Showing 78001 words to 81000 words out of 128353 words
kwanta shima, ji take kamar tadan shiga jikinsa ta rungumeshi suyi bacci a haka, sai dai yanda ya juya baya yasa tasan ba zata iya ba.
Cikin baccinta ta dinga ganin wani abu mai ban tsoro wanda bata taba ganin irin hallitar
ba yana biyota a cikin wani bakin daji, gudu take iya karfinta sai dai abin yaki daina binta, gaba daya zufa ta gama karyo mata ta ko ina, sai girgiza kai take cikin bacci.
Aminu cikin bacci yaji kamar ana motsi da karfi, gashi basu dade da kwanciya ba,
juyowa yai ya dan kunna wayarsa, ganin yanda take gumi yasa ya jawo ta jikinsa ya na tofa mata addu’a.
Gaba daya tausayinta ne ya kara kamashi, badai karfi ya nuna mata ba har take zabura cikin bacci ba?
Idanu ya runtse lalai Aminu baka kyauta ba. Haka y
ai tadan shafa bayanta kafin bacci ya dauketa.
*****
*SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA
🗣
️
*
*SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA
🗣
️
🗣
️
*
*SAUKI.... MTN, AIRTEL, GLO, 9MOBILE DATA
🗣
️
🗣
️
🗣
️
*
*NUCEEYLUV
😘
NA MUKU ALBIS
HIR DA DATA DINTA ME SAUKI AKAN FARASHI ME RAHUSA, MAZA KU GARZAYO SAUKI DATA A CANCARE KU DA DATA A BAGAS
🤸🏻
♀
️
, TURAWA BABU BATA LOKACI
📤👌🏻
*
*MTN*
50mb-50
150mb-100
500mb-200
1GB-300
2GB-600
3GB-900
5GB-1500
10GB-3k
20GB-5k
*Codes fo
r check balance, *131*4#*
*1MONTH VALIDITY*
*AIRTEL*
100mb-150
300mb-250
500mb-300
1GB-600
2GB-1200
5GB-3k
11GB-4500
*Codes for check balance, *140#*
*1MONTH VALIDITY*
*GLO*
1.35GB-550
2.9GB-1200
4.1GB-1600
5.8GB-2200
7.7GB-2600
10GB-3200
14GB-4k
*Codes for check balance, *127*0#*
*1MONTH VALIDITY*
*9MOBILE*
1.5GB-1200
2GB-1500
3GB-2k
11GB-4k
*Codes for check balance, *228#*
*1MONTH VALIDITY*
CALL 09039118754 OR CHAT ME PRIVATE 09039118754
✅
*YADDA ZAKI BIYA
, ZAKI TURO KUDI TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 1445626295. NUSAIBA MUSTAPHA ACCESS BANK*
*IYA KUDIN SIYEN DATA IYA SHAGALIN KU
🤸🏻
♀
️
BANA AMSAR KATI PLS
😁👌🏻
, KADA KU BARI AYI BA KU WANNAN GARABASAR
😍
, ZAKU IYA SAVING NUMBER NAN 09039118754 DOMIN SIYEN
DATA KAI TSAYE BABU BATA LOKACI KO BANA ONLINE KU KIRA KAWAI MASOYA
💃🏻
*
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
32
Idan
u ya bude jin alamun kiran sallah, wani irin bacci yakeji gashi yau Monday, dan gyara kwanciyarsa yai tare da sake rungumeta a kuma take ya tuno wacce ya runguma da abinda ya faru dasu a daren jiya, nan fa idanunsa suka dan firfito, a hankali yasa hannu ya
na kokarin zareta daga jikinsa. Ibty kam wani baccin dadi ne yake kara kamata nan ta kara makaloshi, hannu yasa yadan shafi goshinsa ya zaiyi ya janyeta? Banda abin kunyar daya tafka jiya yanzu inta ganshi a haka ai shikenan ya gama yawo.
Sake kokarin za
re jikinsa ya sakeyi cikin sanda kamar irin munafikin nan, dakyar ya samu yadan janye hannunsa daga jikinta, yana kokarin zare gangan jikinsa ne itama tadan bude idanunta, da yake yadan kunna fitilar wayarsa yana san ganin yanda zaiyi dabarar janyeta. Nan
fa idanunsu suka hadu da juna, cikin sauri ta nemi mikewa ganin yanayin da suke, shima cikin sauri ya nemi janye jikinsa ji kake kum sun mauje gushinsu, cikin jin azaba ta saki dan kara, da sauri yasa hannu ya toshe mata baku, idanunta ta sadda kasa tana n
eman mulmula gun dan taji zafi. Shikam idanu yadan runtse kadan, bayan ciwon daya ji mata yau yanzu ma ya sake wani.
Daurewa yai cikin maganar rada yace “Yi mana uzuri da ihun nan kar Iman taji.”
Kai tadan jinjina, sake bakinta yai a hankali taji yace “
Sorry!”
Kallansa tai harya mike yai toilet, sannan ta hau shishitu tana sosa gun, garin ya suka kwana a haka?
Sai kuma ta rufe fuskarta da sauri tuno yanda jiya ya dinga sarrafata lalai jiya ya manta da shekarunta, dan san girma irin na Ya Aminu da yai y
awa.
Nan tadan ja bargo ta shige ciki ita kanta kunyar abinda ya faru jiya takeyi.
Shikam a toilet bayan yayi alwala tsayawa yai yana dan sauke iska, dolene ya daure fuska ya nuna kamar wani abu bai faru jiya ba. Sai dai anya zai iya? Dan tabbas a yanda
yake jinsa baiki yanzu ya jawota jikinsa ba.
Kai ya girgiza da sauri tare da sake zuba ruwa a fuskarsa lalai Aminu, wai kaine ka koma haka? Sa’ar Ainah ce fa? Banda girman daka zubar jiya yanzun ma neman zubar da wani girman kake?
Haka ya d’aure fuska
ya fito daga toilet, ko kallan kan gadan baiyi ba ya fito daga dakin, itakam sai dataji alamun rufe kofarsa sannan ta fito daga cikin bargon tare da yin murmushi da kyar ta sauko daga kan gadan, ta dade tana sake yin tsarki da ruwan dumi dan haryanzu zafi
gun yake mata.
****
Bayan ya dawo daga masallaci yana juyo karatunta, harta gama, yau bai nufi dakin ba ya dan kishingida a falon tare da rufe idanunsa. Ita ma ganin ta kammala karatunta ta fito zata wuce bangarenta dan shirya yara zuwa makaranta.
Gani
n sa a falo yasa tana daga dan nesa kadan tace “Ya Aminu ina kwana?” Kasa amsawa yai dan ji yake kamar yana bude ido zai ganta daf dashi tana mai kallan abinda yai jiya. Ita kuma jin shiru yasa ta dauka ko bacci yake, bata kawo komai ba ta wuce bangarenta
tana tafiya a hankali.
Juyowa yai yadanbi bayanta da kallo, ganin yanda take tafiya yasa kunya ta sake rufeshi, idanunsa ya maida ya rufe, shidai kam tabbas ya tabbatar ciwo yaji mata dan Na’imah ba abinda tai, ko jinin da ake cewa anayi ita batai ba, day
a mata magana tace ai ba kowace mace keye ba, sannan ya tafi da ita cikin soyayya ne shiyasa wai duk wacce tai jini to karfi aka mata. Wannan tunanin shiya sake tabbatar mai da abinda take nufi.
******
A bangaren Hajiya kuwa duk yanda taso tai bacci
ta kasa, juyi kawai takeyi saboda takaici da zafin da takeji daga duburarta, lalai itakam dole ta nemo wata hanyar dan bazata yadda ta dinga kwanciya kowa yana hawa kanta ba, to me zai hana ta nemo karuwa? Ko irin ‘yan duniyan nan ta biyash kudi su aure Am
inu? Bayan aure su hada kai su saci kudi mai yawa su gudu?
Wani murmushin jin dadi tai lalai ba shakka inada kwakwalwa, na kuma tabbatar ni ba jinin talaka bace ba kuma a kauye na cancanci rayuwa ba.
Tunowa tai da yanda suka ja Aminu itada Na’imah, sai
kuma ta saki murmushi tace “Wato banaji za’a samu munafiki mai fuska biyu irin Na’imah!” Tai ajiyar zuciya gashi yanzu ta tafi ta barni inata saka da warwarewa.
Wayar boka ce ta shigo wayarta karfe shida na safe, kamar bazata dauka ba sai kuma ta daga tan
a ayyana inda zuwa ne wlh bazatai ba.
“ Hajiya muna cikin matsala!”
Tadan harari wayar tace “matsalar me? Bayan wacce ka sani jiya?”
Yai tsaki cikin takaici yace “Jiya aljaninmu yaje dan a karasa farrakasu sai dai ya dawo ya sanar damu sun sake hadewa,
dole dole yanzu akan Aminu kadai za’ai aikin, zamu turamai muguwar tsanarta cikin ranshi, in da yanda zakiyi ki hada da zargi ki hada, daga sanda ya tsaneta zai saketa ba’a hayyacinsa ba kinga shikenan komai yayi daidai, ita kuma dama mun fara aikinmu na h
anata kwanciyar hankali a gidan.”
Hajiya tadan mike tsaye tace “sun sake hadewa kamar ya? Badai sun sadu da juna kake nufi ba?”
“Ni Allahn musurune da zan sani? Kwalbar da muka hada aljani ya nuna min kwalbar sun hadu, wannan saduwa da rashinta ya rage
naki ki bincika.”
Wani dogon tsaki taja tace “Dama yanzu na kula aikinka sam ya daina aiki, inba haka ba taya karamar yarinya zata tsaya tana wahalar dakai? Ni in har baka sa ya saketa ba to kasa ran bazan sake zuwa gunka ba.” Bata jira mai zai ce ba ta k
ashe wayar tare da cillata kan gado. Goshinta ta dafa tana fitar da wani huci na takaici, dayan maganin da wannan malamin ya bata ta dauko ba shiri ta fara dama kunun kanwa dashi, ta gama ta juyeshi a flask, sannan ta fito waje wurin karfe bakwai, gun Bala
taje tace “Bala dan Allah in Aminu ya fito kace ina san magana dashi.”
Yace to sannan ta juya bangarenta.
Gidan ubanwa zata sa zargin Ibty aran Aminu bayan kullum tana gida? Sannan bataga alamar tana yawo ba balle tasa ran akwai wanda yake santa. Wani d
ogon tsaki ta sake ja, lalai bokan nan ya tabbatar mata aikinsa ya daina ci. To yanzu ita zata dau komai a hannunta.
****
Duk motsin datai idanunsa na kanta ta kasan ido, har suka gama cin abinci, sam idanunsa da nata basu hadu ba, ko alamu yaga tana sa
n kallansa da sauri yake dauke kai, itama ya kula da hakan, sukam su Islam sai zuba labari sukeyi har aka gama suka fito, Iman ma ta shirya cikin nata kayan makarantar dan Aminu zai saukesu sai ya wuce gun aiki, saboda Mamman sunyi tafiya da Abba.
Har ya
kai bakin kofa ta daure tace “Ya Aminu!”
Tsayawa yai yadan kalleta kadan fuskarsa a dan daure, harta karaso yana kallan yanayin tafiyarta, tadan matso tana wasa da hannunta tace “Anjima zamu makarantar da Ainah……”
Cikin sauri ya katseta “A’a ki bari sai
gobe.”
Kallan mamaki tamai tace “Jiya da daddare na…….”
Nan ma ya katseta yana dan sa hannu a aljihunsa yace “Ki dai bari sai gobe, bakiga yanayinki ba? Ko so kike kowa yasan…..”
Sai kuma yadan juya baya yace “Ki dai bari sai gobe, registration ne ai ba
wani abin.” Bai jira tace komai ba yai saurin fita.
Baki tadan turo sannan ta juya ciki duk ranta ba dadi, aikam Ainah dole tai hakuri tajirata suje tare dan sam batasan zuwa ita kadai ji take kamar Umar zai bita school din.
******
Suna fitowa
Bala ya sanar dashi sakon Hajiya hakan yasa yai parking ya kalli Iman yace “Iman bari nadan shiga yanzu zan fito. Mamaki nenya kamata wai dama a jikin gidan take? Lalai itakam tunda Allah ya halliceta bata taba ganin wannan kwamacalar ba, yana zaune tana k
allanshi harya shiga, kallan Ilham tai tace “Dama Hajiya anan take?”
Islam tai caraf tace “A’a da cikin gidan mu take yanzu ne aka mata katanga da gate dinta.”
Idanu Iman ta zaro tace “Cikin gida?”
Kai ta daga tana cewa “Da mun dauka saboda Dady yayi au
re ne aka maidata can amma Aunty Ibty tace ita kawar Aunty ce, ko Ilham?”
Kallansu kawai Iman take tana mamakin kalamansu, cikin dan bugar ciki tace “Waye ya fara muku da saboda Dady yayi aure ne aka maidata can?”
“Hajiya!” Abinda Islam tace kenan tana k
allan window.
Iman tai shiru tana tunanin wannan lamari, lalai ba shakka Hajiyan nan neman hada Ibty take da jikokin ta inba haka ba meya kawo zancen nan? Takaicinta daya Ibty sam ta fiya kawaici, balle tasa ran zata dau mataki. To wai ma uban me matar ta
ke anan bayan ‘yarta ta rasu?
*****
Gaisheta Aminu yai sannan ya tambayeta jikinta, ta amsa cikin jin dadi, tace “dama da safe ne naji sha’awar shan kunu to dana tashi damawa sai na manta na dama dakai dan nasan yanda kake san kunu sosai, to kuma banasan
na mika ma cikin gida saboda kar Amarya taji ba dadi, shine nace ama magana ko office ka wuce dashi.”
Cikin jin dadi ya dau flask din yace “Nagode sosai Hajiya sannan Ibtisam bazata ji haushi ba dan kin kaimin, kun dan samu sabani ne amma tanada fahimta
da zurfin tunani.”
Kallansa tai cikin ranta tace “Tabbas Aminu ya fara zaucewa akan tsinaniyarnan.”
A fili tace “Ai da alama kayi sa’ar mata, bandauka akwai masu tunani a shekarunta ba. Sam batada rawar kan yaran xamani.”
Murmushi taga yayi yace “Ni k
aina wani sa’in mantawa nake da shekarunta saboda hankali da tunaninta.”
Daukan flask din yai yace “Bari mu wuce kar muyi latti.”
Ko magana ta kasa yi haka ta saki baki tana kallansa harya fita, Lalai Aminu ya zama asarare akan yarinyarnan, ta kuma tabba
tar asiri sukamai dan ko sanda yake gigin san Na’imah saboda karfin magani yana kunyar yabanta a gabanta, amma yau ko kumya yake yaban yarinyarnan?
Iman tana zaune taga ya fiyo da flask ya ajiye sannan sun tafi, mamaki yabi ya isheta, gashi abin takaici
an hanasu zuwa da waya makaranta tabar tata a gida balle ta sanar da Ibty abinda wannan matar keyi.
******
Saukesu yai ya wuce office yana aiki sai dai jefi jefi yana tsintar kanshi da tunanin Ibty, wannan karan shine karo na hudu daya dau wayarsa yan
a san kiranta sai ya ajiye, kunun nan ya jawo ya cika cup ya zauna yana sha.
Sako ya tura mata ganin hankalinsa ya kasa kwanciya.
“Kin warware?”
Kallan sakon tai sannan ta turamai da reply “Eh, ya aikin?”
Kamar zaiyi reply sai kuma ya ajiye wayar tare
da kifata.
Ganin yakiyin reply yasa ta kirashi.
Dagawa yai tare dayin gyaran murya, “Ya aikin?”
“Alhamdulila! Sai ke kadai?”
Ta daga kai kamar yana ganinta tace “Na saba ai baya damuna.”
“Keda gidanku keda mutane ta ina kika saba?”
Tadan gyara kish
ingidar datai tace “Dayake banasan zaman falo saboda kar…….”
Sai kuma tai shiru, murmushi yai yace “Saboda kar mai karfin jini ya shigo ya zaneki?”
“Ya zaneni kamar ya? Sai kace ‘yarsa?”
“Dake da ‘yar tasa menene maraba? Tunda ko fita baki isa kiyi ba s
ai da saninshi?”
Tadan turo baki kadan, “baki kika turo ko?”
Kallan gefe da gefe tai da sauri tace “Umm?”
“Harda kunkuni ma hala kinyi? Da na hanaki zuwa makaranta.”
Ta girgiza kai da sauri tace “A’a banyi ba.”
Shiru suka danyi kai kace wasu kurame, g
anin ba abin cewa yasa yace “Ina aiki ne later.” Bai jira me zata ce ba ya kashe wayar, yanasan ya cigaba da zolayarta amma inya tuno da abin jiya sai yaji kunyar kansa da kansa.
Yasha kunu yafi kofi daya sannan ya cigaba da aikinsa.
******
Hajiya sai
safa da marwa take a falo tabbas dole ta samu yarinya ‘yar duniya mai kyau da cikar zati sannan dolene tayi abinda zata dasa zargin Ibty a zuciyar Aminu dan ba shakka yanda yau ya nuna mata tabbas Aminu ya gama fadawa san Ibty ta kuma tabbatar nan bada ji
mawa ba zatasa a koreta.
{Nace wannan mata anyi tsinaniya mara imani
🤧
}
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
Ki ha
nzarta ki mallaki naki
🤸🏻
♀
️
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*
2083371244
Zenith Bankima
33
Iman tana dawowa daga school ko zama batai ba ta ja Ibty cikin dakinta, a bakin gado suka zauna ta kalli Ibty cikin k
ulawa tace "Yaya dama matarnan a jikin gidanki take?"
Yanayin fuskarta ne ya canza ta danyi murmushin yake batace komai ba, "hauka kike Ya Ibty? Taya zaki bar matarnan a kusa dake haka? In taimako yake san mata ya nemar mata gida a wani gun mana dole sai
daf dake haka?"
Shiru Ibty tai dan itakam batasan me zatace ba, hannu Iman tasa tadan riko hannunta tace "Ki cire wannan sanyin naki ki kwaci mijinki, wlh in bakiyi wasa ba sai tasa an sakeki, yanzu yau zamu tafi ta ba Ya Aminu abu a flask, kina zaune a g
ida tana doramai abu, kinsan da wace zuciyar takeyi?"
Kallanta tai idanunta suka dan ciciko da kwalla, maidasu tai tare da daga kanta sama tace "Karki damu, Allah yana tare dani sannan Ya Aminu yasan me yakeyi sanda ya fahimci halinta shi da kanshi zai sa
llameta."
Tsaki Iman taja tace "Zama zakiyi tayi kenan harsaj sanda yasan halinta sannan zai dau mataki? In kuma kafin yasan halin nata ta gama yi miki sharri fa?"
Shiru tai tare da dan dafa kanta, Iman ta dan juyo da ita tace "Wlh koni akawa aure sai na
fiki iya kissisinan jan miji, ke kenan kamar wata matar liman, bakya janshi a jiki, ga mata a kusa dake tana neman shiga tsakaninku?"
Mikewa Ibty tai tace "To ya kikeso nai? So kike inje ince ya koreta ko me?"
Iman ta mike itama tace "Wai ke dan Allah k
amar wata mara wayau? Ki ja Ya Aminu a jiki yanda zai manta da komai sai ke, daga sanda ya mato a kanki kisamu ya canza mata gida, shikenan."
Murmushi tai a ranta tace "Gani kike kamar jan nashi sauki gareshi."
Kamar Iman ta shiga ranta sai jitai tace "K
i cire wata kunya da wani shekaru ki tarerayi mijinki, duk shekarun namiji tareraya tana sa ya ajiyeshi ya koma yaro."
Baki ta bude tace "Tashi ki fita! Lalai karatun novel yasa gaba daya kinzama fitsarariya."
Iman ta fita tana cewa "Nidai wlh na fada mi
ki, wannan wani irin abu ne banbarakwai?"
Tana fita Ibty ta zauna a bakin gado, tabbas dolene ta cire wannan shirmen kunyar tata taja Aminu a jiki, wayarta ta dauko ta kira Ainah sukai maganar sanda zasu makaranta gobe, suna kokarin yin sallama taji Ainah
tace "Wai ga Ummy."
Amsa tai cikin girmamawa suka gaisa, Ummy tace "Ibtisam sannu da kokari Aminu yace ashe har abinci kika yiwa matarcan da batada lafiya."
Kai tadan