Showing 72001 words to 75000 words out of 144990 words

Chapter 25 - FARAR WUTA COMPLETE

tsarin da tayi na kokarin boyewa kowa, kowan d

a Hajiya Kilishi ta zamo sila babu Ma'aruf, hasalima shine daya hannun da zai talkafa mata wajen cimma dukkan abinda ta tsara din, tsarin da ko Amma bata san shi ba...

Amma kuma tun kafin tazo gaban nasa, sai ta rasa ta yadda ta yadda zata iya harhado kala

man da zasu tashi ma'anar da zata gaya masa, ta kasa tunanin konai, tana jin kwakwalarta dama zuciyarta fayau, don haka ko a yanzun babu abinda ta iya cewa sai kawai ta shiga bashi labarin gidan nasu da kuma yadda Hamida ta sake da ƴanuwanta.

Har ya shirya

suka koma falo inda ya cika cikinsa da abincinta kafin Hamida ta cika kansa da nata surutun, har suka yi bacci, tana rungume a jikinsa tana jin numfashinsa a hankali kafin ya koma mai nauyi alamun gajiyar dake jikinsa tafi ƙarfinsa.

Har Asuba da tayi, ya

fita masallaci ya dawo ya same ta akan tata sallayar, tana zaune gaban Mahaliccin data idar da ibadarta yayin da zuciyarta ke karanto tarin addu'o'in da basu da ƙarshe.

Daga bayanta ya tsugunna akan gwiyoyinsa, sannan ya zuro hannayensa duma biyu ya kara s

u a bayan nata, ya tsayar dasu yadda ta yi wa nata wajen addu'ar sannan ya

ɗ

ora ha

ɓ

arsa a saman kanta.

Tayi murmushi a hankali tana jin ƙamshin sabon turaren da ya fesa a jikin sallayarta na shigar mata har cikin kai, ƙamshin mai sanyi ne, amma ita tana ji

n ƙarfinsa har cikin kanta, ta kai ƙarshe a addu'ar kuma yana ganin ta motsa hannunsa ya ha

ɗ

e su da nasa gaba

ɗ

aya suka tafi kan fuskar tata.

"Ameen ya Allah Noor."

Ya fa

ɗ

a daga saman kan nata sannan ya juyo da ita gaba

ɗ

aya tana fuskantarsa, a lokacin ne ta

rasa dukkan wani tunanin kanta, yadda yake kallonta a cikin duhun dakin ya warware dukkan wani lissafinta,  a lokacin ne bakinta ya furta abinda ya zama mafarin bude wata sabuwar rayuwa a tsakaninsu.

"Ma'aruf..."

Bakinta ya furta sunan ba tare da ta san m

a me ta fada ba, kuma kafin ya amsa sauran kalaman suka biyo baya, bi da bi, wani na tunkude wani akan lebbenta.

"I think we're pregnant....!"

( Ina tunanin muna da ciki...!)

****

*No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*

*Gidan Hajiya Salamatu.*

"Kar ki damu Haj

iya, gobe-goben nan zan sako miki su a mota, an riga an ha

ɗ

a sun cika cif, laces guda talatin da biyu ne, atamfa arba'in, sai materials

ɗ

in guda takwas Nylon da kuma cotton guda goma..."

A cikin wayar dake kare a kunnen Hajiya Salamatu take wannan bayanin,

tana zaune ne a barandar gidanta, daga ƙasan rumfar yayin da iskar yammar ke kadawa a kowanne

ɓ

angare na harabar gidan.

A gabanta akwai wani dan karamin tebur da ta ajiye jotter da kuma biron da take karanto adadin kayan da take lissafawa a ciki, bayan jo

tter akwai jug mai garai-garai yana

ɗ

auke da lemo kakar yalo tar da kuma kofinsa wanda aka zuba lemon a ciki.

Ta kai ƙarshe a wayar tata, sannan ta sauke wayar, kuma kai tsaye hannunta ya lalubo nambar Hajiya Kilishi wadda taji shigowar nata kiran a lokaci

n da take waya.

"Ina tare da mutane na ne ranki ya da

ɗ

e..."

Ta fada kai tsaye bayan Kilishin ta

ɗ

auki waya daga nata

ɓ

angaren.

"Na sani ai shi yasa ban takura ba... Saratu ta kira ni da safe take gaya min cewa zasu dawo kasar nan kunyi waya?"

Hajiya Salama

tu ta gya

ɗ

a kanta tace.

"Mun yi tun jiya, nake cewa komai labari ne, yaushe take ta daga hankalinta akan yaƙi tafiya da ita gashi har ya dauke ta da ƴaƴan nata kuma zasu zo hutu."

Hajiya Kilishi tayi murmushi mai kama da dariya kafin tace.

"Da ta biyo ta h

anya ta ba, a baya ta tashi hankalinta a banza, amma da ta fahimce ni ta ja da baya ta zama macen kanta ba gashi yanzu komai ya dawo hannunta kishiyar tata ma ta kama gabanta ba."

"Wallahi kuwa..." cewar Hajiya Salamatun kafin ta canja zancenta da cewar.

"

Kin samu kayan ne?"

Hajiya Salamatun ta tambaya tana kurbar lemon hannunta.

"Wai sai Jibi zasu iso, abinda nake ta tunani kenan Salamatu, karo na farko da zuciyata ta kasa kwanciya akan wani abu, haka kurum nake jin cewa kamar jibin nan ba zata karasa ba w

ani abu zai faru."

Hajiya Salamatu tayi dariya kafin tace.

"Ki kwantar da hankalinki Hajiya, kin san hausawa sun ce aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, gangarar kawai kika zo shi yasa kike jin haka, ban da abinki ma daga ni sai ke fa muka san wannan abin

da kike shirin yiwa Awwalun nan, kuma ni dai kin san ko yanka ni akayi baza'a iya fitar da sirrinki daga cikina ba ko?"

Kilishi ta gyada kanta.

"Na sani Salamatu, kawai ban san me yasa ba bana gane komai ne a yanzu sai na fara gamawa da Awwalun nan,

ɗ

azu

munyi waya da Maigaskiya yace min yana office abubuwwa sun yi masa yawa, bai ce min komai bayan hakan ba amma na fahimci kamar binciken nan suke yi kuma sun gano wani abu Salamatu, da ba Awwalu na dora akan harkar nan ba da na bari ko sau daya ne dun ganni

da tuni inaga abubuwa sun canja kala daga yadda nake kallonsu."

Salamatun ta girgiza kanta itama.

"Ki daina wannan tunanin, ki fuskanci abinda ya rage kawai bayan Awwalun, zancen yarinyar nan tasa Hamida sai kuma mutuwar shi mai gidan naku da har yanzu ba

ki tsara yadda zata kasance ba."

"Na tsara komai Salamatu, zan gaya miki da zarar mun hadu, a yanzu bayan wadannan biyun kuma ina so da Amina idan ta gama yi min aiki akan yarinyar in raba ta da mai gaskiya itama, a fuskokinsu kawai zaki gane kamar rayuwa

na tafiyar musu daidai, ba zan iya basu wannan farin cikin ba Salamatu... Ba zan iya barin Ma'aruf da wani abu mai haske a rayuwarsa ba, so nake har ƙarshen rayuwarsa ya dauwama yana tunanin ni ka

ɗ

ai ce haskensa."

Hajiya Salamatu ta ta

ɓ

e bakinta ka

ɗ

an kafi

n tace.

"Ba zaki canja tunaninki akan yaron nan ba Kilishi, amma wannan

ɗ

in ma daidai ne, ai bai

ɗ

ara daga cikin aikin ki ba, sai dai tsaya... Wane tabbaci ma kike dashi cewa har i yanzu yarinyar nan bata

ɗ

auke da wata hamidar ko kuma Hamidu?"

Kilishi tayi

murmushi mai fadi kafin tace.

"Na dade da bata magani Salamatu, kuma a yadda yarinyar nan ta yarda dani ba zata saba min alkawari ba, abinda zanyi musu ma idan ta gama yi min wannan aikin na Hamidan zai rufe musu ido ba zasu ga komai a rabuwar tasu ba dag

a iyayenta har ita din. Kuma yadda zan raba sun babu wuya, ni na san abinda zanyi, na san abinda zanyi yadda Mai gaskiya ba zai sake kallon yarinyar nan a duniya ba."

Hajiya Salamatu ta gyada kanta.

"Na fahimci har yanzu da saura a harkar nan Kilishi, shi

yasa kika ce zuciyarki ta kasa kwanciya... Amma kar ki damu, tunda kin iya da tarin abubuwan da kika shallake a baya wa

ɗ

annan ma ba zasu yi miki wahala ba, ki cigaba da tsarinki kawai, ina garin nan har sai kaya na sun ƙare, don haka kar kiji komai."

Da ha

ka wayar tasu ta ƙare.

Hajiya Salamatu ta

ɗ

auki jotter da kuma bironta sannan ta miƙe tare da wayarta ta shiga ciki tana barin jug

ɗ

in lemon anan, kuma shigarta kenan bata ko yi minti biyar ba, wata ƴar aikinta mai suna Sadiya ta shigo, ta durkusa har kasa

tace.

"Hajiya kinyi baƙo, yace wai mai karbar kaya ne shi yasa maigadi ma ya barshi ya shigo."

Ta

ɗ

an kalle ta tsawon wasu sakanni tana son tuna wadanda suka yi alkawari dasu a yau cewa za'a zo a kar

ɓ

i kaya, bata tuna

ɗ

in ba don haka sai kawai tace.

"Je k

i shigo dashi."

Ta tashi ta juya ta fita, idonta yabi ta da kallo har ta fita daga ƙofar falon nata da yake na biyu a jerin tsarin gidan.

Minti guda bayan haka Sadiya ta dawo, biye da ita Wani ne da bata ga fuskarsa a karo na farko ba kasancewar ya saka ri

ga irin ta sanyi mai hula ya rufe kusan rabin fuskar tasa, don haka bata sallami Sadiya ba ta tsaya tana kallonsa, idonta akan kofin lemonta wanda ta baro a waje dake rike a hannunsa yanzu, kuma kafin tayi magana yasa hannu ya cire hular zuwa baya, a lokac

i guda fuskar Awwalu ta baiyana a gabanta.

Yana murmushi ya kai kofin bakinsa ya kur

ɓ

a, sai kawai ta

ɗ

agawa Sadiya hannu alamun ta sallame ta, Sadiyar ta juya ta tafi shi kuma ya karaso ya zauna a kujerar dake gefen tata.

"Me ya kawo ka wajena Awwalu?"

Ta

tambaya fuskarta a hade tana kallonsa, da murmurshi a fuskarsa ya sake kurbar lemon sannan ya taso ya fuskance ta sosai yana rike kofin da duka hannayensa biyu.

"Ni ba mutumin banza bane Hajiya, na san ƙawarki, na san Kilishi tun bata da komai a duniyar na

n sai ku biyu ke da

ɗ

ayar da bata magana Saratu... Yau sati guda kenan Kilishi bata kira ni ba, tun bayan da na karbo mata wannan hodar a Lagos, don haka dole na san akwai abinda yake faruwa kuma na san ba zan sami bayani a ko'ina ba sai a wajenki ko kuma

wajen wannan

ɗ

ayar yarinyar da ta shigo da ita cikin al'amarin.

Don haka zuwa nayi ki gaya min ta inda Kilishi ke shirin kashe ni..."

Hajiya Salamatu ta kalle shi tsawon sakanni, cike da mamakin yadda akayi yasha jinin jikinsa game da Hajiya Kilishin tunda

ta gaya mata cewa bata bashi wata dama da zaiyi tunanin cewa tana shirin juya masa baya ba... Kuma ko mutumin da ta saka ya kusance shi mai suna Sadik bai bada damar da zai zarge shi ba har yanzu. Sai kawai ta ha

ɗ

iye yawu a makogwaronta sannan ta girgiza

kanta.

"Ban san komai ba Awwalu, ka tashi ka fitar min daga gida."

Ta ƙarasa tana nuna masa hanyar kofa, sai kawai ya saje wani murmushin yana kallonta, ya girgiza kansa sannan ya sake kai kofin lemon bakinsa, wannan karon ya shanye shi tas! Sannan ya

ɗ

ago

ya sake kallonta.

"Na gaya miki ni ba mutumin banza ne bane Hajiya, ina da abinda zaki miko min Hajiya Kilishi yanzu ba sai anje koina ba."

"Me kenan?"

Ta tambaya tana kallonsa cikin ido. Ya sake wani murmushin yana kallonta cikin ido shima kafin bakinsa

ya sake motsi.

"Kina da labarin inda

ɗ

anki yake?"

Mamaki ya bayyana tar a fuskarta, mamaki irin wanda ke sauka a fuskar mutum lokaci guda, ba shiri bakinta ya furta.

"Wane

ɗ

an nawa?"

Awwalu yana sake wani murmushin da shi kadai ya san ma'anarsa kafin yace

.

"Ɗan da kika haifa tare da mijinki na farko, wanda ya mutu a asibiti ranar da kika haife shi!"

***

_Ku gaya min me yake shirin faruwa ne?_

_Me Awwalu ke shirin haddasawa tsakanin aminan guda biyu?_

_Me ya faru a wancan lokacin?_

_Me Amma ke shiryawa game

da tsarin Hamida?_

_Su Ma'aruf zasu sami Awwalu kuwa?_

_Ta yaya kuke tunanin fa

ɗ

owar Kilishi zata fara?_

_Gashi tana ta lisaafo wasu sababbin tsarikan...

😅

_

_And yes! BabyDoll think they are Pregnant!

😃

.... Ta yaya ake

ɓ

oye ciki ne wai

😅

?_

Littafin nan na

siyarwa ne akan naira #300

Account Details

0251365383

Wema bank.

Aisha Mahmoud Shafii.

Whatapp number 08067794315 ( Domin tura shaidar biya)

#Aysha shafi'ee.

#fikrawriters

#FararWuta.

°°°°°°°°°

*FARAR WUTA 2.*

*©AYSHA SHAFI'EE*

*PAID BOOK*

*15*

*Ina mika

ta'aziyyata ga al'ummar musulmi na rashin babban malamin da muka rasa a yau, Dr Ahmad Bamba BUK. Allah ya jimansa ya kyautata namu zuwa Ameen.*

~~~~

Awwalu ya cije lebbensa, kansa yana gyadawa... Gyadawar da shi kansa bai san yana yi ba, idanunsa sun canja

, dun cika kuma sun yi fayau, suna tsaye akan fasashshen gilashin kofin dake gabansa, kofin da ya tarwatse tun daga lokacin da Hajiya Salamatu ta fe

ɗ

e masa biri har wutsiyarsa game da dukkanin shirin Kilishi akansa.

"... Haukata take shirin yi Awwalu, tace

zaka ƙare rayuwarka ne kana biyan bashin abinda kayi niyyar yi mata, ta shirya komai tare da abokin ka Sadik, zai saka maka maganin bacci ne a cikin wani abu da ka sha ka fita daga hayyacinka zasu

ɗ

aure ka, akai ka cikin gidan gonarja da yake Janguza, ana

n zata je ta same ka, zata yi maka bayanin komsi idan ka farka sannan zata saka Sadik yayi maka wasu allurori a gabsn idonka, tace guda takwas ne, suna nsn tayi odar su zuwa jibi zasu iso, kuma bana tunanin zata bata wani lokaci idan har sun iso din, don t

ana da tarin wadu abubuwan da zasu yi bayan naka..."

A lokaci guda yaji wani abu na cika idonsa, kuma kafin ya lissafa dumin hawayen dake tahowa ya shiga saukowa kan kuncinsa... Yana jinsu, yana jinsu duna fitowa wani na bin wani, cikin gudun dake son kwat

antawa da yadda zuciyarsa ke masa a wannan lokacin, cikin gudun da zaiyi daidai da rawar da yatsun hannayensa ke yi a gabansa.

"Babu abin hawaye anan Awwalu, abinda kuka yi kai da ita yafi karfin hawayen a wasu zukatan, ko ka manta suma wadancan mutane ne

kamar ku?"

Hajiya Salamatun ta tambaya tana kallonsa kai tsaye a gabanta. Sakanni kusan biyar kafin ya girgiza kansa a hankali.

"Baki san komai ba Hajiya, baki san abinda nake ji ba, ba zaki iya kwatanta zuciyata ba watakila sai kin ji naki tukunna...Kilis

hi ta cuce ni, ta cuci dukanninmu, ta cuci tarin al'ummar da har yau bana hango kwakwkwaran dalilinta na yin hakan, na dade da dawowa daga rakiyarta, na dade da nadamar abinda son ku

ɗ

i na ya jawo min, shi yasa na da

ɗ

e da fara gyara rayuwarta.

Ba tun yau ba

na san Sadik yaron Kilishi ne, na san ita ta aiko shi ya kusance ni tun daga lokacin da ta kula na fara canja mata, ina sane na biye masa na ja shi jikina kamar yadda take so kuma nake gaya masa dukkan sirri na, ina sane na gaya masa cewar na shirya kwace

dukiyar da take tarawa kuma na tara hujja ta akanta, ina sane na gaya mata hakan don in san irin tunaninta akaina.

Amma ba wannan ne shiri na ba, don ko kudin da nake samu a wajenta na dade da daina cin su, suna nan a banki ina tara su don na san ba halal

i bane, bayan na gama karatu na sami aikin koyarwa a wata makaranta, da albashi na nake rike kaina bana taba wadannan kudin ko kadan.

Kuma nayi niyyar kawo karshen komai ne saboda na gaji, shi yasa na gayawa Sadik wannan maganar don in san in tsayar da abu

buwa a tsakaninmu kuma in kawo karshenta. Kilishi ta cuci tarin mutane a duniyar nan Hajiya, ta cuci al'umma ta hanyar da bana tunanin ubangiji zai ƙona ta a wuta iri daya da ta sauran mutane, tayi abubuwan da idan ina tuna su a cikin kaina, na kanyi kokwa

nton idan har ba wani

ɓ

angare ne na shaidan ya sauko duniyar nan ba."

Ya juyo ya kalle ta a hankali, hawayen dake fitowa a idanunsa sun tsaya, sai shatinsu daya rage akan fuskar tasa.

Hajiya Salamatu kallonsa kawai take yi da abinda ba zata iya fassara sh

i ba a cikin kanta, duk abinda yake fa

ɗ

a game da Kilishi ta sani, ba tun yau ba ita kanta ta sha wannan tunanin a cikin kanta, tasha fada mata hakan ma cikin magana, amma daga wannan tunanin zuciyarta bata kara komai, tana

ɗ

aukan komai dinne a matsayin lab

ari kawai, bata jin wani emotion ko feeling na tausayi ko kuma na jin ciwon abun a zuciyarta, zata cigaba da harkokin ta ne kawai kamar babu wani abu da ya faru.

Don haka a yanzu ma ba wani abu taji ba, ita ba ta wannan take ba, zuciyarta na rawa ne tare d

a kuma hankoron bayanin da Awwalun ke shirin bata, bayanin da yayi mata alkawari kafin tayi abinda take jin kamar tasa hannu ne ta kashe aminiyarta tata a gabansa.

Kuma har yanzu zuciyarta bata gama kokwanto ba, bata gana kokwanton cewa idan har bs zata ds

uki nasa bayanin ta kai mata ba, don Kilishi kamar wani barin ta ce, bata taba tunanin akwai wani abu da zai sa ta iya sarayar da sirrinta cikin sauki haka a duniyar nan ba, amma idan ta duba ba saukin bane, babu sauki a cikn soyayyar uwa ga danta, ga abin

da ta haifa ko da kuwa bata ta

ɓ

a tunanin da wanzuwarsa anan duniya ba.

Awwalu yasa tafin hannunsa duka biyu ya share hawayen fuskarsa sannan ya sake kallonta.

"Na san har yanzu kina kokwanton ki dauki maganata ki mayar mata, idan na gaya miki naki bangaren

labarin, kwalwarki zata fahimta, watakila ko kadan ne, zaki ji irin abinda naji a zuciyarki, watakila hoton Kilishi zai iya canjawa a zuciyarki da siffar da kike kallonta."

Kuma bai bari ta ce komai ba ya cigaba da cewa.

"Shekaru talatin da hudu da suka w

uce idan baki manta ba a lokacin kika yi aurenki na farko, watanni kadan da kuka kare karatun sakandirenku, ke kika fara aure

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login