Showing 33001 words to 36000 words out of 128353 words

Chapter 12 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

34

/>
Ido suka zaro suka ajiye cokalin da suke cin abinci suka rarafo inda take, cikin matukar tsoro Ilham tace “Kenan muma haka za’a maidamu?”

Ta daga kai sannan ta shafi kansu tace “Sai dai inhar ina raye bazan bari a cuce

ku ba, shiyasa nake zaune anan duk wulakancin da za’amin saboda ku bazan yi fishi ba.”

Ai kamar ta tabosu nan suka sa kuka suka rungumeta, ta shafi kansu tace “Abu daya zaku taimaka dashi ku kwaci kanku, kunga dai yanzu dole zaku koma gun matar Dadynku sa

i dai kada ku yarda ta cuceku ta dinga muku wasa da dariya ko tana muku wasa kuna biye mata, tana ganin kun yarda da ita zata fara cutar daku.”

Ai da sauri suka girgiza kai sukace bazamuyi ba Hajiya.

Dadi ne yadan shigeta dole fa ta shirya kwatan kanta

, bayan magani sai ta hada da amfani da jikokinta.

{Nace andaiji asara wallahi an kuma fado ba nauyi

🤔

}

*******

Yanda yaketa zagaye a layin ne yasa wani mai gadi dake kusa da gidan Aminu ya fara tsarguwa dashi, gidan Aminu yazo ya kwankwasa kofa nan

mai gadinshi ya fito.

Kallansa yai sannan ya nuna masa Umar yace “Mutumin can tun yama yake safa da marwa anan layin, bansan meyasa ba hankalina yaki kwanciya.”

Kallansa yai sannan yace “Muje muji me yake anan in bashi da huja mu rikeshi mu kira ‘yan

sanda, kasarmu yanzu ta zama abinda ta zama, yanzu sam ba yadda

a kasar mu, kana dai ji tsabar san zuciya abinda malamin makaranta guda ya aikata.”

Kai tsaye suka nufi inda Umar yake, lokacin yana duba agogo yana jiran abokansa da sukai zasu zo dan tayas

hi sace Ibty.

Jiyai an tabashi ta baya, ya juyo cikin fada yaga mutane guda biyu, kallansa sukai daya yace “Malam me kake anan layin tun yamma? Gashi har isha’i ta gabato?”

Umar ya hararesu yace “Kan hanya nake fa ba gidan wani ba.”

“Bari mu kira ‘ya

n sanda sai ka musu bayani.”

Ganin suna neman ja mai masifa yasa yai saurin cewa “Ni yayan Ibtisam ne, matar da Aminu ya aura, ga gidan can.”

Kallansa sukai, ganin basu yadda dashi ba yasa yace “ Munzo jere dazu to sun manta ba’a kawo wani abinda za’a

daure kasan gado ba shine nake jira, yanzun dakukaga ina duba agoggo ganin dare yayi ne nakesan wucewa gida.”

Kallanshi sosai mai gadin Aminu yai yace “Amma banganka ba sanda suka shigo jere.”

Yace “ Tare mukazo baka kula bane, mata su hudu ne mu kuma m

aza biyu.”

Ganin da gaske yaga mata hudu sannan yaga namiji daya yasa yace “To yanzu ka wuce daga nan, koma menene kwayi da safe. Tunda Amarya bata tare ba ai akwai lokaci.”

Umar cikin damuwa ya kalleshi a ransa yace “Bata tare ba?”

Ganin karsu gane y

asa ya juya ransa duk a bace, iska ya nausa yana huci shikenan mai afkuwa ta afku wani katan banza ya kwacemai budurcin da yake tattali shekara da shekaru……

{

🤭

Ansha tattali}

******

Sai datai magrib sannan ta fito ta dan tattare kwanukan, kallansh

i tai duk da batasan mai magana amma ya zatai?

Ta daure tace “Ya Aminu wannan kafin ya lalace ko zakaba masu aikin hotel din?”

Kallan abincin yai yace “Na safen ne baki cinye ba?”

Ta daga kai tace “Dana gani dayawa na dauka dama hardakai.”

Ya mike

ya zo inda take, hannu yasa ya na kokarin amsar tiren, hannunsu ne suka hadu da juna, a hankali ya zare hannunsa ya amshi tiren, tadan daure tace “Nagode sosai da waya. Allah yabkara budi.”

Kai kawai ya daga mata ya fita, kalan hanyar dayabi tai tace “Ik

on Allah sai kallo, labarin da Ainah take bata akanshi ashe itace zatai rayuwa dashi, dan dama Ainah tace tun bayan rasuwar matarsa ko hira bayayi, Ummy ma intana hira yana gun sai dai yace to ko kuma amsar yar kadan.”

Ajiyar zuciya tai tace “In na koma

makaranta ai shikenan, a kala ina hidimar karatu na rashin kulani da zaiyi bazai damen ba, sannan gasu Islam sa debemin kewa.

🏌🏻

‍♀

️

💫

IBTISAM......

💫

(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą A

̤̈

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA* *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar

biya ta wannan* 07065283730

14

🤸🏻

‍♀

️

Haka ya dawo ya zauna yana tunanin wai haka zai ta zama a falo ba abinyi? Sannan jiya bacci sam baimai dadi ba dan bai saba kwanan falo ba, an hanashi zuwa aiki sannan gadan ma an hanashi kwana? Shi raini ne bayas

o amma da tsaf zai wuce ya kwanta akan gadan inyaso ita ta kwanta a falo tunda dai ita yarinyace basu da matsala da inda zasu kwana.

Haka yai ta zaune, ya kishingida ya mike duk dai takaici ya isheshi, ganin magrib tayi yasa ya nufi daki dan yin alwala,

Ibty kam tana mimike akan gado tanata latse laten waya, inama zataga Iman ta nuna mata wayarta? Itama ganin magrib tayi yasa ta mike tana dan danna wayarta tana nufar hanyar toilet.

Yatsa taji a goshinta, an dan turata baya kadan, da sauri ta dago ta kal

leshi, yatsarsa na saman goshinta yace “Babbar mace me kikeyi hakan?”

Kallan kanta tai da alama bigeshi ta kusa yi bata kula ba, itakam meke damunta dan Allah? Ji take kamar ta saki ihu saboda kunya da haushin kanta, daurewa tai saboda tasan daga ta nuna

zai sake ce mata yarinya tace “Ya Aminu nice fa a dakin kaga kaine baka kula ba ka kusa bigeni.”

Haryanzu yatsarsa na goshin ya kalli yatsar sannan ya kalleta yace “Then me hannuna yake anan?”

Tadan daga ido sama ta kalli yatsarsa, idanu tadan rufe sa

nnan ta bude guda daya tana kallansa.

Yace “Ehen?”

Murmushi tai tasa hannu tadan sauke hannunsa daga saman goshinta tace “Yanzu dai Ya Aminu na bar ma ka farayin alwalar.” Ta fada tana komawa kan gado.

Kallanta ya kuma yi ta zauna ta ajiye wayar tana

murmushin da kana gani kasan na ya ke ne, kai ya girgiza sannan ya wuce toilet, shidai kam zaman nan ya isheshi, bari ai gobe tai ya kira Ummy gaskiya gobe yakesan komawa gidansa.

Harya fito tana nan zaune inda ya barta ta wani kame kamar gaske, shi abin

ma so yai ya bashi dariya yanda taci serious haryanzu wayarta tana gefe bata dauka ba.

Kai ya kauda sannan ya bude jakarsa dake dakin da alama abu yake san dauka.

Ibty ta daure ta mike tare da daidaita tafiyarta cikin nutsuwa tanayi fuskarta haryanzu a

hade, toilet ta shiga sannan ta rufo kofa.

Da kallo yabi kofar toilet din lalai yarinyarnan, zai gani in zata iya canzawar, ai dai yarintar a jikinta take.

Ibty kam tana shiga toilet tadan danne bakinta tana dariya, ta kalli kanta a madubi tace “Kai d

a kanka zakacemin babba, dan daga yanzu na bar yin shirme a gabanka.”

{Nace ni ai ‘yar kallo ce

😂

}

********

Da safe Aminu yana cikin bacci akan kujera wayar Ummy ta shigo, mikewa yai sannan yai gyaran murya yana kallan agoggo, lalai rashin abinyi

ya kamashi, bayan yayi asuba yau shine da komawa bacci? Sannan gashi bai tashi ba wai har tara da rabi na safe?

Daga wayar yai suka gaisa da Ummy, daga can tace “Aminu Allah yasa ba ni na tasheku ba.”

Yadan yi gyaran murya kadan yace “Ummy dan Allah s

o nake yau ko zuwa yamma na koma gida, zaman kurkukun nan ya isheni.”

Tadanji ba dadin kalamansa sai dai ta fahimci dama dole fa sai anyi hakuri, tace “Ba wani abin dan dama yau sukace zasuyi jeren kujerun da kayan kitchen, labulaye ne dai sai a hankali

dan san an dinka sannan za’a kawo.”

Kai ya jinjina yace “Yau din da yamma in dauketa mu wuce kenan?”

Tace “Eh itama ya kamata ta samu tagama gane gidanta kafin ta koma makaranta”

Bai tanka ba dan a ganinshi wannan abinda ya shafeta ne bashi ba, Ummy

ce ta katseshi “Me kukeso a abin kari? Kai dai na sa an soyama doya da farfesun kayan ciki, ko zaka tambayi Ibtisam me take so?”

Mamaki ne ya kamashi yace “Ummy ni zan tambayeta me takeso?”

“To ni da nake nan ko ni zan taso nazo?”

“Ummy ba kinada numb

erta ba? Ki kirata kiji mana.”

Tadan yi shiru kadan kafin tace “Yanzu dan neman magana kuna guri daya sai na kiraka na kashe sannan itama na kirata? Ni tambayomin ita dan Allah.”

Mikewa yai ransa duk a bace yace “Ummy Allah da saninki kike wannan abubu

wan ga kawarta nan a gida ai na tabbatar tasan me take so.”

“Kawarka takai mijinta ne? A kalla dai kai kuna tare itafa?”

Dan kai ya kauda a ransa yace “Duk wani salan a rainashi Ummy ta sani, yanzu kawai sai ta sashi yaje yana cewa Ibtisam me zakici da

safe?”

Yana wannan tunani ya isa kofar dakin, daga waje yai dan knocking.

Ibtisam ta fito daga wanka kenan sanye da towel tana duba kayan da zata sa a jakarta, kallan kofar tai da sauri, sannan ta kalli kanta, gashi towel din hotel din ba babba bane da

n ko gwiwarta bai sauko ba, jin an sake kwankwasawa yasa ta shiga dibi dibi, me zatai? Ganin mayafin data cire na jiya tai a kan hado da sauri ta nufi gadan daidai nan shikuma ya turo kofar dan yayi zatan ko tana bacci ko kuma tana toilet.

Taje daf da ga

do shi kuma ya bude kofar, kallansa tai da sauri duk ta rasa ma me ya kamata tai, mamaki ne ya rufeta ganin ko a jikinsa, kallanta yai yace “Ummy ke tambayar me kikesan ci da safe?”

Kamar wacce aka kamar da ita haka ta tsaya, hannu tasa a saman kirjinta,

dakyar tace “Koma menene zanci.”

Bai jira wani abu ba ya juya yabar dakin, ya maidawa Ummy abinda tace sannan ya kashe wayar.

Zama yai a falo yana tuno abinda ya faru yanzun nan a daki, meyasa ta rufe kirjinta? Badai ta dauka kallan jikinta yake ba? K

ai ya girgiza yace “Lalai yarinta da ciwo.”

Ibty kam kaya ta saka tana sawa tana mamakin yanda ya nuna ko a jikinshi daya ganta a haka, a kalla ta dauka zai koma ya barta ta shirya, to ko dan yana waya da Ummy ne? A ranta tace haka ne ma.



******

W

ajen karfe sha daya aka kawo musu abinci, yanzu kam batai gigin cewa zasuci tare ba, ta hada kwanukan jiya Mamman ya koma dasu, kasancewar Aminu na wanka yasa ta zauna a falo ta zuba doya da farfesun kayan cikin, sannan ta hada tea, ta kuna tv ta zauna tan

a ci tana kallo.

Ko bayan ya fito daga wanka kin zuba abincin yai, mamaki ya kamata ta daure tace “Ya Aminu ko na zuba maka?”

Kai ya daga mata alamar eh yana duba abu a laptop dinsa, a ranta tace “Maza sai a barsh da tsinanen san girma abinci a gabansu

amma sainsu baje suna jiran a zuba musu.” Samai tai sannan ta ajiye kan centre table din, ta kalleshi tace “In hado ma tea?”

Yanzun ma bai kalleta ba sai kai kawai daya daga mata alamar eh, tana kokarin mikewa yace “Karkisa sugar.”

To kawai tace sannan

ta wuce gun fridge ta kuna kettle, tana yi tana kallansa, haryanzu bai dauki abincin ya fara ci ba, so yake sai ya huce ko me? Can tace Hmm ko meya dameni oho? Mutum da cikinsa?

Kawomai tea din tai ta ajiye a kusa da abincin, kallanta yai sannan ya ajiy

e laptop din a gefe itama kallanshi tai ganin sun hada ido yasa ta sauke nata idon kasa, dagowa tai tana neman juyawa. “Thanks.” Abinda yace kenan, juyowa tai suka sake hada ido m, samun kanta tai da mai murmushi mai sanyi, dan harga Allah taji dadi daya g

ode mata.

Kansa ya dauke ya dau abincin ya faraci, ita kuma ta wuce daki tana ganin bai kamata ta zauna ba yana cin abinci.

********

Su Kawu sun shirya tsaf bayan la’asar zasu koma kauyensu, duk da komai ya lafa haryanzu Kawu bai saki jiki da abinda

Umar yai ba, daren jiya suka kai Bilkisu bangarenta ganin Umar ya sauko, sai dai abinda basu sani ba yanda suka kaita haka ta kwana ita kadai, dan Umar baima shigo gidan ba sai da akai sallar asuba, yana can yana lissafin abubuwan da ya kamaceshi.

Balle

dayaga wayar Naziru yana sanar dashi ankai Bilkisu bangarenta ransa ya sake mugun baci, haka yai zamansa a masallaci sai bayan asuba ya shiga cikin ‘yan gida suka koma.

Abba kam duk sun dauka a bangarensa ya kwana dan sun ji alamun shigowarshi da suka l

eka sukaga yayi bangaren da aka kai Bilkisu, sai dai abinda basu sani ba yana shiga ya fita ta kofar gidan, haka Bilkisu ta kwana, taci kukanta har ta gaji, da asuba kawai taji sallamarsa.

Dadi ne ya kamata ta kalleshi tana zubar da kwalla, da yake an ju

na musu solar a gidan hakan yasa gidan yake da wuta kamar ta nepa.

Dauke kai yai daga kallanta ya fara kallan gidan yana daddaga pillow din da akai jere dasu akan kujera. Kai ya jinjina yace “Ba laifi kujerun suna da kyau, kuma giredi ne amma menene amfa

ninsu bayan wacce aka siya dominsu bazata iya morarsu ba? Dan soyayyarnan aja mace in tana tsaye su fada kan kujera baza’a iya yi da ita ba?”

Wasu zafaffan hawaye ne suka zubo mata tasa hannu ta share, labulayen dakin ya daga yadan tabe baki yace “Nan ir

in soyayyar nan da ake na mace ta boyewa miji zaki iya?”

Kasa tai dakai hawaye suna gudu akan fuskarta, ya zauna akan kujera ya daura kafa daya kan daya yana dan girgizawa yace “Da alama jikina ya bani kece silar rugujewar farincikin rayuwata kila shi ya

sa ko sau daya ban taba tsausayin ibtila’in da Allah ya dora miki ba dan ni Ibty nake so tunda ita lafiyarta kalau hankalina bai taba karkata akan wahalar da kikesha ba, ashe ashe kece bala’i da masifar rayuwata, wacce zata rabani da masoyiyar da duk duniy

a ba wacce nakeso sama da ita.”

Umar ya buga mata wani kallan tsana da kiyayga yace “Bandamu da auren da aka mata ba dan wlh ba wanda ya isa rabani da ita, matatace ni kadai shi kanshi wanda yai gigin auran nata tausayinsa nake dan ina tausayawa halin da

zan jefashi.”

Ya zo kusa da ita yadan buge keken da take kai sannan ya wuce daki yana wani kallo yana tabe baki, kwanciya yai akan gadon ya mike kafa yana girgizasu, inhar wannan tsinanen mutumin ya kuskura ya kusanci Ibty to lalai ko sun bar Kano sai y

a sa an mai tsinanen dukan da bazai sake kusantar wata mace ba a duniya.

Haka su Kawu bayan la’asar lokacin su Goggo sun dawo daga jere suka dau hanyar garinsu, bayan Kawu yayi tayiwa Umar fada wanda a zahiri fadan ko a kwalar rigarsa bai dauka ba. Amma

a fili ya dinga daga kai yana cewa “Insha Allah.”

*******

Da yamma yana sallar la’asar ya kwankwasa mata kofa, tana zaune akan sallaya bayan tayi sallah tanata lazimi, mikewa tai ta bude ta kalleshi.

Kallanta yai sannan yace “Ki hada kaya zanje na

i check out sai mu wuce.”

Bata san sanda tace “Ina?”

Dan sam ta sha’afa wani gidan za’ankaita ta dauka gidansu za’a maidata dan har gabanta ya fadi tana tunanin karfa in Umar ya ganta komai ya dawo sabo.

Jitai yace “Gida mana, ko ke zaman nan din dad

i yake miki?”

Sai a lokacin ta tuna ashe fa tayi aure yanzu gidanta daban, kasa tai dakai tace “Bari na hada kayan.”

Juyawa yai ya fita ita kuma ta fara tattare musu kaya, tanayi tana tunanin ko ya su Islam zasuji in suka ganta? Murmushi tai dan tanasan

kyawawan yaran nan.

Aminu bai dade ba ya dawo, hannu yasa ya amshi jakukunan datake kokarin fitowa dasu falo daga daki, kallansa tai bayan ta sakar mai tace “Nagode.”

“Ki dauko basket din da aka kawo abincin, sannan ki sake dubawa in akwai abinda kika

manta, banasan sai munyi nisa kice kin bar wani abin anan”

Aranta tace “Magana ce dai baza’amin cikin dadin rai ba.”

Kamar yasan me take cewa sai jitai yace “Tuna miki dai nake.” Ya wuce hannunsa dauke da jakukunan, dan baki ta turo tace “Kowa ma ai y

ana mantuwa, kaima kila ka manta da wani abin.”

Mamaki ne ya kamata ganin duk abinda aka manta nata ne babu abinshi ko daya.

Haka ta fito ta shiga mota……

******

Hajiya sai zagaye takeyi tana leken katanga sam bata damu da masu aikin ginin ba har mas

u jere suka fita sannan tai wuf ta shiga bangaren, mamaki ne ya kamata ganin gidan a garkame, ta gwada key dinta na gidan yaki shiga, kallan gun sa key din tai wato canjashi ma akai? Lalai Ummy wato ita take nema taciwa zarafi?

Haka ta dawo bangarenta zu

ciyarta duk a dagule,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login