗ
a a cikin kan Kilishi ta sigar tashin hankalin da ba'a saka masa rana ko lokaci. Accord motar Ma'aruf ce! Me ya
ke shirin faruwa? Ta yaya zasu gano Awwalu? Ta ina? Ta ina
tunaninsu zai iya samo Awwalu? Ba shi yaje ya miƙa kansa ba ta tabbata, don idan haka ne a ƙofar dakinta wa
ɗ
annan motocin ƴan sanda ya kamata su tsaya ba'a gidan Awwalu ba.
"Sake komawa Sadik, sake
komawa yanzun nan ka karanto min lambar karamar motar..."
"Hajiya..." Sadik ya furta muryarsa na shaida fargaba.
"Laifi ba'a manne yake a goshi ba Sadik, babu wanda ya sanka kuma babu wanda zai gane ka, ka koma ka karanto min lambar."
Yadda muryarta ta fi
to a kausashe tana shaida tsananin tafasa da kuma rudanin da take ciki yasa Sadik ha
ɗ
iye maganar dake bakinsa sannan yace.
"Shikenan, bani minti biyu..."
"Kar ka kashe wayar..."
Ta katse shi da sauri, don bata sani ba idan har kofofin hancinta zasu iya sha
ƙ
ar iska tsawon lokacin da zata jira shi. Tana jin ƙarar takunsa, zuciyarta na bugawa tare dasu har zuwa lokacin da ya isa wani waje da hayaniyar mutane ta shiga kunnenta a lokaci gyda, taji shi yana ratsawa ta cikin mutanen kafin muryarsa ta fito da haraf
an nambar motar Ma'aruf cikin amon muryarsa da Kilishi ta sani cewa har bayan ranta ba zata ta
ɓ
a mantawa da ita ba. Don a wajenta, a bangarenta wannan lokacin shine mafarin komai, shine mafarin wata rayuwar da a yanzu bata santa ba.
***
*Current Situation.
..* *( Halin da ake ciki.)*
"Ta farka?"
Sune kalamai na farko da suka fara shiga cikin kanta, sune abinda ta fara ji kuma cikin amon da yake mafifici a wajenta, amon muryar da take tunanin ko a bayan kasa take babu ta yadda za'a yi ta kasa tantamce shi. Ma
'aruf. Ma'aruf...
Zuciyarta ta biya sunan sau biyu kafin wata murya a cikin kanta ta ƙwallara kara, Ma'aruf? Me ya kawo Ma'aruf inda take? Me yazo yi a wajenta a wannan lokacin? Tsaya wane lokaci ne ma? Sannan a ina take tukunna? Tayi yunkurin bude idanun
ta amma kai tsaye sai wata zuciyar ta hane ta da hakan kai tsaye don haka ta fasa a daidai lokacin da muryar wata mace ke cewa.
"Gashin idonta yana motsi, da alama yanzu zata farka..."
"Tun
ɗ
azu abinda kike fada kenan, just go and call the Doctor."
Taji Ma
'aruf ya sake fada yanayin muryarsa kamar a hasale.
"Yalla
ɓ
ai na san aikina fa, idan da bukatar kiran likitan ai..."
"Ni zaki gayawa kin san aikin ki? Kin san aikin ki tun 8 kike zirga-zirga anan ta tashi ne?"
"B, Calm down ta san me take yi mana..."
Murya
r Ishaq tayi saurin katse shi.
"Wannan tabe-taben banzan ne ta san abinda take yi Ishaq?"
Ya sake fa
ɗ
a muryarsa na cigaba da
ɗ
agawa cikin fushin dake fitowa karara, kuna matar bata yi shiru ba ta sake cewa.
"Amma dai ka san mu bamu isa mu tashe ta ba idan
har..."
"I don't f*cking care! Idan har me?all I know is mun kawo ta nan ne don ta sami lafiya."
Ƙ
arar sakin wani abu ta cika iskar dakin kafin muryar matar ta sake cewa.
"Then ga ka nan gata ai, sai ka bata lafiyar."
Da haka taji matar ta juya karar takun
ta na yin nisa daga inda Kilishi take a kwance yayin da maganganun su Ishaq
ɗ
in ke ƙara shiga kunnenta, sai dai ba su Hajiya Kilishi ke saurare a wannan lokacin ba, tunaninta yayi baya ne yana tarewa ga abinda ya faru jiya don ta fahimci abinda ke faruwa y
anzu.
Abinda ya faru bayan Sadik ya kira mata lambar motar Ma'aruf a ƙofar gidan Awwalun, cewa tayi ya jira ta a wajen gata nan zuwa. Don a lokaci guda kwakwalarta ta gaya mata cewa tunda har ƴansanda suka zo neman Awwalu basu same shi ba, to tabbas dole n
e ita ta fito su san yadda zasu yi su nemi inda Awwalun yake a wannan daren ita dashi don ta gama da babinsa kafin komai ya ca
ɓ
e mata.
Don haka tayi saurin yin transfer wasu kudade daga bankinta na ajiya zuwa na amfaninta da kowa ya sanshi da ita sannan ta
debi kayan wa
ɗ
annan allurorin ta zuba a leda ta fita, ta fita a lokacin da kusan duk jama'ar gidan ke
ɓ
angaren Hajiya Maimuna na murnar dawowar Abdurrahim, ta fita babu wanda ya ganta don ko Maigadi bata samu a gate ba shima.
Da kafarta ta taka har bakin
titi inda ta samu wani mai keke napep
ɗ
in da ya sauke ta a shagon wani mai POS ta ciro dubu dari biyar daga account din ta zuba su a wannan ledar don ta riga ta gama shirya yin asarar ko nawa ne a jiyan don samun inda Awwalu yake.
Tana iya tuna yadda zuciy
arta ta dinga bugawa a kirjinta a lokacin, tana iya tuna yadda ta kasa zama waje guda cikin keke napep
ɗ
in zuciyarta na cikowa a ƙirjinta,
har ƙoƙarin tsugunnawa tayi ta kuma yi ƙoƙarin tashi tsaye, daga baya ma taga kamar mutumin baya gudu sosai don haka
tace dashi ya tsaya, ta sauka ta bashi kudinsa sannan ta tsaya neman wani, tana tsaye tsabar ru
ɗ
ewa da kuma yadda kanta yake juyawa sai taga kamar daya barin titin an fi samun keke napep
ɗ
in da babu kowa.
Kuma a lokacin ne abin ya faru, a lokacin da tazo t
sallakawar ne motar ta buge ta, taji lokacin da ta tashi sama, numfashinta na biyo ta sannan taji lokacin da ledar hannunta ta su
ɓ
uce, tana gaya mata cewa kuma abu na ƙarshe da zata iya tunawa kafin numfashinta ya yanke shine taji hayaniya da kuma salatin
mutane da yawa a saman kanta.
A yanzu a asibiti take kenan, asibiti ne daga maganganun da taji suna yi a saman kanta.... Salatin da bakinta ba zai iya ba shi zuciyarta ta karanto ta kuma sake karantowa, ina ledar dake hannunta ina kuma wayarta? Me yake sh
irin faruwa ne? Wane irin mummunan mafarki ne wannan? Ta yaya Allah zai jarabce ta da hadarin da har zai kai ga kwanciya a asibiti a wannan halin da take ciki? Ina ledar hannunta ina wayarta? Inalillahi wainna ilaihir raji'un... zuciyarta ta ambata tana sa
kewa, don abu na ƙarshe da zata so yanzu shine ace ledar hannunta dama wayarta tana hannun da bai dace ba, hannun da zsi iya tona asirinta ba tare da wata wahala ba.
Tayi kokarin yin motsi ka
ɗ
an, a lokacin ne taji yadda kanta ke juyawa kotawanne
ɓ
angare, j
ikinta yayi tsami kamar anyi mata duka.
"Har yanzu akwai ƴan sanda a ƙofar?"
Taji muryar Ishaq ya tambaya, tambayar da ta haddasa dokawar ƙirjinta a lokaci guda, bugawar da ta nemi dagargaza zuciyarta, bakinta ya sake karanto kalar wani salatin da bata tab
a sanin ta iya shi ba... Ƴan sanda? A ina?
"Suna nan baza su tafi ba ai, Baffa yace babu yadda baiyi dasu ba, amma har sun tura maganar sama, don haka babu yadda za'ayi a rufe case din tunda shi DPO din da ya kade ta ma yaki saurarar Baffan su sake magan
a."
DPO? DPO'n ƴan sanda ne ya ka
ɗ
e ta? Kuma yaga abinda ke cikin ledar hannunta? Yaushe duniya ta tsuke har haka?
Muryar Ma'aruf ta fito da kaushi, kaushin dake shaida tsananin
ɓ
acin rai mai ha
ɗ
e da tashin hakalin da baya
ɓ
uya. A cikin kanta ta kintaci ce
wa ya girgiza kansa kafin ya cigaba da cewa.
"There must be a mistake dole Ishaq, me Mami zata yi da allurar ƙwaya irin wannan? Sannan har da kudi five hundred thousand a cikin leda? Na yarda framing dinta kawai wasu ke ƙoƙarin yi tunda ko Baffa ma bai san
da fitar ta ba... Kuma ban san me yasa ba amma jikina yana bani cewa wannan al'amarin yana da alaka da case
ɗ
in da muke yi, shi yasa nake so ta farka tayi bayanin komai wa
ɗ
annan ƴan i*kan su bamu waje."
A wannan lokacin ji tayi kamar ta miƙe zaune ta girg
iza kanta, ta gaya musu cewa ba zai yiwu ace komai ya ca
ɓ
e mata a wannan lokacin ba...
Ba zai yiwu ba, tana da sauran lokaci, damarta bata taba karewa ta sani, tsarinta kullum daidai yake tafiya don haka ko a yanzu da take iya jin tsananin damuwa daga mur
yar Ma'aruf ta sani zaren bai ƙare mata ba, tana nan a Mamin da take a idanun kowa abunda ya rage kawai shine ta bude idanunta ta ture wannan ƙalubalen ta cigaba daga inda suka tsaya... Zata san yadda zata yi ta fidda kanta ta sani... Sun ga ledar a hannun
ta amma hakan ba zai basu tabbacin komai ba tunda babu wayarta.
Wayarta, babu wayarta, basu same ta ba, don haka ba shiri ta ha
ɗ
iye wani abu a maƙogwaronta, komai da sauki, komai zai zo da sauki kenan, ba'a kama Sadik ba, tana da sauran fata ta san yadda z
ata yi komai ya tafi daidai, ta sani.... Ita Kilishi ce kuma ko a wani hali tana da mafita...
"Ka cire tunanin wadannan mutanen a ranka B, babu inda zasu je idan har ba umarni aka basu daga can ba."
Ishaq ya fa
ɗ
a daidai lokacin da ya daga wayarsa kuma ba s
ai yayi wani bayani ba daga gaisuwa kawai Kilishi ta fahimci cewa da Hajiya Maimuna yake magani.
"Mami baza su barku ku shigo ba, mu ma da I.D cards
ɗ
inmu muka yi amfani, yanzu ma so muke mu samu ta farka watakila komai zaiyi sauki..."
A lokaci guda hankal
in Kilishi ya dugunzuma ya ƙara tashi, ak'amarin ya kai har a hana nakusantan ta ziyartar ta? innalilahi wa'inna ilaihir raji'un! Ta ina zata fara neman mafita idan har al'amarin ya kai haka? Me zata fara kamawa a yanzu? Ta ina zata fara bayanin inda ta sa
mu allurar da kuma wajen da zata je? Wannan wane irin mummunan tashin hankali ne? Me yasa komai zai
ɓ
are a lokacin da bata shirya ba? Me yasa sai a wannan nisan sannan ƙalubalenta zai zo? Don ta yarda har yanzu wannan ƙalubale ne, babu ta yadda za'ayi ace
wannan shi zai kawo ƙarshen ta, tana da mafita a komai na rayuwarta, tana da ita ta sani! Kawai zata fuskanci wahala ne kafin ta daidaita komai.
"Hajiya ce, wai su Samirah ne har da kuka zasu taho..."
Taji Ishaq ya fa
ɗ
a bayan ya ajiye wayar da yake yi.
"Ba
bu wanda zai zo, su bari mu san me ake ciki ma tukunna, idan sun zo me zasu yi?..."
Cewar Ma'aruf yana jin tasirin abinda ke zuciyarsa na yin yawa, kuma Ishaq din bai ce konai ba, shiru ya ratsa dakin kafin wayarsa tayi kara, kuma yana jin ya dauka ya far
a waya zuwa office
ɗ
insu, sai kawai ya miƙe, ya miƙe tsaye ya nufi kofar
ɗ
akin, kuma bai kira komsi ba ya kama hanya ya fita.
Missed call
ɗ
in Faruk guda biyar ne, duka bai san lokacin da ya kira ba sai kuma na Amina guda biyu.
Amina ya fara kira kafin Faru
k
ɗ
in, kuma sautin muryarta, wannan sassanyar muryar tata, shine abu na farko da ya tuna masa da irin tarin wahala da kuma gajiyar dake jikinsa, wanka kawai yayi a jiya lokacin da Baffa ya kira shi da zance mafi tashin hankalin da hafi ba zagayen halin da
yake ciki, cewar wani dan sanda ya kira shi da cewar ya kade Mami akan titin hanyar gidan Gwamna, sannan sun tsinci wasu miyagun kwayoyi a cikin ledar dake hannunta.
Yana iya tuna magiyar da ta dinga yi masa a lokacin, magiyar cewar ya fada mata abinda ke
faruwa, amma bai iya ba din,rigar da take miko masa a lokacin ya kar
ɓ
a kawai ya zura a jikinsa sannan ba tare da ya damu da taje barbajajjen gashin kansa ba ko kuma ya shafa mai ya dauki mukullin motarsa kawai ya fito, ya fito ya barta ita da Hamidan dake
binsa a baya da nata tambayoyin da kuma kwanukan tuwon nan da yaci burin huce gajiyarsa dashi kamar me...
"Babydoll...."
Muryarsa ta fito a hankali bayan ya shige cikin motarsa. Kuma maimakon ta amsa sai tace.
"Ya jikin nata? Hajiya tace har yanzu bata far
ka ba."
Hannunsa daya ya miƙa cikin barbajajjen gashin kansa sannan ya rufe idanunsa gaba
ɗ
aya yana jingina da kujerar motar.
"Bata farka ba, amma soon insha Allah."
Amina ta gyada kanta, tana zaune ne akan kujerar falon gidan tare da Hamida tmda tayi bacci
akan cinyarta, basu dade sosai da dawowa daga cikin gida ba, don kamar kowa suma kusan a zaune suka kwana ana jimamin abinda ya farun, a yanzu ma ta dawo ne ta yiwa Hamidan wanka ta kuma bata abinci, wanda bayan ta gama ne bacci ya dauke ta.
"Kana tare da
ita ne?
Ta sake tambaya a hankali. Ya girgiza kansa a hankalin shima.
"Na fito,ina mota yanzu."
"Dan Allah ka dawo gida kafin ka tafi wani waje... Baka ci komai ba fa.." ta fada ksmar zata yi kuka.
Yayi shiru ka
ɗ
an kafin yace.
"Kina ganin zan iya cin wani
abu yanzu?"
Ta gya
ɗ
a kanta a hankali.
"Zaka iya Sugar, saboda babu abinda zai faru insha Allah, komai zai tafi daidai kawai jiran sakamakon ne mai wuya..."
Ya gya
ɗ
a kansa a hankali.
"Na sani Noor, da wuya sosai... Mami kamar mahaifiyata ce, ina jin ta har
cikin raina wallahi hankalina ba zai ta
ɓ
a kwanciya ba ace wasu sun saka ta a cikin wannan halin, babu abinda ya same ta amma har yanzu bata farka ba Amina, bamu san meye matsalar ba har yanzu, amma kuma duk da haka ace gaan saka ƴan sanda suna gadinta sun
hana kowa shiga..."
Ƙ
wallar da ta cika idanun Amina ta gangaro zuwa kumatun ta, Allah ya sani tsoro take ji, tsoro take ji sosai na ranar da Ma'aruf zai san wacece Kilishi, don bata san yadda za'ayi zuciyarsa ta iya daukar masa hakan ba, bata sani ba ma i
dan har zai iya daukan...
Sai ta share su da bayan hannunta
ɗ
aya sannan tace.
"Babu abinda zai faru Insha Allah Sugar, alkhairi ka
ɗ
ai Allah zai azurta rayuwarmu dashi insha Allah."
"Insha Allah." Ya fa
ɗ
a a hankali yana bu
ɗ
e idanunsa sannan yace.
"Zan aiko
direba ya kar
ɓ
a min abincin, ba zan iya dawowa gida yanzu ba Babydoll, ayyukan dake jira na a office suna da yawa, yanzu ma na ga missed call din Faruk kusan biyar ban dauka ba."
Ta cije lebbenta ka
ɗ
an na ba hakan ta so ba, amma tasirin uzirin da ta san do
le ne tayi masa ya danne son ran nata don haka tace.
"Shikenan Allah ya kaimu yazo
ɗ
in..."
"Kar ki sake yin komai, ki bar min
ɗ
umamen tuwon nan kawai."
Tayi murmushi jin da
ɗ
in cewa har yanzu bai manta da tuwon ba sannan ta gyada kanta a hankali.
"Insha All
ah Habibi albi."
Ma'aruf ya sake lumshe idanunwansa yana jin tasirin muryarta da kuma sabon sunan a jikinsa. Yayi shiru kawai ba tare da yace komai ba, itama tayi shiru bata sake cewa komai din ba, kuma a cikin shirun yake yake jin kamar dukkan gajiya da k
uma damuwarsa suna bin iska ne, sai dai hakan baiyi nisa ba sakamakon shigowar kiran Faruq da ya sake shigowa, ya
ɗ
ago da wayar ya kalla kafin ya sake maida ita kunnen nasa.
"Babydoll ki min hakuri please, zan
ɗ
auki kiran Faruq."
"Ba komai, kaje kayi aikin
ka kawai, amma dan Allah ka turo direban da wuri."
"Insha Allah thank you so much for ur care." ( Nagode sosai da kulawarki.)
"Aiki na ne Sugar."
Ta fa
ɗ
i abinda ya saka