Showing 24001 words to 27000 words out of 144990 words

Chapter 9 - FARAR WUTA COMPLETE

/>
Ta maida wayarta jaka lokacin da Nurses din nan suka shiga tura gadon da suka

ɗ

ora Ma'aruf

ɗ

in dake bacci har yanzu, don tun bayan wannan farkawar, bai k

ara bude idanunsa ba.

"Amina."

Muryar Ishaq da ya karaso cikin

ɗ

akin bayan fitar Nurses fin tasa ta dawo dq hankalinta kansa.

"Bai ce miki komai ba bayan sakon da kika bani lokacin da ya farka?"

Ta girgiza kanta a hankali.

"Cewa kawai yayi in gaya maka ka

zo ka fitar dashi, kuma bayan kiran ya katse ma bai sake cewa komai ba."

Ta gyada kansa yana maida wayarsa cikin aljihu.

Shiru ya ratsa na dakika biyu kawsi kagin ymuryarsa ta sake fitowa.

"Mun gode sosai da abinda kika yi Amina, this is the first time da

wani ya taba zama da Ma'aruf a irin wannan yanayin bayan ni."

Bata san me zata ce ba, don haka ta gyada kanta a hankali tana kallon jakar hannunta da ta rike. Ya juya ya fita daga dakin har a lokacin bata dago ba, rayawa take a zuciyarta cewa idan har daga

yanzu za'a fara yi mata godiya akan duk abinda zata yi, watakila za'a zo lokacin da za'a rasa wajen ajiye godiyar ma.

****

Hajiya kilishi ta tsirawa sakon da ya shigo wayarta ta nambar Awwalu ido, ta karanta ta sake karanta yadda yake gaya mata dukkan tsa

rindu ya tafi daidsi lokaci kawai yske jiracda kira ta kafin wani irin murmushi ya subuce a bakinta.

Me yasa take mantawa ne wai? Itace fa, itace wannan Kilishin da ba ta taba saka abu a gaba bata cimmasa ba, to don me kuma a yanzu take iya saka kokwanto a

ranta? Me yasa take yiwa komai tunani biyu bayan gashi Aminar ma ta riga ta sami kanta.

_Saboda faruwar komai yana sauri da yawa..._

Wani gefen tunaninta ya ambata mata amma sai tayi cilli dashi gefen da ya fito a lokaci guda, ai yarinyar ta gama tsorata

da ita ta sani, ta gaya mata cewar ta

ɓ

a dan'uwanta da tayi ba karamin abu bane da ba za ta so a sake irinsa ba, don haka ta riga ta gama yarda da ita, tunda har ta iya aikata wannan umarnin da ta bata a kudundune, umarnin da yaci sunan lauje cikin nadi, am

ma kuma tsaf cikin hikimarta ta ware nadin ta fidda laujen cikin sauki.

Don haka bata da sauran matsala ta sani, ko an dawo da Ma'aruf gidan umarni kawai zata bata na cewar kar ta sake ta bari ya fito, da wannan ta san zasu iya gama komai ita da Awwalu kaf

in jibi, tunda ko Baffa sai gobe zasu dawo suma.

Ta sake wani murmushin a hankali tana hango lissafinta. Tazarar fa ka

ɗ

an ce, saura ka

ɗ

an su ƙarasa ga ƙarshe inda komai zai fashe, taji tana taya Amina murnar shigowa cikinsu, don wahalar da zata yi kadan ce

, ita da Awwalu sun da

ɗ

e suna tsarawa da gina komai bi da bi.

Wayarta tayi kara a lokacin, Awwalu ne, ta dauka ta kara a kunnenta,

"Hajiya ki fito yanzu komai ya kammala."

Ta gyada kanta ba tare da ta amsa a fili ba.

Ta kashe wayar tana wani murmushi sanna

n ta jawo mayafinta, ita da dawowa gidan kuma sai lokacin da ta kammala kaso mafi yawa na cikar burinta.

Abinda bata sani ba shine, ubangiji ya kadarta tafiyarta a wannan lokacin ne don faruwar wani abu da tunaninta bai taba hango mata ba.

****

*Karfe biya

r da rabi na wannan ranar.*

Karo na farko a rayuwar Ma'aruf da ya ta

ɓ

a bude idanunsa cikin irin wannan yanayin yaga ƴanuwansa zagaye dashi fal, Awa kusan uku kenan tun bayan farkawarsa amma har yanzu zuciyarsa ta kasa ƙarasa yarda da ganinsu gabadaya tare

dashi kuma ba a ko'ina ba a cikin gidansa.

Samira ce ta gaya masa cewar Amina ce ta sanar dasu an dawo gida don haka tun da rana kafin ya farka suka zo har dasu Salma, Shukra da Safiyya wanda suka zo a ranar, ga dadin dadawa Inna Danejo da itama Mama Rabi

ta rako ta tun daga cikin gidan har nan.

Tana zaune daga gefensa inda aka kwantar dashi a falon tana ta karanto tarin addu'o'i daga cikin carbin ta take ja tana gaya masa cewar rubutu zata sa ayi masa na Alkur'ani gaba

ɗ

aya don  ita ta gaji da yawan maganin

asibitin da har yau bata ga amfaninsa ba.

Kuma tun da Ma'aruf yake a rayuwarsa, tun daga lokacin da ya sami ciwon nan, idan har bashi da lafiya ya sani cewar sai dai ya farka ya ganshi a London asibiti ko kuma tare da Ishaq a gefensa.

Ko lokacin da yana

tare da Rukayya baya bude idonsa ya ganshi a gida kuma ko shi a baya bai taba ganin wani abu game da hakan ba, don idan ba zai manta ba a cikin hira Mami tasha gaya masa cewar hakan shine daidai, bai kamata ya dinga mu'amalantar kowa ba har sai yanayinsa y

a sauko ya daidaita.

Shi yasa a karo na farko da ya farka a yanzu yaga mutane zagaye dashi sai yake jin wani iri a zuciyarsa, wani irin yanayi da bai san dame zai fassara shi ba, kallonsu kawai yake yi tun bayan da ya bude idanun nasa, kowanne da murmushi

a fuskarsa suna tambayar lafiyarsa da kuma yadda yake ji.

"Ya MB kace min ka warke dan Allah, ni ban san haka ciwon ka yake ba wallahi, ban taba ganinka a haka ba."

Shukra ta fada tana gyara glasses din dake fuskarta tana kallonsa. Kuma sunan da ta kira sh

i dashi ya tuna masa da dadewar da yayi bai gansu ba tun bayan aurensu, ya san dai kowaccensu ta kira shi sau daya sun gaisa amma bai kara jinsu ba bayan hakan, dukkaninsu sun canja, musamman Safiyya da tayi wata irin kiba a watanni biyu kawai tana gaya ma

sa cewar da wuri zasu tsufar dashi idan ska kalle su aka cewa su kannensa ne.

Kuma maimakon ya bata amsar abinda ta tambaya sai kawai yace.

"Ya project work

ɗ

in naki kuwa Kin gama?"

"This is your answer ya warke kenan, don ni na tabbata da yace miki da sau

ki to wallahi Yaya bai warke ba."

Cewar Salma tana karasowa rike da kwanon furar da Inna Danejo tasa taje har bangarenta ta dauko shi. ta zubo wani potate

ɗ

in dankali a ciki daga kitchen, tana karasowar kuwa Inna Danejo dake gefensa ta karba tana fadin.

"M

uhammadu juyo nan kasha wannan, na gaya maka ni ban yarda da wannan she*gen ruwan da ake sawa ba ace wai shima abinci ne, gashi nan tunda ka farka ai kake ta shan ruwa da yana aiki ai ko shi ba zaka nema ba."

Ya juyo ya kalleta, ta debo abincin da niyyar b

ashi, sai kawai ya girgiza kansa yace.

"Ni ba haka matata take bani abinci ba."

Su Salma suka kyalkyake da dariya ba shiri yayin da kafin Inna Danejo ta kai karshen salatin ta Surayya ta shigo tana fadin cewar ga wani likitan nan ya karaso da sakon cewar B

affa ne ya turo shi, don a dazu bayan farkawarsa sun yi waya da Baffan har ma da Baba Usman suna tambayar yaya jikin nasa, kuma a cikin muryarsu ka

ɗ

ai ya fahimci su ma sunji dadin yadda wannan karon ciwon nasa bai tsawaita ba.

Inna Danejo ta ajiye farantin

hannunta tana fadin ace masa ya shigo, Ma'aruf ya juyo yana ce mata ta bashi furar tace ai kuma yayi wa kansa kenan ya zauna da yunwar cikinsa idan matar tasa tazo ta bashi.

A lokacin ne kuma yadso ya tambayi inda Aminan take don tun bayan lokacin da ya f

arka sau daya ya ganta sanda da ta kawo masa ruwan farko da ya tambaya, amma kafin ya bude baki Shukra ta matso tana dariya ta

ɗ

auki plate din tana fa

ɗ

in ita zata bashi.

A lokacin ne kuma Zahra da Sahla da suka fito daga hanyar koridon dakunan gidan.

"Ina

Aunty Amina?"

Suka tambaya a tare muryarsu na shaida murna.

"Me kuka je kuka yi mata a daki?"

Safiyya ce mai tambayar tana kallon hannun Sahla data boye a baya.

"Babu komai, kawai tambayarta zamu yi wani abu."

Salma ta kalle su tace.

"Makaryatan banza ai i

dan bincike ne kun iya shi, na gaya muku duk ranar da zaku zo gidana walkahi ku gaya min kulle koina zanyi ku zauna a falo.

Munaya dake zaune a gefe ta kalle ta.

"Har yanzu baki san abinda ke tsakaninku da Samirah bane, shi yasa kike ganin na wadannan yara

n wani abu suke yi."

Da sauri Salman ta juyo tana rokonta ta gaya mata abinda Samiran ta daukar mata amma tace ita ba zata fada ba ba,  ta bari duk ranar da Allah ya tashi tona mata asiri zata gani da kanta yayin da Inna Danejo ke fadan hada husuma babu ky

au.

"Wai ina Samiran ne ma, ni tazo in bata sakon cupcakes."

Safiyya ta tambaya daidai lokacin da Surayya ta shigo tare dasu Faruk da kuma likitan nan, hannunta na dauke wani dan karamin yaro da a lokaci guda Ma'aruf ya gane cewar Aarif ne

ɗ

an gidan Faruk,

kuma bai gama tunanin ba Shaida natar Faruk din ta shigo biye da sauran ƴaƴansu biyu mace da namiji.

"Yaya, su Aunty Shaida ne duka zo."

Cewar Surayyan kasancewar dama ita tun da ta san Shaidar don yayar ƙawarta ce.

Kowa ya amsa sallamar su da fara'a yayi

n da Munaya ta taso a lokaci guda tana  kokarin daukar Aarif din dake ta mika hannu zai koma wajen mamansa alamun kyuiya yake yi.

Shahida ta karaso har gaban Inna Danejo tana gaishe ta yayin da likitan nan ke kokarin cire allurar drip din daje hannun Ma'ar

uf din, shima ta gaishe shi sannan ta gaya masa cewa Faruq din yana waje tare da Ishaq wanda shima ya karaso a lokacin.

Da haka ta juya wajensu Safiyya tana gaishe su da tambayar Yaya mai jiki. Tambayar da tasa sai a lokacin hankalin kowa ya lura cewar Ami

na bata wajen kuma kowa ya tabbatar da cewar bai ga lokacin da ta fita ba.

Sai dai kafin hakan ya kai ga nisa, kofar falon ta bude, kuma Aminan da ake nema ta shigo a lokacin tare da Samiran da suka fita tare, sai dai duk wanda ke

ɗ

akin basu yake kallo a l

okacin ba.

Wadda ke zaune akan kujerar da Samira ta turo zuwa cikin falon a hankali ce... Hajiya Maimuna.

Shiru ne ya ratsa ilahirin falon a lokaci guda kafin kowannesu ya rufe da kiran sunanta, hatta Inna Danejo sai da tayi murmushi tana kallonta, don a t

arin jama'ar gidan kaf, kowa ya san kawaici irin na Hajiya Maimuna, ba karamin kokari Amina da Samira suka yi na sawa tazo ba, tunda tun rana ta san inda dukkaninsu suka taho amna bata ce zata zo ba.

Ma'aruf ya kasa rufe bakinsa a lokacin da yake kallon Ha

jiya Maimunan dake Samirah ke turota tana karasowa gabansa. Keken tayar ya hawo har kan carpet din ta iso daidai gabansa da kuma Inna Danejo wadda ke fadin taso Baffa yana gari yau yaga Maimuna a gidan Ma'aruf, don ko sanda yana tare da Rukayya har suka ra

bu bata taba takawa gidansa ba.

A lokaci guda wani abu kamar kwallar da bai san dalilinta ba ta cika idanunsa lokacin da  Hajiya Maimunan ta gama gaishe da Inna Danejo ta juyo tana tambayar yaya jikin nasa, bai ma san da wadanne irin kalamai ya amsawa tamb

ayarta ba, ya san kawai a wannan lokacin idanunsa na kallon Amina ne dake can tsaye a baya da murmushi a fuskarta tana gaisawa da Shahida tana kuma kokarin daukar Aarif da ya gudo daga hannun su Munaya ya koma wajen Shahidan.

Zuciyarsa yaji tana gaya masa

cewa ko da iya wannan alkhairin nata na yau ka

ɗ

ai, zai kyautata duniyarta da dukkan iyawarsa.

***

*Ƙarfe tara da rabi na dare.*

Kowa ya tafi a lokacin, hatta su Ishaq bayan ya takura musu sun shaida masa dukkan abubuwan da yayi missing dinsu a ranar, farko

shine shari'ar Hamida da shi kansa ya manta da ita a yau,Ishaq din ya gaya masa cewar yaje ya dauko yarinyar ya tafi da ita kotun, kuma duk iya kokarinsa a gaban Alkalin, ba'a je koina ba alkalin ya yanke hukunci da cewar yarinyar ta koma wajen mahaifiyar

ta idan yaso tunda ya bada uzurin mahaifin nata bashi da lafiya, ya yanke hukunci cewar duk sanda ya warke zai iya sake shigar da kara sai a zauna a sake tattaunawa.

Na biyu kuma shine zancen haduwarsa da mutanen RTL din nan, Faruq ya gaya masa cewar babu

yadda baiyi yayi contacting mutanen ba amma ya kasa samun su kuma suma basu ce masa komai ba. Sannan Ishaq ya shaida masa cewayasa snyi deactivating gaba

ɗ

aya cards dinsa da aka

ɗ

auke kuma barayin basu sami danar fitar da komai ba.

Har suka tafi Faruk yana

ta kokarin ya kwantar da hankalinsa akan cewar ya san ba wani issue ne babba ba amma har suka kammala zancen suka tafi jikinsa bai bashi haka ba, kawai ya ajiye zancen ne a gefe sanin cewar idan ya saka a ransa tabbas abin zai hadu ya dame shi tunda wancan

case din ma har yanzu basu karasa shi ba, don haka ya hakura ya barwa karin samun saukinsa komai.

A yanzu gidan daga shi sai Amina ne, kowa ya tafi, su Salma tare suka koma cikin gida tare dasu Inna kuma ya san zuwa yanzu ma duk sun tafi. Kuma Hajiya Maim

una da har ta tafi fara'ar fuskarta bata

ɓ

oyowa, kuma yana jin sanda taje ta addu'a da sawa Amina albarka daga can bakin kofa inda suke sallama.

Hatta Faruk sai bayan da suka yi sallar Isha ma sannan suka tafi don suna ta hira tare da Ishaq, yayin da Amina

ke tare da Shahida a kitchen don dukkaninsu basu tafi ba sai bayan da suka ci abincin dare, har Samira ta dawo daukan wayarta da ta manta tana ta korafin me yasa basu kirata ta taya su ba.

A yanzu fitowarsa kenan daga wanka yanzu tunda ya samu a dazu suny

i jam'in sallah tare dasu Ishaq.

Yana zaune daga bakin gadon dake dakinsa, safa yake kokarin sakawa a ƙafarsa saboda sanyin da yake ji yayin da zuciyarsa ke kara hasaso dukkan abinda ya faru a yau yana ganin kamar  a wata guda akayi komai ba yau kadai ba.

Kofar

ɗ

akin ta bu

ɗ

e a hankali, ya juyo da kansa lokacin da Amina ta shigo hannunta dauke da wani dan madaidaicin tray a hannuta.

Tun bayan tafiyar kowa bai ganta ba, kuma tun a adibitin nan da ya farka yace ta kira masa Ishaq basu kara magana ba, jayan jik

inta suka shaida masa cewa itama tayi shirin ba ci don doguwar riaga a jikinta wadda bara sauka sosai, ba, wani abu acikin kansa ya shiga gaya masa cewa yana missing wadannan siraran kafafun nata kamar me.

Ta karaso gabansa a hankali, idanunsa na kallon ko

wanne takunta, kaginnya maida su fuskarta.

"Yaya ka kara ji da sauki?"

Muryarta ta tambaya kamar wani abu dake tashi sama a hankali.

Kuma baiyi tunanin komai ba yace.

"Ke kike ta bani reason din da nake jin saukin ai."

Sai kawai tayi murmushi ka

ɗ

an sannan

ta tsugunna a gabansa, ta durkushe kafafunta daga ganinsa, hannunta ya bu

ɗ

e plate guda

ɗ

ayan dake kan tray din tana fadin.

"Na san yanzu zaka iya cin wani abu ko?"

Bai amsa ba ta sake cewa.

"Inna Danejo tace kar in bari ka kwanta haka baka ci wani abu."

Ta

karasa sanda ta saka cokali a cikin plate din hadadden potate din dankali da alaiyahun dake ta ƙamshi a hancinsa.

Ta dago ta kalle shi, har yanzu idanunsa na kanta, kuma ga mamakinta sai taga kawai ya sauko kasan shima ya zauna daidai gabanta, sannan ya r

iko hannunta daya da bata rike plate din dashi ba, kamar koyaushe ya ratsa yatsunsa a tsakanin nata. Ta kalli hannun nata daya rike  ba tare da tace komai ba sannan ta

ɗ

ebo abincin ta shiga bashi, yana ci tana gaya masa yadda akayi kafin likitocin asibitin

nan su sallame shi.

Kuma bayan sun gama ne yace ta dauko masa wasu magungunan gargajiya da ya taba siya ya ajiye a saman drawer dakin, kamar zata iya sai da taje gaban drawer sannan taga da saura dosai kafin tsawonta ya Kai, don haka ta shiga neman abinda

zata taka, amma kafin ta motsa tajinsanda ya karaso daidai bayanta sannan kai tsaye hannayensa duka biyu suka zagayo ta kasan cikinta kuma kafin ya hade su waje daya tana jin irin rawar da suke yi alamun har yanzu jikinsa bai gama kwarin da zai tsaya haka

ba.

Don haka bata san lokacin da ta juyo ta fuskance ba da sauri idanunta na haskawa da mamaki.

"Me yasa ka taso? Zan iya daukowa fa..."

Sai ya girgiza kansa yana sake rike ta a jikinsa.

"I want to talk to you."

Har yanzu ji take yi kamar basu gama tsayaw

a daidai ba don haka tasa hannunta duka biyu ta rike gaban rigarsa kadan tana cigaba da kallonsa, kuma bata ce komai ba ya cigaba.

"I'm sorry game da abinda ya faru Amina, I'm sorry for how you saw me, (Ki yi hakurin yadda kika ganni) Na gaya miki dama I'm

a mess..."

Sai tayi saurin girgiza nata kan itama tana cigaba da kallonsa.

"You dont need to be, lafiya da rashinta ba mallakin kowa bace, Allah yana bamu ita ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login