Showing 51001 words to 54000 words out of 144990 words
dariya kafin Amina ta koma ta sami waje a kujerar da Hamidan ke zaune, s
uka gaisawa da matar da har a lokacin Ma'aruf bai gane daga ina take ba.
"Ai maman tata ce tace inzo in kawo mata wasu kaya da aka manta ba'a hado dasu ba, har da na wasanta ma."
Ta fa
ɗ
a tana miƙo wata jaka dake gefenta.
Kuma yana ganin yadda Amina bata ka
r
ɓ
i jakar ba, amma fuskarta da murmushi tace.
"Ai kuwa ƙika tana kewar kayan wasan nan, don tunda tazo kallo kawai muke ta sha."
Matar ta sake dariya kafin tace.
"Sai kuma wata mantuwa da akayi, a cikin waccan jakar tata wai akwai wani kayanta data manta
shine take son in taho mata dashi yanzu."
Mariyan ta fada har yanzu da murmurshi a fuskarta, murmushin dake tsayawa iya fatar bakinta kawai ba tare da ya ƙarasa ko'ina ba, don a wannan lokacin tana jin muryar Rukayya tana amsawa a cikin kanta da umarnin da
ta bata kafin tahowarta, umarnin da ta bata bayan tasa ta shafe hannunta da wani bakin ruwa.
_"Idan kika gaya mata haka ta dauko miki jakar, zip din farko zaki bude, akwai wata bakar leda a ciki. Kina zaro ta sai ki bude kamar zaki tabbatar da abinda ke ci
ki, budewar kawai nake so kiyi Mariya, da kin bude shikenan kin gama cika aikin ki, sai ki kulle ta kawai ki dawo, ki dawo min da ita ki karbi kudinki. Cif dubu hamsin babu ragi."_
Tana iya tuna yadda zuciyarta ta cika da murna a lokacin, ta cika da wani i
rin
ɗ
oki da kuma farin ciki, albashinta dubu ashirin ne kowanne wata idan an cire alkhairin da take samu a gidan, kuma ta kwashe shekara da shekaru tana aikin, don haka idan har ba adashi ta
ɗ
auka ba, ƙarya ne ta tuna ranar data riƙe dubu hamsin a lokaci g
uda ta kanta.
_"Zip
ɗ
in baya zaki bude ledar tana ciki, babu mai ganinta sai ke da kika wanke hannunki da wannan ruwan don haka kar ki tsaya komai, kina budewa zaki ganta .."_
Maganar da Hajiya Nafisa ta sake jaddada mata ta shiga kunnenta. Sai tayi saurin
gyada kanta lokacin da Aminan ke miƙewa da niyyar zuwa
ɗ
auko jakar.
"Who's she?"
Ma'aruf ya tambaya lokacin da ƙafafunta suka tsaya a gabansa, fuskarta na nunawa da mamakin ganinsa da tayi a wajen. Sai kawai ta matso dab dashi sannan a hankali tace.
"Daga
gidansu Hamida take, saƙo ta kawo."
Tana fa
ɗ
in haka kawai ya girgiza kansa.
"Dan na kawo miki Hamida bance har da Family
ɗ
inta ba, babu ruwanki dasu, don me yasa zaki bu
ɗ
e mata kofa?"
Yadda yayi maganar yana ƙoƙarin
ɗ
aga muryarsa yasa tayi saurin dago da
hannunta ta rufe bakinsa. idanunta na haskawa da wani abu kamar mamaki, wani abu da yasa shi fahimtar cewa ransa ne ke ƙoƙarin
ɓ
aci, don haka sai kawai ya girgiza kansa yana riƙe hannunta data fora akan bakinsa sannan yace.
"She's leaving." (Tafiya zata yi
.)
Tafiya? Saboda me? Ta yaya zai ce yace mata ta tafi? Sai dai kafin tayi magana yace.
"I have my plans against mutanen nan, babu wanda zai sake ganinta for the meantime a cikinsu, don haka kar ki sake bu
ɗ
ewa kowa kofa idan har kin san daga nan suke."
Mur
yarsa ta fito ne da wani irin kauri da kuma ikon da bata ta
ɓ
a ji ba yayin da fuskarsa take
ɗ
auke da wani irin yanayin da har yanzu bata san shi ba. Sai ta gya
ɗ
a kanta, amma duk da haka ta daure tace.
"Yanzu zata tafi, amma dan Allah ka bari in
ɗ
auko mata s
akon tukunna,
ɗ
auka kawai zata yi sai ta tafi."
Idan har bai bari ta
ɗ
auko mata jakar nan ta duba taga cewar babu abinda suke nema ba, bata san me zata ƙirga a matsayin nasararta da kuma sakonta da zai isa gare su ba, ya tsaya kamar ba zai ce komai ba sai
kuma ya gyada kansa a hankali yace.
"Ki
ɗ
auko ta tafi, I'll be out in two minutes, idan na fito ganta zan mata duk abinda yazo kaina wallahi."
Tana jin haka tayi saurin gya
ɗ
a kanta sannan ta saki hannunsa da sauri ta karasa dakin, bata ko tsaya rufe wardro
be din ba ta dauko jakar ta fito, ta samu baya wajen don haka kai tsaye ta karasa cikin falon.
"Ai tace saƙon itama ba nata bane, wai can Adamawa za'a kai, sai da aka zo tafiya dashi ta duba taga yana nan wallahi."
Cewar Matar tana ƙar
ɓ
ar jakar har yanzu d
a murmurshi a fuskarta, ta miƙa mata da nata murmushin itama sannan ta zauna a kujerar dake fuskantar ta tana cugaba da murmushin dake nunawa tar a fuskarta.
_...wasa da hankalin mutane yana daya daga cikin abubuwan mafiya da
ɗ
i a duniyar nan, ina jin dadi
duk lokacin da na koma baya na kalli fuskokin mutanen da na
ɗ
aure su tamau da hannayena ba tare da sun sani ba._
Wannan na daya daga cikin maganganun da Kilishi tayi mata ranar da ta fara bude mata ko ita wacece, amma ta manta su, basu sake zuwa cikin kant
a ko sau
ɗ
aya ba sai a yanzu, sai a yanzu da take kalllon fuskar Mariyan dake bayani tana kokarin neman zip din da aka kwatanta mata, da sanda ta gane shi, da
sanda ta bu
ɗ
e, da kuma sanda hannunta ya shiga ciki kafin yanayin fuskarta ya canja a lokaci guda
jin babu komai.
Sai kawai wani murmushi mai fa
ɗ
i ya
ɓ
alle daga bakinta, tabbas mata masu wayo dole ne su ji da kansu.
***
"Tunda bank statement dinki za'a bayar, dole za'a ha
ɗ
a da affidavit da kuma I.d card dinki wanda yake dauke da signature."
Muryar Muh
d, wani ma'aikaci a wajen da ake harkar shige da fice na visa ya fada cikin wayar dake kare a kunnen Hajiya Kilishi.
Hajiya Kilishi ta nisa sannan tace.
"Babu damuwa Muhd, duk zasu taho dasu, idan nasa kudin da zasu isa a cikin account din shikenan komai z
aiyi daidai ko?"
"Eh, amma idan da hali Hajiya ki dan bar wani abu ko da dubu dari ne."
"Shikenan babu matsala, nagode."
Da haka ta katse wayar, tana tashi ta dauko wata jaka da ta fito da ita a gefen wardrobe din dakin, ta koma kan gadon ta zauna sannan t
a fito da dukkan takardun ciki, a cikinsu ta dauko wata ƴar karamar takarda mai dauke da rubutun nambobi ta kwafi nambobin masu shaida wata account number sannan ta tura iya adadin kudin da ta san zasu isa a komai da komai na tafiyar su Aminu har kuma da d
orin da muhd
ɗ
in yace.
Ta tura kuma bayan an turo mata da sakon kwasar kudin, bata san sanda tayi murmushi ba ganin yadda wani
ɗ
an mitsitain adadi ne kadai ya sauka akan zunzurutun kudin dake cikin wannan account din.
Jiya ta turawa da ƴanuwanta kudin da t
ake basu a karshen kowanne wata suma, amma duk da haka gani take kamar bata taba kudin ba... Kudin da take da yakinin ko Baffa bashi da adadinsu a yanzu, bama shi ba, kamfaninsu gabadaya da suke takama dashi na Bakorin bata jin adadin da suke dashi ya kai
jimlar na accounts dinta gaba daya.
Ita kanta ta sani cewa tayi kokari kokarin da ba kowacce mace irinta ce zata iya shi ba, ganin tsawon shekarun da aka dauka tana cika rantsuwa da kuma burin data daukarwa kanta tun zuwa gidan nan, tun bata da komai sai z
uciyarta da tanadinta, gashi har an rufa shekarun da ta tara manya-manyan ƴaƴan da har ta aurar da biyu a ciki.
Wani abu ya ratsa zuciyarta na cewar ƴaƴan da take wa rabin wannan hidimar ma har yanzu basu da masaniyar komai, matsalarta kenan, wajen da tak
e ganin faduwarta kenan... A kokarin binne komai don ta tafi a tsaftatacciyar hanya, bata ta
ɓ
a nunawa waninsu kalarta ba, har gwara Salma, a kwanakin baya ta kan gaya mata cewa tanadin da take yi musu mai kauri ne, don haka idan har akwai wani abu da zata
iya kira da ƙalubalen da take shirin fuskanta, shine na yage su Samirah da zata yi daga wannan gidan da kuma mahaifinsu.
Ta nisa a hankali, tana lissafi a cikin kanta. Komai yana tafiya daidai, ta riga ta gama da dukkan wata harkar kashe ku
ɗ
i a shirye-shi
ryen tafiyar mahaifin Amina da kuma
ɗ
anuwanta Aminu, so take su tafi har su isa can a fara yi masa aikin kafin ta tunkari Amina da hodar da Awwalu zai kar
ɓ
o mata a lagos, don ta haka ne Aminan zata sami kwarin gwiwar yi mata aikin.
Da taga komai ya fara ku
ma, zata san ta yadda zata yi ta siya musu gida, wannan zai bawa Aminan ƙwarin gwiwar cigaba da yi mata aikin, sai kuma ta biya musu kudin aikin hajji ta kuma basu adadin kudin da zasu iya buƙata, idan tayi hakan ta tabbata babu makawa Amina zata cigaba da
yiwa yarinyar amfani da hodar har lokacin da idanunta zasu rufe gabadaya.
Ta gama wannan tsarin ta ajiye shi a gefe sannan ta jawo na
ɓ
angaren sauran adadin kudin da take son ta lahanta kamfanin Bakori dasu.
Gobe litinin, Ma'aruf zai koma aiki, ta san zai
cigaba da bincike akan mutumin nan da ta tabbata yanzu an gaya masa kamanninsa kuma sun fara nemansa, baza su ta
ɓ
a ganinsa ba kamar yadda har yanzu basu iya gano inda wannan Mr. Okafor yake ba don haka a ajiye hakan a gefe, ta san Ma'aruf, ta san cewar wa
nnan abin ba zai sa ya tsaya da aikinsa ba, zasu cigaba da aiki ne kamar wancan lokacin kuma suna cigaba da binciken su, don haka meye kwangilarsu ta gaba?
Ta jawo wani file ta buda cikinsa, ta dauko takarda ta karanta, sunan wani kamfani mai suna Rotel& C
o ta shiga idanunta, sai tayi wani murmushi mai fadi, ta san kamfanin don lokaci bayan lokaci suna yawan yin aiki dasu Baffan, kuma basa wasa da harkar biya ko shi Baffan ya gaya mata.
Lissafinta yayi kwana zuwa wani lokaci na gaba, lokaci mai zuwa, lokaci
n da har su Ma'aruf zasu gama yi musu aiki azo gabar karbar kudi, idan zata lissafa ba zai fi cikin wata guda mai zuwa ba, don haka me zata yi a wannan lokacin da zai dauke hankalin su kudin su shigo hannunta?
Wace hanya zata bi ta karbi kudin kuma wace ha
nya zata bi ta fara karkato hankakin ƴaƴanta don ta sami wannan kudin ta san ta kassara kamfanin Bakori kenan har abada, babu ta yadda za'ayi su iya tasowa tunda bata sani ba amma zata iya rantsewa cewa a yanzu da ragowar kudin Ma'aruf zai yi amfani wajen
karbar wannan kwangilar, to idan suma suka narke me kuma zasu sake samu suyi wani aikin.
Ta ajiye wannan lissafin a gefe ta shiga lalube a cikin kwakwalarta wajen neman mafita, a lokacin wani tunani ya haska a cikin kanta cewar zata iya samowa kanta hanya
guda
ɗ
aya da zata cimma wadannan abubuwan guda biyu, hanya daya da zata dauke hankalin kowa kudin nan su shigo hannunta kuma hanya guda da zata sa ko ƴaƴanta baza su ja da ita ba idan lokacin tafiyarsu yayi...
Hanya daya,
Daya kacal!
Jifan tsuntsu biyu da
dutse daya...
Hanyar da zata ƙarkare komai kuma zata kawo ƙarshen komai...
Hanya
ɗ
aya...
Jigo kuma ginshiƙin komai...
Bango...
Meye Bangonsu?
Meye Bangon da zai jijjiga kowa?
Me zai rikito da komai?
Meye abinda zai ta
ɓ
a kowa ya
ɗ
auke hankalin kowa?
Meye za
i taba har zuciyar ƴaƴanta su yarda cewa basu da wani zabi banda nata?
Idan har za'a je ƙarshe, to dole ne ta tabo komai tun daga tubali.
Meye tubalin?
Meye mafari kuma ginshiƙinsu?
Meye Bangon da kowa ke jingina a jikinsa?
Baffa....!
Tabbas Baffa!
Alhaji
Muhammad Mansour Bakori.
Mutuwarsa zata zo daidai da rikicewar kowa a gidan kuma daidai da samun nasararta!
Mutuwa...
Ta
ɗ
an tsaya tana nazari a cikin kanta amma kuma sai wani tunanin nata ya kore wannan nazarin, ta ta
ɓ
a sonsa ne? Tun da suke tare taba jin
wani abu mai kama da son sa koda kuwa
ɗ
an burbushi...
Mutum
ɗ
aya zuciyarta ke so, mutum
ɗ
aya zuciyarta ta ta
ɓ
a russuna akansa, kuma mutum
ɗ
aya ne ruhinta ya taba kallo da wannan sigar, Ma'aruf...
Amma kuma son nasa yazo mata ne ta haramtacciyar hanya, har
amtacciyar hanyar da duk kaifin basira da kuma wayonta bata isa ta mallake shi ba. Da wannan karyayyiyar zuciyar take rayuwa a kodayaushe kuma da ita take ganin yadda wasu sa
ɓ
anin ita ke samunsa.
Shi yasa take yin duk abinda ta san zata faranta masa kuma z
ata zauna a zuciyarsa, kuma take kore dukkan wani abu da zai
ɗ
ara matsayinta a ransa. Ta yarda da wannan, ta yarda iya shi ka
ɗ
ai zata samu, ta yarda shi ka
ɗ
ai ne nata, shi yasa take kare hakan da dukkan iyawarta.
Ba zata ta
ɓ
a bari wani abu a duniyar nan ya
keta ta a cikin zuciyarsa ba... Duk sanda ta tashi tafiya kuma zata barshi ne da ragargajajjiyar zuciya irin tata ta yadda ba zai ta
ɓ
a samun wata dama da wani abu msi kyau zai sake tasiri a ransa ba.
Zata kashe mahaifinsa,
Zata nakasta ƴarsa,
Zata kassara
jarin kasuwancin da suke taƙama dashi,
Zata raba shi da Aminar da yaga kamar hankalinsa ya fara karkata zuwa kanta.
Idan tayi haka, me ya isa ya sake ratsa cikin zuciyarsa kuma?
Dole ne kowa ya biya bashin rashin samunsa da ba zata yi ba.
Hannunta ya
ɗ
auk
i wani biro a gefe, a saman takardar Rotel&Co ta rubuta talatin ga watan yuli.
30th July.
Wasu abubuwan zasu fara kafin wannan ranar, wasu abubuwan kuma zasu faru ne a wannan ranar.
Abinda Kilishi bata sani ba shine, wani lokacin Bawa da hannunsa yake rubu
ta lokaci da kuma ƙaddararsa!
***
"Ni ba jahili bane Sadik, na gaya maka nafi shekara goma ina tanadi akan matar nan. Da ni take shirya komai, na san duk irin butulci da kuma cin amanar da take shiryawa makusantan ta, to ni waye da zan yi tunanin cewa zata
ware ni?"
Awwalu ya fa
ɗ
a yana kallon abokinsa Sadik, suna zaune ne a tsakiyar falon gidan Awwalun, inda a kodayaushe Sadik
ɗ
in ke zuwa suna hira.
"Me kake tarawa? Kana tunanin abubwan da kake tarawa sun isa su tozarta ta a idon mutanen nan, kai da kanka f
a kake bani labarin irin yardar dake zuciyarsu game da ita."
Awwalu ya jinjina kansa, ya dauki kwalbar lemon dake gabansa ya kur
ɓ
a sannan yace.
"Ina da CDs na recording
ɗ
in bayanan da take yi min sun fi guda ashirin Sadik, dukka a cikinsu bayanai ne masu m
utukar muhimmanci na abubuwan da tayi, a wayata nake recording sai in bayar a mayar min dasu cikin Cd, sannan ina dasu a duka computers dina ma.
Kuma na dade da sanin cewa sune sanadin arzikina, don ni ba mahaukaci bane da ina kallo zata sami wa
ɗ
annab maƙu
dan ku
ɗ
a
ɗ
en kuma in tsaya kawai ta gutsirar min wani abu a ciki? wane tabbaci ma nake dashi na cewar zata bani
ɗ
in? So hanyarta take gyarawa kawai nima ina gyara tawa."
A lokaci guda Sadik ya
ɗ
uro wani zagi yana dariya, sannan ya jinjina kansa yana fa
ɗ
in.
"Sh*gen duniya! To amma baka tsoron idan kayi mata wannan barazanar ta saka a far maka kaima?"
Awwalu ya kalle shi sosai sannan yace.
"A wannan
ɓ
angaren matar nan dakiƙiya ce Sadik, don duk wadanda ka san suna mata aiki ni nake nemo su. Shi yasa nayi mamak
i a yanzu da har ta sami wasu a Mexico tayi cinikin hodar nan dasu ba tare da na sani ba, kaga hakan ya nuna min cewar ta fara shirin juya min baya da ta sami wani connection
ɗ
in.
Allah yaso dama zuciyata a tsaye take tun daga lokacin da ta shigo da yariny
ar nan cikin wannan al'amarin, don na sani babu ta yadda za'ayi mu'amala mutum uku dole sai biyu sunfi jituwa... Kaga kenan da banyi wa kaina wannan tanadin ba ai na shiga uku."
Sadik ya jinjina kansa kafin yace.
"To me kake so? Fiye da abinda zata baka?"
Wannan karon dariyar ta Awwalu ce, ya ƙyalƙyala ta iya son ransa sannan ya dago ya kalle shi.
"Duka abinda ta tara Sadik, Duka!"
Ya fadi kalmar karshen yana daga murya.
"A irin abinda ta shuka, cin amana da kuma butulcin da tayi, bata cancanci taci ku
ɗ
in n
an ko ƙwandala ba Sadik, ban ma san me zata yi dasu ba, matar nan ta tsufa sannan ƴaƴanta duka mata ne, ub*n me zata basu da zai fi ta aurar dasu, kawai dai an halicce ta ne da wani irin son zuciyar da ban san ta yaya zan misalta shi ba.
Ni namiji ne, yanz
u zan fara rayuwata, aure zanyi in tara iyali, don haka ka gaya min wa yafi cancanta da wadannan kudaden?"
Sadik ya jinjina kansa yana cije lebbensa kafin yace.
"Kaine, kai zaka ci su, kuma nima dole in taya ka mu same su ko ta wace hanya ce, don