Showing 36001 words to 39000 words out of 128353 words

Chapter 13 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

30

dole in yaran nan suka dawo ta sake hure musu kunne in har ba so take a maidata kauye ba dan wlh akan a maidata kauye lalai zata iya yin abinda har su mutu bazasu manta da ita ba.

🏌🏻

‍♀

️

💫

IBTISAM......

💫

      (.......

..In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zen

ith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

15

🤸🏻

‍♀

️

Cikin katafaren gidan yai parking, kallan harabar gidan tai duk da tasan kudinsu Ainah bata kawo gidan Ya Aminu yakai haka girma ba, gan

in ya fito daga mota yasa itama ta fito tabi bayansa. Mai gadi ne ya taho da gudu bayan ya rufe gate yazo yana gaishesu, cikin girmamawa ta amsa, sannan ta kada bin bayan Aminu.

Key ya dauko ya bude gidan sannan suka shiga, cikin katafaren falanshi suka

tsaya tana kallan yanda falan ya tsaru, kallanta yai yace “Tacan kofar ne bangarenki” kallan inda ya kalla tai batace komai ba, harzai shiga ciki sai kuma taga ya dawo, gaba yai ta sake bin bayansa zuwa nata bangaren, da alama akwai kofar da in aka tashi s

higowa ba sai an shigo ta falansa ba, itama falanta ba karami bane sai dai baikai girman nashi ba, gashi ansa mata kujeru masu kyau, labulaye ne dai sai mai shara shara na ciki aka saka, kallan dakunan dake jikin

falan yai guda uku, yana daga tsaye a bakin

kofar dake tsakanin falan biyu yace “wancan ne dakinki, na kusa dashi nasu Islam ne sai dayan na baki in kinyi.”

Kallanshi ta juyo tai tace “Ina su Islam din? Naga basa nan?”

“Suna gun kakarsu.”

Kai ta jinjina tace “Da mun sani mun biya gidan Ummy mu

n taho dasu ai.”

“Bagun Ummy suke ba.”

Mamaki ne ya bayyana a fuskarta tace “Gun wa? Naji kace kakarsu?”

Yadan daure fuska kadan yace “Gun dayar kakarsu, sannan suna nan daya bangaren insuka san na dawo zasu shigo.”

Gaba daya ta kasa gane me yake nu

fi cikin dauriya tace “Kakar tasu anan daya bangaren take ko me?”

Juyawa yai yace “Eh! Agurina take a zaune.”

Zaro ido tai cikin tsananin mamaki tace “Kakarsu ba mahaifiyar Aunty Na’imah kenan ba? Me take a gidanka?”

Wani kallo ya watsa mata fuskarsa

ya sake murtukewa yace “A karshe cewa kikai gidana ko? Kenan inada ikon ajiye wanda naso.”

Tsananin mamaki yasa ta zubamai ido, bata gama tattaro tunaninta ba taga yabar gun, kasa daurewa tai a fili tace “Ina aka taba wannan abu?” Yana jiyota bai tankata

ba.

Tana tsaye tana dogon nazarin wannan lamari itakam tunda take bata taba jin inda uwar matarka data rasu take zaune da namiji ba, mutum ba muharaminta ba bakomai ba?

Sam kwakwalwarta ta kasa nutsuwa dajin wannan saban lamari mai abin mamaki.

*****

*

Aminu kam rai a bace ya wuce dakinsa wato daga zuwanta hartana neman nunamai abinda yai baiyi daidai ba? Ita a wa? Haryaushe ma tazo gidan da zatamai gadarar banza?

Toilet ya shiga ya watsa ruwa sannan ya fito, waya ya dauka yaga missed call din Hajiy

a, da sauri ya kirata.

Ringing biyu ta dauka, dan tunda taji bude gate ta kasa zaune ta kasa tsaye, daki ta shige tabarsu Ilham a falo suna wasa.

Sallama tai cikin muryarta, ya amsa cikin girmamawa sannan ya gaisheta, ta amsa kafin tace “Tunda su Islam

sukaji karar gate dinka suke ta ihu wai su sai sunje sun gaisheka.”

Murmushi yai yace “Su shigo mana Hajiya, sannan inda hali ma su kwana anan tunda gobe asabar.”

Tace “Ayi haka kuwa? Daga zuwan Amarya sai a daura mata wahala?”

Jikinsa ne yai sanyi ya

ce “Kiyi hakuri Hajiya nayi aure bansanar miki ba.”

Shiru tai kafin tace “Aminu magana ta gaskiya naji ba dadi, dan bansan da auranka ba sai ranar da akazo jere, nayi mamaki kwarai da gaske, a tunanina nima mahaifiyarkace, saidai yanzu ka nunamin iyakata

, ka tabbatar da banida daraja a gunka.”

Kai ya girgiza da sauri yace “Wlh Hajiya ba haka bane, komai na auran nan ya faru ne cikin gaggawa, nikaina bansan ya akai abubuwan nan suka kasance ba.”

Murmushi tai na rashin jin dadi kafin tace “Yanzu dai bari

na rako su Islam, sai dai daga jiya zuwa yau na yanke shawarar barin gidan nan, dama nacigaba da zama ne saboda yaran nan, tunda yanzu sunada mai kula dasu inaga gwarw……….”

“Hajiya ki bar maganar nan dan Allah! Ke amanace a garrni.”

‘Yar karamar ajiyar

zuciya tai da alama haryanzu aiki na jikinshi.

Nan sukai sallama akan zata rako su Islam.

Falo ta fito ta kallesu tace “Ku dauko dankwalinku muje ku gaida Dady ya dawo.

Tsale suka fara cikin tsananin murna, Hajiya tace “Kardai ku manta Dady ya kawo m

atarsa.”

Yanayinsu ne ya canza lokaci daya, Ilham tace “Muguwar matar?”

Kai Hajiya ta daga alamar rashin jin dadi tace “Kardai ku manta inhar kunaso karta wahalar daku ta dinga dukanku, kada ku kuskura kuyi hira ko wasa da ita, ko abinci tai kuce baiyi

dadi ba kunfi san nawa.”

Da sauri suka daga kai alamar to, tace “Sannan kada ku kuskura kuce ni na fadamuku inba haka ba in taji nasan sirrinta zatasa Dady ya koreni.”

Hankalinsu ne ya kara tashi da sauri sukace bazamu fada ba Hajiya sannan bazamu taba

yadda a koreki ba.

Ya shafa kansu sannan suka fito tare.

Ibtisam tana tsaye inda Aminu ya barta haryanzu ta kasa tattaro tunaninta, amma ai su Ummy basu sanar a gidansu ba, itakam wani abu ne wannan? Banbarakwai wai namiji da suna Hajara? Ji tai ana kwa

nkwasa kofar dake jikin falanta.

Kallan kofar tai haka kawai taji gabanta ya fadi, daurewa tai ta tako a hankali tana tunanin wanene wannan daga isowarsu?

Jikin kofar taje tace “Wanene?”

Daga waje Islam cikin tsiwa tace “Su Islam ne.”

Murmushi ne ya

bayyana a fuskar Ibty da sauri ta bude kofar.

Kallanta sukai a tare sukace “Kawar Aunty?”

Ta rusuno ta lakuci kuncin Islam tace “Mai dimple?”

Ilham tace “Kema kinzo ganin amaryar Dady ne?”

Murmushi tai tana kallansu, dan dagowa tai idanunta suka had

u da babbar mace dake tsaye a waje tana kallanta.

Yanzu ma gabanta ne ya sake faduwa, ta daure tace “Ina wuni?”

Hajiya ta kalleta fuska dauke da Murmushi tace “Kece Amaryar tamu?”

Tadanyi kasa dakai cikin kunya, kallansu Islam tai tace “Ashe ma kunsan

Amaryar Dady din?”

Kwace jikinsu sukai daga gun Ibty suka nufi gun Hajiya da sauri suka rike hannunta.

Shigowa sukai tace “Kuyi maza ku gaida Mumy dinku.”

Kallanta sukai fuskarsu duk ta canza, ciki ciki sukace “ina wuni?”

Kafin Ibty ta amsa sunyi ba

ngaren Dady dinsu da gudu.

Cikin mamaki Ibty tabi bayansu da kallo, Hajiya tace “Yara ne basu san da auran ba shiyasa.”

Kai ta daga sannan ta tsuguna ta gaisheta, amsawa tai tana kare mata kallo, da alama yarinyar zatai saukin juyawa dan kana ganinta kas

an ba irin yaran zamani bane masu wayau ba.

Ibty tai kasa dakai gashi ko kitchen bata sani ba balle ta duba ko akwai ruwa ta kawo mata.

Mikewa tai tana tunanin inane kitchen din? Muryar Hajiya taji a bayanta tace “ga kitchen din can.”

Yanzun ma gabant

a ne ya fadi dan sam batai zata. Jin muryarta a bayanta ba, cikin sanyin jiki ta nufi kitchen din, itama Hajiya tabi bayanta.

Suna shiga ta kalli kitchen din tace “Ansha jere, kamar Na’ima bata zauna a gidan ba, angyarashi tsaf.

Dakyar Ibty ta dan daga

kai, Hajiya ta dan matso ta dafata tace “Nasan zakiga zamana a nan bai dace ba, sai dai inasan sanar dake karki damu, dama rashin auransa ne yasa na hakura na zauna, sai dai yanzu tunda kinzo nakuma yaba da hankalinki zan tattara na koma garinmu.”

Itakam

Ibty kai kawai tai kasa dashi dan batasan me zatace ba, bari muga dakin amarya.

Kafin Ibty tai magana sai gani tai ta fito daga kitchen, da sauri ta biyo bayanta dan ko ita kanta bata shiga dakin nata ba.

Kai tsaye taga ta shiga dakin daya nuna nata ne

, bin ta tai a tsaye ta ganta tana murmushi tana sanya albarka, Ibty ta kalla tace “Sai naji kamar karar ruwa na zuba daga bandaki ko?”

Kunne tadan kasa kafin tace “Banji ba, sannan banma shigo dakin ba balle na kuma.”

Hajiya tadan dafata tace “Kin manta

‘yan jere sunzo? Kije ki duba nidai naji karar ruwa.”

Kallan wata kofa tai wacce da alama itace ta toilet din, tana shiga Hajiya tai saurin daga gado tasa wannan layar da aka bata a kasan katifa, tana maidawa Ibty na fitowa da sauri ta zauna akan gadan t

ana cewa “Daki yayi kyau masha Allah! Allah ya kawo kazantar daki.”

Itadai Ibty ko Amin din ta kasa cewa saboda jin abin take wani banbarakwai.

Hajiya ta sake takowa inda take ta dafata tace “Allah ya baku zaman lafiya, Aminu a haka zakiga kamar mutum n

e mai wuyar fahimta sai dai ina tabbatar miki zakiji dadin zama dashi, dan haryau ina tuno irin kulawa da farincikin da Na’imah ta samu a gunsa.

Kanta na kasa kawai tana wasa da yatsun hannunta, Hajiya tadan shafa kanta tace “Bari na wuce, su Islam yace

zasu kwana anan saboda gobe asabar.”

Kai kawai ta daga dan haka kawai ta samu kanta dasan matarnan ta tafi.

Tana fita ta sauke ajiyar zuciya, tare dayin hamdala, tace “Mata ba kishiya ba bakuma uwar miji ba, dame zan kirata?”

****

Bangaren Aminu ta

nufa, tana juyo ihunsu Islam da alama labari take bashi, murmushi tai sannan ta shiga cikin falan, daga daki take juyo maganarsu, kunya takeji ta shiga dakin daga zuwanta, komawa tai bangarenta tana sake kallo, ba shakka Abba yayi kokari a yanda tasan bay

asan sakin kudi lalai yayi kokari.

Kayanta ta dauko ta fara jerawa a cikin wardrobe tana yi tana tunanin yaushe Ainah zatazo?

Kamar daga sama taji ana kiranta, da sauri ta fito yana dan jingine da bangon falanta.

Kallansa tai tace “Ya Aminu gani.”



“Kun gaisa dasu Islam?”

Ya daga kai alamar eh sannan tace “Gaisuwa kawai mukai da alama zumudin san ganinka suke basu tsaya ko hira munyi ba.”

“In ke baki jasu da hira ba su ta ina zasu saki jiki?”

Kalamansa sun bata mamaki, yau fa aka kawota? Ai dai a

mata kara a bari susan juna sosai ko?

Jitai yace “Sorry bawai takuraki nai ba daga zuwanki jinai Islam tace kin daure fuska bakyasan su miki magana.”

Yanayin fuskarta ne ya bayyanar da tsananin mamakinta tace “Tare suke da Kakarsu, Ya Aminu so kake na

i abin da za’acemin yarinya a gabanta?”

Shiru yadanyi da alama ya fahimci laifinsa, amaryace fa ya kamata a barta a hankali tukun.

Gyaran murya yadanyi yadan shigo cikin falan yace “Kin shiga kinga gidan?”

Fuskarta a hade tace “ A’a.”

Yanda tai maga

nar ya tabbatar ranta ne ya baci, ganin basu da abin cewa yasa ya koma bangarensa.

Kallansu Islam yai dake kan gadansa suka hira, yace “Islam kun manta Mumy dinku Amaryace? Sai a hankali zata saki jiki, sannan laifinku ne da baku dade a gunta ba.”

Kalla

n juna sukai Islam da Ilham, a ransu sukace wato har anfara hadasu fada da Dady kamar yanda Hajiya tace ko?

Dama Aminu bamai zama yai wasa bane, sai dai in suna hirarsu zai jisu, gaba daya yanayinsu ne ya canza, suka zauna sukai shiru duk suruntu Islam ba

ta sake cewa komai ba, a haka har sukai bacci.

Ilham ya fara daukanya nufi bangaren Ibty da ita, yana shiga ita kuma tana fitowa daga daki zataje kitchen dan kishirwa takeji, kallansa tai da sauri ta bude kofar dakin daya nuna nasu ne, jitai yace “Thanks

.”

Nan ya wuce ya kwantar da Ilham a gadan sama, sannan ya fito ya koma ya dauko Islam ya kwantar a gadan kasa, karasowa tai ta gyarawa Islam kwanciya sannan ta luluba musu bargo, addu’ar bacci ta musu ta shafa sannan ta dago.

Yana tsaye yana kallanta

harta iso bakin kofa.

Hanya ya bata ta fara fita sannan shima ya fito, hannu yasa a aljihun jalabiyarsa yace “Akwai ruwan tea kuwa?”

“Bansan kan kitchen din amma nasan dai ruwan zafi bazai gagara ba.”

Kitchen din ta nufa yabi bayanta, ruwa tasa a kettl

e yana tsaye yana kallanta, wato haryanzu bata ware ba? Badai so take ya bata hakuri ba ko?

Neman cup ta shiga ta dauko spoon ta zuba, ina sugar? Da lipton?

Muryarsa ce ta katseta “ki zuba ruwan a flask dashi zan wuce, sannan inada lipton a dakina, cup

da spoon kawai nake so.”

Bata kalleshi ba sainto kawai datace, hadawa tai tasa akan tire, sannan ta nufo kofa, hannu yasa ya amsa.

Kallan juna sukai, a hankali ta dauke idanta jitai yace “Barshi zan wuce dashi.”

Kai ta daga alamar to, amsa yai sannan

ya sake kallanta, “Akwai abinda zakici da daddaren nan ko nasa a kawo miki?”

Kai ta girgiza alamar a’a tace “Akwai ragowar doyar safe zanci, amma kai daga tea shikenan?”

“Zan hada da bread naba mai gadi ya siyo kayan tea da bread.”

Shiru suka danyi ka

fin yace “Wajen nawa zaki kwanta?”

“In na gama gyara kayana abinci kawai zanci na kwanta.” Abinda tace kenan, dan ta tabbatar babu wata sha’awar janta a jiki da Aminu yake dashi balle tasa ran zai nemi su kwana tare, idanunsa kadai inta kalla tasan bashi

da wannan ra’ayin, to ita ta zauna tayi me?

Kai ya jinjina yace “in akwai abinda kikeso kimin magana, sannan kafin ki kwanta please kikai Islam toilet tai fitsari, Ilham tana tashi da kanta.”

“To”

Yadan sake kallanta yace “Gobe sai kimin list din abind

a kikeso na kayan abinci, dan duk kayan abinci a gun Hajiya suke, daga bangarenta take dafa mana.”

Sakato tai tana jin wannan lamari, ikon Allah sai kallo, Aminu ya juya ya tafi bangarensa, daki ta koma ta zauna a bakin gado tana kallan kayanta.

Wannan

aure anya zataji dadinsa kuwa? Ai ko a garin gala galu mutum yaji ance zai zauna guri daya da mahaifiyar matar miji wace ta rasu to fa ansan akwai matsala, ta dauka yara ne kawai zataja a jiki yanzu wani irin zama akeso tayi? Itakam anya tanada raban samun

farincikin aure a rayuwarta? Ta rabu da Umar yanzu kuma wace rayuwa ta fada?

😢

Nikaina Ayusher tambayar datazomin kenan.

🏌🏻

‍♀

️

💫

IBTISAM......

💫

(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą

Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA* *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar

biya ta wannan* 07065283730

16

🤸🏻

‍♀

️

Kallan dakin tai, tausayin kanta ya kamata, ada in tana karanta novel ji take inama abinda ke faruwa a ciki ya faru da ita? Yanda namiji ke dokin daren farko? Asha love, a kaika toilet a gasa ka? Sai dai duk wa

nnan bori nata ya tsaya ne daga sanda ta fahimci lalai Umar bazai barta taji dadin rayuwa ba, ko a skul in kawayenta na hirar kwanciyar aure sai dai tai shiru tana kallansu, to ita gashi ta auri wani ba Umar ba amma ko kadan bataga alamar sha’awarta a tatt

are dashi ba.

Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki bayan ta kara kallan dakin, namijin da kuka kwana a hotel ku biyu tare bai nemeka ba ina zakasa ran zai nemeka a gatan gida haka? Inda bangarensa daban? Ga yara? Ga kuma wata mata a can bangaren da bat

asan me zata kirata ba.

Kayan bacci ta saka sannan ta saka hijab ta fito daga cikin dakin, haka kawai ta samu kanta da rashin san kwanciya a dakin.

Bude dakinsu Islam tai kawai ta dauko pillow da bargo ta kwanta a kasa, akalla dai ta dingajin numfashin

mutane.

Ta dade tana juyi a kasa bayan takai Islam fitsari kafin bacci ya dauketa, bacci tai sosai dan ta dade tana juyi a kasa.

Aminu kam bayan ya dawo daga masallaci harzai wuce daki sai kuma ya dawo, tunani yake da alama batasaba da gidan ba kila ta

makara sallah.

Dakinta yadan murda kadan tare da haska fitilar wayarsa, da karfi naga ya tura kofar ganin ba kowa a ciki.

Ga kuma bandaki a bude, babu alamar mutum a ciki, samun kansa yai da rikicewa, ina ta shiga? Fitowa yai daga dakin ya wuce kitchen,

nan ma ba kowa, tashin hankali ne kiri-kiri ya bayyana a fuskarsa, dakin baki ya bude nan ma babu alamarta, saman goshinsa ya shafa sannan ya bude dakinsu Islam dan ya tabbatar ko su lafiyarsu kalau.

Tsayawa yai kawai daga bakin kofa yana kallanta tana

bacci a kasa, kai ya girgiza sannan ya shiga cikin dakin, sake haskata yai yana tunanin me takeyi a kasa? Bayan ga dakinta can? A kalla dai ba tsoro take ba tunda yaga ta kwana a daki a hotel ita kadai, sannan bawai kwanciyar kasan takeso ba tunda tai bake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login