Showing 90001 words to 93000 words out of 128353 words

Chapter 31 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

46

ya

nufi bangarenta batanan harzai juya yaji alamun kuka, gaba daya jikinsa ne yai wani irin sanyi ya nufi dakinta, hannu yasa kamat zai bude kofar sai kuma ya fasa dan ya tabbatar inya bude ma maimakon lalashi kara bata mata rai zaiyi. Ya dan dade a tsaye a b

akin kofar zuciyarsa na wani irin tafasa dan yanzu kam ya tabbatar yana tsananin kaunar Ibty baisan yaushe santa ya kamashi ba amma yanada yakinin wannan so ne.

Haka ya nufi masallaci dan yasan an idar da sallah yai tashi sannan ya juyo. Yana shiga ya zau

na a bakin gado kenan yaji sallamarta, amsawa yai jiki a sanyaye tare da dan zuba mata ido, harta rame kwana daya sa alama jiya bataci abinci ba sam. Idanunsa yadan kawar, karasowa tai ta gaisheshi, idanunsa na gefe ya amsa mata, mikewa tai zata fito, kall

an bayanta yai da sauri yace “Ya jikin naki?”

Juyowa tai jiki a sanyaye, sai dai suna hada ido ya juyar da kansa da sauri, yanzu kam ta fara fahimtar kamar ganinta ne bayasan yi. Hakan yasa itama ta juya baya da sauri sannan tace “Da sauki.”

Ga mamakinta

sai jiyai yace “Ki koma ki kwanta inda wani abin da kikeso ki fadamin sai nasa a siyo.”

Tabbas abinda akai akan fuskarta akai dan tunda ya fara abin nan baiyi mata magana mai dadi ba sai yanzu.

A hankali tace “Nagode.”

Tana kokarin fita taji ya daga w

aya yace “Mamman bazaka fadamin inda kuka kai Hajiya ba?”

Gabanta ne yadan fadi kamar zata juyo sai ta fasa kawai tai waje, ruwan tea ta hada ta zauna tasha, dakyar tadan ci wani karamin bread sannan ta mike ta nufi toilet dan tai wanka.

Tana wanka tana

tunanin yanzu in Aminu ya dawo da Hajiya ya zatai? Dole tai wanka ta sanar da Ummy dan ta dakatar dashi daga neman ta, tana fitowa ta bude wardrobe dinta bangaren inda aka jera mata english wears dinta ta kalla, ba sababbi bane dan nata ne data siya gwanj

o tun tana gida, tanasan sakawa a gida sai dai shakkar Umar da abinda zai aikata yasa bata taba sakawa ba, sai dai ko t-shirt shima in zata sauko sai ta zura hijab.

Wata riga da wando ta dauko wanda duk a ciki dama tafi ji dasu, milk colour ne sai dai any

i kwaliya da orange, a jikin rigar, wandon mikk ne irin mai budewa daga kasa din nan, sun amsheta dan sun mata kyau kwarai da gaske, ta dauko orange din mayafi ta dan yafa a kanta sannan ta fesa turare, husnul muslim ta dauko ta fara yin azkar.

******

Acan hotel din Hajiya kuwa wajen karfe biyu na dare ta farka a zabure, mikewa tai ta zauna tana kallan dan dakin, jitai idanunta na neman cikowa da kwalla, lalai bazata taba kyale Ummy da Ibty ba sai sun san ita suka tozarta, haka ta zauna ido biyu har asu

ba tai, ko sallah batai ba ta zari hijab ta fito daga hotel din ta nufi titi, ta dade sosai a tsaye kafin tai sa’an samun dan adaidaita.

Kai tsaye ta wuce gun Malam sai dai abin haushi yau dakin nasa a kule wai bai karaso daga gidansa ba, haka ta zauna a

bakin barandar dakin ta baza uban tagumi, batasan sanda ta dan fara gyangyadi ba.

Sai karfe takwas sannan ya iso lokacin bacci ya mata dadi ta jinginar da kanta a jikin bango tana shan baccinta harda minshari.

Malam ya kalleta jiyai kamar ya sheke da da

riya, wato matar nan jiya ta gama zazzagamai masifa sannan yau ya ganta wai har jiransa take? Kamar zai kulata sai kawai ya wucewarsa cikin dakin, nan ya fara shirin sana’arsa sannan ya kira wannan alhajin ya sanar dashi gafa Hajiya tazo da alama ta matsu

ne dan anan ma ya sameta.

Dadi ya kama mutumin cikin hanzari yace gashinan zuwa.

Hajiya ta bude baki tanata makar bacci taji abu ya wuce mata makogaro ai a zabure ta mike ta fara kakarin amai dan tabbas ta fahimci kuda ne, kakari take iya kakari dakyar k

udan ya fito da dan karamin amai wanda bakomai a cikinta irin yalan nan.

Ajiyar zuciya tai sannan ta fara gyara kanta, lalai tasha bacci, jakarta ta jawo da sauri ta bude, me zata gani? Dubu goman da Hajiya ta bata jiya babu su a ciki, bama wannan ba ‘ya

r wayar tata an sace.

Ai fa nan hankalin Hajiya yai mumunan tashi ta hau sintiri kafin ta shiga gun Malam hankali a tashe.

Kallansa tai tace “Malam anmin sata wlh.”

Kamar ya kwashe da dariya sai kuma ya dake yace “Sata? Aljanunmu basa bari ai sata anan

in har an dauke miki abu to lalai ba anan aka dauka ba, ko kuwa kina so kice aljanunmu ne suka daukar miki abu?”

Hankalinta ya kara tashi ta zube tace “Ba haka nake nufi ba, sai dai…….”

“Na dauka mun rabu dake mun kuma gama magana jiya? Meya kawoki yau

?”

Ta dan sake zubewa tace “Ka gafarceni jiya sam ba’a hayyacina nake ba.”

Yai dan dube dubensa yace “kinci sa’a babban aljani na kaunarki dan haka yace ya hakura yanzu meya kawoki?”

Nan ta zayyane mai duk abinda ke faruwa ta karasa tana hawaye tace “Ya

nzu bansan ina zan zauna ba sannan ni wlh koma menene zan iya yi akan in koma kauye, Malam ka taimakeni ka taimaki rayuwata ka sa Aminu ya kasa zaune ya kasa tsaye sai ya nemoni, sannan wannan tsinaniyar uwar tasa ka daura mata jinyar da zata kasa ko motsi

balle ta iya aikata wani abu. Ita kuma matarsa ka daura mata ciwon hauka.”

Dariya ya bushe dashi yace “Indai wannan ne mai sauki ne a gurin mu amma wai ke meyasa kika nace sai kin zauna da sirikinki?”

Kallan mamaki tamai tace “Inada wanda ya fishi ne?”

Yai ‘yan dube dubensa ya sake dariya yace “Akwai wanda zai baki jin dadi ya kuma baki gida ki zauna in har zaki dinga yanda da duk sanda ya kawo bukatar da aljani yazo mai da ita.”

Kallan mamaki tamai me ya ke nufi?

Ya dan sake dariya yace “Mutumin ra

nnan, a shirye yake tsaf ya baki muhali in har zaki amince da bukatunsa.”

A zabure ta mike tace “Badani ba, naji ni dama can mai saban Allah ce amma a ciki banda in bada gurin nan da girma na a dinga surfata.”

Boka ya jinjina kai yace “Shikenan sai ki ji

ra sak sanda magani yaci amma inaso ki sani matarsa tafi karfin aljanun da muke turawa, sannan uwarsa ta tashi tsaye akansa itama bata baci tana mai addu’oi mu kuma kinsan bama san a dinga mana addu’a ana ruguzamana shirin mu.”

Hajiya tadan ciji yatsa ta

ce “koma menene ka taimaka yanzu kamin.”

Ya dan kalli dakin da suka saba shiga yace “To mu shiga?”

Kanta tadan dafa sannan ta mike, haka suka shiga tana shiga yau taji kanta na juyawa kafin tai auni ashe ta suma.

Mutumin ne ya shigo ya shafa magani sann

an yahau aiki ta bayanta, yau yafi awa daya yanayi kafin ya kammala.

Fitowa sukai suka sheke da dariya, Malam yace “Karka damu zansa ta dawo gunka, gaba daya hankalinta ba’a kwance yake ba, wanda take takamar dashi ya koreta.”

Dariya suka sakeyi cikin ji

n dadi ya dauko bandir din dubu daya guda biyu ya ajiye mai yace “Ka tabbatar an kawota saboda wadancan mata daka hadani dasu duk sun gama yagwalgwalewa ga ciwuka shiyasa duk na fatatakesu, yanzu ita wannan ita nake hari.”

Nan ya fito yana murmushin mugun

ta, matansa hudu sai dai ba wace yake kusanta domin umarnin boka ne, dole haka yake samo manyan mata ya dinga badala dasu ta baya, da zarar ciwo ko wani abin ya samesu ko kuma ya dainajin komai a tattare dasu sai ya koresu. Babban mutum ne dan yanzu ma uba

ngidansa ne ke neman takarar gomna na jahar Kano.

*****

Hajiya bata farfado ba sai da Malam shima ya kara mika nashi sakon, tana farkawa taji ko zama ta kasayi, samun kanta tai kawai da fara hawaye dan ta tabbatar Malam yau ta baya ya nemeta itakam ta

tsani abin nan.

Haka ta fito tana tafiya dakyar, Malam ya daure fuska sosai yace “Yanzu ki koma zan kammala aikinki zan nemeki”

Tace “Ka taimakeni Malam inba Aminu bazan taba jin dadin rayuwata ba.”

Wani kallo ya kara yace “Wani in yaji abinda kikeyi da

uka zaiyi kece matarsa ba ‘yarki ba.”

“Wani irin zance kake haka?”

“Ban manta sanda Na’imah wato ‘yarki ta kwato kansa dakyar ba, sannan itace tw hadamu dake, sai dai in kina wani abin sai naga kamar san mijin ‘yar taki kike.”

A fusace tace “Malam wani

kazamun zance kake haka?”

“Haryau ina mamakin meyasa bakyasan yai aure? Naji ni nace inyai aure matar zata koreki amma ai zaki iya neman maganin da za’a rufe mata baki ko? Sai dai sam baki nema ba kullum kedai burinki ya rabu da matarsa.”

Mikewa tai ciki

n takaici tace “Sai naji daga gareka.”

“Kudin aiki fa?”

Kallansa tai tace “Kayi hakuri anmin sata amma zan turo gaba daya.”

Haka ta fito yabi bayanta da wani kallo……..

*******

Tunda ta shigo falan yake kallanta ta bayan ido, yau ko hijab batasa ba?

Anya Ibty ce kowa?

Haka yai ta satar kallanta harta gama shigowa da kayan abincin, ji yake kamar ya jawota tsam ya rungume, bata bari sun hada ido ba idanunta nakan kayan abincin tace “Yaya abinci.”

Gyaran murya yai sannan yace “Kedanace in kinasan abu

kiyi magana? Baki da lafiya meye na dagewa sai kinyi abinci?”

“Daga kai sai Bala shiyasa naga abincin ba yawa zan iyayi.”

“Kefa?”

“Banajin yunwa maybe in muka je school da Ainah na samu naci.”

Cikin hanzari yace “Baki da lafiyan zaki skul?”

Har zata

juyo sai ta fasa tace “Yaya kaga tun yaushe nake cewa zamuje registration din nan, inhar kaban izini gwara in daure in je muyi.”

“So kike kije ki fadi a skul? Sannan makaranta zaki kikai wannan shigar?”

Dan karamin murmushi tai duk da bai fada ba taji d

adi a kalla ya damu da ita.

Kamar zatace a’a sai tace “Riga da wando ne fa kawai in nasa after dress shikenan.”

Fuska ya daure sosai yace “Inji wa yace shikenan?”

Ta dan dake tace “Haka na dauka zakace.”

Ya kara hade rai yace “Bance ba sannan banda jiy

ar cewa, sannan ki jira sai wajen azahar inhar jikin naki yayi sauki sai kuje.”

Kai ta daga sannan tace “Shikenan.”

Gani yai ta juya cikin ransa yace “Ko kunya wai ta dauka haka zance? Ce mata akai bansan darajar matata ba ko me? Sannan meyasa ma taki ka

llo na? Ganina ne batasan yi saboda abinda na mata ko me?

Goshinsa yadan shafa to in ma hakan ne ai batada laifi tunda koshi kunyar abubuwan daya mata jiya yake, haryanzu haushin kansa yakeji da tsanar abinda ya aikata mata.

Itakam magani ta karasha t

a zauna akan kujera tana tunanin wannan abu, meyasa wasu mutanen basuda imani? Metawa matarnan da zata rabata da mijinta?

Wayarta ta dauka ta kira Ainah bayan sun gaisa ta sanar da ita sai bayan azahar in Ya Aminu ya yarda, sannan ta sanar da ita neman da

Aminu yakewa Hajiya.

Ainah tace “Karki damu Ummy ta gama jawa Mamman kunne.”

Ajiyar zuciya tai tace “Iman fa?”

Ga wuce makaranta daga can wai zata wuce gida.”

Kai ta jinjina sannan sukai sallama.

*******

Cikin magiya Bilkisu tace “Ya Umar dan All

ah kaban wayata, tun jiya nakesan nai waya amma ba…..”

Cilo wayar dayai da karfi ne yasa gabanta ya fadi ji kake tas ta bugu da bango ta fadi kasa, ai basai ta duba ba screen din ya gama fashewa.

Kallansa tai kawai taji hawaye sun zubo tace “Yaya nikam m

e na maka dana cancanci wannan wulakancin?”

Wani kallan tsana ya mata yace “Tambaya kike? Ai har abada indai dani zaki zauna to wallahi bazaki taba jin dadin aurenki ba, yanda kika rabani da masoyiyata nima sai na rabaki da duk wani jin dadi na duniya.”

Ta share hawayenta taja kekenta tabar dakin, wani irin kara ya saki kai kace mai aljanu ne, ya cilo pillow da karfin gaske shikam ya tsani yaga keken guragun nan, ya tsani yarinyar nan kamar ransa.

Abinda Ibty tamai daya kira ya tuna, idanunsa sukai jaa y

ace “Ni mutumin daya ke tanadinki tun kina yarinya ni zaki tozarta? Ni zaki wulakanta saboda wancan jan mutumin? Nunar rana? Wanda na tabbatar kudin nasa ma daga sata ya hadasu?”

Yai kwafa….

Nima kwafar nai nace {Malam Umar kai dai kace kana kishi

🤪

ya

fika komai}

[3/23, 11:22 AM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*n

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004jiki

2083371244

Zenith Bank

38*

Harya shiga toilet yai wanka gaba daya ya rasa meke damunsa, taya zai kula da ita bayan sam baya san ko ganin fuskarta? Ga damuwar

sa halin da Hajiya ke ciki.

Surar ta da shigar datai ne ta fadimai ya runtse ido sannan ya kara karfin ruwan shower din, yana jika kansa sosai, wannan wani irin abu ne? Kanasan kasancewa da matarka amma daga ka ganta sai kaji tsanarta? Ya dade yana zuba r

uwa kafin ya gaji ya fito, gaban madubin bandakin ya tsaya wanda nason ruwan zafi duk ya sa baka ganin komai, hannunsa yasa yasan goge saman madubin tare da kurewa fuskarsa kallo, wannan kaddarar ce ko me? Kanasan abu wanda yake mallakinka amma ka gagara n

unamai?

Yadan shafi sumar kansa, dole ko ma me zaiji ya daure yaja matarsa, dan shikam har mamakin yanda zuciyarsa ta kamu da yarinya karama yakeyi.

Ya fito cikin dakiya ya kira gun aikinsu ya sanar dasu matarsa ba lafiya, dayake gun aikinsu ne shida Ba

ffa ba wani matsala da ya samu.

Fitowa yai ya zura jallabiya ya dan fesa turarensa sannanya fito, kai tsaye bangarenta ya nufa, yana shiga tana fitowa daga kitchen, yana kallanta yaji wata muguwar tsana da kyama sun rufeshi balle in ya tuno abinda ta aik

ata mai jiya, fuska ya daure sosai kamar wanda aka bashi mumunan labari, Ibty jikinta a sanyaye ta taho zata wuce daki dan yanayin fuskarsa kadai ya isa tasan bayasan ganinta.

Aminu ya runtse ido sosai sannan ya dake a ransa yace “Dole inje kusa da ita n

aga meke faruwa, in bata kusa dani sai naji kaunarta kuma daga naganta sai naji ba wanda na tsana a duniya sama da ita?”

Ibty bataji takowarsa ba harya karaso ta bayanta, hannu tasa zata bude kofar dakin kawai taji an sakalo hannu ta kugunta, wani irin ya

nayi ta shiga wanda yasata dan lumshe ido.

Aminu bai juyo da ita ba yace “Meyasa kika aikatamin abu jiya har kikasa nakejin tsanarki haka a raina?”

Idanunta haryanzu a lumshe suke duk da yanzu bawai yanayin data shiga bane yasata barin idan a rufe ba.

“Haryau bansan mena aikata ba, naji in har kace nayi laifi to na dauka, ko wani iri ne ka yafemin.”

“Meyasa banga alamun kina neman yafiyar ba?”

“To Yaya me kake so nayi na nuna maka ina neman yafiya?”

Hannunsa ya sake matsowa dashi saitin cikinta sosai

hakan yasa tadanyi wata karamar ajiyar zuciya, shi kansa wani yanayin yake neman shiga, kokarin kwantar da kansa yake a kafadarta kawai yaji kansa ya fara wani irin sarawa, dan kansa ya girgiza saboda yanda ya fara jin abun na damunsa, da karfi yadan tura

ta hakan yasa ta buge da jikin kofar, ji kake kum.

Idanunsa yadan bude ganin yanda ta bige yadan matsa da baya da sauri yana kallanta, Ibty ta juyo ta kalleshi kamar zatai magana kawai ta bude daki ta shiga.

Zama tai a bakin gado kawai sai jitai hawaye s

un zubo mata, wannan wani irin masifa da bala’i ne? Haka kawai dan burin duniya sai ka juyar wa mutum kwakwalwa ka maidashi ya dinga abinda ba halinsa ba.

Qur’ani ta dauko kawai ta hau karantawa tana neman Allah ya kawo musu sauki cikin wannan bala’in da

aka jefasu.

Shikam Aminu bangarensa ya wuce cikin sauri ya zauna a kan kujera tare da dafe saman kansa, tabbas akwai abinda ke damunshi, to ko dai akwai wani ciwo ne a jikinsa? Wannan tunanin yasa hankalinsa yai mugun tashi ba shiri ya kira abokinsa wan

da yake doctor ne yasanar dashi yana bukatar yazo a dubashi.

Cikin kulawa yace “Kazo sai muji menene matsalarka.”

Shida yake tunanin zaman gida dan ya kula da matarsa to zaman nashi ma sam ba amfani dan baisan ganinta, ita kuma ba lafiya ba, da alama ka

ra mata ciwo yake saboda munanan abubuwan da yake mata.

Wayarsa ya dauka kawai ya rubuta mata sako akan zai fita.

Ibty tana dan kishingide a daki taga sakonsa da sauri ta mike ta fito, a falo ta ganshi daidai haryar fita ya canza kayansa zuwa manyan kaya

na shadda.

Bakinta nadan rawa tace “Yaya muje makarantar?”

Bai kalleta ba yace “Ki kira Ainah ta biyo kuje, ni zanje wani gun ne. Sannan ki tabbatar kin canz…..”

Sai kuma yai shiru, cikin dauriya tace “Dama taya zan fita a haka? Nima ai……”

Bai jira t

a gama magana ba taga yayi waje, da kallo ta bishi sannan tadan hadiye abunda ke makogoronta, tanasan sanar da Ummanta halin da take ciki ko zata tayata addu’a sai dai sam bazata iya ba, haka nan ta taso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login