Showing 42001 words to 45000 words out of 144990 words

Chapter 15 - FARAR WUTA COMPLETE

kanta a hankali tana son tayi maganar amma ta kasa, ta kasa don bata ma san me zata ce ba, ya gyada kansa shima ba tare da ya damu da jin abinda zata fada din ba, kuma tana ji yan

a cigaba da wasa da hannunta kafin yace.

"Bani na kashe Jamal ba Doll, ni na san bani na kashe shi ba don haka bayan abubuwa sun fara tafiya daidai sai na fara bincike akan wannan accident din, kuma sai da na shekara uku ina bin wannan hanyar ina tuntubar

mutane kafin na samu wasu mutane biyu da suka tabbatar min cewa wasu mutane ne suka harbi tayar motar mu a lokacin da nake tuƙin, da silencer suka yi amfani a bindigar ta yadda babu wanda yaji wata ƙara sai kawai ta fashewar tayar.

Bayan nan, nayi iya binc

iken da zan iya don gano mutanen da suka yi wannan aikin, ina living rayuwata ina kuma yin binciken don ban taba amma duk hanyar da na bi bata

ɓ

ullewa bana samun komai, kuma duk lokacin da hakan ya faru I felt emotionally high, sai ciwona ya tashi, sai inj

i komai ya tsaya, abu kadan yana bata min rai kuma idan ran nawa ya baci bana jin ina son komai sai tsananin yadda zan iya wanke kaina a wajen Jamal.

Kuma abu daya ne kawai yake zuwa kaina cewa zan iya aika masa da sako, shi yasa duk wanda ya bata min rai,

sai inji ina son in kashe shi kawai, in kashe shi in bashi sakon cewa ya gayawa Jamal abinda ya faru bani na kashe shi ba, this is crazy! I'm crazy na sani Amina, na san banbancina da mahaukaci a irin wannan lokacin bashi da yawa, amma wallahi hakan ne ka

ɗ

ai abinda nake so shi yasa nake tunanin idan har na samo wanda suka yi abin nan watakila zan iya jin sauki a raina."

Amina ta hadiye wani abu da bata san sunanshi ba a maƙogwaronta, tana jin yadda maganganun ke zagawa cikin kanta kowanne da tarin ma'anar

da yake fitowa da ita, kowanne da nauyinsa kuma kowanne da tasirin da yake zama dashi a zuciyarta. Kuma bata sab lokacin da hawaye ya cika a idanunta ba sai zubuwarsa taji a gefen fuskarta.

"Wannan ciwon shine dalilin rabuwata da Rukayya, ta bata min rai a

ranar da nima nawa ran yake a bace, so bana cikin hankalina sanda na karbi Hamida daga hannunta tana Baby lokacin nayi wulli da ita, ita kuma nayi mata dukan da ba don Allah ya kawo Ishaq a lokacin ba ban san me zai faru ba.

Ba zan

ɓ

oye miki ba Amina, duk

yadda nake jin zuciyata na sakewa dake wallahi ina tsoron ranar da ciwona zai iya tashi akan ki, shi yasa lokacin ayrenmu na aika miki da wannan takardar don ki fasa, bana son in sake abinda nayi tare da Rukayya ..."

Ya kara kallonta sosai, yana kallon id

anunta da suka cika da kwalla kafin ya ƙarasa.

"... Na yarda ƙaddarar haduwa dake itace bata sa na mutu ba tun a wancan lokacin, sabida haka idan har wani abu ya same ki ta dalilina yanzu, na tabbata wannan karon nima mutuwa zanyi, don ba zan ta

ɓ

a iya sake

wata rayuwa a duniyar nan ba idan har na kara sanadin rasa abu nsi muhimmanci irinki..."

Wadannan kalaman suka tada tsigar jikinta a lokaci guda, taji wani abu ya ratsa tun daga zuciyarta har zuwa bayanta. Sai kawai ta sake matso da kanta cikin jikinsa so

sai, tana rike da fuskarsa har yanzu ta shiga girgiza kanta a jikin fuskarsa.

"Babu abinda zai sake faruwa, babu abinda zaka yi min Insha Allah, babu wanintashin hankalin da zai kara samunka, sauran da suka faru ma, sun faru ne saboda haka Allah ya tsara k

omai ya kasance, amma Allah ba zai kara kawo su cikin rayuwarmu ba insha Allah, all I care is that ba kai ka kashe Jamal ba kuma na san shima ya san hakan, da zai dawo nayi imanin zai gaya maka hakan, zai gaya maka cewa ya san ba laifinka bane."

"Laifin wa

ye Doll? Har yanzu na kasa gane laifin waye, ko zai dawo

ɗ

in ta yaya zai yarda dani?..."

"Zaka sani insha Allah, nayi imanin idan ka cigaba da nema zaka sani, Allah ba azzalumin bawansa bane Ma'aruf, ya sani cewa ko su waye sun cuce ja kuma sun hargitsa ra

yuwarka, zai maka sakayya ta hanyar tona musu asiri insha Allah."

Maganar ta fito tare da tahowar wani hawayen mai dumi daga idanunta, sai kawai ya sake sunkuyo da fuskarsa kan goshinta yayi kissing idanun nata duka biyu yayin da ta rufe su.

"Insha Allah D

oll, fatan da nake yi kenan a kodayaushe."

Wasu hawayen suka sake biyo bayan na baya suka fito masu

ɗ

umin gaske. Abinda ta sani kawai a wannan lokacin shine idan har da sa hannun Hajiya Kilishi a mutuwar Jamal, to tabbas kuwa Ma'aruf ya kusa samun amsar sa

.

***

*Ƙarfe tara da rabi.*

Tunda suka tashi take iya kokarinta wajen ganin tayi komai kamar yadda suka saba, yau asabar ce don haka ta san vabu inda zai je, wajen karfe takwas ta fito ta sake yin wanka sannan ta shiga aikinta, tana jiyo shi daga daki yana

ta waya kuma bayan taje kai masa daya wayarsa da ya bari a falo wadda ake ta kira, ta ganshi ya fito da system har guda biyu yana ta faman dube-dube. Basu yi wata magana sosai ba amma yayi mata murmushi fiye da yadda zata kirga a iya safiyar kawai.

Ta kam

mala hada breakfast din tana dauraye kwanukan da tayi amfani dashi ne lokacin da ihun Hamida ya ziyarci kunnenta, ta tashi tana ta kiran sunan Mary.

Ta fahimci Mary ce ƴar aikinta da kullum suke tare, kuma takaicin da ya kasa barin zuciyarta shine na yadda

sunan arniyar ya zauna a bakinta, ko mahaifiyarta bata kira sama da ita, yanzu ma ace yaro ya tashi daga bacci babu kiran sunan Allah sai wata arniya... Da sannu zata canja mata hakan a hankali.

Kuma ko da ta isa dakin har ta sauko daga gadon tana shirin

fitowa, don a bakin kofa ta tarar da ita. Kuma cikin siga da dabararta sai da ta sa ta fadi addu'ar tashi daga bacci kafin su wuce zuwa bandaki inda tayi mata brush da wanka gabadaya.

Bayan sun fito ta shirya ta cikin wata ƴar doguwar rigarta mai kyau pink

colour sannan suka fito falo,inda anan suka tarar da Ma'aruf har ya fito shima ya

ɗ

ebo kayan breakfast din da kansa zuwa falo ya zuba yana ci.

Yana ganinta ya fara bata hakuri cewa yunwa yake ji shi yasa ya kasa jiransu, Hamida ta makalkale shi tana gaya

masa cewa tayi mafarki da Unicorn, wani shirmen mafarkinta irin cartoon din da kullum take gani.

Wannan lokacin yayi dadi a zuciyar Amina ba kadan ba, sai take ganin yadda yarinyar ta dada sawa gidan ya zama lively a tsakaninsu, har wayar Ma'aruf

ɗ

in ta da

uke lokacin da Faruk da wani Josh ke ta kira babu kakkautawa, sai da ya roƙe ta da Allah ya gaya mata cewar wani suke nema da yayi musu satar wasu tarin kudi masu yawa a kwanciyar nan da yayi na kwana biyu kawai sannan zancen ya dake ta da wani irin yanayi

ta bashi wayoyin.

Ya fita zuwa barandar waje duk da suna jin dukkan abinda yake cewa, kuma ko kafin ya dawo Hamida tasa ta canja mata daga tashar CNN din da yake kallo zuwa Disney Junior dinta, ita kuma ta kwashe kayan nan zuwa kitchen ta shiga karasa wan

ke wankenta da bata gama ba.

A lokacin Ma'aruf ya shigo cikin kitchen din, ya karaso har inda take sannan ya rungumeta ta a hankali cikin hannayensa.

"Hey Angel."

Ya fa

ɗ

a a cikin wuyanta, a lokaci guda numfashinta ya katse a kirjinta kafin tayi  kokarin sa

ita kanta zuwa tambayar dake bakinta.

"Me yasa zaka fita yau weekend?"

Tayi tambayar don taji sanda yake gayawa Faruk cewa gashi nan zuwa. Taji yayi murmushi a cikin wuyan nata kafin ya lalubi daidai kunnenta yace a hankali.

"Saboda babu yadda zanyi Doll,

dole ne muyi abin nan da gaggawa mu samo mutumin nan, babu wanda ya san abinda ya faru a kamfanin har yanzu, ni da Faruk da kuna Josh ne kawai, sai wadanxan mutanen daya kamfanin. Kuma bana son ayi dadewar da dole zancen zai fita balle har Baffa ya sani...

Idan hakan ta faru rayuwata zata sake ta

ɓ

uwa ne na sani."

Tana jin yadda jikinta ke yi kamar ya kama da wuta, sannan tana jin murmushin da yake yi a jikinta alamun yana jin dadin rikita tan da yake yi, kuma kafin daya daga cikinsu ya sake cewa wani abu, s

allamar Samirah da kuma Munaya daga falo ta shiga kunnensu.

Ba shiri tayi kokarin matsawa amma yaki sakinta.

"Su Samira ne suka zo..."

Ya gyada kansa.

"Naji su, me za'ayi?"

Ya tambaya da gaske, hannusa daya na kokarin kwance dankwalin kanta, babu shiri tas

a nata hannun duka biyu ta damƙe shi sannan ta juyo tana kallonsa.

"You are busy ka manta kace fita zaka yi yanzu, suma kuma yanzu zasu shigo nema na har nan."

Ya girgiza kansa yana ƙara jawo ta jikinsa.

"Na fasa, I want this busy yanzu more than anything.

"

Ya fadi hakan idanunta na kan kofa don daga yadda take jin Samirah na kiran sunanta ta san yanzu zata shigo, sai kawai taji ya shiga kissing gefen kumatun ta yana jawo hankalinta daga kofar zuwa kansa.

"Dan Allah ka tafi kar su shigo." Muryar ta ta fito

kamar zata yi kuka.

Ya janye fuskarsa baya sannan murmushi mai kama da dariya kafin yace.

"Yanzu kike shirin roko na kar in fita yanzu kuma kina korata saboda wa

ɗ

annan yaran, wai laifi muke yi ne ko me?"

Girgiza kai kawai take tana kallonsa cike da roko, k

uma kafin ta iya cewa wani abun muryar Samirah ta doso kitchen din tana fadin.

"Matar gidan tana nan ne..."

Ai bata san lokacin da tasa dukkan karfinta ba ta fita daga hannun Ma'aruf ta dawo gaba ta tsaya da sauri tana kokarin daukan wasu kwalayen sugan da

ta juye a jar ta bar kwalayen anan kan worktable din dake tsakiya, kuma kafin Samiran ta shigo tana jin sanda ya juyo shima ya sake tsayawa a daidai bayanta sannan kafin tayi tunanin komai ya sunkuyo daidai gefen kunnenta yace.

"Kina nufin in zuge miki zip

din rigar? Dama wancan karon da na taya ki din nan kamar ba daidai muka yi ba ko?...."

Bakinta ya fa

ɗ

i har ƙasa yayin da numfashinta ya dauke a lokaci guda, sai kawsi ya kyalkyale da wata dariya a hankali sannan yayi gaba ya wuce ta zuwa hanyar kofa, kuma

sai da yaje daidai kofar sannan ya juyo yace.

"Na tafi inda kika kore ni, kiji dasu, amma akwai lokacin da bakin ki ma bai isa yayi magana ba."

Yana fadin haka ya kifta mata idonsa daya yana murmushi sannan ya fita daidai lokacin da taji Samirah bna cewa.

"Ashe kaima kana nan Yaya..."

Sai kawai ta saki wani numfashi a hankali sannan bakinta ya tale da murmurshin da ta kasa tsaida shi.

***

*Karfe goma sha

ɗ

aya.*

Ƙ

arar ƙwankwasa kofar ta kara

ɗ

e gidan gabadaya, Amina ta taho da sauri daga cikin daki inda ta b

ar Hamidah na ƙoƙarin taje girarta a gaban mudubi, yarinyar na son kwalliya da alama, don ko

ɗ

azu da ta raka ta toilet tayi fitsari tana kallonta lokacin da take gyara hularta a jikin mudubin jikin sink.

Allah ya sani a yanzu tana jin son yarinyar nan yana

ƙaruwa a cikin ranta, kwana biyu kawai amma duk sanda ta kalle ta da wa

ɗ

annan idanun nata irin na Ma'aruf sak, sai taji wani abu na yawo a cikin ƙirjinta, don ita kanta yarinyar ta ƙara sakewa da ita sosai.

Tafiyarta a hankali saboda yadda take jin jikint

a ta karaso bakin ƙofar, kuma haka kurum sai taji gabanta ya fa

ɗ

i, taji farin cikin da ta tashi dashi a yau na yayewa, taji zuciyarta tayi fayau yayin da jikinta yayi shafal a lokaci guda kamar fallen takarda.

Sai kawai ta karanto hasbunallahu wa ni'imal w

akil sau uku sannan ta bude kofar daidai lokacin da aka ƙara kwankwansawa.

Kuma a lokaci guda idanunta ya shiga na cikin Hajiya Kilishi dake tsaye a wajen.

***

"Me tace?"

Muryar Amma ta tambaya a cikin wayar da Amina ke yi awanni biyu bayan hakan. A hankal

i taji wani abu na zarcew cikin maƙogwaronta yayin da idonta ke kallon Hamida da tayi bacci a cinyarta.

Kalba take yi mata a cikin gashinta mai tsananin laushi amma kuma babu yawa, laushinsa ne kawai irin na Ma'aruf amma bai yo yawan nasa ba, saura guda da

ya su gama don haka ta da

ɗ

e da yin baccin don tun a farko tayi abinta.

"Me ya kawo ta Amina?"

Amman ta sake tambaya jin tayi shiru, tun dazu suke wayar, tun dazu Amman ta kira take shaida mata cewa ashe a airplane su Hafsa suka sa mata wayar tun jiya shi y

asa bata same ta ba, kuma bayan ta kashe ta sake kira ne ta shiga zayyano en mata zuwan Hamida da kuma layar da ta gani a cikin kayanta.

"Kinyi daidai wajen ƙona layar,don nsyi imanin idan har ba da sunanki aka yi ba to da nasa ne, don da alama asirin kusa

ne,sai yana tare da mai shi sannan zai ci, suna da tasu manufar tabbas, amma nafi danganta hakan da cewar kome take son taui ita mahaifiyar yarinyar, shi yasa suke son su jawo hankalinsa kanta ko kuma ke su kore ki, amma bamu da tabbas, don haka ki dage d

a addu'a, ki kuma cigaba da kiyaye dukkan wani abu a gidan.

Zasu zo, ni na tabbata zasu zo miki don asirin bai fara ci ba tukunna, ki zuba ido kawai ki saurari zuwansu, wannan matsalar mai sauki ce don nasu tunanin bashi da fadi don haka a lokaci kankani z

aki gama dasu.

Amma yarinyar, ki cigaba da rike ta da wannan kulawar da na sanki da ita Amina, Kilishi ba zata kawo miki ita a banza ba amma tunda bata ce komai ba mu saurare ta tukunna, wanda kafin nan ki cigaba da rike ta da zuciya daya don wannan ba kar

amar kofa bace da zaki ƙara bude wata darajar taki a zuciyarsa,

kar ki manta kullum ina gaya miki takamar kowacce mace a duniyar nan zuciyar mijinta ce, samun nasararki akan Kilishi dama duk wani abu da zai biyo baya ba zai kai darajar kyautata rayuwar aur

enki ba."

Da wannan suka kammala zancen Hamida da kuma batun layar nan, sannan Amman ta shiga bata labarin cewa Hajiya Kilishi ta turo da wasu mutane an dauki Baba da Aminu zuwa wajen da za'a fara musu fafutukar visa don kaishi asibiti a india kamar yadda

ta shaida musu.

"Suna nan suna ta yabonta Amina, Babanku da ƴanuwansa har ma dasu Asma'u (ƙannenta) kowa yana ta sambarka, basu  san cewar umarninki bane Amina, don wannan bashi da maraba da cewar umarnin hakan kika bata, umarnin da ita kanta bata sani ba.

"

"Tazo

ɗ

azu Amma."

Kai tsaye bakinta ya fadi hakan, don a wannan lokacin ta kasa daurewa tarin hargitsin da kuma ru

ɗ

anin dake cikin kanta.

"Me tace?"

Sune kalmomi biyu da Amman ta furta wanda taji su a cikin ranta kamar baron da aka cika da ƙasa mai nauyi

yake rike a hannunta kuma tana shirin hawa tudu dashi, don bata san ma ta inda zata fara ba, bata san ta inda zata fara dauko zancen ba, amma shirun wayar dake tafiya yana shaida mata jiran sauraren da Amma ke yi tasa ta hadiye abinda ke bakinta sannan ta

ce.

"Akan Hamidan ne."

Amma bata ce komai ba har ta ƙara ha

ɗ

iye wani abun a cikin maƙogwaronta sannan ta cigaba.

"Kamar yadda kika fada tace bata kawo min ita a banza ba, bata tsallake kowa tace ni zan rike ta ba sai don tana da dalili, dalilinta kuma shin

e bata bukatar yarinyar ta zauna a cikakkiyar mutum, ta gaya min da farko tayi niyyar a kawar da ita ma gabadaya, amma kuma sai taga cewa gwara ta bar Ma'aruf da wani abu ko guda daya ne a rayuwarsa bayan ta tafi.

Bata gaya min inda zata je ba, amma tace d

aga ni har ita mun kusa barin rayuwar Ma'aruf don ta kusa kammala burin da ta shigo dashi gidan, burin da yasa tayi fafutukar auren Baffa tun a shekarun baya, don haka tace min ko bayan bata nan bata son ya zama akwai wani abu mafi soyuwa a rayuwar Ma'aruf

sama da ita.

Tafi son ya zama zuciyarsa na tunawa da ita da matsayin da yafi na kowa a wajensa, don ta gaya min cewar tafiyar da zata yi ma zata tafi ne ba tare da sirrinta

ɗ

aya ya fita ba, zata tafi ne ta barsu suna begenta har karshen rayuwarta don haka

n shine babban burinta kuma ta riga ta tsara yadda zai kasance tuntuni, kawai tana jiran kammala cike abinda ke gabanta ne.

Don haka ta gaya min cewa tana so ta makantar da Hamida ne ta kuma gurgunta ta ta yadda ba Ma'aruf kadai ba, babu wani mahaluki da z

ai kalle ta da daraja a duniyar nan kuma zata yi haka ne ta hanyata, ta gaya min da hannu na zanyi hakan Amma."

Muryarta ta kai ƙarshe da tsananin rawar da take fitowa kamar kuka ne ke shirin kwace mata,amma kuma duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login