Showing 96001 words to 99000 words out of 144990 words

Chapter 33 - FARAR WUTA COMPLETE

fahimci cewa matsalar daga ina take ba amma kuma ya fahimci dukka

n kudirina, kuma ya gaya min zai taimaka, don haka yanzu duk bayan kwana biyu zai dinga rubuto takardar magunguna daga adibiti na yara da suke shaida ciwon ido, a hankali, a hankali ana yin gaba yana kara rubuta cewa ciwon yana habbaka._

_Maryam zata dinga

kawo miki takardun duk bayan wani lokaci kina kai mata da cewar yarinyar ta fara ciwon ido... Rayuwar mace dabara ce Amina kuma Kilishi shaida kawai take nema a yanzu ba zahiri ba Amina, Kilishi tana wani matakin da ba zata saka ido akan al'amura ba yanz

u, saboda ko ba'a fa

ɗ

a ba kin san binciken da suke yi akanta yayi nisa. Don haka a yanzu kamar tana kokarin tattare abubuwa ne don tayi ta gama karasa manufarta kawai._

_Bayan haka kuma, idan kin lura al'adar Kikishi cewar bata da bin diddigi, da ta fahimc

i abinda take so ya faru shikenan kawai zata gama da wannan babin, na fahimci haka tun daga ranar da ta yi miki alkawarin tafiyar su Aminu India a lokacin da aka kira ta da bayanin Ma'aruf yana asibiti kafin ma ta ganshi.Don haka ki kwantar da hankalinki A

mina, komai zai tafi daidai insha Allah."_

Kuma da wadannan kalaman hankalin nata ya kwanta, don kamar yadda Amman tace ne a yanzu hidimar dake gaban kilishi daban ce ita kanta ta lura, don ko a yanzu ma bata gidan tun dazu ta fita ba tare da kowa ya san i

na ta tafi ba, wani abu da ya bawa kowa mamaki kenan, don da wuya ne idan ana hidima irin wannan ta sanya kafarta ta fita, hatta ƴanuwan Hajiya Maimuna da suka zo kowa sai da yayi ta tambayarta ana sa ran dawowarta da wuri amma har yanzu.

Wani abu da a waj

en Amina yayi mata da

ɗ

i sosai, don a kullum tana son irin wannan tazarar ta dinga faruwa tsakanin Kilishi da kuma farin cikin ahalin gidan.

Sai da ta kammala komai a bangarenta sannan ta taho cikin gidan, inda anan ta tarar har wasu daga cikin ƴanuwan Haji

ya Maimuna sun iso ana ta hidimar tarar Abdurrahim

ɗ

in da Ishaq yayi waya yace ya sauka gasu nan a hanya.

Basu yi waya da Ma'aruf ba tun dazu, bai kira ta ba kuma itama bata kara kira ba, don ta fahimci kwana biyu aiki yana yawan yi masa yawa, shi yasa bat

a so ta zama sanadin katse shi a komai, kamar yadda Amma ta gaya mata ne kamata yayi ta zama nutsuwar da zai dinga hanƙoro a duk lokacin da hankalinsa ke juyowa zuwa gida.

Don haka ko a yanzu ma da aka ce sun taho, bata kira shi ba ko kadan, aiki suke tayi

na kokarin ha

ɗ

a miyar taushen da aka manta da ita kwata-kwata, anyi masar tun rana amma sauran sha'anin su Samirah ya mantar dasu miyar sai a yanzu sannan aka hadu gabadaya ake kokarin gamawa kafin karasowar tasu.

"Mami...."

Hamida ta sake kira sanda ta k

araso gabanta da gudu. Amina ta juyo daga yankan alaiyahun da suke yi ita Munaya.

"Su Aunty Sahla sun ce dan Allah in tambayeki su canja min kaya?"

Ta fada muryarta na fitowa kamar haki alamun ta dade tana neman nata cikin mutanen gidan.

"Kaya Hamida? A in

a suka sami wasu kayan?"

"Su suka

ɗ

inka a School

ɗ

insu...!"

Ta fa

ɗ

a da sauri tana katse ta. Kuma kafin tayi magana Munaya tace.

"Wannan shirmen nasu zasu saka miki Hamida... wannan karkatacciyar rigar da suka dinka?"

Tana fadin haka Amina ta gane kayan da

take nufi, don itama har wajenta suka shigo suka nuna mata da murnarsu, rigar bata yi kyau ba sam!

"Wallahi Aunty Munaya tana da kyau... Pink ce fa!"

"Hamida ki bari idan Dadynki yazo sai ki tambaye shi kinji? Zai fi so ki fara tambayarsa tukunna.."

Amina

tayi mata wayo ta tsaya kanar bata yarda ba sai kuma ta gyada kanta sannan ta juya da gudu.

"Har yanzu ina mamaki da akace wai yarinyar nan tana da cutar rashin son mutane da yawa, gashi nan yanzu tagane kowa a gidan nan kuma ta saki jikinta."

Munaya ta fa

da tana kallo ta ta cikin ymgayaniyar sauran mutanen dake shige da fice a kitchen din du Mama Rabi, sai kawai Amina tayi murmushi tace.

"Bata son ta rabu da ita ne kawai, kin san

ɗ

a da uwa."

Munaya ta ta

ɓ

e dan karamin bakinta tana gyara zaman glass dinta t

ace.

"Ba wani kula fa take yi da ita ba, ba zuwa muke yi ba amma mun sani, atbfirst ma ba'a hannun ƴar aiki Yayan ya samo ta ba? Sai gashi kuma sun dawo da ita da kansu, sannan ko ita yarinyar ba kya ji tana nemansu."

"Haka ne." Amina ta fada a hankali ida

nunta na hasko mata hoton wannan layar, da kuma fuskar matar da aka aiko takanas har cikin gidanta, har yanzu basu sake cewa komai ba, basu sake yin wani abu ba, bata sani ba ko haƙura suka yi ko kuma suna shirya wani sabon shirin ne, zata so idan har ma b

asu haƙuran ba su cigaba da

ɗ

aga musu ƙafa har zuwa lokacin da abubuwa dake gabanta a yanzu zasu yi sauki, don haka gudun kar Munaya ta cigaba da maganar yasa ta tsokane ta da cewar.

"Ina fata dai kin ajiyewa Yaya Ishaq nasa special abincin?"

Kuma murmushi

n da Munayan tayi yasa ba shiri ta taya ta itama.

Da misalin ƙarfe tara daidai na daren, motoci guda biyu na Ishaq da kuma Ma'aruf suka shigo gidan, a lokacin sun kammala komai, jiran baƙon kawai ake yi,bakon da sai a yau Amina ta fahimci irin kewarsa da a

l'ummar gidan suka dade suna yi bakidaya,a da yadda kowa ke harkokinsa ba'a zancensa sai jefi-jefi sai taga kamar basu saba dashi bane ko makamancin hakan, amma yanzu ko zuwan wasu daga cikin yanuwan Hajiya Maimuna ka

ɗ

ai ya tabbatar mata da matsayinsa a zu

ciyarsu.

Tana kitchen ita da wasu ƴaƴan Yar Hajiya Maimuna sanda suka shigo gabadayansu bayan sun baro bangaren Baffa inda nan suka fara danganawa dashi. Taji yadda falon Hajiya Maimuna ya ru

ɗ

e da hayaniyar murna kala-kala wadda bata ko gane me ake cewa.

H

annunta riƙe da farantin da aka jera kofunan kemo suka fito tare da sauran, kuma a lokaci guda idanunta suka lalubo Abdurrahim din, fari ne, fari ne sosai duk da bai kai Jamal din da take ganin hotonsa a wajen Ma'aruf ba, sannan yana kama da Ma'aruf din so

sai, yanayin idanunsu da sumar gashin kansa da shima ya tara, sai murmushi yake yi zaune a kusa da Hajiya Maimuna dake kan kujera yayin da kowa ya yanyame shi da sakon gaisuwarsa.

Ma'aruf na tsaye daga bayansu riƙe da Hamida wadda ta makalkale shi, idonta

ya kai kansu sanda Hamidan ke lalubo kunnesa tana rada masa wani abu da ta san ba zai wuce zancen rigar ba, a idanunsa ka

ɗ

ai ta fuskanci tarin gajiyar da ba sai ya furta mata ba.

Sai kawai tayi masa murmushi ta karaso cikin falon suka gaisa da Abdurrahim d

in, bata ji muryarsa sosai ba amma taji kamar ya amsa da 'Lafiya' a hankali, kuma da yake bai santa ba shikenan abinda tace sannan ta juya kitchen din da niyyar dauko wayarta, a lokacin Hamida ta taho da gudu zuwa gabanta.

"Mami, Daddy yace inje a saka min

kayan kuma yace dan Allah shima ki zo ki canja masa kayans..."

Hannunta tasa da sauri ta rufe bakinta don da ƙarfi take maganar sannan ta juyo tana kallon Ma'aruf din da ya juya yana yiwa Ishaq da ya shigo a lokacin magana, ta yaya zai gayawa yarinya wann

an maganar?

Hamida bata jira taji me zata ce ba ma ta fita daga hannayenta ta tafi wajensu Sahlan da saƙonta tana murna, a lokacin ne kuma taji muryarsa yana tambayar Surayya da tazo wucewa.

"Ina Mami?"

Tambayar ta fito daidai lokacin da wani al'amari ya f

aru daga can falon Baffa, inda yake zaune a gaban talabijin

ɗ

in dake ci a gabansa yana kallon labaran NTA na ƙarfe taran dare, a hannunsa guda robar robb ce da yake shafawa a ƙafarsa ta hagu.

Zuciyarsa a cike take da tsananin murnar dawowar Abdurrahim, a

kowanne dare da kuma wayewar garin Allah fatansa baya wuce ganin iyalansa sun ha

ɗ

u waje guda, a kodayaushe yana daga cikin addu'arsa cewar kar Allah ya

ɗ

auki rayuwarsa ba tare da ya ga haduwar iyalansa waje guda ba, duk da cewar ya san akwai wani gi

ɓ

in da

har abada ba zai ta

ɓ

a cikewa a zuciyarsa da ma ta sauran al'ummar gidan ba... Jamal.

Wayarsa tayi ƙara daga kan kujerar da yake jingine a bayansa, ya miƙa hannunsa ta gefe ya dauko ta, sabuwar lamba ce da b sant ba don haka ya

ɗ

auka yasa a speaker...

Mury

ar wani dattijo ta fito daga cikin wayar a lokaci guda.

"Barka da dare yallabai... Ina magana ne da Alhaji Muhammad Mansour Bakori?"

"Barkanmu dai, Eh Ni ne Mansour."

Ya fa

ɗ

a yana ajiye robar robb

ɗ

in dake hannunsa... Kuma kalaman da suka biyo, kalamai ne

da babu shiri suka tsayar da duk wani tunani a cikin kan Baffa.

"Ranka ya da

ɗ

e suna na DPO Umar Nasir, matarka Hajiya Kilishi tana nan tare dani!"

***

*Washegari.*

*Ƙarfe shida da rabi na safiya.*

Motar na tafiya ne a wani irin yanayi da Zainab ta ƙasa gan

e gudu Jawad ke yi ko kuma akasin sa, idanunta na manne da titin dske gabansu yayin da take ji zuciyarta na bugawa a kirjinta da sautin da zata iya rantsewa cewa yana iya jinsa daga inda yake zaune.

Hannnusa ne guda akan sitiyarin motar ya danne shi da ƙar

fin dake baiyana a ido, yayin da ƙafafunwansa ke ƙara take motar suna shillawa akan titin da bata san ina zai dangana dasu ba. Ƙarar sautin shigowar kira a wayarsa yafi ƙirgen da zata iya tunawa, bai

ɗ

auka ba, bai kashe kiran ba ko ma wayar gaba

ɗ

aya, yi ka

wai take tana sakewa kamar ƙarar motar agaji,(ambulance).

Ta hadiye rawu a cikin maƙogwaronta a hankali tana sake matse yatsunta a cikin hijabin dake jikinta, wannan dogon hijabin sabo da ya bata, shi ta saka tayi sallar asubahin yau, sallar da tana sallam

ewa Jawad ya shigo dakin, kuma bai jira komai ba yace ta taso ta biyo shi.

Bata san me yake nufi ba, bata san ina zasu ba don haka ta taso ta biyo shi

ɗ

in zuwa cikin falon da komai yana nan kamar yadda yake a jiya, kayan abincin dake kan dining suna nan ha

r a sannan babu wanda yabi ta kansu, bata ko bu

ɗ

a su ba tun a jiyan, daga su har ledar magungunan da yace mata taje tasha suna nan a wajensu.

Don babu yadda za'ayi ƙafafunta su iya dauko ta daga inda ya bar ta a jiyan zuwa cikin falon, tasirin maganganun d

a ya gaya mata kafin ya fita su suka manne ƙafafunta a inda ta tsaya kuma suke ta maimaitawa a cikin kanta, maimaitawar da duk zagayen da tunaninta ke yi ya dawo a waje guda yake tsayawa, waje gudan da har a yanzu da garin Allah ke kokarin wayewa abubuwan

da ta gane a ciki basu da yawa, don bayan ma kankantar tasu, ita shaida cewa ko giyar wake aka taru aka sha a garin tunaninta baya hango kasancewarsa.

Aure ba ƙaramin abu bane ta sani, ana yinsa kullum, cikin kowanne sati na duniya, amma duk da haka yana d

a wani irin girma da kuma darajar da ubangiji ya

ɓ

oye a cikinsa, shi yasa har kullum yake kamar baƙo a zukatan al'umma, idan za'a gama yau a fara wani gobe, na goben zai zo ne da wani sabon farin ciki da kuma doki a zukatan masu yinsa.

Aure abu ne da rayuw

ar mutum ke tafiya gabadaya akai, rayuwar da zata mamaye farko har zuwa ƙarshe na kwanakin ka a duniya, shi yasa har yanzu bata ga dalilin Jawad na cewar zai aure ta ba don bata ga wani abu da take dashi a duniyar nan da zai iya hada rayuwarsa da tata ba.

Bayan haka ma, ita bata jin cewar tana sonsa, zuciyarta ta riga ta gama tsorata da tarin abubuwa, tun daga rayuwar da ta baro har zuwa wadda take yi a yanzu, sannan shi kansa tsoronsa ya fara dasawa a ranta, tsoron da a yanzu bata san ta yaya zata iya juya

shi ya koma wani abu daban ba....

_"Ko ke baki da za

ɓ

i yanzu Zainab, zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni..."_

Ta rufe idanunta a hankali tana tuna sanda suka iso wajen motar tasa yace mata ta shiga

, a lokacin ne kafafunta suka tsaya waje guda cak! Ta tsaya daga daidai bayansa tana tambayar ina zasu tafi? Ina zai kaita a wannan safiyar ba tare da Hajiya Mardiyya ta sani ba ko kuma ta bata izini.

Abinda tayi dana sanin tambaya kenan tun daga kirgen wa

ncan lokacin har zuwa yanzu, don yadda ya tsaya a gabanta ya rike hannayenta duka biyu da iya karfin da take tunani nasa ne, ya gaya mata cewar baya son  baya son sake jin muryarta kawai tayi dukkan abinda yace, da wani yanayi ne da zata rantse bata ta

ɓ

a g

ani a fuskar wani mahaluki ba, don sandan hannayenta duka biyu suna zafi da tasirin riƙon da yayi mata. Shi yasa bata ƙara cewa komai ba har a yanzu da suka yi nisa cikin tafiyar da bata san ina ne ƙarshen ta ba.

Zuciyarta na faman bugawa ne cike da tsoron

irin tarin laifin da yake kara mata a wajen Mahaifiyarsa, Hajiya Mardiyyan da tun a jiya ta bata umarnin ha

ɗ

o kayanta don ta maida ita garinsu, da kuma Deluwa matar da ta kawo ta gidan, don bayan rashin mutunci Dekuwa gar azaba tana yiwa duk yarinyar da t

a kai gidan aiki ta gudu...

Tunaninta ya tsaya a lokacin da motar ta tsaya kusan a lokaci guda, kusan a lokacin gudun da tasirin hakan yasa tayoyinta gaba daya suka fitar da wata ƙara da ta cika kunnuwan su da suke ciki ma, kuma kafin Zainab ta sake wani t

ayi wani tunani ya

ɗ

auki wayarsa da har a lokacin ke ƙara ya jona da wata waya dake jikin motar.

"Jawad, Jawad... Jawad..."

Muryar Aunty Sadiya ta cika speakers

ɗ

in dake cikin motar a take, daga bayanta hayaniya ce mai yawa ke tashi yayin da sautin kukan d

a babu shakka na Hajiya Mardiyya ne ke barazanar fin muryar tata karfi. A lokaci guda Zainab taji cikinta ya hautsine.

"Jawad kana ji na? Kana ina? Ina ka tafi?"

Tambayar ta shiga kunnen Jawad da sigar rainin hankali, ina ta tafi? Ina suke tunanin zai tafi

bayan inda suka gaya masa?

A daren jiya har wajen ƙarfe biyun dare ana case din da yake gani da jin sa tamjar a mafarki, bayan ya shaidawa Alhsji Bashir komai, shi da kansa ya karbi wayar hannunsa, ya kira ƴansandan da shi ya kira ya tsayar daau daga zuw

a gidan. Sannan shi da kansa ya kira mijin Aunty Sadiya yace ya kawo ta gidan a lokacin, bayan haka, ya kira dukkan sauran ƴanuwan Hajiya Mardiyyan da suke a garin yace suma yana bukatar ganinsu, kuma cikin abinda bai haura awanni biyu ba dukkaninsu su hu

ɗ

u suka hallara, mata biyu da yayyensu maza biyu.

Hajiya Mardiyya itace ta karshe a kiran Alhaji Bashir din, alokacin ta kira wayar Jawad dake rile a hannunsa fiye da kirgen mai kirga, don tana ta nemansa a cikin gidan, bangaren Alhaji Bashir

ɗ

in ne kawai b

ata zo ba don watakila tana tunanin bata da kwarin gwiwar fuskantarsa a wannan lokacin, amma sai gashi kafafun nata sun kawo ta, kuma a lokacin da ta shigo tayi arba dasu, ƴanuwanta har su hudu cikin wannan dare da kuma shi da Alhaji Bashir

ɗ

in dake mata k

allon da babu bukatar asarar kalmomi, sai gashi ta samu kwarin gwiwar ƙarasowa har gaban nasu.

Kuma a jiyan yaji komai, yaji dukkan wani bayanin daga bakin ita da kuma Aunty Sadiyan da suka fahimci tabbas dubunsu ta cika zuwa wata dubun.

Sun tunawa da kowa

shekarun da Hajiya Mardiyya ta shafe babu haihuwa s gidan alhali dukkan sauran kishiyoyinta na tara ƴaƴa, da kuma yadda ita Aunty Sadiyan ta dinga ziga ta akan shawarwari kala-kala, wadda bata dauki kowacce ba sai ta cewar tayi karyar tana da ciki, ta rai

ni abinta kamar gaske idan lokacin haihuwarsa yayi, zasu samo jaririn da zata dawo dashi daga asibiti bayan sun tafi su biyu ba tare da kowa ba.

Kuma hakan suka yi, don kafin lokacin aka bawa Aunty Sadiyan labarin wata ungozoma acan wani kauye dake irin wa

nnan harkar ta siyar da jarirai idan ta karbi haihuwa don a kaidar aikinta ta idan ta karbi haihuwa yaro bai zo da rai ba, ita ke binnewa, wai ladan aikinta kenan saboda jahilci irin na mutanen wannan ƙauyen a lokacin, don haka idan har ta samu masu nema,

to tana basu ranar da zata karbi haihuwa ne su zo, ita kum idan har ta ciro dan, to akwai wani lakani nata da take yiwa jarirai da tun kukan farko basa kara wani, zasu yi ta bacci ne mai tsawo har zuwa wani lokaci ta yadda za'a yarda da ita dewar sun mutu.

Da wannan dabarar take shaidawa nmasu haihuwa cewa dansu ya rasu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login