Showing 72001 words to 75000 words out of 128353 words

Chapter 25 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

47

idanki kamar kinyi kuka."

"Kukan me? Kedai kin fiya sa ido, to ba kukan danai." Ibty tai maganar tana bude wardrobe dan kar Iman ta sa mata ido. Iman ta zauna ak

an gadan tadan kishingida sannan tace "Ya Ibty gadan nan in aka juyashi ya kalli nan bazaifi kyau ba?"

Ibty ta dan kalli dakin sannan tace "Haba?"

Iman ta mike ta fara nuna mata tace "In akasa daga nan dakin ma zaifi space."

"To shikenan, anjima sai k

i tayani mu gwada juyawa."

Fitowa tai daga dakin, ta tabbatar su Islam sunci abinci sannan ta nufi bangaren Aminu.

Tana shiga falansa kamshin turarensw ya tabbatar mata daya shirya, idanunta tadan lumshe kadan itakam tabbas tasan kaunar Ya Aminu ke yawo

da ita, kuma ta daura damarar kwatar mijinta. Sallama tai daga ciki ya amsa sannan ta tura kofar dakin, yana tsaye a gaban madubi yana kokarin sa agoggon hannunsa, kai tsaye ta nufi gun gani yai tana neman riko hannun dayake sa agoggon, da sauri ya daga ha

nnunsa sama yace "Me kike shirin yi?"

Tadan kalleshi kadan tace "Dama...." Sai kuma tai shiru saboda kunyar abinda zata fada dataji, itakam meyasa kunya ta mata yawa?

Aminu yadan matsa kadan yana gyara agoggonsa yace "Su Islam fa?"

"Suna tare da Iman w

ai keke zasuyi."

Bai amsa mata ba hakan yasa ta fara tunanin abinda zatace dan sudanyi magana.

"Zakizo muje tare?"

Da sauri ta dago ta kalleshi, tun dazu take tunanin ta yanda zatai taje ta duba Hajiya, sai dai bataso yai tunanin wani abin daban.

Ciki

n jin dadi tace "Eh Yaya!"

Hularsa ya dauka gani tai ya mika mata, bata amsa ba sai kallan hular datai tana tunanin karta amsa ya fada mata wata bakar maganar.

"Na dauka tunda kin damu ki samin agoggo yanzu kwatar hular zakiyi ki samin?"

Kallansa tai ta

ce "Allah ni ba kwata zanyi ba." Tai maganar cikin 'yar karamar shagwaba.

Sa hular yai yace "Ki fadawa Iman zakije ki dawo, sai ki taho mu wuce."

"Abincin ka fa?"

"Tunda kai mata zamuyi in na dawo naci."

Bai jira me zatace ba ya dau key da wayarsa ya

fita, bayanshi ta biyo itama ta nufi bangarenta, suna zaune a falo suna kallo "Iman zamu dan fita da Ya Aminu yanzu zamu dawo."

Haba Iman ta rike tace "Ah oh ni abin ba kunya? To ai da kin sani cemin kikai zaku fita da Habiby dinki. Sai infi fahimtar ki."

Pillow ta dauka tadan kwada mata tace "A gaban yara kike wannan maganar?"

Gwalo ta mata tai magana kasa kasa "in kun tafi karku dawo sai dare kuje can kusha love."

Daki ta wuce ta gyara fuskarta sosai ta daura dankwalin material din sannan ta dauko ma

yafi light purple wanda akwai kwalliyar material din dashi ta yafa, tayi kyau abinda das.

Nan ta dauko abincin a basket sannan tace “Iman in na dawo ma gyara dakin.”

Haka ta fito ta nufi mota, dan taji alamar tada motarsa dayai, a baya ta ajiye abincin

sannan ta bude ta zauna. Kallanta yai yanzu ma abinda ya saba ji ne yaji yadan tsirgamai, kansa ya dauke da sauri sannan ya maida kansa gaban mota.

*****

Hajiya kam tun fitarshi daga asibiti ta kasa kwantar da hankalinta, ya kamata tai bacci saboda ruwa

n da ake karamata amma dan bala’i da masifa har wage idanunta takeyi dan kar bacci ya dauketa. Ganin tunani ya hanata sukuni yasa ta kira saban Malaminta. Ya tabbatar mata da yana nan yana aiki dan haka itadai ta tabbatar tayi abinda yace mata.

Kwantar d

a kanta tai tana tunanin yanda zata tirsasa yarinyarnan taci magani, batada matsala daba Aminu dan ko a kunu zata iya damawa inyazo gaisheta tasashi yasha matsalarta daya wannan tsinaniyar yarinyar data fara jawo kanwarta dan suci zarafinta.

Tana kishingi

de tanata lissafi har bacci yai gaba da ita.

Kofa Aminu ya tura hannunsa dauke da basket din, shiga tai itama ganin tana bacci yasa tadan kalleshi.

Ajiye basket din yai ya kalli kujerar daki wace take kwaya daya ya mata alama da kansa akan ta xauna. Kai

ta girgiza tadan mai alama dashi ya zauna. Hannu yasa yadan rikota ta dan ja hannunta kadan tare da nunamai bakin gado, alama ya mata da in bata zauna ba zai kinkimeta ya daurata. Garin dan kokarin zama tadan taba kafafun Hajiya, wanda hakan yasa tadan bu

de ido kadan cikin mayen bacci. Me zata gani? Gani tai Aminu na murmushi yana yi ma Ibty alama in ya zauna wai karta mai complain tace ya tashi.

Kallan hannunsu tai dake rike da juna, tashin hankalin da ba’a misaltawa, wato har Aminu ya fara hada jikinsu

tare? Shikenan kila ma ya kusanceta. Itakam ta gama yawo.

Aminu ne ya zauna akan kujerar cikin maganar rada yace “Da sauki yanzu, da na dauka cewa zakiyi sai dai mu zauna a kujera daya, saboda san ki zauna kusa dani.”

Me kunnenta sukeji?

Ibty tadan

turo baki kadan tana dan magana mara sauti “Duk sanda na kamo bakin nan dake zagina a sirrance tun farkon haduwarmu sai na dinkeshi da zare da allura.” Yai maganar idanunsa nakan wayarsa daya dauko.

Dan matsawa tai kadan tace “Inka dinke min baki, dame z

aka samu damar zolayata?”

Dan gyaran murya yai yace “Yaushe na zolayeki?”

“Kullum mana, gashi nan yanzu ma kanayi.”

Dan kafada ya daga ba tare da ya kalleta ba yace “Ji duk abinda na fada I mean it, kece kawai kike daukansa a……..”

Tarin da Hajiya ta f

arane yasa yadan mike tare da dan matsowa, kafadarsu ce ta hadu shida Ibty, Hajiya kam ji take kamar ta rusa ihu.

Cikin dan kokarin mikewa tace “Amarya kece da kanki?”

Ibty ta gaisheta, Hajiya ta amsa fuska a sake. Itama fuskar Ibty a sake tace “Kiyi ha

kuri jiya wlh bansan kina waje ba.”

Kallan Aminu tai wanda takejin haushinsa ji take kamar ta zabgamai mari saboda takaicin saukowar dayai cikin sauki haka. Murmushi tai tace “Haba karki damu ai nasan da kin sani zaki fito.”

Ibty ta kalli Aminu tace “Yay

a kaji ko? Itama Hajiya tayi shaidata.”

Mamakin kalaman nan ne ya rufe Hajiya lalai yarinyarnan makira ce.

“Hajiya ga abinci nan in zubo miki?”

Ta dan girgiza kai tace “in an gama sa ruwan naci, kedai ki koma gida ki huta dan Allah.”

Ba wani ja Ibty t

a kalli Aminu tace “Yaya mu wuce?”

Aran Hajiya tace “Sai dai ya kaiki ya dawo dan in banda lafiya to fa Aminu baya barin asibiti sai dai in aikin dole ne…..”

Batagama yin tunaninta ba taji yace “Hajiya zan dawo wajen azahar ko la’asar in jikin yayi sauki

sai mu nemi sallama.”

Tsananin mamaki ya hanata amsawa sai kai kawai data daga.

Haka tana kishingide galala tagansu sun fita.

*******

Gida suka wuce, Bala na kokarin bude gate din gidan Umar dake jingine da bango ya taho, Ibty tadan runtse ido ciki

n takaici, wato bayan waccen ga wani dake neman kawo musu matsala a rayuwa, itakam mutanen nan biyu bazasu barsu suji dadi ba?

Aminu kam kallan Umar yai dake nufosu ya dan kalli Ibty, yace “Gafa dodonki.”

Tace “Ni Allah na dainajin tsoronsa.”

“Really?”

Ta daga kai, okay bari yazo muga me zakiyi.

Kanta ta kawar dan itakam ko ganinsa batasan yi ji take kamar zai cafketa.

Umar ya karaso yana dingishi, Aminu yadan karkatar dakai ya dan kalli kafarsa kadan wacce babbar ‘dan yatsan harya kumbura.

“A hak

a kake yawo?”

Umar fuskarnan tasa a murtuke yace “Dadin saurayi mai jini a jika kenan.”

Aminu yadan jinjina kai yace “Gaskiya, sai dai me ya kawo saurayi mai jini a jika inda ba’a nemansa?”

Umar ya cilo dari biyar cikin motar, sabuwa yace “Kudinka na da

wo ma dashi dan samun kwanciyar hankalina.”

Aminu ya sunkuya ya dau dari biyar din yace “Ba laifi dan dama taimako ne nayi kuma tunda kanada halin dawo dashi ai ba laifi.”

Umar ya kalli Ibty wacce ta kawar da kanta, lalai yarinyar nan wato ganinshi ne ma

batasan yi?

Ganin kallan da Umar ke mata haka kawai Aminu yasamu ransa da baci, hannu yasa yadan tabota yace “Hajiya! Bakiga yayanki bane?”

Kallan Umar tai fuska a daure tace “Ina wuni?”

Baiko amsa ba sai kallanta kawai dayake, Aminu ya kalleshi yace “

Saurayi matsa mu wuce in kuma kana bukatar wani ciwon ne to.”

Hucci Umar yai kamar bazai matsa ba sai kumabya matsa, meyasa yakejin kamar Aminu ya kara wulakantashi? Bayan har gwada acting din yanda zai wulakantashi da dari biyar din nan yai a gaban madub

i? Bakomai ai wannam masomi ne yajira haduwarsa da abokansa.

Haka yaja kafarsa yabar gun.

Aminu ana shiga ya kalleta bayan ya kashe motar yace “Jaruma na dauka zaki kori yayanki.”

Kallansa tai tadan murza ido kadan tace “Ni fa gyangyadi nai ban masan

mun iso ba.”

“Ohhhhh! Gyangyadi ko?”

“Wani sa’in in ina bacci har magana nake amma bansan me nake cewa ba.”

“Yanzu fa? Kin tashi ko a tasheki?”

Kai tadan girgiza tare da dan rufe ido, “Bacci nake haryanzu.”

“Umar meka dawo yi?”

Idanu tadan bude, Ami

nu ya girgiza kai “Ya kikai da rayuwarki na shekaru masu yawa kina tsoronshi haka?”

Tadan maida kai kasa tace “A haka na tsinci kaina bansan yaushe na fara shakkarsa ba. Amma Allah yanzu in kana kusa bana shakkarsa so……..”

Ganin yanda yake kallanta ne ya

sa tadan hada labanta biyu alamar yin shiru, “Na dauka kina ganin saurayin mai jini zai wahalar dani?”

“Nagane ba hankali ne dashi ba.”

“Hmmm….. kenan nine bakyasan a taba?”

Kunyar kalamansa ne ya kamata, tace “Tunda ka sani sai ka tambaya?”

“Zaki shig

a ciki ko fita ki shiga ne bakyaso?”

Hannu tasa ta dan bude kofa da sauri tana fita tace “Allah nima zan fara maidawa.”

“Zaki iya?”

Kallansa tai, kwarjininsa ne yasa tai saurin wucewa ciki saboda kunya, sai dai harga Allah tanasan yanda yake zolayarta i

ta a ganinta shakuwa suke sakeyi hakan.

🏌🏻

‍♀

️

[3/16, 8:55 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

K

i hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

30

Ciki ta shiga cikin jin kun

ya sai dai fuskarta dauke da murmushin farin ciki, a falo ta taraddasu suna zaune suna wasa, Iman ce shugabar tsaramusu yanda zasuyi.

Suna jin alamun bude kofarta suka nofota da gudu suka rungumeta suna mata oyoyo, cikin jin dadi itama ta rungumesu suka s

higa ciki. Kitchen ta wuce kai tsaye ta yi warming din abincin Aminu sannan ta nufi bangarensa.

Yana zaune a kujera a falo ta shigo ta wuce gun dinning ta ajiye kayan abincin, "Yaya abinci."

Kallanta yai sannan ya zare hular kansa ya wuce ya zauna, "Ke

kinci?"

Kai ta daga alama eh tace "Tun dazu."

"Su Ilham fa?"

"Naga zakaci abinci shiyasa ban fada musu ka dawo ba, inka gama zasu shigo."

Dan kallanta yai a hankali taga murmushi ya bayyana a fuskarsa, cikin sauri tace "Yaya murmushi kai?"

Fuska ya ma

ida ya daure kamar yanda take, da sauri tace "Allah yanzu nagani murmushi kai."

Zama yai akan kujera yace "Bansan murmushina zai saki farinciki haka ba."

Kai tadanyi kasa dashi tace "Zaka fara ko?"

Kafada yadan daga sannan ya fara zuba abinci, fitowa ta

i tana tafe tana wasa da yatsun hannunta, abincin rana ta daura, Iman ta shiga tana tayata, su Islam agun Dady dinsu sukaci abinci sannan ya kaisu Islamiya.

Ganin sun gama komai Ibty da Iman suka nufi dakinta dan canza gado kamar yanda suka tsara, Ibty ce

ta dan daga katifar, ita kuma Iman ta kamo gefe suka sauketa, dawowa Ibty tai ganin wani abu a bakar leda tasa hannu ta bude, tana cewa “Menene wannan?” Karasa budewa tai tana ganin layar nan taji kanta yayi wani irin sarawa. Baya tai sai ji kake tim ta f

adi a kasa, Iman ta dauka wasa takeyi tace “Wlh in ma zaki tashi ki tashi niba Ya Aminu bane balle nazo na lallabaki. In kuma shi kikeso na kira miki basai kin langwabe ba, naji motarsa da alama ya dawo daga kaisu Islam…..”

Ganin dai ba alamun magana yasa

ta nufota, kafa tasa tadan zungureta, ganin ba motsi yasa tsoro ya kamata, da sauri ta fara jijigata, ganin da gaske ta kasa mikewa yasa Iman ta fito a guje ta nufi bangaren Aminu.

Yana kokarin shiga daki ta afko bako sallama, “Ya Aminu!” Ta kwalla masa

kira duk a rikice.

Da sauri ya juyo dan yanda yaji kiran, “Ya Aminu kazo Yaya Ibty….”

Ai bai tsaya jin me zata ce ba ya taho cikin hanzarinsa, dakinta suka nufa tana kwance yanda Iman ta barta, cikin tsananin tashin hankali ya karasa ya dagota ya fara gi

rgizata, ganin bata tashi ba yasa ya dagata cak ya fito da ita daga dakin, kan kujera yasata sannan ya kalli Iman dake tsaye a rikice yace “bani ruwa.”

Nan tai kitchen ta debo ruwa a cup ta mika mai, ya yayyafa mata, a wani firgice ta mike jikinta na kark

arwa, hannunta ya kamo ya dan jijigasu kadan yace “Ibtisam!” Yauce rana ta farko daya taba kiran sunanta haka, itakam batama ji sanda ya kirata ba, haryanzu jikinta rawa yake tana fitarda wani irin numfashi, gaba daya ya rikice bai taba sanin ya damu da ya

rinyar nan ba kamar yanzu, badai mutuwa zatai ba itama? Gaba daya jiyai ya rasa abinyi, kawai yasa hannu ya rungumeta yana shafa bayanta, Iman kam daki ta koma tai tsuru tana tunanin meya faru?

A falo Aminu ya dade yana shafa bayanta yana tofa mata addu’

a kafin jikinta ya daina rawa sai dai haryanzu numfashinan tana fitar dashi cikin sauri kuma akai akai.

Ganinta a jikin Aminu yasa mamaki ya kamata, meya faru? Kanta taji yayi wani irin sarawa mai azaba, cikin dan daurewa tace “Yaya kaina!”

Dagota yai y

ace “Ciwo yake?”

Idanu ta lumshe dakyar sannan ta daga kanta, da sauri ya mike ya wuce daki ya dauko paracetamol ya dauko ruwa ya mika mata, baya iya bude idanunta sosai haka sai shi ya taimaka mata tasha.

Kwanciyarta ya gyara mata sannan ya nufi dakin.

Kallan Iman yai yace “Na bata magani tasha, amma meya sameta?”

Iman ta girgiza kai tace “wlh bansani ba Yaya kawai naji tace menene wannan? Daga nan kawai naji shiru.”

Da sauri ya nufi gun sai dai sama da kasa babu komai a gun, falo ya fito ya kalli han

nunta nan ma ba komai, to me ta gani?

Dan tabbas ya tsorata matuka, tunowa yai da mutuwar Na’imah tana numfarfashi daga nan komai ya tsaya.

Ko daya koma bangarensa kasa zama yai, sai leko wa yake yana dubata inyaga tana bacci sai ya koma.

****

Haji

ya cikin bacci taji wayarta tana kara, dakyar ta dauka saboda baccin na mata dadi, jin muryar malaminta yasa ta bude ido sosai.

“Ke wace irin mahaukaciya ce zakibar layar da na baki inda za’a gani?”

Hankali a tashe tace “Wace Laya?”

Yai tsaki yace “Laya

r dana baki wacce nace kisa a inda yarinyar nan ke kwanciya, badadan layarmu nada karfi ba wanda daga an budeta za’a nemeta a rasa da shikenan kin jawo mana jidali.”

Mikewa zaune tai cikin tashin hankali tace “wannan yarinya anyi tsinaniya, shiyasa na fad

a maka ka tura a sa mata ciwo, ko na hauka ne, ni wlh gaba daya ko wulgawarta bana sanyi.”

“Abinda bata sani ba karfin layar ko ganinta kai to fa sai aljanunmu sun hukuntaka.”

Cikin jin dadi tace “Dan Allah ku hukuntata sosai, dan wlh da alama Aminu ya f

ara san yarinyarnan.”

Tsaki ya danyi “Kinsa munyi asarar layar dan da alama bata taba kwana akai ba, bayan layar ta dawo gun mu ina dubawa naga ba’a taba kwanciya akanta ba, yanzu sai ki samu kizo a sake biyan bukata dan aljanu su samu damar yin hakuri da

abinda kikai su bamu wani abin.”

Takaici ne ya kamata, dan itakam saduwar nan ba dadi takeji ba haka nan yakeyin abinshi shi kadai ya gaji, sai dai yazatai? In har tanasan zamanta da matsayinta dolene ta kauda tsinaniyar yarinyarnan.

“Zanzo gobe yau in

a asibiti.”

Bai bata amsa ba ya kashe, kanta ta dafa itakam ta tsani yarinyarnan, ta tsaneta kamar yanda ta tsani mutuwarta.

******

Ibty bacci tai tayi kamar wacce tasha maganin bacci, shikam Aminu sam ya kasa kwantar da hankalinsa, haka ya dinga wayan

cewa sai ya shigo inyaga ba kowa ya dan tsaya yana kallanta, in kuma Iman na nan sai ya wayance yace ruwa yazo dauka bayan akwai fridge da ruwa a falansa.

Yanzun ma ya shigo dan hankalinsa yaki kwanciya, ganin Iman bata falan yasa ya karasa kusa da ita,

gani yai kamar tana dan sauke numfashi, dan sunkuyowa yai kadan yana san jin wani irin numfashi take saukewa, ya sunkuyo ta bude idanunta, zaro ido yadanyi sannan ya dan dago tare da yin gyaran murya, “lekowa nai naga ko su Islam sun dawo.”

Mikewa tai za

une tare da dan dafa kanta, baisan ya zauna kusa da ita ba yasa hannu saman goshinta, “kan ne?”

Kai tadan girgiza tana murmushi tace “Wani irin bacci nai?” Tai maganar tana kallan agoggo.

Shima agoggon ya kalla, “Yanzu ya kikeji?”

Kai tadan girgiza a h

ankali tace “Bakomai.”

Kamar zai mike sai kuma ya kalleta yace “Meya sameki?”

Tace “Abu na gani a bakar leda na dauka na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login