Showing 144001 words to 144990 words out of 144990 words

Chapter 49 - FARAR WUTA COMPLETE

kallonsa.

Ƙ

arar wayarsa  ce ta katse shi, yasa hannu a aljihu

ya

ɗ

auko ta, nambar Maryam ƙanwarta da ya gani ta tabbatar masa da waye tun kafin ma ya

ɗ

auka.

"Dadddddyyyy!!"

Muryar Hamida ta fa

ɗ

a da ƙarfi daga cikin wayar, ba shiri Amina ta taho da sauri ta kar

ɓ

a tun kafin ma ya amsa tana tambayarta yadda take, makar

antarsu da kuma gaya mata cewa gobe zasu dawo.... Dama a dazun nauyin Amma ne yasa basu gaisa ba, kafin kuma tace Maryam din ta hada ta da ita sai Aminu ya karbi wayar.

Daga inda Ma'aruf ke tsaye yana kokarin karasa shanye tea

ɗ

in dake hannunsa ya cigaba d

a kallonta yana murmushi...

Amina itace rabin rayuwarsa a yanzu ya yarda, itace nutsuwarsa dama dukkan wani fatan samun nasarar sa... Kulawar da yake samu tare da ita, wani abu ne da bashi da inda zai je ya samu idan ba a wajen nata ba.

Komai muƙaddari ne

daga ubangiji ya yarda!  lokacin da ya amince da aurenta, yayi ne saboda Jamal, saboda ya san alakarsa da ita a lokacin da yaga sunanta har ma da adireshin ta, sai gashi daga baya ya fahimci cewa wannan sunan na wata Aminan ce daban da itama take a wannan

unguwar ta gadon kaya, wata Amina ce daban da suka yi makaranta tare a wajen sauran takardunsa na wajen Hajiya Maimuna da bai san dasu ba sai a lokacin da Amina ta haddasa kusancinsu...

Allah ya sani bai san tarin alkhairin da zai lissafa  da ya samu ta da

lilinta ba tun daga lokacin da ta shigo cikin rayuwarsa zuwa yanzu, kamar tana tafiya ne da wani haske a kafafunta dama hannayenta ta yadda duk inda ta taka ko kuma abinda ta ta

ɓ

a sai ta haskaka shi.

Ita ka

ɗ

ai, ita ka

ɗ

ai ce abinda idan ya tuna cewar ta han

yar Kilishi ya samu, zuciyarsa ke yin sanyi da tarin rangwamen da yake jin cewa zai iya kyale ta da iya hukuncin da take fuskanta anan duniya, amma tabbas ne cewa tsakaninsu da ita wani hukuncin sai a lahira, don ko da giftawar sakan guda baya so ko da fus

karta ne ta gifta a tunaninsa balle kuma wani abu nata.

Adadin yadda zuciyarsa ta so ta shine adadin tsanar da yayi mata a yanzu, tsanar dake tafiya tare da albarkacin Aminar da ta zama inuwarsa a yanzu, don abinda ya sani shine ba don ita din da yake kall

o a gabansa ba, ko zai sake yi sau dubu yana kasawa, ba zai fasa ba zai yi ta kokarin da zai aika ta ne har lahirar da danuwansa ya tafi don ta riga shi zuwa da sakon da yake son ya isa ga danuwansa.

Amma saboda Amina, saboda ita da kuma sauran tarin yanuw

a da iyayensa da yake ganin kokarin da suke yi akansa wajen ganin daidaituwar lafiyarsa...

Shi yasa a dole yake ta kokarin kai zuciyarsa nesa yana tuna tarin maganganun da kowa ke yi masa wajen ganin yayi hakurin da komai ya daidaita rayuwarsa, sai dai a d

uk ciki babu abinda yafi rikewa irin kalaman Ishaq da ya gaya masa cewa babu yadda suka iya da Kilishi, babu abinda zasu yi msta da zsiyo daidai da adadin cutar da tayi musu a duniyar nan, dole ne su hakura su kyale ta da iya abinda da Allah ya kadarta a r

ayuwarta kawai,fon wata shari'ar sai a lahira!

"Tabbas wata shari'ar sai a lahira...!"

Bakin sa ya maimaita hakan a yanzu yana kallon Aminan dake dariya a cikin wayar tare da Hamida...

Shine bai fahimta ba tun asali, Kilishi bata daga cikin mutanen da suk

a cancanta a rayuwarsa!... Bata cikin su ko kadan.

Sai kawai ya zaro

ɗ

aya wayarsa ya shiga kiran mutumin da yake son ya hada shi da agency din da zai sayi kujerar makka guda biyu na Amma da kuma Baba (iyayen Amina).

Fatansa a kodayaushe shine ya faranta ra

n wannan ƴar yarinyar fiye da yadda take gyara tasa rayuwar!

*Alhmdlilah.*

*Ƙarshe.*

***

*Fara Wuta...*

_Ba'a kodayaushe ne Ubangiji ke rama cutar da makiyanmu ke yi mana daidai gwargwado da abinda suka zalunce mu a dashi ba, hakki yana da nauyi kuma yana

bibiyar dukkan mai

ɗ

aukarsa, sai dai dukkan wata wahala da kuma azabar da mai zalunci ke fuskanta game da wani hakki da ya

ɗ

auka a duniyar nan baya ƙarasawa ko kaso guda a cikin

ɗ

ari idan za'a kimanta sauran hukuncin da zai je ya tarar a gaban ubangijinmu.

.. Don gaskiya ne abinda masu iya magana ke fa

ɗ

a cewa WATA SHARI'AR SAI A LAHIRA!_

_Ina fatan Allah ya bamu gamawa da kuma wucewa lafiya a duniyar nan ba tare da mun koma gare shi da hakkin kowa ba, sannan ina fatan kuma ba zaku dauki hakkina ba wajen tura

labarin nan ga wasu a matsayin kyauta... Don bana fatan wata shari'ar ta hada mu daku a gaban ubangijin da kowannenmu zai koma gare shi._

_Godiya mai tarin yawa ga dukkan hakuri da kuma jinkirinku har zuwa gabar da muka kammala Farar wuta, nayi laifuka ma

su tari yawa na sani, amma dama da wuya ne kowacce tafiya ta kasance dari bisa dari wajen samun daidaito... Ina fatan dukkan wadanda na

ɓ

atawa rai zasu gafarce ni su yi min afuwa irin wadda zasu so ayi mudu idan sune a matsayina..._

_Nagode ga dukkan masoy

a rubutuna, nagode da hakurinku nagode da lokacinku, Nagode da kaunarku, idan har zanyi wani rubutu a gaba ina fata ba zai karaso gare ku ba sai a cikakken sa insha Allah._

_Ina fatan Allah ya faranta rayuwarku fiye da yadda zan kimanta... Allah ya bamu i

kon amfani da ƴan darussan dake cikin labarin nan... Jazakallah khairan._

*Aysha Shafi'ee.*

*08067794315.*

03/ 2022

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login