Showing 66001 words to 69000 words out of 128353 words

Chapter 23 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

23

tace “Da yanasan girma yanzu kuma baisan girman dayawa.”

Kunkunin kike ko?

Tadan wayance “Kun

dabu da Ya Umar din ne?”

“Tun awa uku da suka wuce.”

Ajiyar zuciya tai wacce har yana juyo ta, “Zan kashe in ba wani abin.”

Tana tunani ko da abin cewa taji wayar ta katse, hararar wayar tai tare da dan sa yatsa ta dunguri wayar tace “Ai dai kadan jira

kaji ko da wani abin ko?”

Sai kuma tadanyi murmushi dan ba shakka hankalinta ya kwanta jin komai lafiya.

*******

Ganin har la’asar bashida wata mafita yasa ya kalli mai shagon tare da dan sosa keyarsa yace “Malam taimakamin da dubu daya ko dari biy

ar dan Allah, wallahi in na koma Kano a daren nan zan turo maka ninkin kudin daka bani.”

Wani banzan kallo mai shagon yamai, yace “Kai da dubu dayan waya ajiye wani?”

Umar a fusace yace “mene?”

Mai shagon ya kalli jallabiyarsa dadan slippers dinsa ga ka

fa daya wajen yatsarsa a kumbure yace “Mahaukaci ne ni zan baka kudi bayan banga alama ko dari ka ajiye ba?”

Ai Umar a fusace ya shako wuyan rigarsa dan dama a sama yake, kafin mutumin yai wani yunkuri ya kaimai naushi.

Yana kokarin sake kaimai wani wasu

dake kokarin shigowa shagon suka rike hannunsa, fizgeshi sukai daga gun mutumin nan fa mai shagon ya nufo Umar shima ya cakumoshi, dambe ne ya kaure gashi abin haushi kafafunsa na ciwo balle ya koyawa mutumin nan hankali sosai.

Haka suka hadu da wadannan

mutanen suka mai tsinanen duka suka turoshi waje iya karfinsu.

Umar dakyar ya mike yana dudura musu ashar, haka yaja kafarsa da ta sake tsami, can ya nufi gun masu mota yana rokarsu su tafi dashi, sai dai duk inda yaje fada da masifa ne ke rabasu danshi

bazaiyi shiru ba suma kuma bazasu yi shiru ba.

Ganin ba haza yasa ya tafi masallaci dan rokar limab dan magrib ta kawo kai gashi tsoro ya fara kamashi, yana tsoron kar kwana ya kamashi a nan garin, ga uban yunwa datake cinsa wanda har ta tafi da karfinsa.

Haka ya shiga masallaci ransa duk a bace, zagi da tsinuwa kam Aminu yashashi har ya gaji, ya kuma dau alwashin ko zai tafi tsirara sai ya rama abinda mutumin nan yamai.

Gun ladan yaje ya danar dashi yazo Wudil ne an sace wayarsa an kuma sace kudinsa, s

u taimaka mai da dari biyar ya koma Kano.

Ladan ya dauko dari biyar a asusun masallaci ya bashi, haka ya fito kamar zaiyi kuka wai yau shine yake roko? A mai sata dannan a barshi da roko?

Haka yaje gun mai kosai yadan sai na hamsin yaci sannan ya shiga

bus, tunda ya shiga yai shiru yana tunanin yanda zaiyi ya wulakanta tsinanen mutumin nan mai kama da fulawa.

******

Abba ya dawo dab da magrib dadi agun Ibty ba’a cewa komai, haka ya zauna ya sake mata nasiha sannan suka fara hira yana bata labarin yan

da suka hadu da Baffa mahaifin Aminu.

Bayan Magrib Aminu ya iso tare sukaci tuwon dare da Abban sannan suka shirya dan su taho. Aminu ne ya kalli Iman yace “Iman ko zaki biyo mu ne ki mata kwana biyu?”

Cikin zumudi zatace eh sai kuma ta kalli Abba tare

da kunshe baki.

Abba ya kalli Aminu yace “Ai ka barta kawai, kaga ba hutun makaranta sukai ba.”

Aminu ya kalleshi yace “Basai su dinga tafiya dasu Islam ba? In aka saukesu sai a kaita ko in aka kaita a kaisu? Bata taba zuwa gidan yayarta ba sannan na ta

bbatar itama yayartata tanaso taje.”

Ibty ta kalli Abba tace “Abba dan Allah ka barta, sati daya kacal, kaga nima Monday zan koma skul.”

Murmushi yai ya kalli Aminu yace “Shikenan amma sati daya.”

Wani tsalle Iman ta daka ta nufi daki da gudu dan debo k

ayanta.

Umma tana zaune tana kallan yanda abinsu ke tafiya abin sha’awa, sai dai tausayin Bilkisu ya hanata sukuni dan itakam kana gani kasan ba dadin aure takeji ba.

Haka suka fito suka shiga mota suka tafi, Aminu ko tambayar Umar baiyi ba, duk da ya da

uka in sukazo tafiya zai nemi tada wata husumar, da alama ganin Abba na gida ne yasa shi jin kunyar fitowa.

*******

[3/4, 8:06 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o

̝

n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

27

Islam da Ilham ana shiga mota sukai bacci da alama sun gaji, Iman kam sai kallan Ibty take tana kallan Aminu, tunda aka shiga ba wanda yai magana a cikinsu.

Wayarta ta dauka tayiwa Ibty text tace “Kunyi fada d

a Ya Aminu ne?”

Da sauri ta mata reply, “fada kuma kamar ya?”

“Naga ne kunyi kus kamar masu gaba.”

Sam Ibty ta manta ashe fa Iman tana baya, ga Iman da tsinanen sa ido, ai bata mata reply ba ta kalleshi tace “Iman na tambaya wai munyi fada ne?”

Yadan k

alleta ta glass yace “Iman fada kuma? Ni ba yaro ba?”

Tadanyi dariya tace “Nagane kunyi shiru.”

Murmushi yai kadan yace “Jira nake ta warware dazu tayi fishi dani.”

Dan ido Ibty ta bude tace “Ni? Kaine fa kai fishi dani.”

Yana kallan hanya yace “Taya k

ika san nayi fishi?“

Shiru tai tana tunani, Iman ya kalla yace “Kingani? Yayarki tsokana gareta.”

Iman tai dariya cikin jin dadi tace “Yaya kaine fa mai tsokanan da alama.”

“Infadi me tace?”

Ibty ta zaro ido da sauri batasan sanda tasa hannu akan ciny

arsa ba tace “Rufan asiri dan Allah, wlh bakasan halin Iman bane.”

Iman ta koma ta zauna tare da kallan waje tanajin dadin yanda suke rayuwarsu.

Shikam Aminu sa hannun datai a cinyarsa ne yasa yaji wani yadan tsirgamai, shikam me ke damunshi?

Kallan ha

nnun ta yai wanda hakan yasa tadan zare hannun itama cikin kunya, dan matsowa tai cikin dan rada tace “Yaya ka taimakeni karkai maganar nan a gaban Iman, dan Allah.”

Dariya taso bashi ya murtuke yana tuki yace “Bakisan yanzu ba’a aikin banza ba? Kin fi ku

ma kowa sanin ba damuwata bace in na fada ko?”

Mamaki ya kamata itakam wai haka mutumin nan yake?

Da sauri tace “Naji! Koma menene zanyi dan Allah karka fada, wlh tsaf zata fadawa su Umma ba saiti gareta ba.”

Yadan kalleta kadan daidai nan sunzo yin kwa

na, dan jijiga motar tai kadan hakan yasa tadan rike cinyoyin hannunsa dake rike da sityari, bai kalleta ba haka kuma baice komai ba, a hankali tadan zare hannunta tare da komawa ta zauna sosai akan kujera. Iman ce tai gyaran murya tace “Yaya Ibty akwai mu

tum a baya.”

Kamar zatawa Iman magana sai ta fasa, haka suka isa gida yai parking sannan Iman ta fara fitowa, Ibty na kokarin fita taji yace “Kin gama wayan ririkenin?”

Juyowa tai da sauri tace “Wayan rikeka?”

Bai amsa mata ba taga ya fita daga motar,

baya ya bude yana daga tsaye yace “Islam!”

Ibty mamakin kalamansa ya hanata rufe baki, dakyar ta daure ta fito daga motar ta kalleshi tace “Yaya bacci suke bari zan dau Ilham, Iman ta dau Islam.”

Kafada ya daga sannan ya wuce ciki. Da kallo ta bishi ta s

ake maimaita kalamansa wai dama haka yake ko kuma yanzu ne ya zama haka?

Daukansu sukai suka shiga dasu, Iman sai kallan gida take tana santi, kwankwasa kofa taji tana dakin baki tana kallo, fitowa tai falo tace “Yaya Ibty waye da daren nan?”

Jin shiru

yasa ta leka dakinta, karar ruwa dataji ne yasa ya fahimci wanka take.

Kofa ta nufa kanta tsaye ta bude, kallan kallo suka farayi da matar dake tsaye hannunta dauke da tire dake dauke da kuloli.

Iman tai murmushi tace “Me aikin gidan ce?”

Hajiya wacce

ke tsaye dauke da kosai a flask da kunu a jug tace “mai aiki?”

Iman cikin ko in kula tace “Ko makota?”

Cikin mamaki da takaicin kalamanta Hajiya tace “Ke din wacece?” Tayo maganar ne bawai dan batasan amsar ba dan kana kallansu da Ibty zakasan ‘yan gida

daya ne saboda kama.

Iman tai murmushi tace “Kanwar matar gidan ce.”

Hajiya ji take zuciyarta kamar zata tsinke, dazu bayan tafiyarsu ta nemi wata kawarta ta hadata da wani saban malami shine ya bata magani yace tasa a abinci daga Ibty har Aminu suci b

a ahinda zai shiga tsakaninsu sai tsana da kyama. Ganin Iman a gidan yasa gaba daya gabobin jikinta sun mutu, bama damuwar ta cin maganin ba a’a haryaushe Aminu ya auri yarinyar da har zata fara kawo ‘yan uwanta?

Iman ce ta katseta da cewa “Goggo in baki

fadi ke wacece ba zan koma ciki, na gaji da tsayuwa.”

Goggo? A gidan uwarki na tsofan da za’a kirani haka? Abinda ta fada a ranta kenan, kamar ta mika tiren tana kuma tsoron kar wannan fitsarariyar taci, to amma ko taci menene damuwarta? Itama tsana ce za

ta biyo baya.

Mika mata tiren tai tace “Kiba Ibtisam din kice gashi inji Hajiya ba Goggo ba.”

Iman ta kalli kwanan tace “Kiyi hakuri Hajiya, nikam bazan amsa ba sai ta fito ta tabbatar da ta sanki, dama na dauka mai aikin gidan ce, duniyar nan ba gaskiya

.”

Hajiya ta zuba mata ido tana mamakin yanda ‘yar karamar yarinya ke zuba mata fitsara haka, wannan dabadan a gidan Aminu bane da tuni ta tsinka mata mari, bata kara shan mamaki ba sai dataga Iman ta maida kofar gidan ta rufe.

Dakin Ibty ta koma haryanz

u tana toilet, drawer dinta ta bude tana kallan uban kayan da ke jere a ciki, lalai gobe zata dau kaya tai hotuna, dan hotunan ta suk sun tsufa, gaban madubi ta zauna tana ta shinshina turaruka masu kamshi.

Ibty ce ta fito daga toilet sanye da towel, pill

ow din kan gado ta dauka ta cilo mata ita karfinta, sai dai bata sameta ba, Iman ta juyo tana dariya.

Ibty cikin dan fada tace “Zaki fara ko?”

Dariya sosai tai tace “Yaya Ibty dan Allah nima in zakuyi aurena ku hadomin kaya dayawa da turaruka, ni na yafe

wasu abubuwan.”

Kai ta girgiza tana goge jikinta tace “Wato dai zancen auren ne bazaki daina ba ko?”

Kayan bacci Ibty ta fara nema, wata yagal yagal din riga ta daga da sauri ta maidata.

Ai Iman ta mike daga kan kujerar da gudu ta fizge rigar ta waret

a, ido tadan rufe tace “Yaya Ibty wannan kika saka ai Ya Aminu sai ya kusa suma.”

Duka takai mata a baya tace “Allah Iman ki fita idona.”

Maida rigar tai tace “Allah kina abu kamar ba wayayyiya ba, ko ni yanzu akai aurena rigar datafi wannan fitsara ma s

awa zanyi. Mazan yanzu sai kana jan hankalinsu.

Hannu Ibty tasa ta turata daga dakin tace “Lalai yarinyarnan, yaushe ta fitsare haka?”

Rigar taje maidawa sai kuma ta kara kallanta, irin ‘yan kananan rigunan baccin nan ne shara shara gashi batakai ko gwiw

a ba, da net akai rigar.” Kai ta girgiza da sauri tace “Dazu daga tabashi yace da sanina, haka jiya da daddare yau in nasa wannan ai cewa zaiyi na matsu.”

Riga ta dauko mai gajeran hannu sannan wandanta shima three quater ne, ta saka sannan ta fesa jikint

a turare mai dadin kamshi, kanta ta tufke da ribbon sannan ta daura zani ta tada sallah.

Iman kam sam ta manta da batun matar dake waje, itama dakinsu Islam ta wuce tai alwala ta wuce dakin baki tai sallah, Ibty ce ta fito sanye da hijab ta bude dakin dai

dai nan Iman ta idar da isha’i, fitowa tai ta wuce kitchen ta kuna kettle tasan ruwan tea.

Iman ta fito da sauri ta shiga kitchen tace “Yaya Ibty? Na manta wata mata tazo wai ko Hajiya?”

Gaban Ibty ne yadan fadi tace “Hajiya?”

Kai ta daga tace “wlh na

manta tun dazu tazo, amma na tabbatar yanzu ta tafi.”

Yanda Aminu ya rufeta da fada ranar ta tuno, da sauri ta karasa ta bude kofar, bakowa a gun, fuska Ibty ta shafa shikenan yanzu gobe zata kara kai kararta gun Aminu. Itakam ya zatai da wannan bala’in?

Dawowa ciki tai tace “Iman meyasa baki kirani ba?”

“Kina wanka lokacin, ni kuma na dauka mafa mai aiki ce, wai wacece?”

Ruwan tea ta zuba a flask tace “Mahaifiyar matarsa ce data rasu.”

Cikin rashin fahimtar yaren tace “Mahaifiyar matarsa?Ban gane ba.

”

Murmushin yake kawai Ibty tai ta dau kayan tea din tace “Hakan dai dana fadamiki.”

Ta kalleta tace “Dan Allah kafin ki kwanta ki kai Islam fitsari.”

Cikin mamakin da har yanzu bai saketa ba ta daga kai alamar to.

Wucewa Ibty tai jikinta duk yai sany

i, dakin Aminu ta nufa, sallama tai tana kokarin budewa taga anbude kofar daga ciki.

Kallan juna sukai, ya kalli kayan tea din yace “ Bakya tsoron wata rana ya zubar miki a hannu garin bude kofa da hannu daya? Yanda kike din nan ba karfi ba?”

Tai dan m

urmushi tace “Yaya ramawa dai kai ko?”

Falo ya fito yadau wayarsa ya koma dakin, kallanta yai ya zauna akan kujerar da take guda daya a dakin yace “Wai dai a yanda kike din nan na tambatar dakyar kike rike kayan tea din.”

Ta dan fara karkade gadan tace “

Allah Yaya kabar ganin mu sirara karfi garemu.”

Yadan tabe baki kadan yace “Ko a kira Iman a tambayeta?”

Kai ta girgiza da sauri tace “Dan Allah ka rabani da Iman, Allah dan baka santa bane.”

Hannu ya mika mata, kallansa tai sannan ta tako a hankali zuw

a inda yake zuciyarta cike fal da tunanin me yake nufi da miko hannu? Isowa tai wata zuciyar tace “ko so yake ya tabaki yaji karfinki?” Wannan tunanin shine ya tsaya mata, hannunta yaji a cikin nashi, hakan yasa ya kalleta tare dadan murza hannun kadan, aj

iyar zuciya tai kadan da alama yau ta canka daidai.

Dagowa yai ya kalleta yace “In nayi magana ace nace.”

Ta kalleshi cikin kunya tace “Mene?”

Hannunta ya juyo da cikin tafin hannunta yace “Do you like me to hold you that badly?”

Hannunta ta zare da s

auri tadan zauna a bakin gado cikin wani yanayi tace “Wai Yaya meyasa kake min haka dan Allah?” Tai maganar kamar me shirin kuka.

“Lipton dina dake kan madubi nake nufi ki bani.”

Jitai kamar tasa ihu, ta mike ta dauko ta mikamai cikin fishi, tana neman j

uyawa taji ya riko hannunta. Juyowa tai idanunta sun ciko da kwalla, kiris suke jira su zubo, kallansa tai batai magana ba.

“Okay, yanzu na rikeki da kaina, happy?”

Hannunta ta shiga fizgewa wasu hawaye suka zubo mata, duk yanda taso ta kwace ta kasa, sh

ikam Aminu baisan meke damunshi ba haka kawai tun randa yasan abinda ke faruwa tsakaninta da Umar ya samu kansa da san zolayarta, har mamakin kansa yakeyi, dan bai taba jin yanasan tsokanar mutum ba sama da ita.

Ganin tana hawaye ne yasa ya dan jata kada

n yanasan yi mata magana ganin ta juya, kasancewar bata kawo zai jata ba kawai ta fada kan cinyarsa, wani yanayi ya tsinci kansa a ciki, tare da dan hadiyar wani abu dake makoshinsa.

Saitin kunnenta ya matso yace “Yanzu fa? Gashi har cinyata kin samu kin

zauna, am sure yau zakiyi baccin dadi.”

Kallansa tai cikin hawaye tace “Yaya Allah ka daina min haka, yaushe na…….”

Yatsarsa yasa akan labbanta alamar tai shiru, kwarjininsa ne yasa ta kasa magana, sai wani yanayi data tsinci kanta a ciki, itakam ta tabb

atar tana san Aminu, sai dai shi ta tabbatar ba santa yake ba.

“Kina cewa wani abin zan sanar da Iman me kika ce akanta dazu a mota.”

Tadanyi kasa dakai saboda nauyinsa dataji, gashi yanda sukai daf da juna tana kan cinyarsa kunya duk ta rufe ta.

Gyar

an murya yai yace “Sai yaushe za’a daga ni? Ko so ake kafata tai tsami?”

Mikewa tai da sauri tace “Kaifa ka daurani.”

Yadan matsa inda ta zauna yace “Dama gun ne da jarumin saurayinki ya nemi min illa kinga yanzu kin sake…..”

Cikin sauri yaga ta tsuguna

tasa hannunta agun tace “Dukan kafar taka yai? Inalila.” Tai maganar tana taba gun, duk ta rude.

Gyaran murya ya sake yace “In kin gama tattabani inasan nasha tea kafin ya huce.”

Da sauri ta mike ta wuce gun kwanciyarta taja bargo da sauri ta rufe har

fuskarta.

Baisan murmushin daya bayyana a fuskarsa ba yadau tea yana kallanta, haka yara age dinta suke ko itace haka? Sake murmushi yai yana kallan wayarsa.

*******

A galabaice ya sauka daga cikin motar, dan an matseshi yaji jiki sosai a motar, dan k

osan dayaci duk ya gama tafiya daga cikinsa.

Adaidaita ya tara ya nemi taimako akan ya kaishi Tarauni in ya shiga gida zai dauko kudi ya bashi.

Mai adaidaita ya kwashe da dariya yace “Kai yanzu malam banda ka rainani in daukeka sai naje gida ka gudu? Sa

nnan in tambayi gidan da ka shiga ace ba’a sanka ba?”

Umar saboda yunwar dake damunsa yasa bashida karfin masifa yace “In na gudu ina zani? Ka taimaka ka kaini.”

Ai kafin ya karasa magana mai adaidaitan ya tafi. Haka ya dinga takawa dakyar duk adaidaitar

daya tare in yaji sai yaki amincewa da uzurinsa, ga uban yunwa ga gajiya, ga dukan dayasha ga kuma kafarsa dake azabar ciwo.

Haka ya dinga jan kafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login