Showing 111001 words to 114000 words out of 128353 words
kuma ta dade a gidana muna tare taya zaka ce min tana aikata zina? Kuma ma ta hanyar inda A
llah yai gargadi da cewa kar a kusanta?"
Likitan yai shiru ganin yadda lokaci daya Aminun ya canza masa, sai da likitan ya tabbatar Aminu ya gama magana kafin ya bashi amsa.
"Wannan ne kuma bansani ba kamar yadda alamu suka nuna cewa kaima baka san yad
da akai haka ta faru ba. Ada dakace sirikarka harna fara zargin kaine to sai dai yanzu ka tabbatar min da bakaine ba. Sai dai ga babban hujja, lokacin da tana nan zaka dinga jin wani irin wari tusa yana tashi in ta zauna a kusa dakai zaka dinga jin abin na
tasowa daga jikinta."
Aminu yai shiru yaki cewa komai duk da cewa yaji warin kamar na tusa, amman da yake bai yarda da kalaman likitan ba sai yaki cewa komai.
"Bansani ba ko kaji ko kuma ni kadai naji, irin wadannan masu aikata laifin basu iya rike tusa
. Kuma basu iya rike kashi, sannan suna yawan yin ciwon ciki saboda tsotsotsi ne a ciki wanda dole sai ana yawan yi spam yana shiga shine abincin su. But akwai magani, sai dai akwai tsada."
Aminu dake zaune gumi duk ya jika masa jiki, ya rasa yadda zai d
auki abin cikin zuciyar shi. Tashin hankalin daya shiga baya misaltuwa, ko sanda akaga takardar nan bai shiga rabin tashin hankalin daya shiga yanzu ba.
Hajiya ce da wannan kazantar ? Uwar matarshi? Kakar 'ya'yanshi? Jiyai kansa na wani iein juyawa gaba d
aya ya kasa fahimtar abinda ke faruwa.
Wayarsa ta yi ringing ya zaro a hankali, ibty ce yana kuma da tabbacin Hajiya zata tambaya, me zai ce da ita?
Taya zai rufe wannan mummunar kazantar ba tare da kowa yaji ba? Baya so aji dan abin kunya ne abin Allah
wadarai. In 'ya'yansa suka taso sukaji wannan kazantar fa? Kafin ya daga harta katse hakan yasa shi kallon likita kamar zai fashe saboda tsabar fushi da tashin hankali yace masa.
"Meye abin yi likita?"
"Zamu yi iya yin mu wajan ganin mun taimaka mata in
dai kunshirya yin haka."
"Kuyi mata duk abinda ya dace zan biya, amman dan Allah ya zama sirri. Sannan zan turo wanda zai dinga zuwa yana dubata yana kuma jin abinda ya kamata."
"Babu matsala indai akwai kudi, dan irin wannan abin kudi sune best saboda m
agungunansu tsada garesu. Wasu ma sai munyi order dinsu daga wata kasar."
Tashin farko kawai Aminu sai da ya biya dubu tamanin da biyar, ko takan Hajiyar beyi ba ya fice yaja motarsa saboda wani irin bakin ciki da yake ci masa zuciya. Da kyar ya iya koma
wa gida, yanayinsa kawai yasa Ibty shiga tashin hankali dan daki kawai ya wuce ba tare da ya kalli inda takeba, kuma yana shiga yasa key ya kulle.
Itakam Ibty abinda yazo mata shikenan an sake rabasu, da alama yanzu numfashinta ne ma ba'aso.
*******
Kayansa dake shanye kan igiya ya kwaso, tabbas yau babu abinda zai hanashi komawa Kano, bazai iya zaman kauyen nan ba ko kadan. Gwaggo na kallasan har ya gama zuba kaya a cikin jakarsa ya fito yana ta faman hura hanci. Batace masa uffan ba taci gaba da ai
kin ta, Umar ya takarkare yace.
"Gwaggo kudin mota zaki bani." Tayi masa kallan mamaki.
"Da kazo kasan zaka tafi me yasa baka yi aikin kudi ba? Kai ni wannan jarabar ta isheni, tunda kazo gidan nan ka fitineni daga kace wannan sai kace wancan haba."
"Ki
ban kawai nidai dan Allah, yau fa kinyi cinikin kosai da yawa."
"Ido kake samin kenan? To idan nayi cinikin ina ruwanka? Man tuya ka bani ko waken yin kosan? Ni ba abinda zan iya baka kudina na sana'a ne bana hawa mota ba, idan kaji haushi kaima ka fara s
ana'ar."
Umar yai shiru haushi da takaici sukai masa yawa, gurinta kawai zai iya samun kudin saboda shi ba wani mutunci yake yiwa yan uwa da abokan arziki ba a kauyan, dalilin da yasa suke ce masa mai girman kai.
Umar ya janyo turmi ya zauna tare da yi
n tagumi yana neman mafita. Yau Insha Allahu zai koma Kano dan ba zai iya rayuwa a cikin kauyen nan ba. Yana zaune yaji an cilla masa abu, ya kalli saman kamarsa sai yaga dubu daya da sauri ya kalli Gwaggon tare da yin murmushi ya mike tsaye.
"Thank you m
y Gwaggo, Kinga ai hakan yayi da ace miki na saci na wasu." Suka hada ido sai fara'a yakeyi.
Babu sallama ba komai Umar ya dafe dubu dayarsa yai gaba, Gwaggo ta girgiza kai a ranta tana masa fatan shiriya. Inda Allah ya taimakeshi yana fita yaga wani abik
insa zai fita bakin titi a mashin ya rage masa hanya, yana tsaye har Allah ya kawo masa mota ya shiga suka tafi yana ta sauke numfashi, ji yake tamkar an ciro shi daga kaya saboda tsabar ya gaji da garin...
Ayusher ce
🏌
️
♂
️
[5/10, 3:11
PM] Hauwa Galadima:
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
Ki hanzarta ki mallaki naki
🤸🏻
♀
️
*TURA 500 Ka samu rahusar novel
bakwai tare da shirye shirye TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004
Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*46*
Tunda ya shiga daki ta koma ta zauna akan kujera dabas gaba daya mamaki ya hana Ibty
yin motsi, tasan za'ayi haka tabbas dan tunda yace gurin Hajiya zashi tasan da wahala ba'a sake hargitsa mata shi ba. Haushi duk yabi ya kamata saboda ita ta barshi ya tafi, inda ta dage akan cewar tare zasu tasan zai yadda. Wai har sai yaushe ne Hajiya z
atabar Aminu yai rayuwar jin dadi? Daga auran yarki shikenan sai abu ya zama masifa da bala'i? Kodama auran ai ba dasaninsa ba.
Ibty kam ganin zancen zuci bayi mata zai yi ba yasa ta koma daki, wajan madubi ta nufa tana kallan kanta. Ko har sai yaushe za
su samu kwanciyar hankali kamar ko wane ma'aurata?
Kwana biyu ta huta da matsalar Umar, amman ta kasa rabuwa da matsalar Hajiya. Ibty ta kuma matsar da fuskarta tana karewa kanta kallo tace "Ada ta dauka uwar miji itace matsala sai dai a nata bangaren ta
rasa da me zata kira Hajiya, wannan bala'i dame yai kama" Kanta ta dafe, ada ta bari Umar ya takurawa rayuwarta, nan ma Hajiya ta takura ma rayuwar auranta sai dai tana ganin yanzu bazata bari a kara shiga tsakaninta da Aminu ba, shine farincikinta, turar
e tasa hannu ta janyo ta feshe jikinta dashi sannan ta fito. Dakin Aminu ta nufa, cikin shahada ta dan murda tana fatan Allah yasa ya bude kofar, jin kofar ta bude yasata yin wani ajiyar zuciya, a hankali ta tura kofar gani tai bakowa a kan gadan, dan tura
kofar ta sakeyi yi sosai, me zata gani? ganin kasan dakin tai duk kaya hakan yasa tai saurin shiga.
Turarukan kan madubinsa ne duk ya watsosu kasa, sannan takardar hutansa shi da Na'ima wanda glass din ya fashe Aminu duk ya yaga shi, yana tsaye rike da
kai alamar ya rasa mai zaiyi. Ibty ta kalli Aminu zuciyarta na bugawa dan tana tsoran ya juyo ya ganta yai mata wulakanci. Amman duk da haka sai da ta nemo juriya ta dake sosai ta karaso ciki ta tsaya a bayansa tayi masa magana cike da kulawa.
"Zuciyar d
a aka ginata da hakuri babu abinda ya kamaceta a koda yaushe sai hakurin, Abban Islam kana cikin jarabawa mai matukar wahala, sai addu'a da fatan Allah ya baka ikon cinyewa. Kayi hakuri ka fitar da kanka daga jikin Hajiya shine kawai zai sanya ka samu lafi
ya da nutsuwar zuciya."
"How?" Ibty taji ya fada cikin juyowa a fusace, kafin ta kuma magana yaci gaba da cewa.
"Taya zan yi nesa da ita bayan akwai Ilham da Islam a tare damu? Meyasa Hajiya zata min haka? Ta cuceni ta cuci yarana da zasu yi mata kallon
kaka. Wallahi nayi da..." Sai kuma ya kasa karasawa ya kalli ibty yana cizon labansa.
Taku daya ta kara ta kwantar da kanta a gadan bayansa, dan yanada tsayi duk da itama tanada tsayi amma bata kaiwa samansa, idanunta tadan kumshe ta daura hannu a gefen k
anta tace "Kayi hakurin daka saba yi, Habibty........." Kalamanta sun matukar sanyaya masa zuciya har besan lokacin da ya juyo tare da kamo kafadunta ya rike ba ya rungumeta a jikinsa tsam.
"Thank you." Ya fada, dagota ya sake yi yadan karkatar dakai yace
"A tabbatar an cigaba da kirana da wannan sunan."
Labanta ta hade jitai ya sunbaci saman goshinta. Tadanyi murmushi tace "Ni kunya nakeji in kiraka haka a gabansu Islam."
Kunnenta ya matso yace "Ya zakiyi?"
Tace "Dame?"
Yai wani murmushi "Dole ki kira
ni haka, dan in bashi ba bazan amsa ba."
Baki tadan turo, yatsarsa ya dan hade kamar sai rankwashi goshinta hakan yasata runtse ido da sauri, ji tai ya jawota jikinsa ya rungume, "Gobe kinada skul ko?"
Kai ta daga, ya jinjina kai yace "Yara fa?"
Suna d
aki suna wasa, yadan daga kai, sannan ya juya kallansa tai taga yanda yanayinsa ya canza, jiki a sanyaye ta kalleshi dan yaki sanar da ita abinda yake faruwa da Hajiya ita kuma batasan tambayarsa, shikam a ganinsa shi kadai ya dace yaji wannan abin.
***
*****
Sanye take cikin riga da skirt na lace maroon color, tayi kyau sosai, Iman ce dake koyan kwalliya ta fente mata fuskarta, ta fito das da ita, sai murmushi takeyi ita kadai. Kekenta ta gunguro har zuwa falo ta tsaidashi a inda ta saba, wayarta ta c
iro a gefen wani aljihu dake jikin keken ta fara daukar selfie, tana juyar da wayar zuwa wajan kofa sai kawai ta ganshi ya daga labule. Cikin tsananin zumudi ta juya gabaki daya, suka tsaya kallan juna kowa da abinda yake sakawa a ransa.
Umma ta fito dag
a kitchen dauke da robar alayahu xata yanka a falo tagansu, Umar yai kasa da kai jiki a sanyaye. Ganin haka yasa Umma tayi saurin karasawa inda Bilkisu take. Gungura keken tayi zuwa hanyar daki ranta fuskarta a hade. Bilkisu kuma hankali ya tashi, ganin Um
ar a yanzu ba karamin taso mata da miken daya fara warkewa yai mata ba.
Suna shiga daki ta rufe kofa tare da kallanta tace "Ina so idan kinga Umar ki dinga kama kanki Bilkisu, saboda har zuwa yanzu hankalinsa yana wajan yar uwarki. Ke ko zuciya baki da it
a? Daga dawowarshi yau kike neman bada kanki?"
Umma na kaiwa nan ta fice zuwa falon tana faman hade rai.
"Umma barka da rana." Umar ya fada yana sosa kumatu. Taki tanka masa bare yasa ran magana mai dadi, zama tai ta jawo robarta ta fara yankan alayahunt
a.
Ganin batada niyyar kulashi yasa ya tsuguna yana gaisheta, nan ma ba amsa, ya daure yace "Umma! Abba baya nan ne?" Yaji ta kuma yin shiru sai aikin ta kawai takeyi.
"Dan Allah Umma ki kulani." Kamar ya tunzura ta nan ta juyo tana masa kallan wulakanci
tana cewa.
"Umar ka matsa min da tambaya fa, idan na goya Abban ai zaka ganshi a bayana ko? Ni abinda ya bata min rai ma shine mekadawo yi gidan nan? Bakace sai Ibtisam ta kaso auranta ta dawo ba sannan hankalinka zai kwanta? Bari kaji in gaya maka wani
abu, IBTISAM tana gidan mijinta, sakamakon biyayya da tayi na karbar zabin da aka yi mata yanzu haka babu wanda Aminu yake matukar so da kauna sama da ita. Kai kuma an baka ka raina ko? Toh ba zaka bar gidan nan ba sai da takardar sakin Bilkisu a hannuna."
Umar ya kalli Umma cikin wani irin yanayi, har zai ce su kwada Bilkisu su cinye, sai kuma ya tuna kauye da sauri ya durkusa kasa kamar zai mata kuka yana magiya.
"Umma dan girman Allah karku rabu mu, nifa na hakura zan zauna da Bilkisu har mutuwa walla
hi. Naso Ibtisam amma yanzu da Bilkisu zan zauna."
Hannu ta daga mai tace "Kaga Umar bana san shirme da shiririta kaji ko? Idan har dan zama ne ai ba guri Bilkisu ta rasa ba a gurinmu."
"Umma ina nufi ina san Bilkisu."
"Karya ne, nasanka sarai Umar. Ko
ka manta rashin albarkar daka dinga gabza mana saboda kana ganin mun rabaka da rabin ranka?"
"Wallahi da gaske nake Umma, dan girman Allah ku sake bani dama na kasance tare da Bilkisu." Umma ta yatsina fuska tace.
"Zanyi shawara tukunna." Tana kaiwa nan
ta shige daki tabarshi a inda yake. Umar ya cije lebensa ya tashi ya fita dan jiran Abba ya dawo ya karbi mukullin bangaransa. Wai akan wacen nakashashiyar ake wani juyashi? Tsaki yai ya zauna akan benci yana tunanin yanda yasha love dinsa da Ibtisam, lala
i duniya ta juyamai baya dole ne ya lalaba Bilkisu.
Koda Abba ya dawo da daddare yaga Umar ba karamin mamaki yai ba, amman saboda yasan haukansa yasa Abban kin kula yasan da zamansa a bakin gate din. Abba na fitowa Umar ya zube a kasa yana rokansa akan
ya yafe masa, sannan yayi hakuri ya bashi Bilkisu su koma bangaransu. Abba yaki kulashi ya shige gida Umar yabi bayansa.
"Wai Umar bakace sai IBTISAM ta baro gidan auranta ba? Ka zauna har randa zata fito din, amman ba zan baka Bilkisu ba dan bansan mekaj
e kauye ka kullo mata ba. Wulakancin daka mata da yanzu bazan bari a mata kwatan kwacinsa ba.
"Haba Abba." Cewar Umar yana turo baki.
"Nayi karya ne?"
"Abba meka maidani?"
"Oho maka."
Tashi Umar yai kawai sukaga ya wuce zuwa dakin Bilkisu, babu wanda
yabi ta kanshi ganin fitina yakeji da ita yau din. Zaune ya sameta tana ninke kaya, tunda ta kalleshi sau daya bata kuma ba duk da cewa ba haka zuciyarta taso ba. Shima Umar karewa dakin kallo yai wanda ke faman kamshi. Nashi dake kauye ya tuno banda warin
akuyoyi da kaji babu abinda yake yi.
Zama yai a bakin gado kawai ya baza wani uban tagumi, kallan Bilkisu yai kamar mai shirin kuka yace "So kike ni dake mu zama zawarawa?"
Bakinta tadan motsa tanasan magana sai dai tasan tana farawa zata kwafsa, yadan
ja hanci yace "Naji na miki laifi amma ai ke mai fahimtace, kinfi kowa sanin ba halina bane, abinda ya faru ne yazomin cikin ba zata koni abinda na miki baimin dadi ba....."
Yadan rike hanci kamar mai neman yin kuka, jikinta ne yai sanyi, ta kuramai ido t
ana tunanin abinyi, jitai ya jawo kekenta ya rungumeta wai shi a dole kuka yake, rikicewa tai tace "Na hakura Ya Umar dan Allah karkai kuka....."
Ya dade sosai a dakin shida Bilkisu, abinka da miji da mata akace sai Allah Abba da Umma sukaga Umar yana gu
nguro Bilkisu, babu wanda yai magana har suka karaso falon, Umar yace.
"Abba mukullin." Wani kallo Abba yamai, Bilkisu tace "Abba dan Allah."
Babu musu ya dakko keyholder dinsa ya ciro ya mika masa yana mai wani kallon tuhuma.
"Zamu tafi bangarenmu tare
da matata." Umar ya fada kai tsaye. Suka hada ido da Umma ganin batace komai ba yasa Abba yi masa sallama da hannu. So hana ganin laifi, kiri-kiri soyayya ta rufewa Bilkisu ido ta yadda bata ganin komai sai Umar koda kuwa zai kaita wuta.
*********
H
ajiya kam jiki yayi tsanani, anata yi mata magani amman da ta farajin sauki sai wani ciwon ya bullo. Hajiya duk lokacin da take cikin sauki bata da zance sai na tambayar likita yaushe Aminu zai zo? Likitan ya sanar da ita cewa shima baisani ba. Shi kuwa Am
inu yau tsab ya shirya tana dawowa daga makaranta yace da ibty ma ta shirya zasuje unguwa.
Murna ta cikata dan tasan gida zai kaita, bayan ta fito daga wanka tsayawa tayi gaban wardrobe yatsanta a cikin bakinta sai ciza takeyi, tunanin kayan da ya dace t
asa takeyi, amman duk wanda ta kalla sai taji be dace da yau din ba. Tafi minti biyar kafin idanunta ya tsaya kan wata doguwar riga ta atamfa golding brown an jera stones sosai a jiki, Ibty ta janyo ahankali ta warware tasa.
Murmushi tasaki ganin tayi kya
u sannan ta daura dankwalin tabi jikinta da turaruka. Tana cikin saka lipstick da wayarta cikin handbag Aminu ya shigo, ta dago tana kallansa sukai ido hudu. Wani irin yanayi Aminu ya samu kanshi, zuciyar shi ta shiga cikin wani irin shauki. Yana mamakin y
adda a hankali yar yarinyar nan take sake mallakar duk wani sashe dake jikinsa, yana mamakin yadda karamar yarinya kamar ibty take neman sarrafa duk wani tunani da yake dashi.
"Ka gama na fito ne?" Aminu ya kasa magana sai matsawa da yai gab da ita, ta ka
war da kai saboda yadda kirjinta yake bugawa.
Hannunsa yasa a kan kugunta hakan yasata dan sakin wata karamar ajiyar zuciya.
"Wai kin dauka lunch zamuje wani gurin?" Ya fada yana dan matso da ita kusa dashi. Ibty ta zaro ido.
"Ina zamuje to? Nazata gida
zaka kaini mu gaisa dasu Umma?" Aminu ya bude ido.
"Gida kuma? Ba gida zamu ba unguwa zaki rakani."
"Daga unguwar fa sai ina?" Tayi maganar tana shagwabe fuska. Murmushi yayi tare da sumbatar saman lebenta yace.
"Sai mu dawo nan gidan."
"Kai Yaya."
"
Dagaske nake miki." Ya saketa yana juyawa.
"Idan kin gama ki taho ina mota."
Ibty ta bubbuga kafa a kasa irin na yan yara, yana jin ta amma yaki waigawa sai dariya da yake yi har ya bar dakin. Mayafinta ta dauka tasa takalmi