Showing 93001 words to 96000 words out of 128353 words

Chapter 32 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

19

bata iya fadan matsalarta ba, sannan yawanci iyayenm

u nada ba ruwansu da tambayar matsalarka, wannan dalili yasa a haka ta taso, har mamaki take in taga Iman ko Yaya Bilkisu na sanar da Umma abinda suke so da wanda basa so, ko dayake saboda ciwon Yaya Bilkisu ita kafin ma ta fada Umma ke tambayarta, Bilkisu

me kikeso? Me za’a miki? Akwai abinda kike so? Meya sameki? Me ya faru naga kin canza? Sau da dama in taji ana irin wannan tambayar murmushi kawai takeyi dan tasan ba mai mata irin wannan tambayar, a haka a haka abin ya zama jikinta shiyasa ko matsalar Um

ar ba wanda ya sani a gidan.

*****

Hajiya dakyar ta koma wannan dan iskan hotel din, tana shiga sukace ta kawo kudi inba yau zata tafi ba, bakin ciki ya isheta haka ta sake fitowa ta nemi atm ta ciro kudi ta basu na kwana biyu dan tabbas kwana biyu k

awai zatai ta koma gidanta.

Zama tai a dan iskan dakin ga uban yunwa ta isheta, cikin bakin ciki ta fito ta nemi gun saida abinci ta siyo waina da miya.

Ga ba waya balle ta dan yi tunanin abinyi, tana gama ci tadan kishingida dan azabar datakeji haryan

zu yaki barinta.

Cikin baccinta banda mafarke mafarke ba abinda ta dinga yi, a zabure ta farka ta sauke ajiyar zuciya ta bakin ciki sannan tai kwafa, bari dai maganinta yaci wallahi wannan karan kwatar kudi zatai sosai yanzu ina amfani ace duk shekarun n

an ko kudin gida bata tara ba?

******

Acan gidan Ibty kuwa Wajen karfe biyu na rana Ainah ta iso, nan Ibty ta saka abaya doguwa ta yane kanta da mayafi sannan suka shiga mota aka fara tafiya.

Shiru Ibty tai tare da dan sa kanta a jikin window din mot

ar, Ainah tadan jawota ta zaunar da ita daidai tace “Matarcan bata dawo bako?”

Murmushi tai tare da daga kai, “Yaya fa? Ya dawo hayyacinsa?”

Murmushin yake tai tace “Ji wani tambaya, sai kace wanda hankalinsa ya gushe?”

Ainah tadan sauke ajiyar zuciya

tace “jiya Ummy kusan kwana tai akan sallaya tana addu’a insha Allahu komai zai dawo daidai.”

Ibty hartayi shiru sai kuma ta kalli Ainah sosi tace “Ainah dan Allah tambaya, nikam ya akai Yaya ya hadu da matarshi marigayiya? Nadaiji kina labarin yanda yake

tsananin santa.”

Ainah tasa dariya tace “kishi ne?”

Dan dungure kafadarta tai tace “abinda yafi kishi.”

Ainah tadan gyara zama tana dan dariya kafin ta dan dake tace “Hmmm abinda aka kusa tafka abin kunya?”

Kallan rashin fahimta ta mata tace “Abin kun

ya?”

Ainah ta dan matso kusa da ita cikin rada tace “Baffa da yayarta zai aura yayarta wace suke uba daya, abin mamaki da al’ajabi wai kawai sai Ya Aminu yazo da labarin yanasan kanwar?”

Idanu Ibty ta zaro tace “Me?”

Ainah tadan tabe baki tace “Ai kishi

yar Ummy da yanzu yayarta ce to tunda Aminu yazo da maganar yana san Aunty Na’imah shi Baffa ya janye, gashi lokacin wace yakeso ance tana bala’in sanshi wai hardasu kwanciya a gadan asibiti.”

Gaba daya mamaki ya kama Ibty tace “Ikon Allah! To shi Yayan b

ai sani ba? Itama Na’iman bata sani ba?”

Baki Ainah tadan tabe tace “Haka dai tace amma ita Ummy ta dage akan ta sani, gani take sai dama taga Abba sannan ta nemi dansa, dan a lokacin Ya Aminu fa baifi sati biyu da dawowa daga karatu daga kasar Canada ba,

har yaushe ya ganta harya mutu akan santa? Da har a lokacin yake tunanin ba mai iya rabasu?”

Shiru Ibty tai, Ainah tadan yi murmushi tace “Saukinta daya dai ita Na’iman ba ruwanta sannan tanada kirki gasan mutane ba kamar Mahaifiyarta ba.”

Ibty bata am

sa ba sai shiru kawai datai tana sake mamakin wannan abin, har suka iso skul suka fita suka shiga cikin friends dinsu kowa na mata iskanci akan taci amanarsu bata sanar dasu auranta ba, Ainah ta shiga tana kareta wai su daina damun matar yayanta……

*****

Duk wani bincike likitan yayi amma baiga komai ba, kallan Aminu yai yace “ Babu wani matsala kawai dai ka dage da exercise dan naga cholesterol dinka yadan hau kadan.

Aminu ya kalleshi sannan ya sanar dashi abinda ke damunsa, shiru abokin nasa yai yace

“To dai gaskiya ba abinda ke damunka ka tabbatar kuma haka kawai kakejin tsanar?”

Aminu ya jinjina kai yace “Bansan meke faruwa ba kwanan nan abin nan duk ya hanani sukuni.”

Dan shiru ya sakeyi yace “To ko za’a duba islamic chemist? Ko harkar jinnu ne?”

Dariya Aminu yai yace “Kai dai daga likita kana neman komawa wani abin, karka damu zan duba meke damuna.”

Mikewa yai ya fito gaba daya yana sake mamakin wannan abin.

Yana shiga mota Baffa ya kirashi nan ya dauka yana tambayarsa jikin Ibty, cikin rashin

damuwa yace ai tana makaranta shima ya fito.

Baffa yai shiru kafin yace “Aminu kadai san amana ka dauka ko? Dan daga sanda iyayenta suka amshi sadakinta to fa sun salama maka komai, hakkinka ce ya zama dole ka kula da ita.”

Jikinsa ne yai sanyi yace “Na

sani Baffa amma nikaina bansan meke damuna ba.”

“Sakaci da addu’a shike damunka.”

Mamaki ya kama Aminu yace “Sakaci?”

Baffa cikin dabara yace “Aminu ita rayuwa da kake gani inhar ka fara karancin addu’a da karatun qur’ani sai kaga abubuwa suna neman dag

ule maka. Dolene mu dage dan kara kusanci da Allah.”

“Insha Allah! Amma yanzu Baffa haka za’a bar Hajiya? Nayita kiran wayarta a kashe…….”

Jiyai an katse wayar yabi wayar da kallo sannan ya tada motarsa.

🏌🏻

‍♀

️

[3/25, 10:39 PM] Hauwa Galadima:

👩

‍

⚕

️

*MACE KE CE LIKITAR KANKI*

👩

‍⚕

️

https://www.facebook.com/103555998971126/posts/103561482303911/?substory_index=0

*Anfanin Hulba*

_Hulba tana da matuk'ar anfani a jikinmu musamman yayin gyaran nono, idan kikayi anfani da ita wajen guara

n nono tana sa nononki ya ciko sosai, haka ma idan kikayi aiki da ita a gabanki yana cikowa yayi b'ulb'ul, sannan ga macen data haihu idan tana son duk wani jini daya taru ya fito ba tare da gargada to ana cewa ta yi anfani da hulba, kad'an daga aikinta ke

nan._

*Illar Hulba*

_Ita dai hulba tana da k'arfi sosai wanda kamar sha yanzu ne magani yanzu, hulba tana da zafi sosai wanda idan kana yawan anfani da ita a wuri to zafin na taruwa har ya kai ga zuciya, wanda hakan zai iya jawo miki babbar

illa, sannan hulba tana da d'aci shi ma yawan anfani da ita zai iya tab'a miki kayan ciki musamman hanta. Babbar illar da hulba ke yi shine tana iya zubar da ciki idan akayi aiki da ita ana d'auke da ciki, sannan wannan d'acin na ta shima ya kan kawo hana

d'aukar ciki._

_Da wannan muke shawartar yan uwa da mu dinga yin komai saisa-saisa, mu dinga kula da abinda muke aiki da shi, mu dinga sassautawa kanmu wajen ganin dole sai mun birge wajen saduwa, kamar yanda muke fad'a shine mu saka Allah a gabanmu

kawai sannan mu bauta masa shi kad'ai._

*MKLK ADMIN'S*

[3/25, 10:39 PM] Hauwa Galadima:

👩

‍⚕

️

*MACE KE CE LIKITAR KANKI*

👩

‍⚕

️

https://www.facebook.com/103555998971126/posts/103561482303911/?substory_index=0

*Lalle*

_

Lalle a jikinmu mata yana da matuk'ar tasiri, lalle wani d'ad'add'an abu ne daya samo asali tun zamanin Annabi Muhammad (S. A. W), lalle ana shafashi a jiki wajen gyaran jiki, lalle ana d'aurashi a k'afa wajen ado da kuma maganin duk wata cuta da kuma kari

ya daga wasu cututtuka da akan iya d'auka daga k'afa. Sannan lalle yana da anfani a k'asan (farji) mace, yana taimakawa sosai wajen maganin cutar sanyi, dan ana matsi da shi sannan ana had'a sabulu da shi wajen maganin cutar sanyi, bugu da k'ari lalle yana

maganin ciwuka da dama wanda muka sani da wanda bamu sani ba._

*Illar lalle*

_Yawaita anfani da shi ga mace yana jawo k'ank'ancewar azzakarin namiji, sannan yana rage kuzarin namiji wajen saduwa, kunga kenan me akayi? Kinyi dan gyara

dan a ji dad'i amma kuma kin jawowa mijinki matsala. Kamar *lemun tsami* ne, shi ma yana wanke k'arni da dattin dake gaban mace, sai dai yana k'anka'nce gaban namiji sannan ya sa namiji ya rasa kuzarinsa._

_Da wannan muke shawartarku yan uwa da mu ha

nkalta mu daina kashe kawunanmu da sunan gyara, mafi aksarin abubuwan da muke anfani da su masu mahimmanci ne, amma sun zama masu matsala a garemu ne ta hanyar da muke anfani da su, ma'ana yawan aiki da su shi ke ja suna zama mana matsala a jiki._

_Al

lah ka sa mu dace_

*MKLK ADMIN'S*

[3/26, 2:28 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*n

Ki hanzart

a ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004jiki

2083371244

Zenith Bank

39*

Har suka gama registration itadai gaba daya sai sake tunanin wannan abin, haka kawai takejin akwai wani abu

a kasa game da soyayyar nan, batasan Ya Aminu da ba amma gani take baiyi kalar mutumin dazai nuna wai akan so zai iya aiwatar da komai ba.

Suna zaune a waje suna dancin meatpie da drinks din da suka suyo saboda yunwa, wata a cikin friend dinsu tace "Ah

yanzu ai ma samu salama tunda dai wannan anacin ya daina biyoki."

Suka sa dariya, dagowar da Ainah zatai ta hango Umar daga can inda ya saba tsayuwa yana tsaye yana duba agoggon hannunsa.

A zabure ta tabo Ibty tace "Wanene wancan?"

Cikin halin ko in k

ula Ibty ta kalli gun, wa zata gani? Ai kuwa Umar din ne, shima dai dai lokacin ya dan kalli gun nan ya daga musu hannu yana murmushi.

Ido suka zaro, Ibty a tsorace tace "Shifa wancan ina ganin kwakwalwarsa tanada matsala."

Ainah ai tuni Ibty taji wayar

ta tana ringing, cikin mamaki tace "Me kikeyi?"

Kafin ta bata amsa yaji an daga, muryar Aminu taji, cikin sauri tasa hannu zata wafce wayar, Ainah ta mike da sauri tai gefe suna juyota tana cewa "Yaya wancan mahaukacin fa ya biyo maka mata har makaranta."

Aminu dake tuki ne yaja wani zazzafan burki wanda ita kanta Ainah sai data jiyo karar taya yai, cikin wata irin murya yace "What?"

Tsoro ne ya kama Ainah badai laifi tai garin rawar kanta ba?

Cikin tsawa taji yace "Ina take ita din?"

Bakin Ainah na ra

wa tace "Gatacan ta koma class dan karsu hadu."

Bata ji amsar sa ba sai karar katse waya kawai dataji anyi, Aminu kallan bayansa yai yayi sa'a ba mutane sosai sai dai duk da haka mutanen dake bayansa horn suke mai suna zagayeshi, wani har zagi ya dunkula

mai, ko bi ta kansu baiyi ba ya karkata mota ya nufi skul, lalai zaisa a kama Umar din nan in har bai shiga hankalinsa ba.

Cikin makarantar ya nufa yai parking.

Itakam Ibty tana zaune a class ta kifa kanta akan desk, Ainah na gefe tana bata hakuri dan t

a tabbatar tayi laifi, Ibty ta dago ta kalleta tace "Ainah kina gani a hakan ma lalabashi nake yanxu in ya kara birkicewa ya zanyi?"

Ainah tadan kama kunnenta kadan tace "Wallahi ni kawai gani nai Yaya ya kamata yazo ya takamai birki kar a fara lecturers

ya hanaki karatu."

"Da sai ki bari sai ya dawo daidai wannan ko ni zan fadamai, amma yanzu ni wlh kallansa nai ma shakkarsa nake gani nake kamar xaice nayi wani laifin."

Baki Ainah tadan tabe kadan tace "Ko ma dai me ke kanshi wlh Ya Aminu na sanki, dan

yanda ya xabura dayaji Umar yazo ni kaina sai dana tsorata."

Harara ta maka mata tace "Ba wani zabura, neman laifina yakeyi yanzu kin bashi hanya shikenan yanzu zai kara tsanata."

Shiru sukai suna neman mafita, Ainah tai saurin cewa "Ko na kira nace mai

April fool?"

Tsaki Ibty tadanyi tace "February fool ne ba April ba."

Dan gefen fuskarta ta sosa tace "Ashe fa a February muke ko?"

Kara harararta Ibty tai sannan ta maida kanta ta kwantar, kawayensu ne suka shigo suna sheka dariya, daya tace “Wai ko ku

nya mutumin nan wai mu kira masa Ibty?”

Ibty ta kallesu tace “yana nan haryanzu?”

Kai suka daga kallan Ainah tai tace “Tashi ki rakani.”

Ainah tadan ware ido tace “Me zakiyi?”

“Da aurena wani katan banza yana bibiyata sai na barshi?”

“Inyeee! Kin tabb

atar dai zaki iya magana ko? Kar muje ki gudo ki bani kunya.”

Fara tafiya tai ba tare da ta kula Ainan ba, ganin haka yasa Ainah ta mike tana dariya, nan suka fito.

Ai Umar yana hangota wani dadi ya rufeshi ya fara washe baki kai kace wanda akawa albishi

r da kujerar makka.

Fuskarta a daure tamau ta karaso, duk yanda take shakkarsa gani take yanzu batada lokacin batawa akansa, hankalinta nakan Aminu tana neman su daidaita bazata iya bari wannan mahaukacin ya kara shiga tsakanin aurenta ba.

Yana gani ta

iso ya kara matsowa yana murmushi yace “Ibtisam ni nasan zakizo.”

Ta kalleshi sosai tace “ Ya Umar nikam islamiyar da Abba ya sakaka hala baka karanci komai a cikinta ba?”

Kallan rashin fahimta ya mata yace “Bangane ba?”

Tace “Bakasan haramun bane ka di

nga bibiyar matar wani?”

Yanayin fuskarsa ne ya canza sosai ya tsuke fuska yana mata wani irin kallo na kunar rai sai dai kaunarta kullum karuwa take a ransa.

Idanunsa suka jaa yace “Ni kike fadawa matar wani?”

Cikin kunar rai tace “To matarka ce?”

Ai

nan zuciyarsa ta harzuku ya danyi wani hucin takaici yace “Ibtisam? Ni kikewa magana haka?”

Ta dan runtse ido ta bude tace “In kanasan in baka girmanka a matsayin mijin yayata to ka rike girmanka, inba haka ba………….”

Hannu ya daga a fusace cikin fishi ya

na neman kai mata mari, jiyai an rike hannunsa ta baya, sam basu san Aminu ya karaso ba, Ainah ce kadai ta ganshi dan dama daga dan baya ta tsaya tana tsaye yana text akan a ina suke ta sanar dashi.

Gaban Ibty ne ya fadi ganin Aminu a baya, shikam Umar j

in an murde mai hannu ta baya yasa ya dan runtse ido da karfi saboda azabar dayaji, juyowa yai sukai ido biyu da Aminu.

Kallan Ibty yai yace “Wuce keda Ainah ku shiga mota, in kuma akwai kayanku a ciki ku dauko ku wuce.”

Jiki na rawa suka juya ya mikawa

Ainah key din motarsa tarr da fada mata inda yai parking.

Kallan Ibty yai ta baya sam bayasan ganin fuskarta, ganin ta tafi ne yasa hankalinsa ya dawo ya kalli Umar wanda yake ta kokarin kwace hannunsa cikin kunar rai.

Yarfar da hannunsa yai da karfi y

ace “Kaje Abba na jiranka a kasuwa.”

Idanunsa ne suka canza yace “Me?”

Dan kafada kadan Aminu ya daga yace “Ka gode Allah ba gun ‘yan sanda nakai kararka ba, ahhhh sannan bansan ya zaka kare kai da Abban ba, gashi ya baka gida ya baka aiki ya baka mata a

mma duk baka gani ba, da alama kauye ce zatai kira.”

Ai nan Umar ya hasalo ya zaburo kamar zai kaiwa Aminu duka, dan yatsansa Aminu yadan girgiza alamar a’a yace “Kada ka kuskura dan ni ba mahaukaci bane irinka, in kuwa ka bari raina ya baci wallahi bansa

n halin da zaka tsinci kanka ba.”

Umar yai turus yana wani irin huci, kafadarsa Aminu yadan dafa ya dan sosa kunnensa da dayan hannun yace “Nikam meka sani bayan fishi? Kai ko kunya bakaji? Sannan wannan ne last warning dina wallahi in ka sake zuwa inda

matata take ka shirya fuskantar tashin hankali.” Ya karasa maganar tare da dan sake bugar kafadarsa kadan sannan yai gaba.

Umar baki kawai ya saki yana kallan Aminu, kafin ya naushi iska yai dan wata kara shikam ya tsani mutumin nan kamar mutuwarsa, amma

shi Ibty ta fadawa magana haka? Ba mafarki yake ba? Yanzu duk shaharariyar soyayyar da suka sha tana san cemai a wata daya wancan babban mutumin ya tureshi a ranta?

Labansa ya ciza, yanzu me zai cewa Abba?

Haka ya juya kamar wani wanda yake yake bukatar

taimako.

Aminu mota ya wuce, shiga kawai yai baiko kula daya daga cikinsu ba, nan yaja mota suka wuce, a bakin gate ya sauke Ainah ko kallan gidan baiyi ba itakam ta fito sum sum, tasan abinda ya hadasu da Ummy ne kila ya hanashi shigowa.

Gida ya wuce

kai tsaye, yana parking ya wuce ciki, a hankali Ibty ta fito ta nufi cikin itama, a falanshi ta gashi a tsaye ya juya baya, jiki a sanyaye ta shiga tana tafiyar sanda.

Waigowa yai cikin bacin rai yace “Sanar dashi kikai kinje makarantar ko?”

Kamar zatai

magana kawai ta fasa, dan ba abinda zata fada dazai gane tunda tasan tabbas bakalau yake ba.

Hannu yasa ya rikota da karfi yace “Ba tambayarki nake ba?”

Addu’a kawai take jerowa a ranta yanzun ma ta ki magana, mamaki ya kamashi yace “Ba magana wai nake

miki ba?”

Kanta na kasa tana ta addu’a itakam, yasa dayan hannu ya dago habarta da karfi yace “Dan na kwana dake sau daya shine kike tunanin kin cancanci ki rainani?”

Idanunta ne suka ciciko haryanzun taki magana, ya dan matse bakinta kadai yace “Karki

kaini bango wallahi zan turaki gidanku dan gaba daya na gaji da wannan auran da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login