Showing 102001 words to 105000 words out of 128353 words

Chapter 35 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

15

a yanzuma yakeji zuciyarsa

na mata kallan da yake ta fata kuma cikin hayyacinsa.

  Abincin ta zuba cikin plate hannunta nadan rawa, karfa ta nemi bashi ya hankadeta? Karfa ya ci zarafinta? Wadannan tunanin sun rike mata kai, haka ta bude miyar gaba daya wajan ya dauki kamshi, cik

e da jin dadi Aminu ya lumshe ido. Ibty ta janyo kujera ta zauna, kafarta na gogar tashi, kamar tana yiwa dan karamin yaro magana tace dashi. "Haaaaa." Aminu besan lokacin da ya tuntsire da dariya ba, karo na farko da ta taba ganin dariyarsa sosai kenan. I

do ta dan kifkifta tana motsa baki.

  "Kin rainani yarinyar nan ko?" Shikenan abinda take tsoro ya tabbata, dama tasan wani abin yake shirin yi.

Jiyai ya kai bakinsa kan taliyar da ta nado masa jikin fork.

  Kallan mamaki kawai takemai, sai da ya dade d

a cinyewa kamar bazata sake bashi ba sai kuma yaji tace. "Haa." Ya kuma sakin murmushi a haka ta dinga bashi har yaci da dan yawa. Yau itakam ta tabbatar mafarki take sai dai bataso a tasheta daga wannan dandaddan mafarkin.

******

Hajiya gabaki

ɗ

aya

ta rasa abinyi, banda safa da marwa da takeyi a gaban hotel tana kuma jan numfashi babu abinda takeyi. Tunda boka yace mata kullin da akai tun zamanin Na'ima ya warware taji hankalinta gaba

ɗ

aya yaki kwanciya.

  Ya akai haka? Wane shegen ne yai mata wann

an danyan aikin? Sai da akaga ta kusa samun Aminu a hannunta sannan za'a ruguza mata komai? Duk yawan shekarun data dauka tana juyashi ana neman tarwatsa mata rana tsaka?

Aikuwa bazai sabuba, duk yadda zatayi sai ta yi wajan karkato da hankalin Aminu. Bab

ban tashin hankalinta ma yanzu shine gurin kwana, masu hotel din sun koreta wai dakin wari yake saboda sun raina mata hankali. To wai ita yanzu ina zataje?

  Gidan Aminu ko gurin boka da yace mata sai an sake shiri sannan komai zai koma yadda yake? Taja

tsaki yafi ashirin saboda rashin mafita ga batada kudi.

Bari dai taje gurin bokan taji abinda zai yi mata shima tsohon dan iskan, gabaki daya batasan yadda zatai dashi ba akan harkar da yake sata dole, ita dama da Aminun aka ce zata yi sai ta fijin dadi d

an shikam namiji ne dan camas a kalla ta huce takaicin dadewa datai ba aure.

  Kuma a kalla taci riba dan ko a baya da ta fara ganinshi sai data san lalai Na'ima tayi sa'a, jinta dingayi inama itace? Kawai dai ta hakura ne dan tasan ba za'a yarda suyi aur

e ba tayi masa girma.

Juyawa tayi tana kwafa tana zagin mutanan hotel din, ta janyo ma'ajiyar kudinta wanda yanzu gaba daga dubu hudu ne a ciki, oh yanzu idan suka kare ba'a gama yi mata aiki ba ya zatayi? Ko kudin zuwa gun bokan batadashi kenan? Kodai

gidan Aminu zata fara zuwa ta gani ko zata dace ya bata wasu?

  'Karki soma Hajiya, kinaji boka yace komai ya ruguje, kinga kila yanzu ma nemanki sukeyi.' Kuma yin kwafa tayi, tana tarar napep, yana tsayawa ta shiga ta sanar dashi inda zai kaita. Jin ungu

war da zata yasa yace "Hajiya gidan karbar magani zakije ne?" Taji mai napep din yana tambayar ta bayan sun hau hanya sosai. Ko ina ruwansa? Ta fada cikin ranta ba kuma ta bashi amsa ba.

  "Zaki karbo maganin mallakar wani ko wata kike so tabi duniya Haj

iya?" Gabanta ne ya bada wani irin ras. Karfa turo shi akai yasa mata ido. Zuciyarta ta shiga kitsa mata hakan. Waye zai turo shi? Ummy! Hajiya taji zuciyarta na sanar da ita, a tsorace tace dashi.

"Turoka akai kasa min ido?" Yace, "A'a mafi akasarin mat

a idan sunce a kaisu unguwar da kika fada, to gidan wani boka suke zuwa." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ganin ba sa mata ido aka turo yayi ba. Karamin tsaki ta saki tana cewa.

  "Ni wazansa tabi duniya yaro? Ai ni na iya zama da mutane ba tare da boka ko

malam ba. Ko yana bada maganin ciwon daji?" Hajiya ta masa tambayar cike da rainin hankali. "Ya za'ai na sani Hajiya? Nifa ban ma taba ganin fuskarsa ba, wani ne yake ciwon?" Dadi ya kama Hajiya taji yace besan shi ba. "Yatace take fama dashi muna ta neman

magani har yau bamu dace ba. Ko zaka fara ajiyeni a gidan na tambaya ko Allah zaisa a dace yana badawa, sai na karba." mai napep ya dan sai ta madubi yana kallo Hajiya ta ciki, karaf suka hada ido ta yatsina fuska.

  "Yaro na fadi wani abu na rashin dadi

ne?" Ya cigaba da tuki. "A'a gani nayi nace miki boka ne kuma kina cewa a kaiki. Keda yanzu ya dace kuyi ta istigfari kuna tuba harta Allah ta kasance."

Hajiya ta rintsa ido, kaji tsinannan yaro. Cikin hade rai tace.

  "Ai zaka rigani mutuwa dan ba a gi

rma da shekaru mutuwa take ba." mai napep najin haka ya fara tangal-tangal dasu, aifa nan Hajiya ta fara ihu tana surfa masa zagi, ta ririke napep tana cigaba da zunduma ihu, ganin bashida niyyar bari ta fara bashi hakuri tana rokarshi akan yayi hakuri ya

taimaka ya daina.

Ta madubi ya kalleta yaga yanda idanunta suka firfito yai kwafa tare da murmushi....

(Anya Hajiya Nason mutuwa? To ba ruwa na ita da mai napep

😂

)

Ayusher ce

⛹

🏻

‍♀

️

[5/6, 9:26 AM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌

️

‍♂

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Na Kudine ki Bada 500 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku*

208

3371244

Zenith Bank

Aisha m salis

+447894142004

*43*

"Tsaya na sauka, idan baka tsaya ba zanyi sanadin mutuwar mu harda kai." Mai napep na jin abinda Hajiya ta fada, cikin ransa yace, 'daga wasa? Afili kuma sassauta tukin yayi yana cewa.

 

"Allah ya baki hakuri Hajiya, irin wasan nan ne na kaka da jikanta." Ware ido tayi tana kallansa hannunta dafe a kirji. "Karka raina min hankali kaji, Kaga nayi kama da kalar kakarka ne da zaka min wasa da rai? Yata dana haifa bata kai ka ba bare har ta h

aifo min jika kamarka."

  "Allah ya baki hakuri." Ya fada yana shan kwanar da tace ya sauketa. Sai ta ya gaba parking sannan ya juyo yana kallanta yace. "Hajiya kudinki dari hudu."

   "kace mene?" Ta tambaya cikin jin karin bayani.

  "Kudinki dari hudu

zaki bada." Tace, "Ai da yake daga Lagos ka dakkoni ko? Ni na zatama cewa zakai na barshi." Da sauri yai wata irin juyowa, kallan juna sukayi yace.

  "Tab four hundred naira zaki miko Hajjaju, fetur tsada yake." Ta zaro ta mika masa tana cewa. "Kayi hakur

i ita kadai garan." murza kudin ya shiga yi cikin bacin rai yace, "Haba Hajiya dari biyu?" Ta fice daga napep din tana cewa.

  "Ko na tsaya ka maidani inda ka dakkoni ne?" Haushi ya kama mai napep sai dai kuma babu yadda zai yi da ita, ya burga napep din

tare da bula mata kura yabar wajan. "Shegen dan sa ido, gobema ka sake dakkoni kayi min maganar da bance ba." Hajiya ta juya ta nufi gidan boka ranta duk babu dadi.

*******

Yana rike da jakarsa ya rasa abinyi, tunani kawai yake wacce makoma zai fada?

Ya rasa Ibty wacce ta zamemasa tauraruwar zuciyarshi.

  Tabbas Aminu ya dace da samun mata mai kyau, Abba ya bashi ibty abagas tunda yana can inuwa yaji an bashi mata. Shi kuwa yayi rainonta ya bata kyakkyawar kulawa amman karshe ya kare a nakasasshiya.

"Bilkisu ina san yayarki, hakika bake nake so ba amman ya zanyi?" Umar ya fada a fili yana furzar da iska a bakinsa. Jin wata mota tana tambayar inda zashi ne ya fara tunanin kodai ya koma? Dan shi yanzu ba komawa kauyen ba a'a rashin ganin Ibty kadai ya

isheshi, ga kuma noma dan shikam yafi karfin yin noma yanzu.

  Idan ya koma kauyen mezai yi acan? Bilkisu. Yaji zuciyarsa ta ambaci sunanta tana sake sanar dashi.

Ka koma wajan Bilkisu tunda tana sanka da yawa. Ibty fa? Zuciyar shi ba zata taba yarda ta

dinga ganin ibty tare da wani kato bashi ba. "Ina sanki Ibty, me yasa ke bakya so a?" Ya fada yana rike kafadun kwandasta, jin an saki tsaki yasa Umar kallansa.

  Da sauri ya dauke hannunsa ganin kwandasta. "Wai kai a haka soyayya ce ta ratsaka? Wato baka

gane wuta da aljanna ko? Ware ka bamu waje muna da aikin yi." Kwandastan ya fada yana ture Umar gefe.

  Akan idanunsa suka ja motar su, Anya mutane sun san yadda yakeji akan ibty? Shifa yana ji a cikin zuciyarshi ake hada duk wata wuta a duniya saboda ra

dadin rashin Ibty.

  Banda rainin hankali kuma an barshi da wata nakasashiya, gashi ta nace masa itama kodan tasan ba wata moruwa zatayi ba?

  Yaja tsaki yana kuma kallon gefe da gefensa kamar mai jiran wani.

Shawara ya yanke kawai tafi koma menene ya

faru. Yana tsaye har wata motar tazo ya tara ya hau zuciyarshi cike da tunani.

********

Kwance tayi akan gado tana faman kuka a hankali, duk zuciyarta babu dadi ta rasa dalilin da yasa take masifar san Umar gashi shi batatata yake ba.

  Amman me ya

sa baya santa? Kamar tana magana da wani a kusa sai ji tayi ance mata. Ke nakasassa ce, ibty kuma lafiyayya ce. Ta fashe da kuka a fili ta fara magana ba tare da tasan da hakan ba, ji kawai tayi tana magana cikin girgiza kai.

"Kaddara ce, wallahi kaddara

ce Allah ya doramin. Please Ya Umar dan Allah ka soni koda bekai na wacce kake so ba. Ina sanka zan kuma kasance da kai a cikin kowanne irin yanayi, dan Allah karka rabu dani Ya Umar, idan kayi hakan ka ruguza duk wani ragowar farin cikin da nake tare da s

hi."

  Cikin tausayawa Islam ta goge kwallar data zubo ta bata mata fuska, tabbas Ya Bilkisu tana cikin jarabawa. Babu abinda ya fi ciwo irin kana so ba'a sanka, halin da Bilkisu take ciki kenan.

"Dan Allah Ya Bilkisu kiyi shiru, ki nemi zabin Allah. Ida

n har Ya Umar alkairi ne agareki zai dawo, idan ba alkairi bane Allah ya hada kowa da rabansa." Bilkisu kallon Iman tayi cike da mamakin kalamanta, batayi magana ba ta maida kai gefe tana dafe da saitin zuciyarta.

"Kizo kici abinci inji Umma." Kai Bilkis

u ta girgiza tana cewa. "Nakoshi." Iman ta sauke numfashi "Kina jin yunwa ya kamata kici abinci, karki sawa kanki damuwa, in har kika rame Ya Umar zai kuma tsanarki. Amman idan yaga kinyi fresh dole zai rage wani wulakancin."

Maganganun Iman gaskiya ne, s

ai dai taya zata iya cin abinci bayan Umar din ta ya bada sharadi akan auran su. Aminu ba zai taba sakin Ibty ba bare harta sanya ran cigaba da kasancewa dashi. Kuma idan Ibty ta bar Aminu kenan aurenta da Umar ya tabbata tsinkakke, tunda tasan sai ya rabu

da ita ya auri Ibty tunda ba abin aure daya shiga tsakaninsu balle.

"Ki tashi dan Allah Ya Bilki kidena damun ranki, addu'a zamuyi Allah ya dawo da hankalinsa gareki."

Bilkisu ta mike zaune ta kamo hannun Iman, cikin wani yanayi tace. "Kiyi min addu'a

karya rabu dani, wallahi ina jinsa har cikin jinina." Iman ta kuma matse hannun Bilkisu cikin na ta "Karki damu kullum kina cikin addu'a ta." Daga haka ta janyo kekenta, da taimakon Iman ta hau suka fito, Iman tana mamakin wannan mahaukacin san, tabbas da

Bilkisu kanwartace da dukan tsiya zata mata a dakin nan.

******

Sai da ya gama cin abincin kafin ibty ta gyara wajan ta maida komai kitchen ta gyara. Lalai yanzu kam ta tabbatar ba mafarki take ba. Amma Ya Aminu a hayyacinsa yake kuwa? Yana zaune duk

inda tai sai ya bita da kallo. Sai da ta gama komai sannan ta tsaya a wajan kitchen tana tunanin abinyi. Kota koma wajansa? Idan taje me zata yi? Ko hira? Toh tace masa mene?

  Yana hangota shima a nashi bangaran yana ta tunanin me zai yi mata yanzu?

D

awowa tai ta tsaya tsakanin falanshi da nata tana dan lekensa ta labule.

"Idan kin gama leken kizo." Ibty taji Aminu ya fada. Saurin komawa ciki tayi tana zaro ido. Ya akai ya ganta? Kai wannan mutumin yana da ido sosai.

"Bazaki zo ba?" Ibty taji yana k

iranta, rintsa ido tayi tana murmushi. Kunyarsa takeji sosai, yanzu menene abinyi? Taje ko ta zauna a falanta tace bataji shi ba?

Bata gama tunani ba sai kawai ganinsa tayi tsaye a bakin kofar, suka hada ido tai saurin kawar da nata tana dariya kasa kasa

. "Ya haka madam?" Ibty ta tsuke baki. "Muje." Ya fada yana mika mata hannunsa. Ibty ta mika masa nata a hankali ya mikar da ita, yana rike da ita suka shiga fallonsa sannan suka nufi dakinsa. Itadai da kallo kawai take binshi.

A zahirin gaskiya Aminu nem

an maida hankalinsa da tunaninsa yake kokarin yin gun Ibty dan sam bayasan ya zauna shi kadai saboda ya tabbatar tunanin abinda ya faru ne zai dinga dawomai, matar daya dauka duk duniya ba kamarta lokaci daya ya fahimci ba haka ba? Uwar 'ya'yanshi? Sam bay

aso ya cigaba da zargin abubuwan data aikata a kanshi, gwara ya maida hankalinsa kan matarsa kila hakan ne zai samar mai kwanciyar hankali.

**********

Tunda ya sauka a bakin titinsu mai jar kasa yake ta yatsina fuska, ya juya tare da hango yadda maza

ke zazzaune a inuwa sun kishingida, daga masu shan rake sai masu fushe gyada suna jefawa a baki, yaja tsaki tare da gyara jakar bayansa ya fara tafiya. A da dayake hutu yake zuwa bai damu da komai ba amma fa yanzu da yaga alamar zama ya ganshi sai yake ga

nin mutanen garin wasu kucakai kauyawa.

  "Umaru ya dawo." Yaji wani yaro daga can gefe yana fadawa abokan wasansa. Wai Umaru gatsal, yaro dan karami yana fadar sunansa saboda raini. Gasu Ibty can su Bilkisu Ya Umar a gayance suke fada amman nan kamar sun

a kiran wani dabba. Ko takan yan majalisar bebiba ya wuce yana ta wani kwambo shi a dole ya dawo daga birni.

  Yana shiga cikin gari kuwa yan matan kauyen nan suka fara yi masa caaa kamar sunga gasasshen nama,  dan wannan abin yana daga cikin abinda ke sa

shi jin wani girma in yazo kauyen nan, ya tabbatar dan sunga dan gayu ne. Kota kansu beyi ba ya shige gida yana zaginsu shi a dole yafi karfin su.

"Wallahi duk wanda aka cewa dan kauye an cuce shi." Wata mace dake karya kara tana turawa cikin murhu ta kal

leshi. "Umaru? Mazan fama, saukar yaushe kenan? Waye ya tabo mana kai a hanya?" Yaja tsaki tare da naushin wata akuya dake gabansa.

  "Su Hansai ne, yadda kika san basu sanni ba, banzaye gajoji kawai." Cikin sanyin jiki matar tace. "Haba mazaje, ya kake y

i musu wannan maganar? Ko babu komai su Hansai yan uwanka ne." Umar cikin sauri yace. "Yoni menace? Abu daya kawai na sani ba wacce zan aura saboda ina da mata a can birni. Kima gaya musu dan wallahi zan iya fasawa yarinya baki." Dama ya dawo da bacin rai

ga ana neman sake batamai rai.

  "Dama basu ce suna sanka ba ai, kai daga dawowarka sai jaraba da neman fitina."

Umar bai koma cewa komai ba ya bude wani dan daki ya shiga. Bango ya dafa yana karewa dakin kallo, wanda yake dauke da 'yar tabarma da wani

filo duk ya kare, dakinsu ne shida yayansa, tsaki yaja yana tuno yadda ya baro narkeken gadon Bilkisu da lumtsuma-lumtsuman kujerun da aka zuba, nan da nan ya fara jin kamar ya cuci kansa. "Anya bazan koma ba?" Ya tambayi kansa yana sosa haba.

Ai daga wa

je ya fara jin ana cewa "Umaru ne da gaske?"

Jin muryar Babansa yasa gabansa ya fadi, tabbas zaici duka in mahaifinsa yasan abinda ga aikata, ita kanta mahaifiyarsa bazata yarda ba.

Sum sum yadan leko yana washe baki ya tsuguna yana gaida mahaifinsa.

*******

Gyara mayafi Hajiya tayi tana kuma waigawa baya, ji take tamkar ana binta idan ta juya kuma bata ganin kowa. Rai a bace ta shiga sai faman jan numfashi take, Allah dai yasa kar yace sai ta bashi kanta, idan yai mata haka tabbas zai ilatata, saka

makon wani irin zugi da takeji gurin nayi mata tun wancan zuwan nata.

  Yana ganinta ya fara dariya yana kuma dukan cinya, tai masa kallon mamaki batace masa komai ba har ta samu wajan zama. Ji tayi yace.

"Daman nasan dole zaki zo Hajiya, akan Aminu na t

abbatar zaki bar duk wani abu kizo wajena. Sai dai k..." Cikin takaici ta dakatar dashi tace. "Menene abin yi?"

Shiru yai yana kallanta yace "na fadamiki sai kin samu macen da zata dauke hankalinsa daga kan matarsa, a da can abu bai yiwu ba balle yanzu da

komai ya wargaje."

Shiru tai tana tunani, cikin bacin rai tace "Kafi kowa sanin banda kowa a duniya banda Naima ina......."

Sai kuma tai shiru ta kalleshi ta dan kauda kai tana motsa baki, kallanta shima yai kafin ya bushe da dariya yace "Badai ke ka

nki kike tunani ba ko?"

Wani kallo tamai tace "Me kake san cewa? Ai ko da ba auransa ba zan iya dauke hankalinsa daga kan tsinaniyar 'yarnan, na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login