Showing 126001 words to 129000 words out of 144990 words

Chapter 43 - FARAR WUTA COMPLETE

cusa kanta tsakanin cinyoyinta biyu tana kokarin goge hawayen.

Banda Jawad ba

bu namijin da ya taba rike ta a duniya, kuma shi nasa daban ne, baya kallonta da niyyar komai, yawanci fushinsa ne ma ke sawa ya rike ta, fushinsa da take mutukar jin tsoro a lokacin, amma a kwanakin nan musamman tahowar da suka yi, idan ta kalle shi a wan

nan yanayin, sai taji kamar ta rungume fuskar sa a jikinta tsawon lokacin da ba zai kara ganin komai ba bayan ita...

_"...zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni."_

Wani abu tsaya a makogwaronta a lokac

in da ta tuno hakan, Jawad bai sani bane amma halayen rayuwa sun sa tun a yanzu ta fara koya...

"Baiwar Allah..."

Muryar wata mace dattijuwa ta sa ta dago da kanta bayan wucewar wani lokaci, fara ce, farin da bata sani ba idan na gaske ne ko kuma wanda ta

samawa kanta, fuskarta dauke da fara'ar da ta sa a lokaci guda tasa bayan hannunts ta goge hawayen dake kan fuskarta.

"Ance min taimakon kudin mota kike nema ko?"

Ta sake tambaya da wani murmushin, kuma kafin ta bata amsa ta cigaba.

"Gidan abinci ne dani a

nan baya, kuma almajiran dake min wanke wanke bai zo ba yau, idan zaki yi in biya ki kinga sai ki samu ku

ɗ

in motar ko?"

Babu shawara ta biyu tunanin Zainab ya amince da hakan, bata ga aibun hakan ba, bata ga komai ba... Don hausawa sun ce wanda yake ruwa a

ka miƙa masa takobi kamawa zai yi, ƙafafunta suka mike a daidai lokacin da nasa suka ƙaraso wajen.

*

"Kace ta san sunan garin ko?"

Jawad ya tambaya a cikin gudun  da motar ke yi, gudun da suke yi daga gefen titi wajen da babu komai sai kasar dake tashi a b

aya da zarar sun wuce.

Nura dake zaune a gefe ya gyada kansa.

"Ta sani, haka Baban ya gaya min cewa ai tun da da

ɗ

ewa ta san sunan garin.

"Kuma ka tabbata babu wata tasha da ake zuwa garin sai wannan da zamu je?"

Ya sake tambaya yana zura hannunsa a cikin g

ashin kansa.

Nura ya sake gyada kansa.

"Ita kadai ce a kusa yallabai, ita kadai ce wadda zata iya zuwa, kuma gashi ma Isa ya tabbatar mana da cewar ya ganta akan hanya..."

Jawad ya cije lebbensa na kasa, hannunsa ya sake danne sitiyarin motar da babu shiri

suka kara figa da gudu,  Abdallah

ɗ

an wan Hajiya Salamatu wanda bata yarda da tafiyar Jawad ba sai da ta turo shi ya biyo shi yayi magana daga inda yake zaune a bayan motar.

"Easy mana bro,zamu isa yanzu ai Insha Allah."

Jawad ya girgiza kansa.

"A kowanne

lokaci mota tashi take yi a tasha zamu iya sabanin ko kuma minti daya ne Abdallah. Tun yaushe ta fita, tun safe fa yace badu ganta ba."

Nura ya gyada kansa.

"Amma ai da tazarar tafiya,ta dauki lokaci kafin ta isa na san sannan kuma bata da kudi a  hannunt

a, sai da kowa ya caje kudinsa a gidan yau duka bata dauki ko sisi ba, kaga kafin tayi abinda zata samu kudin mota shima wani lokacin ne don haka za..."

"Me zata yi ta samu kudi?!"

Ba shiri Jawad ya katse shi yana daga muryarsa, kafin ya juyo da fuskarsa y

ana kallonsa.

"Me zata yi ta samu kudi a cikin tasha Nura? "

Kafin Nuran ya amsa, wayar Abdallah tayi ƙara a hannunsa ya dauka ya kara a kunnensa da sallamar da Jawad ya riga ya san ko wacece, Hajiya Salamatu... Don tun daga lokacin da suka sauka daga jirg

i a Kaduna suka je gidan abokinsa suka

ɗ

auko motarsa da ya bari a can, ta kira shi da kuma Abdallah fiye da sau goma, sai da ta fahimci shi yake tuƙin motar sannan ta koma kira Abdallahn.

Zai rantse da Allah a lokacin da ya gaya mata cewa zai taho Kaduna a

yau, kalar tashin hankalin da ya sauka a idanunta iri

ɗ

aya ne da wanda ya gani a idanun Hajiya Mardiyya kafin tahowarsa... Tsoro ne karara da kuma taraddadin rasa shi, wani abu da ya kara bashi tabbaci na cewar da gaske ita mahaifiyarsa ce Uwa wadda babu

makamanciyarta a duniya, tunda a kwana daya rak da ta san shi har zata iya tarayya da halin da wadda ta raine shi tsawon shekaru ta shiga wajen tunanin rasa shi.

Har hannunta ya riƙe ya gaya mata cewa zai dawo su tafi can Abujan tare kamar yadda ta tsara h

ar ma da wasu ƴanuwanta, tana gaya masa cewa akwai tarin wasu yanuwan nata da zaau zo wajensa a yau daga Gombe shima yana gaya mata cewa baya fatan abinda zai kaishi ya

ɗ

auke shi tsawon wani lokaci.

Bai gaya mata ba, bai gaya mata abinda zaizo yi ba kamar

yadda shima Abdallahn bai gaya masa komai ba, kawai ya tsinci labarin ne bayan sun dauko Nura a cikin irin maganganun da suke yi na zuwa nemanta.

"Bamu karasa ba har yanzu Aunty muna hanyar..."

Abdallah ya fa

ɗ

a a cikin wayar yana dawo da hankalin Jawad kan

halin da suke ci kuma a sannan ne suka fara hango tashar, daga can saman wani waje da ya danyi tudu alamar tsanuni ne a wajen tunda hayar tana da hawa da sauka da yawa.

Ya cije lebbensa na kasa hannunsa ya sake danne kan motar a lokacin da Abdallah ke cew

a.

"Insha Allah Aunty, insha Allah za'a ganta..."

Ya sauke wayar sannan ya shiga sake tambayar Nura sunan wajen da kuma tazararsa da cikin garin Kaduna, sai dai Jawad baya ko jinsu idanunsa dama duk wani abu mai motsi a jikinsa sun tafi ne ga bakin tashar

nan, baya ko damuwa da gudun da yake yi ganin ya fara shigowa cikin mutane.

Tayoyin motar suka tsaya tun kafin ya ƙarasa kofar tashar, kuma ya fito a lokaci guda da motar ta tsaya yana rufe kofar motar, su Nura suka biyo bayansa suka nufi ciki gabadaya, ta

rin mutane da kuma

hayaniyar dake faruwa a ciki ta cika kunnen Jawad kota wanne bangare, wata yarinya ya fara hangowa dauke da kaya, kammaninta suka koma ba Zainab sak a idanunsa.

Har ya fara tafiya sai ya hangi wata irinta itama daga wani gefen, ya ga wat

a da goyo sannan ya ga fuskoki da yawa daga cikin wata mota duk irin nata, sai kawai ya ja ya tsaya, ya tsaya daidai lokacin da Nura ke tambayar wani inda ake samun motocin Sameru.

"Wallahi maigida nima matafiyi ne ban sani ba, sai dai ko ku gwada tambayar

wancan na ganshi da rigar ƴan union."

Yana fa

ɗ

a yana nuna wani ma'aikaci dake aiki daga can gefe, kuma Nuran ne kadai ya tafi yana ganin kwatancen da mutumin yayi masa tun daga can, kuma tun daga can

ɗ

in ya gane, don haka kafin ma Nuran ya dawo ya riga ya

yi cikin tashar Abdallah na binsa a baya.

Mutum biyu suka samu akan wata mota dake kan layi kuma duk irin tambayar da suka yi musu kai tsaye suka nuna cewa basu ga yarinya mai makamancin kwatancen da suke yi ba.

"Amma bari a kira Sani, sune a wajen da safe

, watakila bakuwar taku da safe tazo."

Dayan ya fada yana yin gaba zuwa wani gini daga gefe. Dayan ya kalli Jawad sosai yace.

"Yalla

ɓ

ai wallahi kar ku saka rai, tashar nan sai mutum dari su zo a kasa da minti goma,wani ko fuskarsa ba zaka kalla ba zaka kar

bi kudinsa ka tambayi sunansa... Da ka rubuta shikenan kai dashi har abada, to ta yaya za'a iya gane wata yarinya?...."

Bai ƙarasa maganarsa ba sai ga daya ya dawo tare da mutumin da aka kira da Sanin, yana tsayawa tun kafin ma Jawad ko Nuran su ce wani ab

u ya tambaya.

"Yallabai farin hijabi ne a jikinta..."

Jawad ya daga kansa da sauri yace.

"Ofcourse bata da tsawo sosai..."

Sanin ya daga kansa shima.

"Ai bata je ko'ina ba, bata hau mota ba, tazo inaga kamar bata da kudi ne saai kuna ta tafi. To bayan haka

n kuma sai na ganta a zaune a wajen shagon Ashiru, amma wallahi tun

ɗ

azu ne, ban sani ba yanzu ko za'a same ta..."

"Ina ne wajen? Nuna mana wajen kawai..."

Cewar Nura.

Mutumin ya shige gaba, dukkaninsu suka bi shi a baya zuwa daya bangaren tashar wajen da

ake lodin motocin dake karasawa cikin Kadunan, Jaji zuwa Kawo.

Kuma Ashirun da Sanin ya ambata shi suka fara gani a wajen yana

ɗ

aukan sunayen wasu mutane a cikin mota. Basu san me Sanin yace dashi ba, don shi ya fara ƙarasawa kafin su, idon Jawad na kan As

hirun a lokacin da yake gyada kansa yana nuna wata hanya da ke gefe don haka bai ko ƙarasa wajensu ba ya yi hanyar.

Ya isa daidai jikin wani shago lokacin da idonsa ya hango masa ita a lokaci gudataa mikewa da aamun zata bi wata farar mata dake tsaye a gab

anta tana yi mata murmushi.

Ta juya bayanta tana fuskantar matar, bata ga tahowarsa ba balle ta ganshi, don haka bai jira komai ba ya ƙarasa da taku biyu ya riko hannunta, yatsunsa suka lankwasa a tsakanin nata tun kafin ta juyo a lokaci guda da ta kalle s

hi, ta kalle shi da idanunta a zare da tsananin tsoron da cikin sakanni biyu kawai ya juye zuwa mamaki.

"Jawad...??"

Bakinta ya furta a hankali yayin da zuciyarta ta buga sau

ɗ

aya, ta buga da wani sauti da ta tabbatar da cewar dukkan sauran mutanen dake za

gayensu sun ji shi. Ba shiri idanunta suka cika da shekin kwallar da bata san ta ina ta fito ba, mamaki take idan shi din ne ko kuma mafarki take yi... Don tunaninta ya kasa bata cewa zai iya zuwa ya same ta a wannan wajen kuma a wannan lokacin.

Sai dai ba

bu wani bata lokaci, yayi abinda ya tabbatar mata da cewar da gaske shi din ne ba wani ba, da gaske Jawad din da ta sani ne...

Hannayensa duka biyu suka zagaye jikinta, ya rungume ta a cikinsu, ya rungume ta a kirjinsa, ya rungume ta a gaban tarin mutanen

dake wajen ba tare da tunanin komai ko kuma abinda za'ace ba..

Sai kawai ƙwallar da ta cika idanunta ta zubo kan fuskarta, ta riga ta sani komai ya zo ƙarshe, wahalar da take tunani ta yanke tun kafin ma ta fara, shikenan tayi sallama wa dukkanin wahalarta

!

***

*03:15 am.*

Tana tsaye daga jikin tagar dakin, hannayenta duka biyu dafe da gilashin da aka rufe yagar wanda ta manna fuskarsa a jiki yayin da idanunta ke tsaye ƙyam! Akan wanda ke kwance a akan gadon dakin, ance mata Ma'aruf ne, kowa yace mata shine

, amma fiye da minti goma da take tsaye a wajen babu wani abu a kwakwalar ta da yatuna mata cewar Ma'aruf din da ta san shi take kallo.

Fuskarsa a kumbure take idan ka dauke katuwar robar zukar numfashin da aka manna a fuskarsa da kuma gashin kansa da aka

aske, wannan sumar... Wannan sumar ta Ma'aruf da kullum take tare da hannaensa, yanayin yadda yake cusa su a ciki kadai Kala-kala ne ta yadda ta kan fahmci wani abun da yake nufi idan yayi tun ma kafin ya furta.

Don haka gaba

ɗ

aya kamanninsa sun canja ta ya

dda ko ba'ayi wa mutum bayanin rashin lafiyar dake damunsa ba shi da kansa zai kintata tun daga harafan dake rubuce

ɓ

aro-

ɓ

aro akan gilasan wajen da launin ja... ICU.

Wani abu ya wuce ta makogwaronta lokacin da ta tuna da san da ta farka ta riski labarin ko

mai... fuskar Amma ta fara gani kafin komai, tana zaune daga kujerar dake gefen gadon da take kwance, hannunta rike da wani carbin ta kalar yalo, wani carbi da a cikin su gaba

ɗ

aya babu wanda zai iya fadar adadin shekarun da suka san shi a hannunta, dashi t

ake lazimi kulum, a kowacce safiya da kuma yammar Allah.

Ta rufe idanunta a hankali sannan ta sake bude shi tana kara kallon Ammar da kanta ke sunkuye tana addu'o'in ta, yanayin sai ya koma mata iri

ɗ

aya sak da wani lokaci a can baya, lokacin da Maryam bat

a da lafiya, lokacin da suke zaman jinyarta a asibiti, haka Amma ke zama a gaban gadonta da wannan carbin tana lazimi.

Fahimtar cewa yau itace ba Maryam din ba ya dawo mata da zagayen halin da take ciki, ya tuno mata da dukkan abinda ya faru kafin sumanta

da ma irin tashin hankalin da ta shiga...

Ko kuma tashin hankalin da har a yanzu ta farka a cikinsa, tunda bata san me ya faru ba har a lokacin, bata san ina Ma'aruf yake ba sannan bata san a wane hali yake ciki ba, tun a lokacin aga yanayin fuskokin su Mu

nayan da suka shigo wajenta tunaninta ya gaya mata cewa abinda ya faru ba labari ne mai da

ɗ

i ba, sannan a lokacin ta ƙara tabbatar da cewar da gaske tunaninta hakan ne tunda bata ganshi ba.

Ta sake bude idonta a hankali, lokaci ya nuna mata ƙarfe goma sha

biyu na safiya wanda hakan ya tabbatar mata cewar har a yanzu tana cikin wannan ranar ne tunda da sassafe ne lokacin da su Munaya suka zo suka same ta.

Ƙ

ofar

ɗ

akin ta bu

ɗ

e a sannan, Aunty Ma'u ta shigo bayanta goye da ƴar ƙaramar ƴar ta, hannunta da rike d

a wani a kwandon kwanukan abinci.

Amma ta amsa sallamarta tana juyawa.

"Bata farka ba dai ko?"

Ta tambaya tun kafin ta karaso.

"A'a har yanzu, amma Nurse din da ta fita tace ba zata dade ba zata farka."

Aunty Ma'u ta ajiye kwandon abincin sannan ta sauko h

oyon yar tata dake bacci Amma ta karbe ta.

"Su Tanti suna hanya, tace akan kwana suka hadu da Safiyya yanzu zasu taho."

Kuma sai da ta zauna daga gefen gadon sannan tace.

"Ya muka ji da wadannan abubuwa da suka faru Amma? Labari haka rana tsaka babu da

ɗ

in

ji..."

Amma ta gyara kan yarinyar dake cinyarta tace.

"Wallahi Ma'u muma haka muka tashi da kira wai an kawo ta asibiti ta suma, yanzu su Maryam suka koma su ma tare da yariyar dake wajenta Hamida, don likitan yace da ta farka zamu iya tafiya, rashin kwari

n jikinta ne yasa suman ya same ta a lokaci guda."

Aunty Ma'u ta gyada kanta tana sake kallon Aminan dake kallonta ta tsakanin gashin idonta.

"Inalillahi wainna ilaihir raji'un...  Ɓari fa akace ta kusa yi Amma, wannan wane irin labari suka gaya mata?"

"Su

wa

ɗ

anda muka tarar anan sun ce ai tun kafin ma su san wannnan al'amarin aka kawo ta asibitin.  Komai ya rikice ne kawai Ma'u don ita kanta Tantin da muka yi waya ban iya gaya mata wani abu ba tunda har yanzu su ma babu wanda ya gama sanin abinda ake ciki,

Munayan tace min sun san dai an tafi da ita Kilshin wajen ƴansanda daga asibitin nan, shi kuma an kwantar dashi."

Aunty Ma'u ta gyada kanta.

"Irin wannan sai an kwana biyu dama za'a san me ake ciki tunda su kansu yanzu hankalinsu ba'a jikinsu yake ba."

Am

ma tace.

"Duk sun taho ma, har da ƴarta daya Sameerah, suran ne suke can gida tare da wasu yanuwansu don Mama Rabin da na hadu da ita tace gidan ya zama kamar na makoki daga safiya zuwa yau..."

"Allah ya kyauta, ni wallahi banyi mamaki ba Amma, a wannan za

manin jama'ar da suke da fuska biyu wajen cutar al'umma suna da yawa, kuma ba ma wai sai a wani babban abu ba, wani ko ba zai samu komai ba idan ya nuna baya kaunar ka a bayan idonka zai ji da

ɗ

i, kawai dai ita nata yayi yawa ne, cuta da kuma zaluntar ciki

tafi karfin tunanin mutane ire-irenta da yawa.."

Amma ta yi shiru kafin tace.

"Zancen babu da

ɗ

in ji Ma'u, iya wanda ya fito a yanzu ka

ɗ

ai balle kuma abinda zai fito daga baya, ƴan uwanta ma wasu basu yarda ba, abin ne kamar mafarki, kamar labari...  Sai da

i addu'a kawai."

"Allah ya kyauta, Allah ya basu hakurin

ɗ

aukar hakan ya bi musu hakkinsu, sai a godewa Allah don watakila da lokaci ya ja, zata iya aikata fiye da wanda tayi ma a baya."

"Wannan haka yake, don al'amarin yafi karfin tunaninki, Allah ya bata

fikira da kuma dabarar da ta bari shaidan ya karbi linzaminsu."

Ƙ

walla ta cika idanun Amina a lokacin tana hana mata ganinsu baki

ɗ

aya sannan tunaninta ya cilla kan maganganunsu tan son fahimtar da kanta abinda bata gane ba... su waye suka yi hatsari? Wand

a take nufi an kawo asibitin Ma'aruf ne? Abinda su Munaya zasu gaya mata kenan? Abinda ta kasa tsayawa ta ji kenan? An kama wani? Hajiya Kilishi ce? To ta yaya hatsarin ya faru? Komai yazo ƙarshe kenan? A wane hali su Samirah ke ciki? Baffa... Sauran mutan

en gidan.... Ma'aruf ma...

Wadannan tambayoyin su suka yi ta haskawa a cikin kanta har lokacin da taji Amman tace.

"Bari na sake lekawa can inda aka kwantar dashi naga me ake ciki dama jiran ƙarasowar ku nake kar a bar ta ita ka

ɗ

ai."

Ta fa

ɗ

i hakan sannan t

a miƙe tsaye ta juya kan wata kujera daga can jikin bango ta ajiye yarinyar.

Amina bata ga sanda ta fita ba ta dai ji ƙarar rufewar ƙofar da kuma muryar Aunty Ma'un bayan nan tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login