Showing 63001 words to 66000 words out of 128353 words

Chapter 22 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

17

daga kan kofar ta maidashi kan Yaya dake kusa da ita.

Umar na shigowa idanunsa akan Ibty suka sauka, gani yai kamar ta kara wani irin kyau, kaunarta ce ke kara mamayemai

zuciya, ji yake kamar ya mamake mutanen falan ya karaso ya rungume ta jikinsa.

Muryar Aminu ce ta katseshi wanda yana zaune yana kallan irin kallan dayake ma Ibty.

“Malan Umar ashe kana gida?”wani irin mugun kallon tsana ya makawa Aminu, shikam duk duniy

a ba wanda ya tsana sama da mutumin nan, kallansa yake yana wani huci, Aminu ya kalleshi yana daga zaune ya mika mai hannu.

Umar a ransa yace badai nufinsa na karaso na mika mai hannu ba?

Kallan Umma yai wacce itama take kallansa, kamar zaiyi ihu haka ya

karaso ya mikawa Aminu hannu, matse hannun Aminu yai iya karfinsa, haka ya kalleshi yace “Karfi kakeji ne?”

Sakeshi yai cikin takaici, Umma ta koma ciki dan dama ta sake fitowa ne jin Bilkisu ta iso.

Umar ya sake kallan Ibty yace “Ibty?”

Dan kallansa

tai sama sama tace “Ya Umar ina wuni?”

Yanda ta gaisheshin ya bashi mamaki kamar irin taga wanda bata sani ba a waje?

Kasa amsawa yai sai ido daya kafeta dashi……

{Nikam na lalabo na fito dan na sha ruwa na koma ina tsoron kar a hada dani a makure}

[3/1, 8:15 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ka

samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

25

Ibty tadan dago kadan ganin idan Umar kyar a kanta yasa tai saurin kallan Amin

u, shikam yana gani zata juyo ya dauke kansa da sauri tare da kallan Umar yace “Zauna mana? Tunda ka gama nuna karfin?”

Ibty ta kalli Bilkisu tace “Yaya mu shiga daki ko?”

Tai maganar tare da mikewa, tana neman tura keken Bilkisu. Muryar Aminu taji yace

“Ranki ya dade inaga zan wuce.”

Gabanta ne yai wani irin faduwa ta juyo da sauri, kalmar ranki ya dade da zancen tafiyar ne suka sake dawo mata, cikin dauriya ta kalleshi tare da san shagwabe fuska tana mai alama daya taimaka karya tafi.

Umar ganin yan

da ta shagwabe fuska tana turamai alamun da kana gani kasan tsakaninsu ne yasa ya daki tabirun gabansa da kafarsa, uban zafin da ya ziyarci kafarsa ne yasa yadan ciji lebe, Aminu ya kalleshi yace “Jarumi badai bigewa kai ba ko?”

Wani mugun kallo yamai yac

e “Ko bigewa nai wannan karamin bugun zai min illa ne? Ko ba ka kula a gajiyar karfi na nake ba?”

Kai yadan jinjina tare da daukan bottle din ruwa daya fadi kasa saboda bugar table din dayai, nunamai robar yai sannan yace “Hakan nada kyau ai, in mutum nad

a karfi ya nuna a gani.”

Ibty kam tunda taga yanda ya bigi table din ta kara tsorata, zuciyarta sai dukan uku uku take, Bilkisu kam gaba daya kanta ta sadda kasa, idanunta suka ciciko da kwalla.

Itakam Iman wani irin kululun takaici ne ya kamata, ganin

yanda Aminu ya mai magana yasa tai murmushin jin dadi.

Ibty ta kalli Aminu da sauri ta girgiza mai kai alamar ya taimaka karya tafi, Aminu ya kalli Iman yace “Iman wannan yayar taki da alama batasan nai nisa, duk zumudin san tazo gida da alama bataso tag

a na tafi na barta.”

Iman cikin jin dadi tai dariya tace “Yaya ai da alama ka gama shagwabata tunda ta zauna ko minti daya na kula batayi sai ta kalleka.”

Mamakin yanda Aminu mai ji da girma yau yake biyewa Iman suna irin wannan hirar ne ya kamata, Umar

kam yazo wuya, ga azabar da kafarsa ke masa ga wani uban kishi dake nukurkusarsa, dan shi Kansa tunda ya shigo yaga yanda take kallan Aminu abin ya tsayamai a wuya.

Kallan Ibty yai idanunsa sunyi jaa sosai yace “Zuciyar mace ai batada amana, yanzu sai ta

i kicin kicin tace kai takeso anjima dan yaudara sai ta auri wani, shima daga ta gama yayinsa sai kaga tana neman tace ya saketa.”

Kowa na falan ya fahimci inda kalamansa suka nufa, Ibty ta kalli Aminu wanda ya dauke kai da alama yanzu bazai tanka ba kena

n, hannunta tadan rike cikin dauriya tana murmushi tace “Ya Umar kenan, ai in kaga mace ta canza ra’ayi to tanada dalilinta, sannan wasu mazan auren in Allah ya hadaka dasu ko na minti daya bakasan ku rabu balle har ka fara tunanin wani saki.”

Aminu yaji

dadin kalamanta sosai, kallanta kadan yai tadanyi raurau da ido tana jiran taga yabo a idansa, gani tai ya dau waya yana dan dannawa.

Kalaman Ibty sunyi matukar dukan zuciyar Umar, kafeta yai da ido yana sake jiyo kalaman a cikin ransa, yana ganin sanda

tai raurau tanayiwa Aminu wani sign, ji yake zuciyarsa kamar zata fito, idanunsa suka kada sosai sukai jaa ji yake kamar ya tashi ya shaketa ta sake maimaita kalamanta a falan nan.

Aminu yana dana waya yana kallan yanayin Umar, jikinshi ya bashi tabbas i

nba kowa a falan wannan ba abinda bazai iya aikatawa Ibty ba, anya zainiya barinta a gidan nan kuwa?

Kallanta yai haryanzu kallansa take da alama batama kula da kallan da Umar ke mata ba “Hajiya in zuba juice din da kaina ne?”

Abinda taji yace kenan, m

amaki ne ya kamata ta sake maimaita kalaman a ranta, takowa tai ta karaso gun ta daga kwalin juice din daya fadi akan table din ta bude sannan ta zuba a cup tare da mikamai, hannu yasa ya amsa sannan yace “Thanks.”

Tana kokarin tashi yadan mata alama dat

a tsaya, tsayawa tai yana sha yana tunanin abinda ya kamata yai, dan tabbas barinta anan ba karamin hadari bane kuma bai kamata ya dauketa daga zuwa ba, shi kuma bazai iya dadewa a gidan surukai ba.

Harya shanye bai gama tsaida shawara ba, cup din ya mik

a mata sannan ya kalli Umar yace “Haka take ko a gida tafiso sai na gama abu kafin ta mike.”

Ibty mamakin abinda Aminu yake aikatawa a gidansu yau take, anya Aminun data sanine kuwa? Umar kam bai ko tankashi ba idanunsa kyar akan Ibty.

“In ba abinda ka

ke ko zamu fita tare? Mu basu guri suyi hira?”

Idanu Ibty ta zare da sauri tace “A’a Yaya gwara ka tafi kai kadai.” Sam batasan sanda ta fadi hakan ba dan itakam ta tabbatar Umar zai iya yiwa Aminu illa in suka fita tare mutumin da kallo aka mata yake ne

man duka balle?

Ganin yanda kowa ya kalleta ne yasa ta fahimci ta kwafsa, daurewa tai tace “Ahh naji dama kace zaka koma gun aiki ne to karka makara.”

Ya fahimci abinda take shakka sai dai shima abinda yake shakka kenan, yana tsoron barinta a gida da wa

nnan mutumin.

Umar ya kalleta cikin wata murya yace “Nine bakyasan na fita da mijinki ko me?”

Tadan maida kai kasa dan batasan me zatace ba, Aminu ya kalleta tare da danyi mata karamin murmushi, itakam batasan wannan fitar.

Umar ya kalla yace “Muje?”

Da Yayi niyar kin zuwa sai dai yanda Ibty tai magana yasa yaji ma dole ya fita, kodan ya nunawa Aminu danyan jini ne.

Mikewa yai yace “Muje, dan dama ba abinda nake.”

Ibty kamar zatai kuma haka ta bisu da kallo har suka fita, ko mikewa ta kasayi daga i

nda take.

Mota suka shiga Aminu ya ja suka fara tafiya, idanu Umaf yadan lumshe kadan dan wani dadi daya ziyarceshi daya tuna inda ya zauna anan fa gun Ibty ta zauna, inama shida ita ne suke tafiya a motarnan? Tunowa da Aminu dayai ne yasa ya bude idanun

sa cikin bacin rai.

Murmushi yaga Aminu yadanyi, murtuke fuska yai tare da kallan gefe.

“Ango ango! Ranar aure ashe kaine kaba motata karfi.”

Umar ya gane mai yake nufi takaici ya hanashi amsawa, shiru ne yadan sake ratsawa, can Umar yace “Tunda kasan

abinda ke faruwa meyasa zakai sata? Da girman ka da komai baka kunyar abinda ka aikata?”

Bai kalleshi ba yace “ Sata?”

Umar cikin hargagi da masifa wanda dama kiris yake jira yace “Sata mana! Kana tunanin dakai da masu shiga gidan mutane ko masu yankan a

ljihu suna daukan kudin mutane kunada banbanci ne?”

Kai ya jinjina kafin yace “Kumafa hakane.”

Ai nan Umar ya kara hawa yace “Banda asarar zuciya da rashin imani ka taradda mutum nasan abu tun yana karami ka sace? Sannan dan asara ma kai ba yaro karami

ba? Kai ko kunyar abun bakayi? A haka a fuska kamar mai hankali da sanin ya kamata amma a boye kai babban dakiki ne mugu azallumi……..”

Karar burkin da aka taka da karfi ne yasa Umar ya kalleshi dan tabbas ya dauka hatsari zasuyi, kallansa Aminu yai yace “

Right? Dakiki? Mugu ko?”

Umar cikin kumfar baki yace “Eh mugu azzalumi mara imani, har duniya ta nade wallahi bazan yafe maka ba, kuma Ibty ce ko kanaso ko bakaso sai ta dawo hanuna.”

Kai Aminu ya jinjina yace “Very good.”

Jan mota yai da karfin gask

e, hakan yasa Umar yace “Meye hakan kake?”

Aminu bai kula shi ba tuki kawai yake, nanfa ran Umar ya kara baci yace “Meye haka? Kasan Allah karka kaini bango zan iya aikata abinda baka taba tunani ba?”

Bashida alamar kulashi jan mota kawai yake, Umar ga

ni yai sun wuce mariri sun nufi hanyar Wudil.

Yanzu kam ya fara jan jinin jikinsa gashi inyai kwakwaran abu zasu iya afkawa hatsari. Bai tsaya ba sai da suka shiga Wudil, da sauri Umar ya fito daga motar ya kalleshi yace “Kai dalla mahaukacin ina ne? Bak

ada hankali ne zaka ja mota ka kawomu harnan?”

Mamaki ne ya kamashi ganin motar tana neman juyawa, cikin sauri ya rike window yace “Tsaya tsaya! Ina zaka? Ko hamsin ban fito da ita ba.”

Hannu Aminu yasa a aljihu ya dauko 500 ya sa akan hannunsa yace “Wai

da zalunci da dakikantar nake so ka tabbatar inadashi.”

Kallan dari biyar din yai yana neman yin magana kawai yaga Aminu yayi gaba. Idanu ya zaro ga kafarsa haryanzu ciwo take mai, wani irin ihu yasa tare da naushin iska yace “Sai naci********** wallahi

sai naga uban daya tsayama a duniyan nan.”

Ibty kam tunda suka tafi tanaji Iman tanata kokarin jansu da hira sai dai daga Ibty har Bilkisu dukansu abin duniya ya taru ya musu yawa, gashi sai waya takewa Aminu taki shiga, itakam ta shiga uku, in aka karya

Aminu fa? Sam tunani sun hanata ko sakewa tai, ji take dama batazo gidan nan ba daya fiye mata alkairi.

[3/1, 8:15 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta w

annan* 07065283730

26

Dukunkune dari biyar din yai cikin fishinya cillar da ita kasa, hannunsa yasa a aljihu ba komai a ciki dan ko wayarsa bai dauko ba, cikin hanzari ya sukunya yana san ya dauki kudi. Me zai gani? Yara ya gani wanda basufi shekara shid

a ba sun falfala a guje suna dariya, ya daga zai bisy da gudu yaji wani uban zugi a kafarsa, da sauri ya tsaya tare da maida numfashi yadan matsa kafar dake mai ciwo kadan, yana kiran kwalla musu kira akan su dawo da kudin amma ina? Abinka da 'yan gari da

suka shiga wani lungun nemansu yai sama da kasa ya rasa. Haka yaja kafarsa yadan jingina da wani shago a bakin titi yadan zauna akan wata kujera yana matsa kafarsa dake mai wani azaba, ga bakin cikin dake zuciyarsa, lalai Aminu ba karamin tsinane bane, wal

lahi sai ya koyawa mutumin nan hankali, tunda har kamar shi zai wulakanta, a dakeshi a hanashi kuka? An sace mai mata sannan ya kawoshi nan ya cillar? Banda tozarci da wulakanci?

Yanzu taya zai soma komawa gida? Tambayar data fara zuwa mai kenan, tagumi

ya baza tare da sauke ajiyar zuciya.

******

Aminu kam kai tsaye gun aikinshi ya koma, sai daya nutsu a office sannan ya dauko wayarsa, kiran Ibty ya gani guda goma, haka kawai ya samu kansa da yin murmushi, kamar zai kira sai kuma ya ajiye wayar yana k

allanta.

Ko minti biyar baiyi ba ta sake kira, yanzun ma yana kallan wayar harta katse, minti biyu bayan nan sak ga sako.

“Ya Aminu? Dan Allah karka bari Ya Umar ya nemi fada dakai? Wlh zuciya gareshi kuma yanada karfi sosai.”

Fuska ya daure sosai kam

ar tana gabansa yadan kifa wayar yace “wato rago kika aura kenan?”

Alamar wani sakon ne ya sake shigowa, juya wayar yai “Ya Aminu? Badai abinda ya sameka ko?”

Sake kifa wayar yai yace “Tunda rago kika aura sai ki shirya ganina da ciwo ai.”

Aikinsa ya

cigaba yanayi yana tuno kalaman Umar, ba shakka kalamansa sun kaishi bango, baisan dalilinsa najin zafin kalaman nan sosai ba. Harzai kalleshi a gabansa ya dinga zancen wai yayi sata? To ko satar matar yai ai akalla dai yanzu matarsa ce.



{Nikam nace Am

inuwa ko dai kishi ne

🤪

}

******

Ibty a gida sam ta kasa nutsuwa, Iman sai dariya take mata wai lalai san Ya Aminu ya mata yawa. Itakam Yaya Bilkisu bangarenta ta koma dan gaba daya zaman ya isheta, haka kawai ta samu zuciyarta da jin zafin Ibty, balle

dataga tanata neman Aminu sai taji zuciyarta ba dadi, ita tana nan zaman auranta yaki dadi saboda Ibth amma gashi ita Ibtyn hankalinta a kwance ita da mijinta.

Iman ta dan matso kusa da Ibty tare da sake daukan wayarta tace “Yaya dan Allah nidai ina kamu

, duk sanda zaki canza waya ki ban wannan.”

Harararta tai tace “Ni dagani na dubo su Islam, haka kawai waya tun tana sabuwa za’a fara kamun ta?”

Iman tana dariya tace “Wlh Yaya Ibty yau ke da Ya Aminu kunsa naji aure nakeso.”

Juyowa Ibty tai da sauri ta

kai mata dundu a baya, Iman tadan gantsare tarw da sosa gun tace “Me kuma nai?”

“Nawa kike? Da zaki dinga maganar aure?”

Ta kalli kanta tace “Lalai ma, to ko madai nawa nake yanzu kunsa naji aure nakeso, ni gaskiya ina gama secondary aure zanyi, nima yan

zu bansan yaro irinsu Ya Umar wanda hankalinsu baya aiki daidai nafisan matashi wanda yasan me yakeyi irinsu Ya Aminu.”

Sake kokarin kai mata dundu tai da sauri ta matsa tana dariya ta dan danna wayarta, mikewa zaune tai tace “Ibty meye hakan?”

Hartakai

kofa zata fita ta juyo tace “Ke nifa bansan rashin kunya, yanzu kuma menene?”

Iman cikin dan mamaki tace “Meye wani Ya Aminu?”

“To ba sunanshi bane?”

Iman tadan bigi goshinta tace “Gaskiya wlh anbani kunya, da na dauka zuba love kuke meye wani Ya Aminu?

Kamar wani Yayanki?”

Harara Ibty ta maka mata tace “To ba yayan nawa bane? Sannan ke har wani sanin sunan daya kamata a sawa miji kikai?”

Iman ta goge sunan tasa Bae sannan ta nuna mata tare da daga mata gira tace “Ya kikaga?”

Juyawa tai ta fita da sa

uri tana girgiza kai, lalai Iman ta rika, wato harta san wani Bae? Gunsu Islam taje tasa suka dawo ciki ta zuba musu abinci sunaci ta koma sama.

Wayarta ta fizga daga hannun Iman sannan ta sake kiran Aminu, Iman tasa dariya tace “Wai tsoron me kike? Bada

i kina tunani Ya Aminu zai zauna a dakeshi ba?”

Ibty ta zauna bakin gado tace “Kinsan Ya Umar kamar wani dan kwaya yake, shikam Ya Aminu ba ruwanshi banaso haukar wancan tasa wani abin ya sameshi.”

Baki Iman ta bude tace “Inyeee? Lalai soyayya manya……”

“Assalamu Alaikum” muryar Aminu ce ta daki dodan kunnenta dan harta dauka bazai daga ba yanzun ma.

Iman ta turo kunnenta jikin wayar tace “Ya Aminu ina ka shiga? Matarka duk ta rikice……”

Hankadata Ibty tai tare da saurin mikewa daga kan gadon tai waje.

Toilet ta shiga tasa key sannan tace “Inata kiranka.”

“Inata ganin kiranki.” Abinda yace mata kenan.

Tadan yi shiru tace “Shine baka dauka ba?”

“Jira nake naga sanda zaki gaji da kira.”

Dan baki ta turo kamar yana ganinta tace “Allah hakan ba dadi, ni

ina nan inata nemanka kai kana jiran kaga sanda zan daina nemanka?”

“Eh! Yanzun ma na daga ne dan na kula bazaki iya hakuri ba, sai kinga na daga.”

Takaici ya kamata tace “Kuma menene na fada tunda kasan hakan ne?”

“Wai gaskiyar ce ba’asan na fada ko m

e?”

Tadan shagwabe fuska batai magana ba, “kunkuni kike?”

“A’a nidai bance ba, kana ina?”

“Gadan asibiti?”

Ido ta zaro da sauri cikin tashin hankali tace “Gadan asibiti? Meya sameka?”

“Mema ya sameni?”

Kafafunta tadan bubuga cikin shagwaba tace “Yaya

dan Allah ka daina zolayata, da gaske kana gadan asibiti?”

“Badai ke a ganinki wannan yaran ya isa yamin dukan da zan kwanta a gadan asibiti ba?”

“Tadan jingina da kofar toilet din tace “Kaine fa kace haka.”

“Ke kuma uwar tsoro harkin yadda ko? Sannan

ni me kika daukeni? Dan shekara sittin ko me?”

“Allah nidai bance ba.”

Yadan ajiye takardun hannunsa yace “Gashinan kina nunawa?”

Cikin magana mai kamar rada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login