Showing 39001 words to 42000 words out of 144990 words

Chapter 14 - FARAR WUTA COMPLETE

abu da bata san sunansa ba a maƙogwaronta, har yanzu ta kasa samun Amma a waya, Allah-Allah kawai take anjima tayi ta kira Baba idan ya koma gida, don duk da ta ƙona wannan layar dazu a bayan fulawoyin gidan har yanzu hankalinta bai kwanta ba, h

ar yanzu zuciyarta bata nutsu ba.

Ta zazzage dukkan kayan Hamidan yafi sau biyar tana sakewa, tun tana tambayarta me take nema har ta gaji ta tsaya tana kallonta kawai, sai da ta gaji ta tabbatar babu wani abu da ta sake gani sannan ta zauna suka shiga nin

ke su suna saka su a kasan drawer.

A yanzu ta riga ta sami amsar da kowa bai sani ba, ta gane dalilin da yasa suka kawo yarinyar haka kwatsam bayan faruwar komai, akwai wani abu da suke son cimma ne wanda bata san takamaimai asirin akan waye ba, amma duk d

a haka bata jin cewa ya dace ta sanar da Ma'aruf tun a yanzu, shi yasa take son samun Amma a waya ta shaida mata komai don ta san yadda zata

ɓ

ullo musu suma, don ta yarda idan har zasu yi yunkurin cin galaba akan Kilishi to wannan ma ba komai bane, kawai t

soronta shine kar ya zamo da wani abin da bata sanshi ba ko kuma bata yi daidai ba wajen ƙona layar nan.

Lokacin da ta gama ta koma falon, Hamida na zaune ita kadai tana kallo, don haka ta fahimci Ma'aruf yana dakinsa kenan, sai kawai ta koma kitchen ta de

bo dukkan kayan abincin data hada ta fito dasu falon, Hamida tace ba zata ci tuwon nan ba, don haka tayi mata wata ƴar jollof din taliya da kifi. Kuma tana miko mata ta karba ta fara ci,ta fahimci yarinyar tana son abinci kawai dai bata iya ci da sauri ban

e.

Sai dai tana fara ci din tace a cire mata ƙayar kifin, don haka ta bar sake kokarin kiran su Amman da take yi tazo ta zauna daga gefenta a kujera tana kokarin cire mata ƙayar tsakiya na kifin da fork din da take ci. Kuma a lokacin ne Ma'aruf ya fito, ya

canja zuwa wata gogaggiyar jalallabiya kalar milk data fito da

ɗ

an hasken fatarsa kadan, yayi fresh din da ba sai yayi bayanin daga wanka yake ba, amma duk da haka Hamida ta tambaya.

"Kayi wankan?"

"Yes, nayi wanka."

Ya amsa yaba tahowa idonsa akan kafafu

nta da ta rasa me yake gani a jikinsu yake kallo, jallon da yasa zuciyarta tayi fayau a kirjinta.

Ya ƙaraso a hankali ya tsugunna a daidai gabanta hannunsa riƙe da wani abu da bata gani sosai ba, kuma tun kafin yace wani abu Hamida ta sake fadin.

"Daddy na

ku tuwo ne kai da Auntyn, ni bana ci shi yasa nake cin wannan."

"For real?"

Ya dawo da ganinsa kan Aminan, don shi har ga Allah ya manta da zancen tuwon da yayi.

"Da gaske na samu tuwon nan?"

Tana murmushin yadda yake tambayar ta gyada masa kai, sai ya zur

a hannunsa daya a cikin gashinsa yana kallonta ba tare da yace komai ba.

Sai kawai tayi murmushi ta mike zuwa wajen da ta ajiye food flasks din tana gaya masa cewa har da na dumame ma duk zai samu, yayin da Hamidan ta shiga tambayar meye

ɗ

umamen.

"Eeeewwww

w!" Ta fada da karfi bayan Ma'aruf yayi mata bayanin.

Suka yi dariya dukkansu kafin Ma'aruf ya taso zuwa wajen da take zuba masa abincin, kamshin miyar ya ratsa hancinsa yana yaba girkin tun kafin ya kai bakinsa don ko daga yadda miyar bata yi mai sosai ba

ma hakan ya burge shi, kamar ta san yadda yake son komai.

Ya tankwashe ƙafafunsa a gabanta yana kallonta yana kallon yadda take zuba miyar, yadda take komai... Allah ya sani baya jin gar ya bar duniya zai taba manta wannan alkhairin na Mami na kawo masa A

mina cikin rayuwarsa.

Wannan wani alkhairi ne da yake tunanin har a kabarinsa zai tuna shi.

****

"Ƙarfe tara da rabi.*

Hamida tayi bacci a lokacin, kuma har a sannan Amina bata sami damar samun su Amma ba don wayar Baban shima bata shiga yanzu.

Ma'aruf ya

shiga cikin gida wajen Baffa, kusan awa guda kenan, tun daga masallacin isha'i yace mata zai wuce. Ya gama cin abincin yayi santi kala-kala da tun tana daurewa har ta dinga dariyarta a fili, kuma bayan hakan ya gode mata lokacin da ta kwashe kayan zuwa ki

tchen.

A cikin kunnenta ya dinga ra

ɗ

a wasu abubuwa da ita kanta idan ta tuna yanzu sai ta runtse idonta don kunya, Ba wai maza ta sani sosai ba amma ta yarda Ma'aruf daban ne, shi da kansa yau ya gaya mata cewar baya ji, kuma itama ta yarda da hakan.

Babu

wanda zai yarda zai aikata dukkan abubuwan da yake yi, idan ka ganshi a fuska very responsible and so stiff akan dukkan abinda ya yanke, amma yafi kowa sanin tarin hanyoyin da zai ru

ɗ

a mace a lokaci guda.

Kamar kullum wajen da ya riƙe ta har yanzu tana jin

kamar shatin yatsunsa a wajen, kamar lokacin da ya riƙe ta yatsunsa sun ƙona wajen ne sai a yanzu iska ke ka

ɗ

awa tana son dawo da fatar tata daidai.

Ta ajiye abin sallar da ta idar da isha'i a lokacin, gyaran kitchen din da tayi ta kuma tsaya yiwa Hamida

Brush da canja mata kaya tana gyangyadi shi ya cinye lokacinta sai yanzu ta samu na sallar.

Ta tafi zuwa gaban mudubi ta dauko wani kwando tana kwashe dukkan abinda ta san Hamida zata iya sawa a ido ko ta bata jikinta dashi, tana yi tana yabawa kanta yadda

tayi kokari wajen kula da yarinyar da kuma sawa ta sake a gidan ysu daya kawai, Surayya na cewa sati guda, idan ta shigo gobe zata sha mamaki.

A lokacin ne kuma kofar dakin ta bude, ta dago da idonta ta cikin mudubin tana kallon Ma'aruf din da ya shigo, f

uskarta ta haska da murmushi tana masa sannu da zuwa.

Ya karaso a hankali yana zuwa inda take, kuma ba tare da ya jira komai ba ya rungumeta ta baya, kansa ya sauka a gefe wuyanta sannan ya karkato da kansa gefe yayi kissing kumatun ta kafin yace.

"Har gud

a nawa zan dinga samun wannan sannu da zuwan ne?"

Tayi kokarin tsaida numfashinta a hankali.

"Duk lokacin da ka fita ka dawo, kana da guda daya?"

Sai ya gyada kansa sannan ya ƙara karkata shi zuwa cikin wuyan nata, ba shiri ta damke kwandon nan dake gaban

mudubin, tana jin kamar wannan karon kusan tayi yawa.

"Yaya jikin naka?"

Ta tambaya a hankali don ji take yi kamar har yanzu da

ɗ

umi a jikin nasa. Yayi shiru jamar ba zai amsa ba tsawon wucewar sakanni sannan yace.

"I'm sorry Doll."

Mamaki ya dan kamata.

"Na me?" Ta tambaya.

Sai kawai ya mike tsaye sosai ya juyo da ita tana fuskantarsa, sannan yace.

"Sorry da nake saki damuwa akaina."

Ya sunkuyo a hankali ya sake kissing daya gefen fuskar tata sanan ya sake cewa.

"Sorry da zuwan Hamida."

Ya sake kissing g

efen bakinta.

"Sorry da dukkan flaws din da kika zo kika tarar a rayuwata."

Wannan karon saman bakinta ya sake kissing sannan ya

ɗ

an matsar da fuskarsa baya ka

ɗ

an yana kallon idanunta yace a hankali.

"Sorry da na bata miki dukkan rayuwar da kike tunanin z

aki samu idan kinyi aure..."

Kafin ya ƙarasa, kafin ya sake cewa wani abu tasa hannunta da sauri ta rufe bakinsa sannan ta girgiza kanta.

"You don't have to be... Babu abinda na taba tsarawa a rayuwata a wannan stage din, babu wani hasashe da na taba yi, s

o dukkan abinda ke faruwa a yanzu shine duniyata kuma shine fantasy dina."

Ya rike hannunta da ta rufe bakin nasa dashi, yayi kissing cikin tafin hannun nata kafin ya janye shi a hankali.

"Ban gane ba Amina, ki kara yi min bayani sosai."

Sunanta da ya fito

daga bakinsa da kuma yadda sautin muryarsa yake yasa jikinta yin rawa kadan, ta hadiye wani abu a makogwaronta har yanzu tana kallonsa sannan bakin ta ya furta.

"Ma'aruf Mansour Bakori, kai ne duniyata kuma kaine duk wani fantasy dina a yanzu, I really lo

ve you so much and I mean it."

Kuma da haka bata jira komai ba ta kara tsawon kafafunta tayi kissing gefen bakinsa kamar yadda yayi mata dazu,da farko bai ko yi motsi ba, yana tsaye ne kawai kamar baya numfashin amma tana kokarin maida kafafunta ta koma ta

ji ya furta kalma guda biyu rak!

"Ya salam!"

Kuma da haka bai jira komai ba yasa duka hannunsa biyu ya jawo ta jikinsa.

"I love you." Muryarta ta kara fada a fuskarsa, yayin da a cikin zuciyarta take mika dimbin godiya ga mahallicinta jalla wata'ala daya k

yautata rayuwar ta da mutum kamar Ma'aruf.

Kafin tayi tunanin komai, hasken dakin ya tafi gabadaya, kuma daga wannan ga

ɓ

ar bata ƙara gane komai ba, abinda ta sani kawai shine ta riga ta yiwa kanta alkawarin cewa da yardar ubangiji daga wannan lokacin, Ma'a

ruf ya daina sanin wani

ɓ

acin rai a rayuwarsa sai dai idan har abu yafi ƙarfinta.

Dukkan wadannan matsalolin da yake fuskanta da sannu zata bu

ɗ

e masa su daya bayan daya, don in dai har a wajen Hajiya Kilishi matsalar take, tayi imanin zata warware masa su

ne hankali kwance ba tare da ita kanta Kilishin ta fahimta ba kamar yadda Amma ta gaya mata a wayar da suka yi ta ƙarshe.

_"Mun riga mun gama haddace dukkkan wani takun matar nan Amina, don haka dasu zamu yi amfani daya bayan daya wajen kassara ta, ba zata

taba tunani ba, ba zata ta

ɓ

a hange ba saboda tana da yaƙinin

hakan tunaninta ne ita kadai kuma saboda mun saka mata imanin cewa ke baiwarta ce, baki da wata mafita ko dabara sai tata kawai!"_

**

_Wannan shine takunmu na farko akan Kilishi... Shine takun f

arko! Gabatarwa kawai, introduction..._

_Shine play button na Game

ɗ

in, don yanzu za'a fara wasan, yanzu komai zai fara, yanzu zaku san mene ainihin suna da kuma ma'anar labarin FARAR WUTA ( A lokacin da abinda kake tsoro yake tare da kai!) Don Amina itace

Farar wutarmu ba Kilishi ba kamar yadda kuke tunani tun daga farkon labarin._

_Amina itace FARAR WUTAR da Kilishi bata taba lisaafinta ba!_

_And Ehem ehem, kun kula cewa yau Ma'aruf muka ruda??_

😅😅🤣

*Asuba ta gari!*

Littafin nan na siyarwa ne akan nair

a #300

Account Details

0251365383

Wema bank.

Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.

#fikrawriters

#FararWuta.

°°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*08*

~~~~~~

_I need you to tell me i

t's okay._ _-Unknown_

**

"Ma'aruf..."

Muryar Amina ta fito a hankali cikin shirun dakin a hankali, ƙarfe bakwai da rabi ne na safiya, don tun bayan sun idar da sallar Asuba basu koma bacci ba. Kuma jin yayi shiru yasa a hankali ta dago da kanta ta kalle sh

i.

Idonta ya sauka akan fuskarsa, ya rufe idanunsa gabadaya kamar ya koma bacci amma ta san ba baccin yake yi ba, wani tunani mai da

ɗ

i ya sauka a cikin zuciyarta na tunanin cewa daga daren jiya zuwa yau ya da

ɗ

a tabbata shi mijinta ne don dukkan wahalar dat

a sha ma da yadda take jin jikinta baya gabanta a yanzu, kawai zuciyarta na kara narkewa ne da tunanin dukkan abinda ya faru.

Daga yadda yake rike da ita kadai a yanzu tana jin cewa kamar a duniya kaf babu wani waje da zata ta

ɓ

a zama a killace sama da ciki

n hannayensa, musamman a yanzu da ya fara bata labarin rayuwarsa, tana jin yadda kowacce kalma da yake fada ke ratsawa cikin kanta har zuwa zuciyarta.

Rayuwarsa mai kyau ce, cike take da wani irin gata da kuma jin dadin da ita bata taba saninsa ba ma, don

ko a tsakanin yan uwan nasa, rayuwarsa daban ce, Hajiya Kilishi ta kyautata rayuwarsa da wani irin gata da kuma jin da

ɗ

in da a yanzu take jin zuciyarta na ƙara dasa aya kan wace irin ƙauna ce wannan da zata so shi irin haka kuma ta dinga cutar dashi.

Sai d

ai bayan duk hakan kuma a yanzu yazo gabar da yake gaya mata labarin yadda ya rasa

ɗ

anuwansa Jamal, ya gaya mata yadda komai yake tsakaninsu, shaƙuwarsu dama dukkan wani buri da kuma ƙudirin Jamal

ɗ

in bayan ya dawo daga karatu, a yanzu yana gaya mata lokac

in da suka yi wata tafiya ne zuwa Bakori don

ɗ

auko Inna Danejo, kuma duk da bsi karasa ba, tunaninta ya gaya mata cewa a wannan lokacin ne wani abu ya faru, shi yasa bayan yayi shiru bata ce komai ba, tana jinsa kawai yana cigaba da wasa da yatsunta daga k

asa bargon da ya lullu

ɓ

e su, sai da shirun ya tsawaita tukunna sannan tayi magana.

Ya bude idanun nasa a hankali ya lumshe su yana cigaba da kallonta yayin da ita nata ke ware akansa. Kuma a hankali cikin rashin hasken

ɗ

akin muryar sa ta cigaba da cewa.

"S

hi ya bani tuƙin a lokacin, kuma abu na karshe da ya gaya min shine kar in kashe shi, bayan mun canja waje na hau titi bamu kara magana ba saboda ya shiga ansa call din wani abokinsa Liman, suna ta magaba ni kuma nayi focusing hankalina akan titin, wallahi

wallahi banyi wani abu ba daidai ba, I was driving safely lokacin da abin ya faru."

Ya sske yin shiru, shirun da ba sai wani ya gaya mata cewar yana shirin gaya mata cewa yana shirin gaya mata dukkan memories din dake binsa shekara da shekaru bane.

"Kawai

naji sitiyarin ya ƙwace daga hannuna ne sannan naga motar tana wullawa akan titin, ina jin salatin da yake yi amma ni ban ma san me nake cewa ba, hannunsa yana ta kokarin ya kama sitiyarin amma juyin da motar ke yi yasa buguwa kawai muke yi kotawanne bang

are, lokacin da motar ta sauka daga kan titi ta nufi cikin daji, daga ni har shi babu wanda yaga karyayyiyar bishiyar dake gabanmu har

motar ta dake ta, ta dake ta daidai saitin inda Jamal yake da karfin da yasa ta faso ta cikin gilashin ta soke a ko'ina n

a kirjinsa."

Ya sake yin shiru, idanunsa na kallon tsakanin girarta guda biyu yayin da suke haskawa da wani irin abu da Amina ta kasa tantance shi a lokacin, sai kawai ta

ɗ

ago da hannunta daya da bai riƙe ta dashi ba zuwa gefen fuskarsa, a hankali dogwayen

yatsunta suka ratsa tsakanin gefen fuskarsa da kuma wuyansa, wani abu da yasa ya sake lumshe idanunsa nasa kafin ya sake cewa.

"Likitocin sunce zuciyarsa ta fasa a lokaci guda shi yasa tun a wajen ya rasu..."

Bata ce komai ba ya cigaba.

"Ya rasu yana kall

ona Amina, idanunsa akaina suka tsaya har lokacin da jama'a suka karaso suka rufe motar ana kokarin fito damu, don tankin mai ya fashe tana shirin kamawa da wuta, ba'a iya fito da Jamal ba sai da aka sare reshen bishiyar nan daga jikinta, aka fita dashi da

su a jikinsa.

Ban ma san ta yaya aka zaro ni ba, na san dai kawai ban ƙara fahimtar komai ba bayan hakan sai farkawa nayi na ganni a asibiti, and that was the beginning na farawar ciwo na, I was depressed, emotionless and even out of my mind."

Taga alamun

ya ha

ɗ

iye wani abu a maƙogwaronsa sannan ya cigaba.

"Kusan haukacewa nayi a wannan time din Amina, bana gane komai bana fahimtar komai, wannan ranar ita kadai take ta maimaitawa a cikin kaina, tun daga safiyar da na ganshi zaiyi tafiyar, har tahowarmu mu,

da maganganun da muka yi da kuma yadda hatsarin ya faru.

Su Mami, kowa da kowa sunyi mutukar kokarinsu wajen tallafa min Amina, musamman Ishaq, Ishaq yayi mutukar kokarin da ban ma san adadinsa ba Amina, kusan shi ka

ɗ

ai yake tare dani a kodayaushe, dashi m

uka yi ta yawon zuwa asibiti a London, shi yake tare dani a gida kodayaushe, su Mami suna zuwa duba ni amma ba kodayaushe ba, ina samun support dinsu da tarin addu'o'i.

A cikin wasa muka yi magana da Jamal cewa zan iya canja rayuwata zuwa tasa idan har wan

i abu ya faru, amma duk da haka bayan naji sauki sai naji ba zan iya rayuwa a matsayin Ma'aruf da wannan nauyin ba, saboda haka sai na ajiye dukkan wani buri na a gefe na fara sabuwar rayuwa.

Tun ina yaro burina ne in zama likita, kafin accident din na sam

i admission a wata makaranta a lokacin amma bsyan na warke ban sake bi ta kan admission din ba na dage wajen canja makaranta dama course din gabadaya, Baffa ya iya kokarinsa don hana ni amma na gaya masa cewa in dai ba karatun business ba ba zan yi karatun

ba gabadaya, a lokacin ne Mami tasa Ishaq ya dawo wajenmu bayan rasuwar iyayensa muka tafi London tare muka yi karatun.

Bayan wannan abubuwan da na canja a rayuwata suna da yawa Doll, this isn't me, mafi muhimmanci shine wannan matakin da nake kai, burin

Jamal shine ya karanci harkar kasuwanci kuma riƙe ragamar kamfanin Baffa kamar yadda nake yi yanzu."

Ya sake yin shiru yana kallon yadda ta kame gabadayanta, har yanzu hannunta na kan fuskarsa,babu abinda take sai numfashi da kuma jiran ya cigaba.

"Kin fah

imce ni Doll, kina ganewa?"

Ya yanke shawarar tambaya, sai tayi kokarin

ɗ

aga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login