Showing 30001 words to 33000 words out of 144990 words

Chapter 11 - FARAR WUTA COMPLETE

na gaya miki cewa ita kanta yarinyar na shirya mata, kuma gashi tun amba'aje koina bakan ta tabbata r miki da abinda na fada cewar babu wata mace da ta isa tayi tasiri a zuciyar Ma'aruf sama dani, a yanzu na gama yi mata shirin

da ba zata ta

ɓ

a iya bari Ma'aruf din yayi tasiri a zuciyarta ba balle har ta iya tsallake umarni na.

Na tsorata ta, kuma ta gama tsoratar akan al'amarinsa, zata ganshi ne kamar yadda na haska mata shi, zata ganshi a matsayin wani abu daban ba mijin aure b

a, don ko ciki bata isa

ɗ

auka ba."

Salamatu tayi dariya.

"Na san zaki aika ai Kilishi, kawai dai a farko ne nayi tunanin ke kanki baki gana sanin halin yarinyar ba na jiye miki wannan tsoron, amma tunda har kin taka matakin nasara akanta tun ba'a je koina

ba, mu cigaba a inda muka tsaya, ki gaya min ta yadda kika sami kudaden nan."

Kilishi ta daga kanta sau daya sannan ta cigaba da magana.

"Kwantar dashi nayi kamar yadda na gaya miki sannan Awwalu ya sanya min yaran sa suka fara binsa tun daga lokacin da ya

bar gida, muka sa wani yaje ya daki motarsa sannan kuma ya zage shi don in tabbatar idan har yarinyar nan ta bashi maganin, ilai kuwa nan da nan mood dinsa ya rikice ya kama dukan mutumin, a wannan hayaniyar wasu da muka saka suka samo min wallet dinsa ha

r dama wayoyinsa wanda muka yi amfani dasu."

Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.

"Ban gane ba, kuka yi amfani dasu ta yaya?"

Kilishi ta ajiye cake din da har a lokacin bata kaishi baki ba, ta gyara zamanta sosai tana kallonta sannan tace.

"Ma'aruf yana da wa

yo da dabara sosai Salamatu, na sha gaya miki tun bai kai haka ba. Don haka bayan sun gama wannan bincijen shi da wannan abokin aikin nasa, sun gano cewar tabbas alert din da suka samu na bogi ne, sai ya canja shawara, yace wannan karon cash zai karbi ku

ɗ

i

ta hannun mutanen da suka yiwa aiki ba ta account ba kuma da kansa yadda zai je ya saka a banki don kar a sami ma wata matsala ba.

Abinda bai sani ba shine, tunanin Kilishi da nasa ba daya bane, a cikin maganganunsa kawai na gane abinda yake shirin aikawm

tawa tun kagin ma su gama aikin a saka ranar karbar kudin, shi yasa na tsara komai, na tsara iya kwanakin da zasu ishe ni har in tunkari Amina ta gama shawararta tazo ta amince dani da kuma iya kwanakin da zata sanya masa gubar har ya kwanta kafin ranar.

K

uma na sami komai Salamatu, I.D cards da kuma wayar Ma'aruf

ɗ

in ka

ɗ

ai muka nunawa mutanen nan da kuma wani dan bayani ka

ɗ

an suka yarda suka bamu kudin a madadinsa, kuma mun karbo ba tare da wata matsala ba Salamatu, Ma'aruf kuma yana nan a kwance duk da an

ce min ya fara samun sauki amma wannan ba damuwata bace, ko yanzu idan ina son ya kara komawa, umarni kawai zan bata, muna zaune anan zaki ji komai ya kara rikicewa."

Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.

"Ba kya tunanin idan ya tashi ya tuntubi mutanen zasu i

ya shaida masa abinda ya faru da kuma yanayinku? A tunanina ba kya

ɗ

anyen aiki Kilishi."

Itama ta girgiza kanta.

Ba tunanin kike ba Salamatu, tabbas bana danyen aiki, don wannan

ɗ

in ma gasashshe ne. Wani saurayi muka samo daga Prison, wata na biyu Salamatu

ina barar da kudi a prison din nan ina neman kafa, don kawai a ara min shi na rana guda yayi wannan aikin kuma da kyar muka samu.

Awwalu ne yayi masa I.D card din kamfanin sak a matsayin babban ma'aikaci, don haka muka tura shi a matsayin hakan ya karbo m

ana kudin da bayanin cewa shi maaikacin wajen an aiko shi ya kar

ɓ

i sakon ne bayan ya nuna musu kayan Ma'aruf harma da wayarsa don haka nan da nan suka yarda.

Suka bashi dukkan kudin mu kuma muka bashi rabonsa tare da na iyayen gidansa muka maida shi inda m

uka dauko shi. Shi yasa nace miki aikin gasashshe ne Salamatu tunda kin san duk naci da binciken Ma'aruf babu ta yadda zai kamo mutumin dake cikin Prison duk kuwa iya bincikensa."

Hajiya Salamatu ta kyalkyale da wata irin dariyar da bata shirya mata ba tan

a girgiza kai.

"Zama dake alheri ne Kilishi, na sha gaya miki yadda kike bude nin kwakwalwata akan abubuwa, yana bani saukin warware nawa matsalolin gabana na nima."

Kilishi ta gyada kanta.

"Abinda na gayawa Saratu kenan ai, kowacce mace tana da irin tata

dabara da kuma mafitar matsalarta a cikin kanta, yanzu da ta saurare ni ba gashi nan daga ita har ƴaƴan ta mijin ya tafi dasu Egypt din ba, amaryar da ake takama da ita da farko wata daya tayi ya dawo da ita.

Kawai jahilci ne yasa mutanen farko ke bin wasu

bokaye da suke maza ma don samun biyan bukatar fa bata dorewa. Kowa ta sani cewa tunda aka halicci duniyar nan har kawo yau, ƙarya ne a samu aikin wani bokan da ya zama mai dorewa har abada.

Amma idan mace tayi amfani da dabara da kuma tunaninta wajen kwa

tarwa kanta ƴanci ko a wajen waye, ina tabbatar miki wannan abin ba mai gogewa bane balle har ya lalace, akwai abubuwa da yawa da suke

ɗ

amfare da tare da halittar mu, kawai bama barin kanmu mu gansu ne.

Kwakwalwar mace kamar littafi take, dauke da tarin ab

ubuwan da tana bude shafukan gaba tana kara fahimta, wadda bata bude ba kuma zata yi ta jallon bangon ne kawai ba tare da ta taba sanin meye a ciki ba.

Salamtu ta kara gyada kanta tana yarda da dukkan maganganun kamar yadda Kilishin ta dade tana ambata mat

a.

"Na taya ki murna kwarai na samun wannan burin da kika da

ɗ

e kina lissafinsa a

ɗ

an kankanin lokaci Kilishi, kin tafi zuwa gaba kuma saura kiris ki kai ga cimma msnufarki gabadaya. Sai dai yanzu na san baza'a sake samun irin wannan aikin a kusa ba, za'a d

auki tazara koda baza'ayi dadeear da nake tunanin ba. Don haka meye a gabanki yanzu?"

Tambayar ta yiwa Hajiya Kilishi dadi, me yasa ne take bu

ɗ

ewa Salamatu cikinta dama? Me yasa take gaya mata dukkan tsarinta duk sanda ta tambaya? Ba saboda tana gaya mata

da

ɗ

a

ɗ

an maganganunn dake wanke zuciyarta suna bata kwarin gwiwa a kodayaushe bane?

"Hamida ce target dina na gaba Salamatu.."

Ta fa

ɗ

a kai tsaye tana kallonta.

"... wannan yarinyar, wannan ƴar ta mai gaskiya, ina son Ma'aruf amma bana son duk wani abu da za

i zana nasa, don hakan ba karamin naƙasu zai jawo min a zuciyarsa ba.

Rukayya bata taba damunsa ba shi yasa nima bata ta

ɓ

a damuna ba har tayi yayinta ta tafi, amma wanna ƴar tata Salamatu, naga wani abu a cikin idanun Ma'aruf a ranar da yake riƙe da ita a

asibiti, na ga wani abu da ban taba ganin irinsa tare da kowa idan ba ni ba Salamatu. Shi yasa tun awanvan ranan na rufe idanuna naso kawo karshenta, amma Allah yayi da sauran ruwanta a gaba shi yasa ban samu nasara ba, amma a yanzu ina jin cewa ko ta hali

n

ƙ

aƙa zan iya canja kaddarar yarinyar nan  Salamatu. (Waiyazubillahi!)

Ta rufe bakinta daidai lokacin da kofar dakin ta bude, Samirah ce ta shigo jai tsaye hannunta rike da wata ƙatuwar jaka kalar Pink mai kyau, dukkaninsu suka bita da kallon yayin da kaf

in Hajiya Kilishin tayi magana Surayya kuma ta biyo bayanta, hannunta dauke da ƴar yarinyar da a lokaci guda kamanninta suka doka wata irin fargaba zuciyar Hajiya Kilishi.

Hamida ce, riƙe a hannun Surayyan ta makalkale ta yayin da take zare manyan idanunta

irin na maifinta sak! akan kowannensu.

"Mami yanzun nan direban gidansu ya kawo ta, wai cewa akayi akai ta wajen Ya Ma'aruf."

Murmushin da ya sabuce a bakin Hajiya Kilishi wani murmushi ne da ya ta

ɓ

o har acikin zuciyarta... Tana son mutane masu saukaka ma

ta ayyuka, a rayuwa, Allah ma ya sani.

****

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un..."

Sune kalaman da suka fito daga bakin Ma'aruf a lokacin da yake zaune kan kujerar falon yana sauraran bayanin da Faruk ke masa a cikin wayar, kayan jikinsa dogon wando ne baƙ

i da kuma wata riga kslar ruwan toka mai haske.

"Wallahi sun nuna min evidence da komai cewa kai ka turo mutumin da ya karbi kudin, don har I.D Card dinka da sauran credit cards dinka ya nuna musu a matsayin shaida."

Ma'aruf ya cije lebbensa.

"Na kasa gane

wa Faruk, na kasa gane wanda zai sace kayana a wannan lokacin kuma har ya san ina da appointment da mutanen a wannan wajen kuma a wannan time din."

"Saboda already sun san hakan ne, sun san kana da wannan appointment din shi yasa suka tare ka a wannan waje

n kuma suka kwashe dukkan wayoyi da wallet dinka."

"Are you thinking this is all planned?" (Kana tunanin duk wannan abin ha

ɗ

awa akayi?)

"Ba tunani nake ba, ina ƙoƙarin tabbatarwa ne, don tun safe muke waya da Ishaq, ya gaya min mutumin da rigimar ta hada k

u har yanzu baiyi filing case

ɗ

in ba, tunda ka san da sun yi dole za'a neme shi, ka duba al'amarin nan ka gani hankali ba zai dauka ba Ma'aruf ace kayi masa wannan abin amma ko shi ko ƴanuwansa basu dauki wani mataki ba."

Yayi shiru kafin yace.

"Amma har d

a nawa contribution

ɗ

in Faruq, ta yaya kake tunanin zasu iya saka ni nayi abinda ban yi niyya ba, ina shan magani na cikin ƙa'ida sannan ina kiyaye dukkan ƙa'idojin da aka rubuta a wannan takardar. To ta yaya zasu iya controlling emotion dina?"

Faruk yayi

shiru shima kafin ya amsa.

"Da wannan kuma B, amma zamu gano komai a hankali idan muka bincika. But there's no way da zan yarda cewa wannan al'amarin accident ne kawai."

Ma'aruf ya rufe idanunsa, ya dafe goshinsa da hannu daya yana rarraba ƴan yatsunsa aka

n goshin. Abubuwan dake yawo a cikin kansa basu da iyaka, motsin kowannensu kawai yake ji yana ihu tare da ƴanuwansa, yana jin kamar tafiya suke yi akan fatar kan nasa suna zagayawa da karfin da yafi na kadawar iska a cikin sakanni.

Me yasa ne sai su? Me y

asa ko waye su ya zaba yana bibiyarsu? Me yasa ko sau daya bai taba tunanin ya barsu su huta ba? Kamar dukkan fafutuka da kuma ayyukan da suke yi na da sauki a wajensa, kamar a rana

ɗ

aya kawai suke kammala komai ta yadda gake diban dukiyarsu hankalinsa a k

wance, yana jin cewa zuciyarsa ba zata tafi da nauyin wahalarsu da ma guminsu ba.

"Na gaya maka B, na gaya maka ka bari sai ka dawo office tukunna ma tattauna, but you still insist. Gashi nan yanzu naji alama you're changing, bana so na jawo maka wata mats

alar kaima ka sani. So mayi magana kawai anjima."

Da haka wayar ta katse kuma Ma'aruf bai sauke ta daga kunnensa ba, ya cigaba da rike ta kawai idanunsa a rufe yayin da kwakwalwarsa ke juyawa da son tantance dukkan wata kalma da ta fito daga bakin Faruq di

n.

Bashi da wanda zai zarga, babu wannan mutumin a cikin lissafinsa, amma ya san a yanzu zargin kamar dole ne, don ta haka ne kawai za'a iya  samun hanyar da zasu fara tunanin kawo ƙarshen wannan al'amarin.

Anyi haka ba sau dayaba, ba sau biyu ba... An da

ɗ

e ana irin wannan abin a kamfanin tun kafin ya kai ga karbar wannan muƙamin, anyi a farkon fara aikinsa ma, watannin daBaffa da Baba Usman suka dora dukkan wani fatansu akansa na cewar abubuwa zasu canja da zuwansa, amma babu abinda ya canja

ɗ

in banda adad

in kudin da suka ninku wajen bata ma fiye da baya.

_Ina so ka sani Ma'aruf ba kowa zaka dinga yarda dashi a duniyar ba, wani lokacin mutanen dake kusa da kai suna iya zamewa abinda makiyanka, ba a kowacce fuska mai murmushi ake samun so ba, ba a kowanne id

o mai kyalli ƙauna take ba._

Kalaman Jamal sula haska akansa tun bayan wani lokaci, a shekarun baya ya kan tuna su fiye da cikin masaki, amma da wucewar lokaci da kuma hargitsin rayuwa ya manta lokaci na ƙarshe da ya tuna su sai yanzu da suka dawo kansa a

lokaci guda, yana iya tuna cewa a wancan lokacin Jamal ya gayamasa cewa bai san dalilin da yasa ya fada masa hakan ba, kawai tunani yake cewar zai iya amfanarsa a gaba...

'Gaban' tana da ma'ana da yawa, zata iya zama shekarun baya da suka wuce, zata iya z

ama shekaru masu zuwa a gaba, zata iya zama kuma yanzu, yanzun da yake jin kamar maganar tana

ɗ

oruwa ne akan halin da yake ciki.

Ya ajiye wayar a hankali daga gefen kujerar sannan ya mike a zuwa hanyar kitchen inda ya baro Amina ya taho amsa wayar, ya san

ma ta gama aikin nata a yanzu, don tun kafin ya fito ta kusa karasawa.

So yake yayi distracting kansa, so yake ya juyar da tunaninsa a yanzu gaba

ɗ

aya daga kan wannan al'amarin, ya samu wani abu da zai

ɗ

auke hankalinsa ya manta da abinda ya gama ji, don bai

san me zai faru ba idan ya cigaba da kasancewa cikin hakan a yanzu, abinda ya sani kawai shine koma waye a bayan wannan al'amarin zaiyi dana sanin da wani mahaluki bai taba irinsa ba duk ranar da yazo hannunsa.

Don haka yayi kokarin maida tunaninsa kan Am

inar a yanzu, yana kuma tunawa kansa da dukkan abinda ya faru jiya, jiyan da a cikinta kadai ya kara yarda cewa da gaske ƙaunar yarinyar nan, zuciyarsa ta manta

da dalilin da yasa ya aure ta don baya ko saka ranar fara wannan binciken, tunda ya taushi kans

a da cewar sai ya saba da ita tukunna shikenan ya ajiye hakan a gefe.

Baya iya wani tunani sai na yadda kusan komai nata ke burge shi, halaiyarta, saukin kanta da kuma kunyarta wadda bata hana ta abinda take so, ya kara fahimtar hakan a jiya sosai, a jiyan

da yaso abubuwa su fi haka a tsakaninsu, amma baya jin dadi, baya jin kwarin jikinsa kuma baya son yin komai a wannan yanayin, don bai yarda da kansa ba, bai san ta yaya ma komai zai kasance ba.

Ya karasa cikin kitchen din idanunsa na nuna masa cewa babu

kowa a ciki, sai kayan girkinta da ta gama ta jera komai tsaf akan table. Karfe sha daya ne na safiya a lokacin, basu dade da tashi ba, don ita kanta ya kula ta gaji jiyan, kwanan asibitin nan da suka yi ba wani mai dadi bane, shi yasa ya sake rike ta a ji

kinsa bayan sunyi sallar asuba, tana ta gaya masa cewa zata tashi da wuri amma ya ture bayaninta ya kashe bakinta.

A haka wani baccin yayi awon gaba dasu su duka biyun wanda basu tashi ba sai ƙarfe goma saura, shi ya fara tashi ma, kuma yana yin motsi ta f

arka, shikenan sai baccin ya kare.

Kofar kitchen din ta baya da take a bu

ɗ

e ta shaida masa cewa fita tayi wajen, don haka ya nufi wajen kuma tun kafin ya ƙarasa ya hango ta, ta wanke wasu ƴan kananan dusters na kitchen

ɗ

in tana shanya su a jikin igiyar da

bai san lokacin da ta

ɗ

aura ta ba.

Wannan rigar ce a jikinta, wannan rigar da bata rufe kafafunta ba, da safen nan bayan tayi wanka ya roke ta da Allah da ta saka don zuciyarsa ta gaji da hasashen kafafun nata da yake jin kamar ya shekara bai gansu ba, kum

a da kyar ta yarda ta maida kayan da ta dauko ta saka din tana fadin ita ta bacci ce, abinda yasa shi tunanin zai siyo wanda ba na baccin ba kenan.

Amina ta shanya tawul na gaba a hannunta yayin da take jin zuciyarta tayi wani irin wasai a yau, farin cikin

ta na karuwa da kowanne wucewar lokaci idan ranta ya tuna abinda ya faru jiya, kokarin da  tayi wajen hada al'ummar gidan nan kaf a gaban Ma'aruf bayan tashinsa, ciki har kuwa da mahaifiyarsa da sai dagabaya ma zuciyarta ta bata shawarar hakan, wani abu da

ta san babu wanda bai ji dadinsa ba, don ko su Shukra kafin su tafi suna ta fadin zasu tambayi Ma'aruf ya barta tazo inda suke suma, yayin da Salma ke fadin cewa zata zo su saka labule, tayi ta binsu da murmushi kawai tana amsawa har suka tafi, Shahida ma

matar Faruqa a jiyan kadai ta sake da ita har sunyi exchanging numbers, musamaman da

ɗ

an ƙaramin

ɗ

anta Aabid yaki kowa duk a tarin jama'ar nan ta jiya sai ita da kuma Inna Danejo... Har Innan na ta tsokanarsa cewa jinin tsofaffi ne dashi don wai tana da k

ishiya data rasu mai suna Amina.

Sannan ga Ma'aruf ma, yadda ya dinga yi mata jiya kadai ya isa ya shaida mata irin nasa jin dadin, don har godiyar yayi ta radawa a kunnenta, godiyar ma da daga baya ta kasa tantance gabadaya ta mecece. Yanzu babban abinda

ya rage shine ta roke shi ya barta taje gidansu kafin Hajiya Kilishi ta sake

ɗ

ago da wani abun ko kuma ita ta cigaba da nata takun.

Don Allah ya sani tana kewar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login