Showing 6001 words to 9000 words out of 128353 words

Chapter 3 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

7

ta kasa hakuri tace “Ya akai kika ga Yaya? Bayan ya tafi?” Cikin maganar rada ta nuna wallet dinta tace “Abinda kika manta ya dawo ya baki.”

Ganin ana kallansu y

asa Ainah tai kasa dakai tace “Allah ya taimakeshi Umar bai ganshi ba da an rotsawa Yayana mota. Baiji ba bai gani ba.”

Wata muguwar harara Ibty ta maka mata, nan suka maida hankali gun abinda akeyi.

*********

Dattijon da ya shigo kalla tare da ams

a sallarmarsa, fuskarta a sake take sosai, tun safe take jiranshi ya iso dan jiya ba a gidanta ya kwana ba sai yanzu ya samu zuwa. Babbar rigarsa ya cire yace “Asma’u kodai zaki fadi abinda ke ranki ne kafin na zauna? Dan naga alama kin matsu.”

Dan dariy

a tai tace “Alhaji dazu da safe Aminu yazo.”

Cikin fara’a yace “Ai ni nasan abin dama ya shafi Aminu, to meya ce miki?”

Ta dan matso kusa dashi tace “Alhaji ya amince, yace in nemar masa matar da hankalina ya kwanta da ita, ko wacece bai damu ba wai in

dai zan bar mahaifiyar Na’ima ta cigaba da zama a gidan.”

Dariya sosai yai yace “kice farin cikinki ya rabu biyu. To yanzu me kike tunani?” Yai maganar tare da zama akan kujera.

Ta zauna itama tare dayin murmushi tace “ Bari yai auran kaga, ko sati baza

n barta tai ba zan tattarata ta koma garinsu, ai ba a garin maguzawa muke ba, wannan jaraba ta isheni.”

Yace “Wato dai kinsamu daidai dake, shiyasa fadan nan naku ke ban dariya.”

Fuska tadan daure tace “Me kake nufi?”

Yace “ Duba ki gani, ke kin nace

sai ta tafi ita ta nace sai ta zauna, kunsa Aminu a tsakiya ke kiyi amfani da matsayin ki na uwa ita tai amfani da ‘yarta dayake masifar so da ‘ya’yansa.”

Kwafa tai tace “Duk nacin ta dai inyai aure sai ta bar gidan, kasan Allah ko hawan jinin da take cew

a tanadashi ni ban yarda ba, nifa komai na matarnan gani nake karya ne.”

Baffa yai shiru yana kallan Ummy, tacigaba “Naji ‘yan uwanta na kauye sun koreta bayan rasuwar mijinta, amma menene dalili? Ai halin mutum wani sa’in shike sa a kyamace shi.”

Ta da

n kauda kai tana murmushin takaici kafin tace “Ni duk na rasa ma ta ina zan fara nemomai mata.”

Baffa ya girgiza kai yace “Rashin bacci yazo.”

Ta fahimceshi sarai dan duk sanda ta fara nemawa Aminu mace to fa bacci dakyar takeyi ta dinga juyi kenan tana

tufka da warwarewa.

********

Yi tai kamar bata ganshi ba ta cigaba da tafiyarta, tsabar tasan nacinshi yau dakanta tawa su Ainah sallama.

Tana tafe ya matso kusa da ita yace “Ya makarantar?”

Cikin dauriya tace “Lafiya kalau.”

Shiru sukai suna

tafiya tana kallan abokan saurayin jiya suna nunashi suna gulma, itakam wannan masifar ta isheta, wannan wani irin bala’i ne.

Dakewa tai tace “Yaya wai dan Allah bazaka dinga zama a kasuwa ba? In Abba ya tambayeka me zakace?”

Adaidaita ya tare yana cew

a, “ Inhar kinaso hankali na ya kwanta to ki amince na fadawa Abba maganar aure na dake, ai alkawarin da kikasa na miki yanzu yaci ace kin bari kowa ya sani.”

Aranta tace “Ai da’a sani gwara ka kamani kaitamin duka dan ni da in aureka gwara nai ta zama a

haka.”

Jin tayi shiru yasa ya kalleta cikin fada yace “Kwanan nan na gaji da kin maidamun magana da kikeyi, sai na miki magana amma sai kiyi kamar bakiji me nake cewa ba.”

Kallansa tai tace “Ya Umar na rokeka da Allah ka barni nai karatu salin alin, ko

ma menene in mun hadu a gida ma tattauna ka taimakeni ka barni na shaki iska a makaranta.”

Isowar mai adaidaita ne yasa ta fara kokarin shiga cikin tsawa ya kalleta ya kalli mak adaidaitr yace “Barnan.”

Tsaki mai adaidaitar yai tare da cewa “Aikin banza

kawai.”

Umar ya maida kallansa gun Ibtisam yace “Me kike nufi da kalamanki? Kinasan cewa na hanaki shakkar iska ko me?”

Saman goshinta ta shafa tace “Magana wannan ta fahimta bamu isa muyi ba, ta ina zaman aure zai yiwu a haka?”

Ai kamar ta kara ingi

zoshi ya hau fada “Me kike san cewa? Ibtisam na dauka jiya na gargadeki ko?” Ya nunata da yatsa yace “Last warning zan miki, inhar kika kara fadamin magana makamancin wannan ki tabbatar zaki ganni a gaban Abba, kin kuma fi kowa sanin Abba bazai taba hanani

auranki ba.”

Idanunta ne suka ciciko da kwalla, matsawa yai ya tari adaidai yana shiga ta juya ta koma cikin makaranta, sauka yai ya fara bin bayanta yana kiranta.

Bata ko tsaya ba balle yasa ran zata waigo ta kalleshi, gudu yadan sa ya sha gabanta da

sauri yace “Ibty meye hakan?”

Tace “Na manta akwai lesson din da zamuyi yanzu, zan kira Umma na fada mata.”

Agoggon hannunsa ya kalla yace “Amma yau dama 3 kike gama lectures.”

Ta kalleshi sosai tace “In kai ba mahaifina bane na rokeka da Allah ka k

yaleni, lesson zamuyi da kawayena, kuma Abba bai hanani ba.” Ji yake kamar ya cafko hannunta sai dai cikin makaranta suke gashi mutane sai wucewa sukeyi.

Hannunsa kawai ya dunkule ya zabga mata wani irin kallo idanunsa sun kada sosai sunyi jaaa. Wayarsa

da tun dazu take vibrating ya dauko ya kara a kunne ba tare da ya duba mai kiran ba, jin muryar Abba yasa ya gyara muryarsa da sauri tare da sake gaisheshi.

Abba yace “Umar wai kana ina? Meyasa baka zama a shagon ka? Jiya nazo bakanan yau ma haka, ina ka

ke zuwa?”

Bayan kansa ya sosa yace “Abba naje wani guri ne yanzun nan zan dawo.”

Da sauri ya juya ya fita daga makarantar zuciyarsa kamar zata fashe yana tafe yana tunanin ga Ibtisam can da wannan saurayin na jiya yana koya mata karatu suna tuntsira da

riya.

Idanunsa ya rufe ya dunkule hannu kai kace zai tafi dambe……..

********

Mamaki ne ya kama su Ainah ganin Ibtisam ta shigo ajin da suke karatu, zama tai a kusa dasu tare da dafe goshinta.

Cikin tsananin mamaki a tare suka ce “Yau mafarki mu

ke ko me?”

Tsaki taja kawai ta kwantar da kanta akan desk din kujerar da take, Ainah ce ta dafata tace “Ibty Allah ki fadawa Ummanki wannan wani irin bala’i ne? Shi bai bar mazan dake sanki sun kulaki ba shi kuma ba mijin aure ba, na tabbatar akwai mazan

dake sanki amma ganin ki kullum da wannan mutumin yasa suka hakura.”

Hawaye ne ya zubo mata tace “Zan fadawa Umma in har bata yarda da abinda nace ba wallahi Ainah zan kawo koma wanene ko ni da kaina zan nemo zan nemo wani na kawo gida a aura min shi na

rabu da wannan bala’in, bacci wannan banayi sosai, in zauna a falo gun iyayena ai hira ban iyawa saboda yana gida yai ta bina da kallo kamar zai cinyeni, ni kenan a daki kamar mayya, a hakan ma ba bari na yai ba wani sa’in sai dai kawai naga mutum a kaina.

Wannan wani irin bala’i ne? Tunda nake bantaba daukan wannan abin da sunan so ba hauka na daukeshi………”

Yanda take zubar da kwalla ne yasa duk jikinsu yai sanyi, Ainah ta dan jawota jikinta alamar lalashi…….

Ayusher Ce

🏌🏻

‍♀

️

💫

IBTISAM......

💫



(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA

KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA KUDINSA TA*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

*Seka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*

+447894142004

*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number

👇🏼👇🏼

*

070

43079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMAR NAN TA WUCETA BA!*

*ƳAN NIGER

🇳🇪

, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91

36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.

Page 4

 

Haka ya isa kasuwa duk zuciyarshi ba dadi, yayi ta kiran Ibtisam video call taki dagawa. A dan karamin shagonsa wanda Abba ya bude mai yake saida atamfofi da shadda yaga Abban a zaune da alama jiransa yakey

i, yaran dake kula da shagon yana zaune shima suna dan hira.

Dakyar ya daure ya boye bacin ran dake fuskarsa ya sake gaida Abba tare da bashi hakuri akan fitar dayai.

Kafadarsa Abba ya dafa ya kalli yaran shagon yace "Kaje shagona kaci abinci kafin mu g

ama tattaunawa." Nan yai musu sallama ya fita. Umar ya zauna daga gefe wajen kaya, Abba yai shiru yana kallansa, yau ya yanke hukuncin akan su tattauna abinda ya dade yana ayyanawa a ransa, babban dalilin dayasa shi dauko Umar daga kauye gun Yayansa, dalil

in dayasa ya kula dashi kamar dan cikinsa harya bude mai shagonsa. Dan ajiyar zuciya yai kadan irin ta manya yace "Umar banaso muyi maganarnan a gida, nafiso muyita tsakaninmu yanda inhar abin ba me yiwu wa bane mu bine shi tsakaninmu ba tare da ya taba zu

muncin mu ba."

Yanda Abba yai maganar cikin kakkausar murya ne yasa shi tattara hankalinsa ya maidashi gun Abban.

Murmushi yadanyi yace "Aure nakeso na hadaka da 'yata."

Wayyo dadi! Shikenan burina ya cika, abinda kawai yazowa Umar kenan, baisan sand

a kwalla ta cikamai ido ba, tsugunawa kasa yai yana kokarin boye tsantsan farincikin dake ransa, yace "Abba! Nagode nagode nagode....."

Mamaki ya kama Abba ganin bai tsaya yaji ko wacece ba, lalai Umar ya tabbatarmai a matsayin uba ya daukeshi kenan baima

damu da ko wacece ba burinsa kawai ya faranta mai rai. Kaunar Umar ta kara ratsashi ya dan matsamai kafads alamar farinciki yace "Nagode sosai Umar, in ba damuwa gobe ka shirya kaje kauye gun mahaifinka, zan kirashi na sanar dashi kaima saikaje ku tattaun

a kafin mu fara shirye shirye."

A ransa yace ai yanzu zai iyayin tafiya wani gun yabar Ibty dan saboda tsaro ko garinsu yaje baya kwana yake dawowa ji yake kamar inya tafi kafin ya dawo wani ya kwace ta, yanzu kam wata nanauyan ajiyar zuciya ya saki ji y

ake kamar ya saki kara saboda murna da farinciki.

Abba kam dadi ya nashi sukuni kai tsaye gida ya wuce.

Kallanta ya tsaya yi tana zaune akan kekenta tanata ninke kaya da alama wanki akai suka bushe take ninkewa, hamdala yai dan babban tashin hankalinsa a

koda yaushe ya zaiyi ya farantawa Bilkisu rai, tun Umar na shekara sha takwas yasa aka dau jinjnsa aka gwada tunda yaga AA yake ta jiran wannan lokacin dan dama da zuciya biyu ya dauko Umar.

Sallama yai ta juya cikin sanyinta tare da murmushi, ta amsa t

ana kallansa cikin jin dadi, shigowa yai yace "Uwata aiki kike?"

Ta dan birgo keken cikin sakin fuska tace "Abbana sannu da dawowa."

Yana murmushi yace "Ina Umman taki?"

Ta nuna daki tace "Ta shiga yin sallah." Wucewa yai ciki bayan ya mika mata leda

r kayan marmari daya taho dasu a leda, Abba yanada kudi sai dai shi bashi da sakin kudi sosai, a cewarsa dan kasuwa baya almabazaranci, kusan komai da akw bukata na gida shi da kanshi yake siyowa. Umma bata damu ba dan duk wani da suke bukata yana kawowa.

Gana zaune tana lazimi ya shiga dakin cikin nishadi ya zauna abakin gado yace "Hadiza! Burinmu ya kusa cika."

Waigowa tai ta kalleshi tafi kowa sanin burin su guda daya ne, cikin jin dadi tace "Kamai magana?"

Ya jinjina kai alamar eh yace "Inhar na au

rar da Umar ga Bilkisu nasan ko bayan raina komai zai tafi daidai, Ibtisam tasan ciwon kanta, lafiyayya ce sannan tana kaunar yayarta sosai, Iman duk da yarinyar dake kanta tana jin maganar Bilkisu, Umar zai kula dasu sai kuma nema musu miji na gari.

Umma

juyawa tai tare dayin sujjada tana godewa Allah.

*******

Sam yau batasan komawa gida, Ainah tai ta nacin akan tazo suje gida tagaida Ummy, dan sun dade tare tun secondary school suke kawaye, nacin Umar da bibiyar Ibty yasa ko sha'awar zuwa gaida Um

my bata tabayi ba.

Yau kam ganin ta samu pass tana ganin ba lalai ya kara barinta ba yasa tace "muje amma ba dadewa zanyi ba kar Umma ta fara cigiyata."

Dadi ne ya kama Ainah, nan tayiwa Mamman waya akan yazo ya dauketa.

Tare suka fito suna tafe suna

hira, Ainah na bata labarin wani saurayi dayace yana santa.

Ibty tana dariya tace "Amma dai ba soyayya zakiyi da mate dinki ba ko?"

Ainah tadan dafata tace "Hajiya soyayya nace zanyi ba aure ba, dan chilling da rage dare."

Mota suka shiga sunata hira d

a shewa, Ibtisam jinta tai kamar ba ita ba, yau wace rana? Wai itace take tafe gidan kawa hankali a kwance?

  Sun isa tafkeken gidan da tun daga waje zai baka sha'awa, gida biyu ne a hade iri daya kana gani kasan tare aka ginasu, gidan Baffa nesaya Ummy c

e a ciki daya kuma kishiyarta.

Na farkon suka shiga yai parking suka fito, hannunta Ainah ta riko duk sai zumudi take, suna shiga ko sallama batai ba tai ba ta fara kwallawa Ummy kira.

Ummy wacce ke kitchen ta fito tana cewa "Ainah nikam dan Allah sai

yaushe zakiyi hankali? Ko sallamarki banji ba sai kiran sunana da kike kamar wacce kika ban ajiya." Tana kaiwa nan ta karaso cikin falan, Ummy ce ta kalli Ibtisam wacce tai saurin tsugunawa har kasa tana gaisheta. Cikin sakin fuska sosai ta amsa, Ainah tan

a dariya ta matso kusa da Ummy tace "Canka Ummy, wacece?"

Kallanta ta sakeyi tace "Yawanci dai kawayen da ke zuwa nasan sunan su wannan ban taba ganinta ba, sai dai tabbas na taba ganin hotonta, ko Ibtisam ce?"

Kasa Ibty tai da kanta tana murmushi tare

da wasa da yatsun hannunta. Ainah tana dariya tace "Bingo! Ummy wallahi in kika shiga exam hall tsaf zaki fito da A."

Alamun duka takai mata ta kauce da sauri, Ummy tace "Ibtisam lale marhaban mutuniyar sinasir."

Kunya ce ta rufeta tai kasa dakai tanaji

kamar ta nutse, Ummy tai dariya tace "Duk sanda akai sinasir sai Ainah tace "Wayyo mutumin Ibty."

Dan murmushi tai nan suka dan sake gaisawa Ummy sai sake binta da kallo take, haka kawai kaunar yarinyar ta shigeta, ita macece wacce takesan taga yaro da k

unya abinda yai karanci kenan a gun 'yan matan zamani, har suka shiga dakin Ainah idanunta nakan Ibtisam haka kawai ta samu kanta dayin murmushin jin dadi.

Da sauri naga ta girgiza kai tace "Lalai Asma'u kin iya san kai, yanzu harkin farawa Aminu sha'awa

r yarinyarnan? Karfa ki manta sa'ar Ainah ce? Danki kuwa yayi aure harda yara biyu."

 

****

Sallar la'asar sukai suka zauna sukaci abinci, bayan sun gama ne suka zauna suna hira, Ibtisam tana kallan picture album din da Ainah ta kawo mata.

Kallan fa

mily picture dinsu tai wanda kana gani xakasan da biki akayishi, tace "Nasan ki nasan Ummy, nasan Ya Aminu, wadannan fa?"

Ainah yadan nuna picture din amaryar tace "Itace marigayiya" kallanta sosai Ibty tai tare da mata addu'a a zuciyarta, Ainah ta nuna

mata saurayin dake gefen Aminu tace "wannan shine maibin Yaya sunanshi Abbas yana karatu a Canada, sai wannan daga shi sai ni shi kuma yana NYSC"

Ibty tai murmushi tace "Sai ke auta mace."

Gira ta daga mata tace "'yar budurwa ba? Yar lele."

Dariya suka

i, Ibty ta kurawa matar Ya Aminu ido lalai sun dace dan dukanninsh farare ne kuma dogaye.

Kofa aka turo da karfi ana ihu da kiran sunan Ainah, da sauri ta mike ta rugume kyawawan yaran guda biyu a jikinta tare da manna musu kiss tace "Saukar yaushe?"

Is

lam cikin zakin murya tace "Mun taso daga islamiya mukai ta rokar Dady a waya akan ya bari a kawomu, shine yace muzo ya zo ya daukemu."

Kallan Ibtisam sukai wacce ta kura musu ido cikin sha'awa, Islam tace "Wacece ke?"

Ibty tai murmushi tace "Kawar Aunt

y?"

Gaisheta sukai Islam ta matso tadan taba dimple din Ibtisman tace " Aunty kawar Aunty nima ina san wannan abin kisamin dan Allah."

Gaba daya dariya sukasa, Ilham tace "taya zata saka miki?"

Tadan matso kusa da ita sosai tace "kinji Aunty kawar Aun

ty?"

Dariya Ibty tai tace "To shikenan, rufe ido."

Da sauri ta rufe idanta, Ibty tadan dangwali kuncinta tace "bude kika na sa miki."

Cikin zumudi ta tafi madubi ganin bakomai yasa ta turo baki tana shirin kuka, da sauri Ibtisma ta matso tace "Kiyi haku

ri kinji, wannan halitace bayanda zanyi na saka miki, kinga kamar ke kinaga ke fara ce nifa?"

Ta girgiza kai, tace "to in nace ki maidani fara zaki iya?"

Da sauri ta sake girgiza kai, tace "to kingani, halittar Allah ba'a canzata, ko?"

Kai ta daga alam

ar gamsuwa.

Ummy da ke jikin kusa da dakin, jin motsinsu Islam ta taho taji muryarsu a dakin Ainah zata shiga taji Ibty na ma Islam bayani, wani irin kaunar ta ce ta kara shigar ta anya itakam basai dai ace tayi san kai ba? Da alama Allah ne ya kawo mata

Ibtisam saboda ya riga ya rubuta, in ta duba yau Aminu ya yarda da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login