Showing 48001 words to 51000 words out of 144990 words
baya gani idan har ya dora ransa akan wani abu, ta san wannan ba tun akanta ba, tun akan aik
insa don hakan shine babban abun da yasa cikin ƴan shekaru kadan matsayinsa ya kere kowa a wajen, to ta yaya don kawai tayi masa wannan bayanin zai haƙura komai ya cigaba da tafiya daidai?
Wayarta tayi kara tun kafin tunaninta ya kai karshe, Mahaifiyarta
ce Hajiya Nafisa, ta
ɗ
auka daga haka tasa a speaker.
"Ki sauko kasa, muna magana ne akan wadda zata je gidan."
Wadda zata je gidan, ba sai Maamahn ta fasa ba, wadda zata je gidan tana nufin gidan Ma'aruf, yarinyar da zata je ta kwance asirin nan, asirin da
kamar yadda suka tsara komai a yau ba sai gobe ba aikinsa zai fara, Ma'aruf zai tsani koma wacece yarinyar dake cikin gidan nan a matsayin matarsa, tsanar da a cikin kankanin lokaci zai rabu da ita, don ta riga ta san ko waye Ma'aruf, idan baya son abu ba
ya son sa har cikin ransa kuma babu wanda ya isa a duniyar nan ya canja ra'ayinsa game da hakan hatta Baffa kuwa, shi yasa shi kansa Baffan baya saka baki akan al'amarin wani hukunci da ya yanke.
Sai kawai tayi wani murmushi mai fadi tana hango yadda rayuw
a zata maida ita bigiren da ta yarda babu kamarsa duk duniyarta.
Ta yi mu'amala da maza da yawa tun kafin aurenta, amma babu wanda ya kamo kafar Ma'aruf a cikinsu shi yasa ta dage har ta aure shi a sannan, kuma bayan zuciya ta ru
ɗ
e ta ta fito, har yanzu ba
ta ga wanda ya kama kafarsa a komai ba... Jawad yana ji da kansa wajen iya kulawa da kuna tarairayar mace, amma ta tabbata zai zubar da dukkan makamansa idan da zata hasko masa kwana
ɗ
aya kawai a rayuwar aurenta da Ma'aruf kafin abubuwa su canja a tsakanin
su.
Wayarta ta sake ƙara, Maamah ce, sai kawai ta sake wani murmushi mai fadi tasa hannunta duka biyu tana gyara dogon gashinta zuwa baya.
Bata san wane irin zama Ma'aruf ke yi da sabuwar matarsa ba, amma koma wane iri ne, yau zata zama rana ta ƙarshe da h
akan zai zo ƙarshe.
***
"Meye wannan?"
Ma'aruf ya fa
ɗ
a a hankali yana laluben gefen fuskar Amina dake tsaye a gabansa, a jikin wardrobe
ɗ
in dakinta ya same ta, tana kokarin samowa Hamida kayan da zata saka sakamakon bata nan jikinta da tayi da hodar ta fa
sa gabadaya kuma ta zube a jikinta, duk yadda ta kai ga kwashe kayan kwalliyar nan bai hana
ɓ
ata kayan nata da take gudu ba.
Dawowarsa kensn daga cikin gida, don can ya fara shiga baysn ya dawo, bata ssn wajen wa yaje ba amma tana tunanin wajen Baffa ne do
n yau ma yans gida. Ɗazu bayan gama wayarta da Amma, Ssmirah tazo sun shiga sun gaishe shi, har da Hamida da taki zuwa wajensa ta makale a hannunta, wani sbu da ya taba zuciyarta a lokscin yayi mata dadin da kuma yabawa kanta na cewar yarinyar ta fara saba
wa da ita.
Kuma sai da numfashinta ya katse a yanzu daya zura hannun nasa gefen fuskarta, tana jin yadda yatsun nasa suka ratsa kunnenta, sanyin jikinsu na bi ta kan fatar ta.
"Ɗan kunne ne, baka sanshi ba?"
Ta fada tana kallon cikin idanunsa hannunta rike
da kayan da ta dauko, ya gyada kansa a hankali yana cije lebbensa kafin yace.
"Na sanshi, kawai bana son shi ne."
"Saboda me?"
"Saboda damuna zai dinga yi."
Sai da ta dan tsaya tana kallonsa kafin tace.
"Ta yaya zai dame ka?"
Bai ce komai ba ya fara kokri
n zare shi a hankali, ya karkato da fuskarsa dab da tata yana kallon ta yadda zai cire kuma bata ce komai ba ta tsaya kawai jiran taga abinda zai yi, ya cire na bangaren dama, sannan ya karkato da kansa daya gefen ya cire na hagun shima, ya hada su a hannu
nsa sannan ya kamo nata daya a hankali, na hagun da bata rike kayan dasu ba, ya bude tafin hannun ya dora mata su a ciki.
"Please in dai saboda ni kike sawa ki daina, bana son su, takura min zasu yi 'Cox bayan kafafunki, I like this curve of your body best
."
Numfashinta ya tsaya cak a ƙirjinta yaki fita yaki shigactsawon wasu daƙiƙai, dama kafafunta burge shi suke? Inalillahi! Ai bata taba tunani ba, ko lokacin da ta saka wannan yaluwar rigar sai da tayi ta ayyana yadda yake kallonsu a ranta amma bai ce kom
ai ba, sai yau Allah ya budi bakinsa ya fada kenan.
Sai kawai ta rufe idanunta ta bude sannan tace.
"Insha Allah."
"Insha Allah me? Baki karasa ba..."
A hankali tana kallonsa tace.
"Me zan karasa?"
"Sunana..."
"Ma'aruf?"
Ya girgiza kansa.
"Wannan na kowa n
e, though I like the way kike fadan 'R' din sunan, amma na fi so ki samo min wani daban, da ke kadai zaki dinga fada."
Ta danyi shiru tana cigaba da kallonsa, kwakwalarta na gaya mata cewa sun bar Hamida a can falo amma wani gefen na gaya mata cewa tunda k
allo take yi vabu komai.
"Kamar me toh?"
Innocence din cikin muryarta ya fito tar, yayin da idanunta ke cigaba da kallon sa. Sai kawai yayi dariya yana zura hannunsa cikin gashinsa sannan ya girgiza kansa, kuma maimakon ya bata amsa sai kawai ya juyo da it
a, tana fuskantar
ɗ
akin, ya tsaya daga bayanta sannan ya sunkuyo da fuskarsa cikin wuyanta, bakinsa daidai kunnenta ya rada a hankali yace.
"Call me the first thing you see..."
(Ki kira ni abu na farko da kika gani.)
Ta cije lebbenta tana murmushi, kuma a
hankali idonta ya sauka akan robar sukarin da ta
ɗ
auko
ɗ
azu tayi amfani dashi a wani kayan gyaran fuska da akace mata sai an hada da sukarin.
"Sugar..."
Muryarta ta fito a hankali, sai yayi wani irin murmushi mai sauti a cikin wuyan nata yace.
"Yes! I know
I'm that sweet Sunshine."
Sai kawai ta juya tana nata murmushin itama ta kalle shi, kuma a wannan lokacin ne kwakwalarta ta gaya mata cewa shine damarta na gaya masa sakon da take jin nauyinsa a cikin ƙirjinta.
"Ina so ne in gaya maka wani abu."
Bakinta y
a yanke shawarar fadar abinda ke zuciyarta kai tsaye tun kafin kwakwalarta ta canja tunani.
Sai ya gyada kansa yana kokarin rike ta a cikin hannunsa alamun yana saurarenta, ta ha
ɗ
iye wani abu a maƙogwaronta a hankali tunaninta na ƙara gaya mata muhimmancin
abinda zata fada.
"Ka yarda dani?"
A lokaci guda taga yanayin fuskar sa ya canja, ragowar murmushin na barin kan fuskar tasa, ya zama so serious
ɗ
in da taji zata iya zagin kanta inda har da ba abu mai muhimmanci zata fa
ɗ
a ba. Ya ƙara gyada kansa sau daya
yana kallonta kafin yace.
"With every cell of my body Doll, na yarda dake."
(Da kowanne kowanne abu dake jikina Doll, na yarda dake.)
Kalaman suka bata jwsrin gwiwar da a lokaci guda ta fara magana.
"Dazu da ka fita ina ta tunanin akan maganar da ka fada m
in, akan maganar wannan mutumin da kuke nema, nace me yasa baza ku duba har wajajen da ba'a tunani ba kamar irin su Prison, saboda wani lokacin mutane suna wasa da hankali ne kawai su yi abinda suka san ba za'a taba zato ba..."
Ta yi shiru, kamar ta kai ƙa
rshe kamar kuma akwai sauran abinda zata fada. Shima yayi shiru bai ce komai ba, tsawon wucewar wani lokaci yana kallonta kafin muryarsa ta fito.
"All this while ina ta underestimating dinki ne ashe Doll, naga alama abubuwan da kika sani sunfi karfin tunan
i na, amma insha Allahu lokaci zai bude min su daya bayan daya.
Abinda kika fada yanzu was amazing, kinyi tunanin da ba ni va har su Faruk wani a cikinmu bai taba yi ba. Tabbas ana amfani da prisoners a irin wannan harkar sosai,mun sani amma Allah bai taba
sawa munyi tunanin hakan ba, thank you so much da kika tuna min, Allah ya saka miki da alkhairi Amina kuma Insha Allah a yau zan kira Faruk, kuma daga gobe zamu fara binciken nan, muna da details din yadda siffar mutumin take da komai, so in har a gidan y
arin yake, ba zai yi mana wahalar kamawa ba insha Allah."
Ta gyada kanta tana jin kamar wani abu zai fashe ne a cikin zuciyarta saboda jin dadin yadda ya fahimce ta a cikin kankanin lokaci yayin da shi kuma ya cigaba da kallonta, kuma kafin tayi wani tunan
i taji ya sunkuyo da fuskarsa dab da tata sannan a hankali yace.
"I want to borrow a kiss right now Doll, don in nuna miki godiyata, amma nayi alƙawarin zan dawo miki dashi Allah."
Bata san lokacin da ta kyalkyale da dariya ba tana kokarin ture shi, amma s
ai ya kara rike ta yana fadin.
"Da gaske nake Allah, yanzun nan zan dawo miki dashi, kawai ki ara min."
Da ƙyar ta samu ta fita daga hannunsa, ta koma falon ta barshi anan yana amsa wayar Ishaq, zuciyarta cike fal da da
ɗ
in yadda ta isar da saƙon Amma cikin
ƙanƙanin lokaci kuma ta samu fahimtarsa, ta gama da wannan babin insha Allah.
Kilishi ta jirayi abinda zai biyo baya, zata sha mamakin yadda asirinta zai tonu alhali ta san bata budewa kowa sirrinta ba, tunda ko ita ta san bata gaya mata ba, kawai sunyi a
mfani da kalamanta ne akanta. A yanzu saura abu na gaba da take da yakinin zai fi wannan... Abinda Amma tace ce.
_'...babu abinda zai faru, babu abinda zai sami yarinyar nan, amma kuma a idanun Kilishi komai zai faru, zaki cika mata wannan aikin nata sanna
n kuma zata kaimu Makkan har da wannan canjin na gida ma!_
Allah ya sani zuciyarta a tsaye take wajen jiran faruwar hakan.
"Zoben Sofia za'a fauko a cikin wannan ramin."
Hamida ta fa
ɗ
a tana nuna mata cartoon din da take kallo a cikin Tvn, ta juya ta kalli
ramin da take fa
ɗ
a kafin tayi dariya tana gaya mata cewa rijiya ce ba rami ba.
A daidai wannan lokacin ne kuma taji karar bu
ɗ
ewar Gate alamun sunyi baƙi don ta san da daga cikin gida ne ta baya za'a shigo.
Ta gama canjawa Hamida rigar sanda aka kwankwasa
kofar
ɗ
akin alamun koma waye ya karaso.
Don haka tayi saurin ajiye rigar a saman kujera sannan ta nufi wajen ƙofar, hannunta ya bu
ɗ
e a hankali daidai lokacin da fuskar matar ta shiga idanunta, tana tsaye da dogon hijabi tayin da fuskarta ke dauke da wani f
affadan murmushi, kuma kafin kwakwalarta ta fara tunanin inda ta santa, taji muryar Hamida daga bayanta tace.
"Mariya???"
***
"Mun yi magana da mutanen, sunce hodar zata samu zuwa jibi, mutumin da zai kawo jirgi zai biyo don haka ka shirya gobe zaka tafi l
agos, don bana son ta ko kwana a hannunsu, kudin dana kashe akanta da yawa, ba zamu yi sske na dage ba."
Hajiya Kilishi ta fa
ɗ
a a cikin wayar da take yi. Awwalu ya nisa alamun a kwance yake kafin muryarsa ta fito.
"Daga wace ƙasa ma kika ce za'a kawo?"
"Me
xico." Ta bashi amsa kai tsaye.
"To wai ta yaya ma za'ayi amfani da ita ne.?"
"Ba kai zaka yi ba, me yasa kake tambaya ta?"
"Saboda na lura tunda kika shigo da yarinyar nan cikin al'amarin nan na fara rage sanin wasu abubuwan. Kuma kina ganin kamar ban can
canci hakan ba."
Sautin muryar tasa ya fito ne da wani irin kauri alamun akwai layin harzuka a ciki. Sai kawai tayi murmushi sannan tace.
"Kar mu fara wannan Awwalu. Ka soke wannan tunanin a cikin ranka, ka kori shaidan daga gefenka. In dai akan wannan hod
ar ne ka bude kunnenka ka ji.
A cikin kwallin yarinyar za'a saka, a hankali take aiki, ana saka mata yau da gobe zata fara da ciwon ido, ciwon idon ne zai ta ƙaruwa ana kuma cigaba da saka mata a haka har idon ya rufe gaba
ɗ
aya ba tare da ko likitoci sun ga
no dalilin hakan ba."
Ta kai ƙarshe ba tare da yace komai ba, kuma jin shirun nasa yasa ta ƙara da cewar.
"Idan mun gama da wannan sai kuma mu koma kan ƙafarta, na tabbata lokaci zaiyi mana daidai da sanda zan gama da abinda ke gabana, kaga kenan zan tafi
ba tare da na bar kowanne dutse a kife ba."
"Haka ne, Allah ya bamu sa'a, zan siya ticket
ɗ
in jirgi anjima insha Allah."
Yadda ya fadi hakan a lokaci guda, kai tsaye, kuma yadda kalmar Allah har sau biyu ta fito a bakin Awwalun yasa ta tsayawa da nata shir
un kafin a hankali a furta kalmar 'Ameen.' din da bata jin ta kai ƙarshe sanda ya katse wayar.
Wayar ta katse tare da katsewar numfashinta da kuma tsayawar idanunta akan mudubin da taje kallo a gaban ta.
Me Awwalu yake nufi?
Me ke shirin faruwa ne?
Wake sh
irin girgiza mata tebur ne?
***
_Kun yarda da tunanin Amma? Kun gamsu da yadda ake amfani da zurfin tunani wajen samun mafita?_
_Ina so in dan haska muku wani abu anan, abubuwa da yawa na faruwa a cikin rayuwarmu da zasu wuce ba tare da mun basu wani muhim
manci ba, wani hira ce wani kuma actions ne._
_Amma kuma a cikin abubuwan nan akan samu abubuwan dake
ɓ
ullewa zuwa abinda zai zame mana mafita a wasu matsalolin namu na rayuwa. Ba komai zamu dinga mantawa ba, ba komai zamu dinga shashantarwa ba... Komai ka
nkantar abu zai iya zame mana mafita a wani babban al'amarin na rayuwarmu._
_An halicci ƙwaƙwalwa da fadi, don haka bude ta ki zuba tarin abubuwan da baki san lokacin da zasu amfane ki ba._
_And kuna tunanin Amina ta gane wacece Mariya kuma daga ina take?_
_Ku taya ni gayawa Ma'aruf cewa
ɗ
an kunne yana da amfani a adon mace...
😅
_
_Sannan team Kilishi, me Awwalu yake shirin jawo muku ne?_
😅
Littafin nan na siyarwa ne akan naira #300
Account Details
0251365383
Wema bank.
Aisha Mahmoud Shafii.
Whatapp number 0
8067794315 ( Domin tura shaidar biya)
#Aysha shafi'ee.
#fikrawriters
#FararWuta.
°°°°°°°°°
*FARAR WUTA 2.*
*©AYSHA SHAFI'EE*
*PAID BOOK*
*10*
~~~~~~~
_A love so wasted._ _- Unknown_
**
"What?"
Ma'aruf ya fa
ɗ
a da tsananin mamaki yana kallon fuskarsa a cikin
mudubin
ɗ
akin dake fuskantarsa.
"Baka ji ni bane ba? Nace maka auren Munaya nazo nema."
Mamaki ya nuna tar akan fuskar sa yana shafa gashinsa ta baya.
"Wallahi da na iya zagi zan
ɗ
ura maka wanda zaka kwana kana juyi Ishaq."
Daga cikin wayar Ishaq yaja tsa
ki sannan yace.
"Ai na gaya mata raini zata jawo min, amma tace in fara tambayarka tukunna, da wallahi sai dai kaji zancen."
Ma'aruf ya girgiza kansa.
"Let's talk serious, me kake nufi wai?"
"Da gaske nake B, ina son kanwarka, zan aure ta, kuma na gaya mat
a itama ta yarda, da Baba Usman zan gayawa amma wai sai tace in fara gaya maka tukunna, ban san me yasa yaran nan suke girmama ka har haka ba."
Tsabar mamaki bakinsa ya kasa rufuwa, sai kawai ta sake girgiza kansa sannan yace.
"Wallahi ban san baka da kuny
a ba sai yanzu Ishaq, ni kake tambaya wai kazo neman auren Munaya Ishaq?"
"Allah ya tsinewa kunya in dai taka zanji Ma'aruf, kai kanka ina ka ganta da za'aji maka? Maimakon ka fara godewa Allah ma kun samu mutumin kirki kama ta sai ka fara aibata ni? Ni da
ma na san wallahi raini Peaches zata jawo min kawai don tayi insisting ne."
Ma'aruf ya gya
ɗ
a kansa.
"Wato Peaches Ishaq, Munayan ce Peaches? Ƴar mutane ce fa..."
Dariyar da Ishaq yayi a cikin wayar, dariya ce da ya dade baiji yayi irinta ba kafin yace.
"Ka
i ta gidanka ba ƴar mutanen bace ba? Malam in zaka shige min gaba muje wajen su Baffa kayi magana."
"Ba zanje ba, baza'a baka ba."
"Nagode Babban Yaya, Allah ya ƙara girma."
Da haka ya kashe wayar, Ma'aruf ya cije lebbensa yana jinjina al'amarin a cikin ka
nsa, yana jin kamar ba gaske ba, wani iri, kamar a labari cewa wai Ishaq ne ke son Munaya, yarinyar gabadaya shekararta nawa? Shekara ta biyu take fa a Jami'a, kuma a
ɓ
angaren karatun da take yi na densistry bai ta
ɓ
a zaton cewa zaiji wannan al'amarin a kus
a ba, Allah ka
ɗ
ai ya san yadda akayi Ishaq ya hure mata kunne.
Sai kawai ya zura wayarsa a aljihu sannan ya fita daga dakin da niyyar zuwa gobe yaje ya same shi suyi maganar hankali.
Tun daga korido yake jin maganganu alamun ƙaruwar wani a gidan, don haka
ya karasa a hankali tafin kafarsa na taka tiles
ɗ
in wajen, ya ƙarasa daidai lokacin da Amina ke kokarin ajiye tiren ruwa da lemo a gaban wata mata yayin da matar ke kallon Hamida tana fa
ɗ
in ta taho wajenta, ya tsaya daidai inda su baza su ganshi ba amma sh
i yana gano su.
"Au ba zaki zo ba sauraniyar Mama? Ba tafiya zanyi dake ba, kinga kaya ne nan ma Mammy tace in kawo miki."
Hamida ta matse kafadarta daya tana cigaba da kallonta ba tare da tace komai ba.
"Haba Princess din Daddy, Mama Mariya ce fa... Har l
abarinta fa kika bani."
Cewar Amina da murmurshi a fuskarta, amma duk da hakan Hamidan ta matse kafadarta.
"Ai shikenan kyale ta, da kanta zata zo,ni kujera ce ai."
Dukkaninsu suka yi