Showing 105001 words to 108000 words out of 128353 words
kai makurar da ba abinda bazan iya aikatawa ba.
Dariya ya bushe dashi wanda ya kasa dainawa har abin ya fusat
ata, yau na tabbatar da abinda na dade ina zargi.
Ta hade rai sosai tace "Me?"
Na dade ina tunanin meyasa bakyasan Aminu yai aure? Bayan zaki iya neman maganin mallakar matarsa ki zauna lafiya? Sai dai yau kin nunamin dalili.
Ni babu wani dalili da nake
nema ka bani magani da mafita wacce zatasa Aminu hankalinsa ya kasa kwanciya sai ya bani gida da motar hawa, ni yanzu su nake san ya siya min sai na barshi da wannan figaggiyar matar tashi." Yayi dariya yana nuna mata kusa dashi, tayi kamar bata gane ba
yace.
"To tunda dai kin dage a barshi. Yanzu kizo nan dan dama Shine dalilin da yasa nace kizo din. Wannan aikin da za'a yi miki babba ne, kedai kawai kibi umarnin abokan aiki wato aljanun da suke yi." Hajiya ta kama baki, ta kuma kallan inda yake tace.
"Menene umarnin nasu?" Boka ya matsa kusa da ita, Hajiya kamar ta fashe da kuka yace. "Zaki kwanta dani, kiyi min abinda ko a mafarki bantaba jinsa, karkiyi korafi ko ki dinga jin haushin abin, yin haka zai sa aikin da za'a yi yaki yin kyau." Ranta ya sa
ke baci tace.
"Wannan aikin kam ya isheni, gabaki daya kun ruguza min guri kun maida shi kamar wani bakin kofi kowa yazo yasha ta wajan. Ni kam babu wata hanyar sai wannan ne?"
Mamaki ya kamashi, ta gaji kenan? Yanajin dadin matar nan gashi ta fara n
una gajiyawarta. Kodai yai mata asiri ta yadda komai yace mata ba zatai masa musu ba? "Nace babu wata hanya sai wadda ka fada?" Muryar Hajiya ta katse masa hanzarinsa.
"Idan har kina san Aminu yai miki abinda kike so, dole sai kin kasance da mutumin nan
dani na kwanaki bakwai." Hajiya ta rintsa ido tanajin wani irin bakin abu a wuyanta, haushi da takaici yasa tace masa, "Sai kai tayi." Murmushin jin dadi yai tare da janyo wani ruwa ya mika mata. "Fara shan wannan, ruwan farin jinine. Idan kika sha muka g
ama tarayya aka gama sauran aiyukan zakiga aiki, Aminu da kanshi zai nemoki." Banda tana san aikin nan da ba zata taba yadda tayi wannan aikin bakar wahalar ba.
Dakyar ta shanye maganin saboda tsananin baurin da yake yi, ga wani wari kamar na kwata.....
Ayusher ce
🏌
️
♂
️
[5/6, 9:26 AM] Hauwa Galadima:
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌
️
♂
️
*
*Top Ten! Takun Ha
ske Batch A*
*Na Kudine ki Bada 500 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku*
2083371244
Zenith Bank
Aisha m salis
Call.... +447894142004
*44*
A can bangaren Umar kuwa tunda ya shiga cikin dakin ya kasa fitowa, ya zauna sai zabga
tsaki yake tamkar wani karamin yaro.
"Ga tuwon dawa nan miyar kuka, sabuwa ce ma Larai ta kawo min ita kyauta."
Umar yabi langar tuwon da ido, ganinsa bakikirin yasa shi kawar da kai. Shifa dama in yazo kauye da kudinsa yake tahowa ya dinga siyan abind
a ransa ke so sai dai wannan karan ya taho ba kudi saboda Abba bai barshi ya shirya ba, gashi ya saida abubuwan kasuwarsa ya tattaro kudin ya boye a daki yana so in ya sace Ibty su gudu da kudin, sam ilimin maidasu banki baizo mai ba.
Kallan Goggo yai yac
e "Gwaggo bakuda fried rice? Ko 'yar shinkafa? Naga da ana kokarin yin abinci mai dan dadi?" Ya tambaya yana sauke numfashi. "A ina take mazan fama? Mace ce ko namiji?" Umar ya kuma jan tsaki dan yasan tasani sarai tsabar ya kona mai rai ne take wannan zan
cen, sau nawa tana zuwa gidan Abba tana ci? Cikin jin haushi ya dago tare da cewa. "Abinci ne fa." Gwaggo ta bude ido. "Ai kaji, ni ina nasanshi banda kinibibinka? Idan zakaci tuwo kaci shi garemu, idan bakaci ka barshi akwai mabukata."
Umar ya sake bin
tuwon da ido tare da cewa. "Kai haba ina! ni gaskiya bazanci wannan bakin tuwon ba wallahi."
"Iyyy ba shakka, to karkaci mana." Gwaggo ta dauke ta fita da kayanta sai fada take yi. "Karyar banza karyar wofi, indai kana cikin kauyen nan kuwa sai dai ka
mutu da yunwa dan banga inda zaka samu irin abincin da kukeci ba a birni. Ai ni tunda naga rashin darajarka a biki nasan lalai jin dadi da rashin godiyar Allah ne ya maka yawa.
Umar naji ya dafe goshi tare da tuno abinda yake yi, cikin isa da iko zai ce d
a Bilkisu ta dafa masa abu, tana rawar jiki take masa kuma mai dadi. Dan in yaso mugunta ko an dafo abinci daga bangaren Umma sai yace shi bayasan wannan abincin sai dai ta sake wani.
"Anya zan sakeki Bilkisu? Na rasa hasken zuciyata Ibty, wannan sheg
en mai kama da aljanu ya rike ta kam. Allah ya isa ban yafe ba, nasha wahalar kulawa dake amman aka cuceni. Har abada bazan yafe maka ba dan banza mai kan agwagwa."
Har aka yi sallar isha Umar yana daki yana shakar bacci, tun Gwaggo na zuwa lekashi harta
kwanta abinta ta rabu dashi. Wajan karfe goma sha daya na dare ya farka da wata masifafiyar jin yunwa.
Alwala yai yaje daki, sallah yai ya fito yana ta raba idanu da alama neman inda aka ajiye tuwon dazu yake. Wajan girki ya karasa yanata bude-bude, kar
ar motsi yasa Gwaggo fitowa daga daki tana haska wajan.
"Wace irin fitinace wannan? Mekake nema a wajan?" Cikeda rashin damuwa yace. "Tuwon." Gwaggo ta rike baki, "Tuwo! Aikuwa babu." Ta fada tare da komawa zata shiga daki yace. "Tuwon ne babu?" Tace "Kwa
rai ma kuwa, ko kana shakka ne?" Kafa yasa yai shuri da murfin tukunya yana masifa.
"Ya za'a ce babu tuwon bayan ansan banci ba? Wannan ai ba daidai bane wallahi. Haba Gwaggo ya zaki cinye?" Mamaki ya kamata. "Wai dama zakaci? Bana kai maka ba ka tsaya k
ana cewa wai kai kafi son menene? Toh tuwo dai ya kare sai kasan abinyi."
Tana kaiwa nan ta shige dakinta, Umar kuma yai kwafa ya koma daki. Kenan yau da uwar yunwa zai kwana, dama ba wani abu yaci ba. Duk ya rasa abinyi dan ko kudin siyan awara bashi d
asu ballantana yace zai siya, kodama yana da ku
ɗ
in yanzu babu kowa a gari saboda dare ne duk antafi gida.
"Idan ka gama kunkunin kazo ka karba, ai da na zata balangun Dan Bale zakaje ka siyo tunda ba zakaci tuwon dawa ba." Umar yaga Gwaggo na miko masa la
ngar yai saurin karasawa zai karba ta rike. "Bazakai min godiya ba?" "Nagode Gwaggo." Ya fada yana cizon lebe.
"Ato gobe ma kace min bazakaci tuwo ba kaga karyar banza." Umar yaki magana ya koma ya zauna tare da faracin tuwon yana lumshe ido saboda dadi
.
Tas ya cinye tuwon ya kura da ruwan sanyi na randa tare da sakin katuwar gyatsa yana faman hura hanci.
Saboda baccin da yai hakan ya hanashi yin na dare, ga duhu ga sauraye sai kuka suke wasu kuma suna gasa masa cizo yana ta buge-buge da riga. Haba
malam birni lafiya ne, idan babu nepa ga inji, idan babu kuma ga sola duk dan kar a zauna cikin duhu. Gashi zuciya ta kawoshi kauye yazo sai wahala yake sha.
Haka yai kwanan zaune gashi ko tunanin yin nafila da istigfari beyi ba, sai tunanin yadda ibty t
ake mannewa jikin Aminu yake, daya rintse ido zai hangesu kwance kan gado suna soyayya a zabura zakaga ya mike yana sauke huci sai kuma ya jawo filo ya nausa yace "Allah ya isa tsakanina dakai mugu, azzalumi dan bakin ciki."
Babu ruwanshi da yadda ya ba
ro Bilkisu bare ya tausaya mata, yasan dai kawai zai bar auransu ne saboda shima yaci gaba da morar arzikin da yakeci.
**********
Aminu ya zaunar da ita kan gado kallansa kawai take itakam mamaki duk ya isheta, gani tai ya koma gefe ya zauna, cikin sa
nyin jiki ta dan sunkuyar da kanta kasa, ita dama tayi mamakin yanda ya canza ashe ba gaba daya ba......"
Jin an jawota ya kwantar da ita akan cinyarsa ne yasata kallansa cikin wani yanayi, hannu yasa yadan zare hijab din kanta sannan ya cire hularta ya s
a hannu asaman gashinta, kallan mamaki kawai takemai sai wani irin faduwar gava da takeji akai akai, shiru ne ya ratsa dakin saboda abu ne da basu taba yi ba, itakam lumshe idanu tai kawai tana addu'a Allah karya kawo abinda zai sake shiga tsakaninsu.
Ci
kin wannan yanayi taji yace "Kiyi hakuri ki yafemin."
Idanunta ta bude a hankali ta saukeshi akansa, dan murmushi yai cikin sanyi yace " I don't know what happens to me, gashi kiri kiri zuciyata nasan tausaya da baki kulawa sai dai jikina baya iyawa, hak
a kawai in na kalleki sai inji duk duniya ba wanda na tsana irinki, sai zuciyata tai ta fadamin abubuwa daban daban."
Idanunta ne suka dan ciciko tana kallansa, ganin ya kalli idanunta yasa tadan sauke idanta kasa, sunkuyowa yai wanda hakan ya kara sa ka
ta faduwar gaba, a hankalinya sumbaci idanunta, sannan yace "Wannan yayan ya saku kuka sosai ko?"
Cikin wani yanayi tace "Eh."
Murmushi yai yace "Madam yaushe na tambayeki?"
Dan baki ta turo tace yanzu mana."
Ya dan girgiza mata yatsa yace "ni ga wanda
na tambaya nan bake ba.."
Ta kalleshi tadan juyo ta ciki saitin cikinsa tana san yin magna sai dai haryanzu kwarjini yake mata "Ya ya? Har an gama maganar dani? Bayan ina kallan yanda kika dage kina magana da Bal......"
Batasan sanda ta dago tasa hannu
ta rufe mai baki ba, dan baya ta turashi hakan yasashi kwanciya akan gadon ita kuma ta dan daneshi da hannunta a bakinsa, kallansa tai da sauri ta cusa kanta cikin kirjinsa cikin kunya, "Ni dama nasan abinda kike san aikatawa kenan."
Dagowa tai cikin mama
ki tace mene?
Yanda ta dadaneshi ya nuna mata yace "Gashinan, so kike ki kwanta a jikina.
Kokarin mikewa ta fara yasa hannu ya rike kugunta, yace "Daga baya kenan, yanzu wayancewa kike shirin yi."
Kallan shagwaba tamai tace "Allah ni....."
Kai yadan ka
rkatar alamar ko?
Hakan yasata yin murmushi, a hankali ya kwantar da ita a kirjinsa shiru suka sakeyi, can cikin wata murya yace "Me kike tunani akan abinda aka gani a bayan hoton can?"
Shiru tai bata dago ba sai dai tace "Banida kwakwaran hujjar dazan b
ada akan abinda banida masaniya a kai."
Yanayinsa kadai xaka kalla kasan lalai yanacikin wani yanayi mai wuyar fassarawa.
Murmushi yai, dakin yai dan shiru kowa da abinda yake sakawa a ransa, "Abinda ya faru dazu yana nuna san da Na'imah ke min da wanda
nake mata ba tsakani da Allah bane?"
Ibty ta juyo tana kallansa dan ya bata tausayi sosai yanda yai maganar, mikewa zaune yai ya dan yi ajiyar zuciya yace "ina tunanin na girma nasan duniya, ni babba ne ashe babu wanda ya kaini kankanta."
Ibty ta bude b
aki zatai magana taga ya mike kallanta ya juyo yai yace bari nai meeting, karfe uku ne gashi ban kula ba har ukun tayi."
Kai ta dagamai a hankali tare da binshi da kallo harya fita, komawa tai ta kwanta rufda ciki s kan gadan tace "Wannan wani irin bala'i
ne?"
*******
Washegari.....
Abin duniya duk ya ishi Hajiya, alakarta da boka ya fara isarta musamman da yanzu take jin idan beyi ba kamar ana tsunkulinta a sassan jiki, ga wancan tsinanen mutumin da yafi boka danshi inya fara ganayin kusan awa biyu k
afin ya gama, takaicinta ma sam ta kasa sanar dashi bata so ta gaji. Dan karamin daki ko ince dan karamin gida wanda daga daki sai bandaki suka ware mata daga kusa da gidan Malam ya take zaune a ciki suna abinda suke so da ita, gaba daya ta kasa nuna rashi
n san da takewa wannan rayuwar, duk ta rame ya jeke, wai kuma duk cikin nemo kan Aminu ne.
Tana zaune tayi zugum kamar wacce taiwa sarki karya, wayarta tai ringing jiki na rawa ta dakko. Dan dazun nan mutumin nan ya kawo
Mata sabuwar waya ya kuma sa an
mata welcome back na sim dinta, dan tun jiya take rokonsa akan ya taimaka mata, sai daya sadu da ita sau biyu s lokaci daya wai kudin yin welcome back da waya.
Ganin Aminu yasa zuciyarta harbawa, haka kurum taji yau bata san daga wayarsa, dan haka harta
tsinke bata samu damar dagawaba. Gefe daya na zuciyarta yana gaya mata aikin boka ne ya fara aiki.
Kiran ya sake shigowa ta dauka jiki na rawa kamar tana gabanshi muryarta har tawa takeyi.
"Waalaikas salam." Tana fada ta sa kuka cike da makirci. Aminu
dake zaune a falo bayan ya
dawo daga aiki, da sauri ya dafe goshi, gaba daya haushinta yakeji, abu daya yasa shi nemanta dan yanasan jin meke faruwa sannan dazu Islam da Ilham suka tambayeshi tana ina? Dan suna dawowa dazu suka nufi bangarenta suka gansh
i a kulle. Wai Suna san ganinta.
"Ina wuni Hajiya?" Hajiya ta hadiye kukanta, mamaki ya kamata a da idan har yaji tana cikin damuwa rudewa yake balle kuka, amman yanzu tana kuka yana miko mata gaisuwa.
"Dama tambaya zanyi kina ina?" Hajiya ta zaro ido
'Mezai mata? Ko gidan ya siya mata ne? "Hello." Taji ya fada tai saurin dafa bango. "Ina gidan wata kawata, ince dai lafiya ko Aminu?" Aminu yace, "Ina so nasan inda kike yanzu." A razane tace,
"Lafiya dai ko?" Yace, "Zanzo gurinki ne." Ta zaro ido tam
kar tana gabansa, Toh me zai yi mata? Gabanta ne yai wani mumunan faduwa badai maganin da akace an bude komai ya karye yake kokarin Tuhumar ta akai ba? Ya san Na'ima ta aikata ne? ko kuma sha'awar ganinta kawai yakeyi? Tana san tasan mezai kawoshi dan tasa
n abin fada masa.
Muryarsa ce ta katseta yace "Hajiya kinyi shiru." Tace "Wallahi ina fama da ciwon ciki ne, sai dai ka bari wani lokacin sai mu hadu. Kaga ba dadi nace kazo bayan matar batasan zakazo ba, ni kuma bazan iya fita ba saboda ciwo."
Kafin
ya bata amsa tayi saurin cewa "Ina su Ilham? A gaishe min dasu." Kafin Aminu yai yunkuri magana yaji ta kashe wayar, abin yai matukar bashi mamaki, ya kuma sake tabbatar da cewa Hajiya tasan da wadannan layun ta kuma san dalilin dayasa yake nemanta sarai.
Tsaki yaja cike da haushi ya ajiye wayar, yana jin tsananin kunya da tsanar kansa yanzu a kalli Hajiya ace surukarshi ce, shi kuwa mai ya kaishi hada zuri'a da wadannan mutanen? sannan su Islam su kalleta suce kakarsu ce, wannan abin yana ci masa zuciya.
**********
Da kallo Abba ya bita, Bilkisu kuwa kamar ta sani taki yadda da dago kai sai wasa tske da wajan key din kekenta. Umma ce ta fito daga kitchen ganin Bilkisu yasa ta saki murmushin jin dadi, saboda bata san ganinta cikin damuwa.
"Kin fit
o kici abinci?" Bilkisu ta daga kai batace komai ba dan har lokacin ranta babu dadi.
"Zonan Bilkisu." Cewar Abba yana ajiye wayar hannunsa. Ta gungura keken zuwa gurinshi bata kallesa ba yace.
Yadan ja numfashi yace "Kina tunanin Umar zai yadda da aure
tsakaninku? Ada ina yiwa Umar kallon mai hankali da sanin yakamata.
Amman yanzu tunanina ya kauce daga wannan kyawawan zuwa akasin su. Kina ganin zakici gaba da zama tare dashi har tsawon rayuwarki?"
Shiru Bilkisu tayi dan ji take ko hauka Umar yake z
ata iya zama dashi, ballanta kuma yana da hankali kawai soyayya ce ta rufe masa ido kamar yadda ta rufe mata duk wani aibunsa. Kuma yanzu ma maganganun da Abba keyi akan shi, ji take kamar ta mutu saboda aibata mata miji da yakeyi.
Cikin sanyin jiki tac
e, "Abba lokacin da kuka yiwa ibty aure batasan waye mijin ba, kunyi mata an kai ta gurinsa, ya taya har ta janyo suka fara kula juna duk bamu sani ba. Abba nima ina so ku bar aurena dana Ya Umar har zuwa lokacin da zai manta da wacce ke cikin ransa."
"M
una so mu karbar miki yancinki ne Bilkisu, barin Umar a haka ba zai sashi ganin mutunci da darajarki ba. Ki bari mu nuna masa ko wacece ke a gurin mu ta yadda nan gaba zaiji tsoran takaki yadda yakeso. Hakan zai yiwune idan har kin bamu hadin kai Bilkisu."
Tayi shiru tana share hawayen da suke bata mata fuska.
"Shikenan Abba amma dan Allah karkuyi yadda zai sakeni, idan Ya Umar ya rabu dani zan shiga damuwa dan Allah Abba."
Tausayinta ya kama Umma, ta karasa wajanta tana lallashinta cikin kulawa "Ya isa
kukan, Insha Allahu yadda kike san yaran nan haka shima zai soki wata rana, zanci gaba da yi miki addu'a Insha Allahu ba zaki kuma rasa wani abu ba, kiyi shiru ki kuma yi hakuri." Abba ya amsa da "Amin ya Allah."
Shiru Abba yai cikin wani yanayi yace "Im
an fa?"
Tace "Tana gidan koyan dinki."
"Kin kira Ibtisam din?"
Tace "Ita da hankalinta yake a kwance? Kana ganin gidan da aka kaita ga mijinta na santa, zan kirata gobe, tunda kaji shiru bata kira ba ai lafiya ce, bakaji hausawa sunce inka ji shiru lafi
ya ba ce?"
Kallanta yai kawai baice komai ba, yana mamakin yanda sam take nuna banbanci karara akan 'ya'yanta, sam bata nunawa Ibtisam kulawa,