Showing 30001 words to 33000 words out of 128353 words

Chapter 11 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

52

"Ki fito kici abinci."

Cikin kunya tace "To."

Uban yunwan da takeji bazai barta tace ta koshi ba, haka ta gyara zaman babban mayafin sannan ta fito daga dakin, a zaune ta ganshi ta kalli tiren abincin sannan ta fara tunani, to yanzu

zuwa zatai ta fara zubawabta mikamai sannan tasa nata? Ko kuma nata zata fara zubawa ta faraci shi inya shirya ci yaci nashi? Kai ta girgiza da sauri ganin hakan ba tunani, to meya kamata tai? Shiya zauna yana dane dane a waya.

Dakewa tai ta karasa tare

da daukan plate, gani tai ya mike tsaye tai saurin cewa "A daki zakaci abincin?"

"Zan dan fita gun aiki ne na dawo."

Ta kalli abincin sannan tace "Kaci abincin mana tukun sai ka wuce."

Jakarsa ya dauka yace "Ke kici banacin abincin waje."

Baki ta

bude sannan ta kalli yanda akansoya dankali da kwai, dayan plate din indomie da soyayyen kwai. Me bawan Allah din nan yake nufi? Ina zata kai wannan abincin?

Kallansa tai tana san magana taga haryasa takalmi, idanunta na kansa taga ya juyo dawowa yai cik

in falan sanye da takalmi ya matso kusa da ita kawai ya zare sim dinsa ya ciro wallet dinsa ya dauko wani sim ya saka a cikin wayar, mika mata yai sannan yace "Kiyi amfani da wayata incase in wani abin ya tashi, ba dadewa zanyi ba amma tsautsayi bashida lo

kaci."

A hankali tasa hannu ta amsa, baiko jira me zatace ba ya juya, sai daya kai kofa ta iya furta "Nagode!"

Bai amsa ba ya maida kofar ya fita, kallan wayar tai wace alan wayar ke dauke da hotonshi da na Na'ima, itakam mutumin nan ta kula sam baya j

ira yaji ra'ayinta, abinda yamai kawai yake aikatawa, ta kalli abincin rufe dankalin tai kawai tadau indomie ta koma kan kujera ta kuna tv tana kallo tanaci, lalai yunwa takeji dan gani tai ta cinye indomie din nan tas, hamdala tai sannan ta mike ta hada t

ea ta zauna tana sha, wayar ta dauka ya cire security dan tana tabawa ta bude, hannu tasa kamar zata shiga gallery dinsa sai kuma ta girgiza kai, hakan bai kamata ba daga taimako?

Haka ta zauna ta rasa abinyi, ta kira Abba harsai uku bai dauka ba, tana n

an a zaune a falo har bacci ya sake daukanta da alama bashin jiya ne bai barta ba. Tv tanata kara dan bata samu ta kashe ko tv din ba.

******

Aminu kam hankalinsa bai kwanta ba sai daya tabbatar ya saita komai a office dinsu sannan ya fito, gun saida

waya ya tsaya yasai waya kirar iphone X Max karamar tashi ya sa sim sannan ya kira Ummy dan ya tabbatar ta nemeshi.

Yana dauka kuwa tace “Aminu inata nemanka wayarka a kashe”

Yai dan gyaran murya kadan yace “Nadan fita ne Ummy……”

Ai bai karasa ba tace

“Ka fita kaje ina? Allah yasa ba barinta kai ba.”

Mamaki Ummy ke bashi to yarinyar sa’arsu Islam ce da zai daukota ya dinga yawo da ita?

Ummy ce ta katsemai tunani, “Aminu?”

Yace “Yanzu na fito ba dadewa nai ba, sannan ba waya a hannunta gashi tana

san kiran ‘yan gidansu.”

Ajiyar zuciya tai alamar kwanciyar hankali sannan tace “Jiya na manta ban tuna ma kasai kaji ba, sai da asuba na tuna, a raina nace ai nasan Aminu nada zurfin tunani bazai bar ‘yar mutane ta kwana da yunwa ba.”

Gefen wuyansa yad

an shafa yace “Ai Ummy ni namanta da wata kaza, sannan yarinya tanata kuka ina ma take da lokacin cin wata kaza?”

Takaici ya rufe Ummy sai dai ta dake tace “Amma kai kaci abinci ka koshi kafin ka tafi ko?”

“Itama ai laifinta ne da bataci abinci a gidans

u ba, Ummy wannan kuma ba laifina bane.”

Ran Ummy ya kara baci tace “Yanzu ta ina zan samu na kirata?”

Shikam kai tsaye yace “Ki kirata da daya layi na nabar mata wayata.”

Jin haka yasa tadanji dadi kafin ta kashe wayar.

******

Ibty kam can taji w

ayar dake kusa da ita tana kara, cikin abin bacci ta dagota sam bata kula da me aka rubuta a jikin alan wayar ba kawai ta kara a kunnenta cikin abin bacci tai sallama.

Ummy daga can bangaren tace "Amarya ko bacci kike? Maman Aminu ce."

Da sauri mike ta

zauna sosai kafin tace "Ina kwana? Au Ina wuni?"

Murmushi Ummy tai tace "Na kira naji konkin tashi lafiya ashe wai ya dan fita ko?"

Cikin girmamawa tace "Eh Ummy ya fita yaje ya dawo."

Cikin dan bugar ciki tace "Dafatan ya kula dake yanda ya kamata?

"

Kunya ce ta kamata kamar tana ganinta tai kasa da kanta, ko ba'a fada ba Ummy tagane kunyar tambayar taji, cikin zolaya tace "Abinci fa?"

Tace "Naci sosai Ummy."

Ajiyar zuciya tai da alama ya kula da ita tunda gashi ya bata abinci, ya kuma bar mata

wayarsa, dan shine yace ta kirata da daya layinsa, da alama hakan na nuna sun fara fahimtar juna.

Cikin jin dadi tace "Ki samu ki huta sosai abinki dan naji kawarki tace wani satin zaku koma makaranta ko?"

Ta daga kai kamar tana ganinta tace "Eh Ummy.

"

"Gidanki ma an fara gyarawa ina ganin gobe ko jibi zaku samu ku kuma.”

Shiru tai dan batasan me zatace ba, Ummy tace “Aminu bayacin abincin waje, anjima zan ba direba ya kawo muku abinci, ki saki jikinki mijinki ne kinji?” Yanzun ma kunya ce ta kara

kamata tai kasa dakai.

Sallama sukai sannan ta kashe wayar, Ummy ta girgiza kai tace “Banda shirman Aminu jiya sai yabar amarya ba abinci?”

*****

Mikewa tai tare da dauro alwala ganin azahar tayi, sannan tazo tai sallah a falo, tagumi ta zuba tana tuna

nin haka zata cigaba da zama kamar mayya?

Wayarsa ta dauko kawai ta duba game ta fara bugawa, alamun sa key taji da sauri ta mike ta fara tunani ko ta shige daki tai kamar tana bacci? Ko ta kame a kujera tai kamar tana kallo? Ganin an turo kofa yasa ta n

ufi kujera da sauri ji kake gum ta make kafa a jikin centre table din, wani irin kara ta saki da karfi dan taji wani azababben zafi har tsakiyar kanta.

Da sauri ya maida kofar ya rufe ya shigo cikin hanzari tare da ajiye ledar hannunsa ya kalleta sannan

ya kalli kafar.

Dan karamin yatsar ta harya fara fitarda jini, kallanta yai cikin bacin rai kamar zaiyi fada ganin yanda take shishitun zafi tana runtse ido iya karfinta yasa ya fasa, hannunta ya rike wanda hakan yasa ta bude idanunta da sauri, kunya da

haushin kanta duk sun rufeta, itakam meke damunta?

Kan kujera ya zaunar da ita tai sauri sa kanta cikin cinyoyinta kunya duk ta isheta.

Tissue ya dauko ya zauna kusa da ita sannan ya riko kafarta, da sauri ta bude idanta ta zubasu a kanshi, kallansa ta

ke yanda yake goge jinin dake kafarta, dan runtse ido tai jin zafi na ratsata.

Dagowa yai hakan yasa suka hada ido, cikin bacin rai yace “Shekararki nawa?”

Rau rau tai da ido tace “Tsautsayine.”

Ya kalli kafar yace “Daga jiya zuwa yau abubuwan tsauts

ayi nawa kikai? Sannan in ance muku yara kuce zakuji haushi.”

Dan kafarta ta zare daga gun ta dan turo baki kadan tace “Ya Aminu wai komai nai sai ace yarinta nafafi shekara ashirin naji daga jiya zuwa yau ina……..”

Kallanta dayai suka hada ido ne yasa

ta kasa karasawa sai ta dan motsa baki tace “Allah ni ba yarinya bace.”

Kafar ya jawo da karfi sannan ya dan nado tissue ya sa a gun ya mata alama data rike da hannunta, rikewa tai ya mike ya kwashi tissues din daya bata sannan ya sa a bin din falan kafi

n yace “Then act like an adult.” Ya wuce toilet

Da kallo ta bishi cikin dan shagwaba tace “Nidai Allah a gida ba wanda yake cemin ina abin yarinta.” A hankali tai maganar dan haka bai masan tanayi ba.

Dan shishitun zafin ta sakeyi.

*******

Masu jer

e kam sunsha kalli, gashi Ummy ta sa an kawo musu lafiyayyen abinci, an sau an kafa gado da wardrobe sannan sukaci suka sha kafin su koma gida.

Shikam Umar yana nan a tsaye a lungun gidan, sai dayaji yunwa na damunsa sannan ya fito ya nufi hanya yana nema

n mai awara.

Sai dayai tafiya sosai dan unguwar masu kudice babu masu awara a titi, yana tafe yana masifa “Banda ma muguwar Unguwa ace ko awara ba’a saidawa? Ba wata ‘yar wainar filawa ko kosai?”

Yai tsaki sannan ya tsaya a jikin wani shago ya siyo brea

d da coca cola ya zauna yana ci yana kurba, sai dayaji ya koshi sosai sannan ya mike ya kalli agoggo ashefa baiyi azahar ba gashi la’asar ta kawo kai.

Nan ya nufi masallaci bayan yayi sallah ya zauna yanata addu’a akan Allah ya bashi ikon dauke Ibtisam d

an ya gama shirinsa tsaf inhar ya dauketa to fa can Sokoto ko Zamfara zai lula da ita tunda yanzu suna cikin kasashen da mutane basa san zuwa hakan zaisa baza’ai tunanin can ya kaita ba.

Can yace “ya kamata na kwashi atamfofi da laces na sarar yanda zan

ajiye kudi sosai”

Yai dan murmushi ai ba matsala tunda ya riga ya sanar da abokinsa wanda yake da dan daki akan zai kawota nan a ajiyeta kafin mutane su daina zarginshi shi kuma ya tattara kudi sai su daga.

Kwafa yai yace “Har na hango idan dan banza a

cell an kaishi da sunan yayi garkuwa da amaryarsa.”

Dariyar keta yai a ransa, ai dama yayi kalar masu shan jini dan ya tabbatar wannan kudin ba na Allah da Annabi bane.

{Nikam Ayusher nace to waya sani ko kai ka taramai kudin?

🤔

}

🏌🏻

‍♀

️

💫



IB

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Littafin kudi ne, kudi kalilan zaki biya ki samu wannan garabasar*

13

Da yamma Mamman ya kawo abin

ci, tunda Aminu ya shiga daki bata ga fuskarsa ba sai yanzu dataga ya fito sanye da jallabiya fara, bai kalleta ba ya nufi kofa, itakam tana zaune tana binshi da ido, wannan shine zaman kuramen, da tana ita kadai yanzu ya dawo ma ba wata maraba.

Kofa ya

bude, tare da amsar banbar ledar dake hannun Mamman, tanaji suna gaisawa kafin ya shigo.

Ajiyewa yai akan centre table sannan ya kalleta, idanunta na kansa dama tana ganin ya kalleta tadanyi kasa da ido.

“Abinci ne Ummy ta aiko dashi, ni yanzu zanci ke

ma in zakici yanzu to.”

Mamaki ne ya kamata nufinshi su ci tare? Kartace a’a yaji ba dadi ko kuma ya dauka gudunsa take, ga kuma dankalin dazu ma bataci ba, sai dai tabawa masu aikin hotel din.

Dakinya koma ta mike ta bude babbar ledar ta dauko manyan

kuloli guda biyu masu kyau da tsada, sai kuma karamin bowl mai murfi.

Shinkafa ce da miyan vegetables sunsha kaji, sai bowl din da aka zuba salad a ciki, ta dauko plate ta zuba musu dadan dama sannan tasa miyan a gefe, ganin zata cika plate din yasa ta b

ar salad din tace “sai kowa yasa a gabansa.”

Ajiyewa tai a kasa tasa spoon guda biyu, tana kokarin fito da sanyayen kunun ayan dake cikin jug ya fito hannunsa dauke da kwalin waya, bai kula da abinda takeyi ba ya mika mata wayar hannunsa.

Kallan wayar

tai cikin mamaki kafin tace “Ta mecece?”

Gefe ya kalla yace “Bani wayata.”

Mikewa tai ta bashi da sauri, yasa hannu ya amsa kafin yace “Akwai sim a ciki kiyi amfani da ita, in aka kawo miki taki sai ki zabi wacce kikeso in kuma zakiyi amfani da duka biy

un to.”

Wani irin dadi ne ya kamata, ta dade tanasan iphone amma sanin Abba bayasan kashe kudi ba gaira ba dalili yasa take lalaba ‘yar vivo dinta.

Cikin jin dadi tace “Ya Aminu! Da gaske tawa ce?”

“To ko tawa ce karya nai?”

Haushi yadan kamata shiw

ai maganar mutunci ne bai iya ba?

Takaici yasa ta kasa mai magana, bai damu sai a lokacin idanunsa suka kai kan abincin dake plate, ganin spoon biyu yasa ya fahimci me take nufi.

Cikin mamaki ya kalleta yace “Badai nufinki tare zamuci abincin ba?”

S

osai wannan kalmar ta tsaya mata ta kalli abincin sannan ta kalleshi tace “ Tace kaine fa kace inyanzu zanci to.”

Sosai ya kalleta yace “Inyanzu zakici to kema sai kici, a wani bayanin nace zan iyacin abinci dake? Shekararki nawa?”

Yanzu kam taje makur

a duk da shakkarsa da take ta kalleshi tace “Wai Ya Aminu dan Allah shekara nawa ka bani? Jaririya ce ni ko me? Sannan maganar abinci ni bangane nufinka ba, tunda ka nuna bakaso ba shikenan ba? Amma meya kawo zancen sheka……”

Kallanta dayai ne yasa tadan

tsaya, kai ta kauda gefe tace “Nagode da kyautar waya sannan bangode ba da bakar magana.”

Tana kainan ta shiga daki zuciyarta na tafasa, kofa ta bugo dadan karfi sannan ta zauna a bakin gado, takaici duk ya isheta, ko Iman ba’ace mata yarinya ba amma ita

komai sai ya wani ce yarinya?

Aminu kam mamaki ne ya rufeshi yama kasa ko magana, sai can yace “Ni ta fadawa magana haka?”

Yadan furzar da wata iska yace “Ni?”

Kallan abincin yai sannan ya dau wani plate ya diba ya rufe ragowar ya zauna yanaci, yanac

i yana sake maimaita kalamanta aransa, sai daya kusa cinyewa sannan yace “Ba yarinyar bace? Meye na jin haushi dan an kirata da hakan? Sannan ita banda madai ta rainashi taya zata kalleshi babba dashi tace zai sa cokali yaci abinci da ita?



****

Ibty

kam a daki sai data gama huce haushinta ta dauko wayarta tana kallo, gani tai yasa mata data ta wata daya sannan akwai katin 2k a ciki, dadi ne ya kamata harta saka number Umma zata kira ta tuna kalaman Abba, jiki a sanyaye ta goge, shige shige kawai ta fa

rayi tanata san gano kan wayar.

Camera ta shiga tanasan ganin kyan hoton canera din, tanata kyas kyas taji an bude kofa, daidai lokacin ta dan gyara zaman mayafinta tana yin selfie, ido tadan zaro ta kasa sauke wayar sai kallansa datai, a ransa yace “In

ance mata yarinya taji haushi.”

Fuska a dan daure yace “Abincinki da kika zuba zai huce.”

Sauke wayar tai ta mike tace “camerar wayar nake gwadawa ba wani abin nake ba.”

Kai ya jinjina yace “In ma wani abin kike ai babba ce kinsan me kikeyi no need t

o explain.”

Ya maida kofar ya rufe, kai yadan girgiza yace “Ni har ina tunanin tana zaune ranta a bace saboda abinda na mata.”

Ibth kam yana fita ta rufe fuskarta da hannayenta sannan tadan rankwashi kanta tace “Ba dole yace miki yarinya ba sai shirme k

ikeyi.”

Mikewa tai ta ajiye wayar sannan ta danci mazu, ta daure fuska sosai, yanzu kam tasa a ranta komai cikin girma zata yishi.

Falo ta nufa, yana zaune yadan kalleta ta gefen ido. Abincin ta dauka sannan ta koma ciki bata kalli inda yake ba.

Baya

n ta shiga daki ta maida kofar ta rufe tadan yi murmushi tace “Ko banza na rama tunda naje daukan abinci ban kalleshi ba.”

{Nikam Ayusher dariya nasa nace haka ake ramawa?

🤣

}

*********

Duk yanda Hajiya taso ta kwantar da hankalinta ta kasa, harsu

Ilham suka dawo daga islamiya, takaicinta ya kara karuwa dataga ko waya Aminu baiyi ba, bayan a iya saninta ko tafiya yai yana kira yaji yasu Islam suke.

Kallansu tai suna zaune a falo suna cin abinci, islam sai zuba takeyi, wani abu ne yazo mata ta sa

hannu ta baza ta gumi, ganin basu kula da ita ba yasa tadan fara abin sheshekar kuka, tana dan goge fuskarta da gefen dankwalinta. Ilham cikin damuwa tace “Hajiya jikin ne?”

Hajiya ta dan ja majina tace “Kun taba kallan film din Murjanatu ‘yar Baba?”

Ka

i suka girgiza alamar a’a tace “Dasu na kalla a wata tasha gashi bakwanan balle mu kalla tare.”

Islam tace “Hajiya mutuwa akai a film din yasaki kuka?”

Ta danyi ajiyar zuciya tace “Yarinyar mahaifiyarta ta rasu tunda ta haifeta to sai babanta ya sake a

ure to matar ta dinga uzura mata tana wahalar da ita, yarinyar duk ta rame kullum kuka.” Tadan yi jugum kafin tace “Haryanzu in na tuna ji nake zuciyata kamar zata fito, tsorona kar abinda ya sameta ya sameku.”

Ai nan danan Islam ta rikice tace “Hajiya a

i mu munada Dady.”

Tace “Itama tana da mahaifi amma matsalar shi da yake aiki ina zai san abinda ake ciki a gida?”

Ilham cikin rawar murya tace “yarinyar bata fadawa Babanta bane?”

Hajiya ta jinjina kai tace “Ta fada amma bai yadda ba saboda matar ta

nada kirki a fuska, sannan har tsakar dare take dukan yarinyar.”

Tsoro ne kiri kiri ya bayyana a fuskokinsu, Islam tace “Amma mu Dady ai bazaiyi aure ba ko?”

Tace “Islam ai Dadynku ya riga yayi aure, shiyasa jiya da yau baku ganshi ba. Yana can wani gur

i da matarsa ya fara manta daku.”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login