Showing 54001 words to 57000 words out of 128353 words
yabi bayanta
dan kallansa tai tare da sakin murmushi. Sai daya gama hadawa sannan suka zauna sukaci abinci tare, Islam sai da Aminu ya kalleta sannan ta daina zuba surutu.
Ai tana gamawa ta ja kekenta ta fito harabar gida, nan suka fara kokarin yi ita kuma tana nuna
musu yanda ake, ba abinda kake juyowa sai dariyar nishadi nasu Ilham da Islam.
Hajiya dake zaune a bangarenta tana yin farfesun kaza wanda takeso ta gama ta zubawa Ibty magani a ciki, ta kai mata da sunan maganin mata. Yanda take juyo muryar yaran ne ya
sa ta fito waje, takaicinta daya babu hanyar dazata ga abinda ake ciki, itakam wannan katangar an cuceta da akayi ta, kunne ta kasa sosai tana juyo me suke cewa. Wasa suke sosai sosai tana juyo muryar Ibtisam, kwafa tai lalai yaran nan, duk abinda ta fada
musu? Kitchen ta koma ta kafa gumbuda maganin a cikin kwanan farfesun data zuba mata, itadai tana fatan an tura mata aljanun da zasu rikitata dan tsanar yarinyar ta kara shiga ranta matuka.
*******
Bayan sallar magrib tana daki tana karatun qur’ani s
u kuma suna falo suna kallo, kwankwasa kofa taji ta mike ta fito gabanta na faduwa dan ta tabbatar Hajiya ce.
Budewa tai bakinta dauke da addu’a, Hajiya tana tsaye sanye da dogon hijab dinta, su Islam suna jin muryarta suka taho da gudu suka rungumeta. I
bty ta daure tace “Hajiya ki shigo mana.”
Kai ta girgiza tana murmushi tace “Islam ku shiga ciki zanyi magana da Aunty au da Mumynku.”
Yanayinsu ne ya canza, Ibty tai saurin cewa “Aunty.” Dariya sukai sannan suka koma ciki, kallanta Hajiya tai a ranta ta
ce “Wato ke ‘yar duniya ko?”
Sai kuma tai murmushi ta ciro dan karamin flask din dake cikin hijab dinta tace “Ina zaune nace bari dai na miki kazar amare, na tabbatar ku amaren yanzu baku damu da kanku ba, ga mijinki ba saurayi ba yana bukatar yajiki yand
a ya kamata.”
Tsananin mamakin da Ibty ta shiga ya wuce duk tunanin mai sauraro, me matarnan take cewa?
Hajiya ta dan riko hannunta ta mika mata tace “Daso samuna nane ma a gabana zaki cinye na kwashe kasusuwan na binne, a matsayin ‘yata na daukeki shi
yasa nake san na miki duk abinda uwa ya kamata tai, ko dan taimakon da Aminu yamin dole ne kuma hakkinane na kula dake. Naga haryanzu bakizo kinga inda nake ba balle na baki acan shiyasa na taso.”
Kallan flask din tai tama rasa abin cewa, Hajiya tai murm
ushi tace “Kimin alkawari zaki cinye tas.”
Ta kalli kwanan sannan ta daga kai batare da tace komai ba, Hajiya tai murmushi sannan ta koma.
Haka Ibty ta shigo da flask mamaki duk ya hanata sukuni, kitchen takai kawai ta ajiye sannan ta fito, dakinta ta
koma ta zauna fuskarta ciki da mamakin wannan al’amari.
*****
Karfe takwas su Islam sukai baccic ta gyara falonta sannan ta wanke ragowar kwanuka, bude flask din tai sannan ta rufe, ita ko da ace ma akwai abinda ya shiga tsakaninsu da Aminu ai batasha ma
ganin nan ba balle ta tabbatar Aminu babu so balle sha’awarta a tattare da shi.
Fitowa tai ta shiga wanka sannan ta saka riga da wando irin masu fadi din nan na bacci, ta zura hijab dinta sannan ta nufi bangaren Aminu, hannunta dauke da flask din ruwan t
ea da cup.
Yana daki yana waya sanda ta shiga, a hankali ta ajiye sannan ta koma kan gado inda ta kwana jiya ta dau wayarta tana daddanawa.
Bayan ya gama ya kalleta yana tunanin ta yanda zaiyi ya tambayeta, haka yasha tea yanayi yana kallanta, Ibty kam
ganin shirin yayi yawa batasan ma sanda bacci ya fara daukanta ba, wayarta na hannunta ko addu’ar bacci batai ba.
Karfe sha biyu Aminu na kokarin kwanciya yaga tana girgiza kai da karfi, da sauri ya karasa inda take yadan dagota kadan, yace “Me nene?”
Gaba daya tana abu kamar mai firgici, hankalinsa ya fara matukar tashi da sauri ya fara kwaroro addu’oi yana mata, dan abun ya bashi tsoro, ya dade yana mata addu’a kafin ta bude idanunta.
A jikinsa ta ganta a kwance ya ririketa sosai, hawaye ne suka ga
ngaro daga idanunta, idanta yayi jaa sosai tace “Ya Aminu wasu mutane ne ina gudu suna bina, bama mutane bane dan ban taba ganin irin hallitarsu ba.”
Tausayinta ne ya kamashi yace “Hala bakiyi addu’a ba kika kwanta?”
Tace “bansan bacci ya daukeni ba, i
nasan ka gama shan tea ne ko sai da safe na maka.”
Haryanzu tana kwance a jikinsa yana kallanta, can ya daure yace “Kin tabbatar ba mafarkin tsohon saurayin ki bane yake kokarin jefaki cikin wani hali?”
Shi kenan ta faru ta kare, Ya Aminu ma yasan abin
da ake ciki.
Mikar da ita zaune yai sannan yace “Meyasa zaki jefa kanki cikin wannan halin in har kinsan kina sanshi?”
Hawaye ne suka zubo saman kuncinta, bakinta na rawa tace “Gujewa masifar da zan fada nakeyi, Yaya in da akwai yanda zanyi da na yakic
i tarihin rayuwata dashi.”
Kwayar idanunta ya kalla, wanda ke zubar da kwalla, kamar zai sake magana sai yaga kamar shi bai dace ya dameta da maganar ba, da alama ita kadai tasan halin da take ciki.
Kwanciya yai tabi bayansa da kallo tana share kwallar
ta, kwanciya tai suka dan juyama junansu baya.
Kamar wanda sukai bacci, itakam addu’a kawai takeyi, sai data gama ta shafe jikinta sannan tace “Kayi hakuri Yaya na boyema abu kafin ka aureni.”
Bai juyo ba sai dai kalamanta sun bashi mamaki, ya dauka sh
ine ya kamata ya bata hakuri?
“Kayi hakuri a dalilina na ina neman hanaka kwanciyar hankali.”
Yanzu kam juyowa yai ya kalli bayanta da take kwance da alama hawaye take dan yana jin muryarta tana dan rawa.
“Kayi hakuri in har nice……..”
Hannu taji an
sa an dagota ta zauna akan gado tana kallansa, shima kallanta yake, sai dai yanzu ta tabbatar kallan tausayawa ne a idanunsa, wanda bata taba gani ba.
Ayusher
🏌🏻
♀
️
[2/19, 7:47 AM] Hauwa Galadima:
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
Ki hanzarta ki mallaki naki
🤸🏻
♀
️
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*
2083371244
Zenith Bank
Ais
ha M.Salis
+447894142004
Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
21
Kasa tai da idanunta cikin jin nauyin sa, a hankali shima ya zare hannunsa daya riketa dashi sannan yai dan gyaran murya yace “In ance miki yarinya kiji haush
i.”
Dagowa tai cikin dan bacin rai tana sanyin korafi, ganin idanunsa akanta yasa tadan kauda kai cikin kunkuni, komawa yai ya zauna yace “Inba yarinta ba, duk darajarsa a gidanku ya kaiki ne? Ko iyayenki zasu bi bayanshi ne suki bin bayanki?”
Ta sab g
askiya ya fara sai dai…. Jin kalamansa ne ya katseta “Tsoronshi kike hala?”
Ta kalleshi tare da dan shagwabe fuska tace “Allah dan bakasan halinshi bane, baiki yamin duka ba da sunan so.”
Kai Aminu ya girgiza sannan ya kwanta ya danja bargo yace “Ke ku
ma uwar tsoro ba? Gashinan kullum kikai bacci kina mafarkin yana dukanki hala?”
Bayanshi ta kalla tace “Allah dan bakasan haukar Ya Umar bane.”
Bai tanka mata ba, tace “Kuma tsoro a musulunci mafa halak ne, ina zanso a jibgeni?”
Yanzun ma bataga ya ku
lata ba haushi ya kamata ta mike ta fito daga dakin, zuwa tai takai Islam fitsari sannan ta dawo ta sake shafe jikinta da addu’oi sannan ta kwanta, aranta tana cewa sai ya dauko magana ya kuma ki karasa magana dakai.
Tana sallar asuba tai karatunta hary
a dawo daga masallaci sannan ta fito daga dakin ta nufi dakinsu Islam ta tashesu ta musu wanka sannan ta dauko musu kayan makaranta ita kuma ta wuce kitchen tana harhada breakfast.
Tanayi tana shiryasu sai data gama tsaf sannan suka nufi bangaren Aminu,
shima ya fito cikin farin yadi, ya sa hula da farin glass dinsa. Ganin su Ilham sun shirya ga abinsu a lunch box ga kuma ta gama jera abinci a dining yasa wani sanyayan murmushi ya bayyana a fuskarsa.
Zama sukai sunaci ita kuma ta wuce toilet tai wanka,
doguwr rigar atamfa ta saka bata tsaya kwalliya ba tasa turare sannan ta fito falo. Ta tarar sun gama, haka ta kwashe kwanukan takai kitchen, ta rakosu har waje hannunta rike da Islam da Ilham.
Aminu ya kalleta bayan sun isa motar sannan ya miko mata led
ar littatafanta yace “Ainah tace kuma jibi zaku fara registration ko?”
Ta daga kai sannan ta dora da “ Eh jibi ne.”
“Allah ya kaimu.”
A hankali tana murmushi tace “Ameen.”
Nan suka ja mota suka fita, da kallo ta bisu kunyar kanta ce ta kamata lalai
fa yanzu ta zama matar gida, sai take ganin abin kamar wasa.
Aminu ta glass din mota ya kalleta ba shakka tanada hankali da tunani, ya tabbatar zamansu zaiyi dadi duk da ba santa yake ba, a kalla ya kula tasan yanda ake kula da gida tana kuma da dogon tun
ani.
Ibty kam Ciki ta koma ta gyara gidan sannan ta mike akan kujera tana kallo.
****
A bangaren Hajiya kuwa jiya sam bata samu baccn kirki ba, haka kawai jikinta ya bata Ibty batasha farfesun nan ba, karin bakin cikinta kudin hannunta sun fara kasa,
gashi jiya kwata kwata Aminu bai shigo ya dubata ba, a kalla yaci ace yazo yaga ko ta warke ai.
Kwafa tai tace “Wato har karuwar nan ta fara dauke mai hankali?”
Mikewa tai bayan taji fitar mota tahau yin faten dankali da wannan ragowar maganin, tana gam
awa ta zuba a flask ta fito waje, gun mai gadi ta nufa suka gaisa ta mikamai ledar flask din tace “Gashi ka mikawa Amarya kace inji Ummy, kasan Mamman ya saba da bangarena can yakai.”
Ya amsa ba tare da wani zargi ba ya wuce ciki, ciki ya shiga ya kwankwa
sa kofar gidan.
Ibty tana kwance har bacci yadan fara daukarta taji ana kwankwasa kofa, gabanta ne ya fadi badai matarnan bace? Mekewa tai jikinta nadan rawa ta nufi kofa, a hankali tace “Wanene?”
Daga waje yace “Bala ne.”
Wata nanauyiyar ajiyar zuciya
tai sannan ta bude kofar, gaisheta yai sannan yace “Sakone Ummy ta aiko dashi da alama Mamman bangaren Hajiya yakai.”
Kallan mamaki tadan mai sannan ta amsa tai godiya, ciki ta shiga ta wuce kitchen. Budewa tai taga fatan dankali, murmushi tai sannan ta k
alli kular Hajiya ta jiya, batasan asarar abinci sai dai ko almajiri taba gani take batai imani ba, tunda har jikinta yabata akwai wani abin a ciki yanzu inta ba wani shi kuma wani abin ya sameshi fa?
Kamar zataci dankalin sai kuma ta rufe tace “Naci anj
ima yanzu bari nadanyi bacci.”
Komawa falo tai sannan ta kwanta, kankace me wani bacci yayi gaba da ita.
******
Karfe sha biyu ta tashi nan ta wuce kitchen ta fara girkin rana, karfe biyu Mamman ya dawo dasu.
Ta fito suka rungumeta cikin murna, har Mam
man zai shiga mota tace “Mamman nagode da sako.”
Kallan mamaki ya mata yace “Sakon me Hajiya?”
Tadan kalleshi tace “Sakon da Ummy ta baka ka kawo da safe.”
Kai ya girgiza da sauri yace “Ni kuwa? Ni ai banzo ba sai yanzu.”
Gabanta ne ya dan fadi, tada
n daure tace “Ayya! Kila mistake Bala yai.”
Ciki ta koma sunacin abinci tana mamakin wannan abin, batasan dogon zargi sai dai babu tantama Hajiya ce kenan ta aiko mata da abincin, wato bayan na jiya ba shine ta aiko mata?
Haka harsu Islam suka tafi maka
rantar Islamiya, hankalinta ya kasa kwanciya da wannan abin mamakin daya faru.
Hajiya kam ta rasa abinyi, gashi ta kira Malaminta ya duba yace haryanzu bataci ba.
Waya ta dauka ta kira Aminu, yana dauka kawai ta sa kuka.
Hankalinsa a tashe ya fara tam
bayarta abinda ke faruwa, kin magana tai sai kuka kawai da takeyi.
Bai tsaya wani abu ba ya nemi uzuri tare da fitowa daga gun aiki.
Kai tsaye ya shiga bangarenta hankalinsa a tashe kai kace Ummy ce ke mai kiran gaggawa.
Sallama yai daga ciki ta amsa
cikin kuka, ya shiga ciki hankalinsa a taananin tashe. A zaune ya ganta ta gama cika akwati da kaya, ga kuma wani akwatin nan tana hadawa tana hawaye.
Taahin hankaline karara ya bayyana a idansa, yace “Hajiya meke faruwa?”
Ta girgiza kai kawai tana hada
kayanta, cikin kulawa da damuwa yace “Hajiya! Wani abin akace miki?”
Kallansa tai tare da zama a bakin gadan tana share kwalla tace “Aminu wannan abin nake gudu tunda kai aure shiyasa na nemi barin gidan nan, yanzu kam dan Allah ka barni ko banda inda zan
je zan fita daga nan gidan, Na’imah ta tafi ta barni banda kowa a duniya, yanda ta tafi nima fatana Allah ya dau raina.”
Tsananin tashin hankali ne ya bayyana a idansa, tuno sanda Na’imah zata rasu yai kalma daya take roko daga gareshi akan ya kula da ma
haifiyarta.
“Meya faru?” Yai tambayar cikin kakkausar murya.
Ta girgiza kai cikin damuwa tace “Aminu tunda kai aure matarka ta kwashe su Islam, na fahimci wannan dole ne inhar muna bukatar ta shaku dasu, banyi magana ba. Na kai muku abinci ta dawo dani
tace bataso na dinga shiga abinda bai shafeni ba, girki da kula daku aikinta ne, nan ma ta dawo dani dauke da tulin abinci haka na dawo na sa abinci a gaba wanda rashin jin dadin yanda ta zubamin munanen kalamai ya sa ciwo na ya tashi, shima ban sanar dak
ai ba saboda banaso ku samu matsala, da daddare nai farfesu naga abin kwalama ne bansan na cinye ni kadai nakai muku shima ina kallo ta shiga dashi kitchen babu alamar taba su Islam, yanzu nayi faten dankali ganin su Islam naso na zuba musu a flask nan ma
ta hanasu akan bata yarda da abinci na ba. Su Islam zasu Islamiya sun biyo na tambayesu sukace bata basu ba.”
Kuka tasa sosai, tace “Zan yarda na shanye komai amma banda kokarin rabani da jikokin da su kadai suka ragemin a duniya, Aminu kafin zaman nan y
a koma na rashin dadi ka………”
Yanda ya mike a fusace ne yasa ta fito itama tare da kallan turaren wutan data hada domin shi wanda yasha magani, tana kallo ya fita.
Kwafa tai tace “Kedin banza ke din wofi? Ni da kika gani bala’in dana shiga da yasa yanzu b
ana shakkar ko wani tsinane, ke din banza?”
*******
Tana sallar la’asar taji alamun mutum a cikin dakinta, addu’arta ta shafa sannan ta juyo, cikin mamaki ta kalli Aminu dan bataji alamun dawowarsa ba.
Mikewa tai fuskarta a sake tace “Yaya Sannu da da
wowa.”
Yanayin fuskarsa kadai zaka kalla kasan yana cikin bacin rai.
Sallaya ta ninke fuskarta dauke da damuwa tace “Yaya?”
Fitowa yai daga dakin ba tare dayace mata komai ba, kitchen ya nufa kai tsaye ya fara bubude flask, can gefe ya hango flask din
Hajiya, nan ya nufi gun ya bude, daya farfesu ne daya fatan dankali, babu alamar an taba dan farfesun ma harya fara tsami.
Ibty kam kallansa take dan bata fahimci me yakeyi ba. Waigowa yai yace “Me yasa ba’aci wannan abincin ba har daya ya fara tsami?”
Ta rasa mema zatace, cikin dauriya da dan tsoron abinda zai je ya dawo tace “Yaya jiya da daddare aka kawoshi lokacin su Islam sunyi bacci ni kuma na koshi.”
“Shine ba’asashi a fridge ba aka barshi a waje?”
Shiru tai tana tunanin abinda zatace, itakam t
a inda ake cutarta kenan, in rai mutum ya baci bata iya yin bayani ba, sai taji duk ta rikici.
Takowa yai yazo inda take daf har tana iya juyo numfashinsa, wani irin faduwar gaba ya sameta akai akai.
“Na dauka na sanar dake matsayin Hajiya a gareni ko?
Ko kina tunanin harkin kai matsayin da zaki shiga rayuwar gidana? Kina abu a hankali ina tunanin eh a kalla ko banasanki, zan iya zaman aure dake saboda bayan yarintarki kina da hankali da sanin abinda ya kamata.”
Ya mata wani kallo yace “Sai dai me? Ashe
kema daya kike da munafukan mata wadanda ke nuna Allah a waje shaidan a zuci, ke bakya ko tausayin baiwar Allar nan? In kin rabata da jikokinta me kika mora? Wannan wani irin bakin hali ne? Ko sati bakiyi a gida ba kina neman hanata ganin jikokinta?”
Dagowa tai cikin matukar mamaki da jin zafin kalamansa, a hankali wasu zafafan hawaye suka zubo idanunta, ta kasa ko magana sai hawaye kawai da takeyi.
“Ki tsaya a matsayinki inhar kinasan zama a gidan nan, sai yanzu na fara fahimtar dalilin dayasa sauray
in can ya takura miki da alama yasan wasu daga cikin halayenki ne yake tsoro.”
Juyawa yai cikin matukar bacin rai, Ibty kam zubewa tai a kasa kawai tasa kuka.
Haryakai karshen falan ya juyo ya kalleta, yanda take kuka yasa kasan ransa ya soso, meya sam
eshi? Duk da tayi laifi ya kamata ya zaunar da ita ya mata fada cikin sanyi, meyasa ya rufeta da fada haka?
Yafi minti uku yana kallanta sannan ya wuce daki, kansa yadan dafa dake ciwo sannan ya wuce toilet ya shiga wanka. A wanka kam ruwa yai ta zubawa