Showing 123001 words to 126000 words out of 128353 words

Chapter 42 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

51

fada gabaki dayansu.

"Mumh unguwa kuka

je ko kuma fita zamuyi?" Ilham ta tambaya tana kallan Ibtisam.

"Dawowa mukayi, maza muje ciki kuyi wanka."

Bata kulashi ba tabi bayansu suka shiga, da kanta tai musu wanka ta shirya su sannan ta zuba musu abinci tace su zauna suci. Ita sam ji tai bata sa

n zuwa wajan zuciyar ta bata so ko abincin ta tuna sai taji kamar tai amai.

********

Bayan kwana biyu….

Zaune yake a falo yana ta faman cin gawasa yaci takai kwallo shida, yana rike da remote idanunsa na kan tv yana kallan film din subulli da subu

lluwa na dan auta da Jamila nagudu. Banda babbaka dariya babu abinda yake yi, yayin da Bilkisu kican cikin daki tana fama da ciwon ciki kamar zata mutu. Ta kirashi yafi a kirga yana can yana kallo, ganin zata mutu yasa ta kira lambar Umma tace suzo su taim

aka mata.

Cikin azama Umma ta fito ta isa sashen tana zuwa ta tarar da Umar yana ta dariya yasa tv a gaba. Mamaki ya kamata tayi zatan babu kowa ne sai Bilkisu ita kadai ashe mijin nata yana nan. Ta karasa ciki yana ganinta ya tashi zaune tace.

"Ina Bil

kisu?"

"Tana daki Umma lafiya?" Mamaki ya kara kamata tace.

"Yaushe rabanka da ita?"

"Tunda aka kawo nepa ina nan ita kuma bata fito ba kila bacci takeyi, kinsan Amare sai da bacci.”

Umma wani abu ya tokareta taji kamar ta zabgamai mari, taja dan karam

in tsaki tace

"Tashi ka rakani wajanta." Sai da yasa pause a tv din sannan yai gaba tabi bayansa.

Suna zuwa suka tarar jini yana bullowa daga kasan zanin jikinta, Umma tai kanta tana salati tana kiran sunanta. Umar kuwa zaro ido yai hankali a mugun tash

e yama kasa yin komai saboda tsoro jikinsa har rawa yakeyi.

"Meyake faruwa dake haka Bilkisu? Yazaki shiru kina cikin ciwo baki kira mijinki ba bayan yana gidan?" Cikin tsananin ciwo Bilkisu tace.

"Umma na kirashi na kuma buga masa waya duka, ganin ban g

anshi ba yasa na kiraki." Umma ta kalli Umar cikin bacin rai wanda be taba gani ba tace masa.

"Umar ka gama zama da ‘yata koda kuwa kai kadai ne namiji a duniya, ko ka saki Bilkisu ko karka saketa sai kabar gidan nan dan banga uban da zaka zauna yi mana b

a. Wato tana nan zata mutu kana can kana kallan su Jamila nagudu ko? Ka tattara duk abinda kasan nakane a cikin gidan nan ka koma inda kafi wayau."

Ta dakkota suka fito zuwa mota gaba daya ta rikice, Iman ce ta fito jin kiran da Umma ke mata, cikin hanzar

i ta taimakawa Umma suka kai Bilkisu asibiti, suna zuwa aka kaita emergency inda suka gano karamin ciki ne da ita amma kuma ya zube. Bakin ciki kamar Umma tayi kuka sai dai babu yada zatayi aikin gama ya riga ya gama, wannan d’a ya cucesu.

Haka aka sa mat

a drip saboda rashin karfi, Umma tana zaune sai sakawa da warwarewa take.

Bayan ta farka ta kalleta rai a bace tace “Kinga Bilkisu idan har baki tashi kin karbi ‘yanci ki ba Umar ne zai yi sanadin rayuwarki. Ki mutu a banza ya auro wata. Dan haka ina san

ki nuna masa kema macece kamar Ibtisam, wannan abin da kike shi yasa bai darajaki ba wannan mutumin wallahi Idan bakiyi wasa ba haka zai sake nakasaki a banza a wofi. A da na amince dashi saboda farincikinki sai dai yanzu bazan iya bari zamanki dashi ya ha

lakamin ke ba.”

Hawaye take sosai ita kanta yanzu ta tabbatar Umar baya kaunarta yanda take kuka tana kiranshi, har amsawa yayi da farko yace “Menene?”

Datace yazo sai yai kamar bai jita ba.

Cikin hawaye tace “Umma ya zanyi? Na rasa yadda zanyi masa wal

lahi."

"Duk abinda nace miki kiyi zakiyi?" Bilkisu ta jinjina kai………

Suna fita shi kuma Umar ya fara zage-zage yana cewa bega uban da ya isa ya rabashi da matarsa ba, kuma babu inda zashi dan bashi da wajan zuwa, kauye ne kuma ba zai koma ba sai in ziy

ara zashi. Jini kila ma al’ada ce ta kufce mata dan kazanta batasan ta kula da kanta ba.

Yaja tsaki yace “Dadinta da ilimi na bawai jahili suka ajiye ba.”

Yai kwanciyarsa yaci gaba da kallo dan ko kudin hawa mashin bashi dashi bare yace zai bi bayan su.

Koda suka dawo Umma wucewa tayi da Bilkisu sashen su saboda an bata bed rest na tsawon sati biyu, idan ta koma bangaren ta Umar ba saurara mata zai yi ba. Har dare babu Umar ba labarinsa, tun Umma tana aunawa harta cire rai ita kanta Bilkisu abin ya bata

haushi fiye da yadda Umma taji, sai wajan tara ya shiga yana muzurai ya tarar da Iman tana cin abinci.

Ya zauna akan kujera yana kallan falan yace “Dan zubo min naci nima wlh yunwa nakeji." Iman tai masa banza saboda duk haushinsa sukeji.

"Bakiji ba?" Ta

kalleshi.

"Babu ya kare."

"Abincin ne ya kare ko kuma me?"

"Shi din." Yaja tsaki.

"Kina da dari biyu to?” Iman ta sake kallansa cike da raini.

"Eh ina da ita."

"Yauwa dan bani naje can na siyo gurasa a bakin titi." Iman, mamaki da takaici suka rufet

a tace

"Kati za'a siyo min bani da data." Fitowar Umma ta hanashi magana inda ta kalleshi tace.

"Au kai har yanzu kana cikin gidan nan dama baka tafi ba?" Umar yai shiru.

"Ba cewa nai kabar gidan nan ba? Ka rubuta min takardar yarinya ka bani bana san a

uranka da ita, ni na haifi Bilkisu bakai ka haifa min ita ba dan haka ka sauwake mata."

"Wai Umma duk meyayi zafi haka? Lafiya lau fa muke zaune, haka kawai duk sanda abu ya hada ma’aurata sai a fara zancen saki?” Umar yai magana yana kauda kai gefe.

"Eh

a lafiyar naje na tarar dakai kana kallo ita kuma tana daki har ciwo yasa ta zubar da cikin jikinta ko?" Umar ya zabura yana zaro ido.

"Ciki? Bari tayi? Wayyo Allah na wallahi ban ma san tana da ciki ba."

"Ya za'ai ka sani tunda ka kwallafawa ranka yar

uwar ta? Ya zaka sani tunda ba damuwa kayi da ita ba?"

Hankalinsa ne yai mugun tashi ya mike yace “Umma da gaske ciki ne ya fita?”

Yatsa ta nunashi da ita tace “Bansan na fara karya ba sai yau ai.”

Bata jira amsarsa ba tace “Abba na Kaduna yana dawowa z

ai kira mahaifinka a raba auran nan, dan wannan karan banga wanda ya isa ya maida ‘yata dakin ka ba, ko wancan karan nice na amince har aka amince dakai.”

Zufa ce ta fara keto mai, bari? Ciki? Raba aure? Kawu? Gaba daya jiyai yunwar da yake ji ma tabar ji

kinsa gaba daya hankalinsa yayi mugun tashi, yana neman yiwa Umma magana yaga ta koma daki, kallan Iman yai itama ta hau sama da sauri, cikin hanzari ya nufi dakin Bilkisu, mai zaiji? Kofar yaji a kule.

Nan ya bubuga kamar mai shirin kuka yace “Billyna! A

marya! Dan Allah bude muyi magana.”

Bata ko kulashi ba bakuma ta da niyyar tankamai……

Ayusher

🏌🏻

‍♀

️

[5/15, 9:39 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye TA*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta

wannan* 07065283730

*50*

Karshe.....

Duk da zuciyarta ba haka taso ba, ba zata iya bude masa ba saboda kamar yadda Umma ta fada ne Umar bazai ga darajarta ba in har bata nuna masa kuskurensa ba.

Yadda yake mata magana kamar zai yi kuka shine

yasa ta toshe kunnanta tana rintsa ido cike da zafin rai, ta jawo pillow din dake kan gado ta rufe kunnenta dashi da karfi tana zubarda kwalla, yanzu kenan laifinta ne yai sanadiyar zubar cikin ta, dan da ta kira Umma tun farko bata tsaya jiran Umar ba ki

la da bai zube ba.

Tana juyo shi daga waje yana cewa “Billyna zoki bude min dan Allah, wallahi bansan kin kirani ba dan Allah ki bude min yake abar kaunata. Kinfi kowa sannin yanzu zuciyata a mamaye take da kaunarki, dan Allah Billyna.”

Gaba daya ta rasa

abin yi a hankali Bilkisu ta taho wajan kofar saboda zuciyarta tana neman fin karfinta, har ta kama handled din da nufin budewa sai taji kiran wayarta, haka ta gungura kekenta taje ta dauka, ganin Umma ce yasa tai saurin dagawa inda tace.

“Kada ki sake k

i budemai kofar nan kinji na fada miki, idan ba haka ba zai daukeki babbar banza kuma sakarai, ki bari ki karbi yancinki wannan fadan naki ne ba nawa bane ba kuma na Abbanki bane. Da alama tun farko dan ina shiga fadanki ne yasa kika saki jiki bakya nemawa

kanki ‘yanci da kanki.”

Hawayenta ta share tace “Umma yana ta hadani da Allah na rasa ya zanyi." Tai maganar cikin kara sakin wani kukan.

Umma cikin dan kakkausa murya dan ta shiga hankalinta tace “Nadai fada miki Karki kuskura ki bude, ke ko haushin ab

inda ya samu jaririnki bai isa ki nunamai kuskurensa ba? Allah yaga zuciyarki yaga tashi, dan haka ki dena ma sauraransa."

Bilkisu ta jijiga kai sannan ta ajiye wayar tana dora kai saman cinyarta.

Ganin taki budewa ya tabbatar masa da cewa itama taji hau

shin abinda ya faru, hakan kuma ya sake tabbatar masa da cewa Bilkisu zata iya rabuwa dashi. Ya matsa kusa da kofar yana mata magana cikin magiya

"Shikenan Sahibata tunda ba zaki bude min ba zanje kan titi na kwanta har katuwar mota tabi ta kaina tunda k

ema kin tsaneni yanzu." Umar na gama fada mata haka yabar wajan jiki babu kwari.

Da sauri Bilkisu ta nufo kofa ta bude sai dai bata ganshi ba alamar yabar wajan. Wani ihu ta saki wanda yasa su Umma fitowa da gudu suna tambayarta.

"Lafiyar ki Bilkisu? Men

ene haka?"

"Umma! Na shiga uku Umar zai kashe kanshi, dan Allah Umma kubarshi yai min duk abinda yaga dama, wayyo Allah Umma wallahi ina sanshi."

Tsabar takaici yasa Umma kasa yi mata magana, ji take kamar ta shaketa saboda haushi. Harara kawai ta zabga

mata tare da wucewa ta koma daki tana ta masifa. Iman ma tsayawa tai tana kallan Bilkisu wacce ta gunguro kekenta ta rike hannun Iman cikin kuka tace “Iman ku tausaya min, ku gane cewa Allah yayi Umar a haka ne, koda Ibty ya aura halinsa ne a haka, dan All

ah ki bishi kice ya dawo." Saboda ta kyalesu yasa Iman cewa.

"Bari naje." Ta fita can bayan wasu lokuta sai gata ta dawo inda ta samu Bilkisu a falo tace.

"Na sameshi a bakin gate yace shikenan amman ki bari Umma ta huce sai a sasanta." Bilkisu ta sauke

wata nannauyiyar ajiyar zuciya tana lumshe ido.

Umar kam yana waje yana safa da marwa yana kallan wayarsa tare da leken ko zaiga wani yazo bashi hakuri.

Ganin Iman yasa yai kwafa tare da yin wani murmushi yace “Ai nasan bazata iya rayuwa bani ba.”

Yan

a kokarin bude kofa cikin kasaita da isa kawai yaga Iman tayi shawaginta ta koma ciki.

Mamaki ne ya rufeshi kamar ya kirata sai kuma ya tsaya yana kallan abinda take ko komawa tai ta dawo?haka ya karashi zamansa ya koma ciki, kitchen ya shiga ya dinga bud

e drawers yana neman abin ci, wannan wani irin iskanci ne? Ace ko abinci babu dafafe?

Bai iya ko kunna gas ba sai abokinsa ya kira a video ya koyamai, haka yai haukar dafa farar taliya ya zuba mai da yaji ya zauna yana ci yanda kasan ya samu nama, wannan

wani irin masifa ne? Yanasan fita yaje ya sai abu amma yana tsoron karya kashe dan kudin hannunsa a zo amai korar kare. Ai dai ance abinci ya kare ko? Gobe dai dole a kawomai in kuma baso ake a kasheshi ba.

Washe gari har wajan karfe goma yaga ba'a kaw

o mishi abinci ba, ga yunwar ji yake kamar zai mutu, yaso dafa wata taliyar amma babu, ita kenan ya samu ‘yar kadan jiya, yana mamakin dama Bilkisu kullum w gidansu take amso abin dafawa kenan ko me? Rai a bace, ya tashi ya fita zuwa sashen su Umma. Yayi s

a'a Abba ya dawo da alama jiya da daddare ya dawo, cikin jin dadi ya kalleshi ganin yana karin kumallo, sum-sum ya shiga ya duka yana gaishe, Abba bai tanka mai ba karahe ma yi yai kamar baisan da zaman sa a gun ba.

Yadan sassauta murya kamar mutumin ar

ziki, yace “Abba kaima fushi kake dani?" Abba ya ajiye kofin shayin hannunsa.

Kamar bazai amsa mai ba sai kuma yace “Ba dai ni kake yiwa wannan maganar ba ko?”

Umar yai kalar tausayi yace “Abba ina san Bilkisu na rantse da sarkin dake busa numfashi ina

santa, duk abubuwan da suka faru tsautsayi ne, bada sanina bane wlh Abba inaji a jikina asiri akamin, sam bansan sanda nake aikata wasu abubuwan ba.”

Ya dan nisa cikin sanyin murya yace “Idan har kuka raba auran nan Abba rayuka ne zasu baci."

"Anzo guri

n, daidai wajan ma kuwa, Umar dan Allah wane rai ne baka gama batawa ba a cikin gidan nan? Ashe akwai ragowa ban sani ba?" Umar yai saurin cewa “Ba haka nake nufi ba Abba, wallahi baka fahimceni bane."

"Tashi kabani guri, ba ance Bilkisun tace ta hakura d

a auran ba? Inaga ai an hutar da kowa ko? Allah ya hada kowa da nashi rabon."

Lallai mutanan nan sun shirya raba su da Bilkisun shi, bema san yanacin arzikinta ba sai yanzu da yaga tabbas za'a rabasu. Ya zauna ya dinga bawa Abba hakuri har Umma tazo waja

n, ya hada da ita yana ta magiya kamar makahon da ya rasa hanyar gida. Umma na shirin magana ta hango Bilkisu a can gefe tana hawaye, hakan yasa ta hadiyar yawu mai daci, babu yadda zatai dole ta hakura kafin Bilkisu tawatsa musu kasa a cikin ido.

Umma

ta daure cikin halin ko in kula tace. "Ni babban bakin cikina yadda kake mata kamar ka samu dabba, Umar ka manta wacece Bilkisu a wajan mu? Bilkisu ‘yarmu ce ta cikin mu, ƴar uwa a gurin IBTISAM idan har kana da mutunci zaka lallabata fiye da yadda zamuyi,

in har da gaske san Ibtisam din kake ai bazakaso abinda zai illata yayarta ba ko?”

Yai shiru yana sauraren Umma, jikinsa duk yadanyi sanyi.”

Umma ta kalli Abba sannan ta kalli Bilkisu tace “Zan sake baka Bilkisu a karo na karshe, idan har ka kuskura tay

i kuka ko ranta ya baci kasan da cewar sai ka bar gidan nan koda kuwa shine karshen rayuwar Bilkisu." Tana kaiwa nan taja tsaki tare da barin wajan.

Abba yai masa nasiha sosai sannan yace zai bashi jari yai sana'a ya rike Bilkisu da kuma kanshi saboda hal

in rayuwa karya saba ana bashi randa Abban ya mutu yazo su rasa yadda zasu yi.

Farin ciki ya lullubeshi tare da daukar alkawari zai riketa kamar kowane miji a gurin matarsa.

Yana kokarin mikewa sukaji muryar Bilkisu tace “Abba ko ka bashi ni bazan koma

ba, takardata nake jira.”

Gaba daya mamaki ne ya rufesu suka kalleta cikin mamakin abinda ta fada, tabbas tana san Umar kamar ranta sai dai gani yanda iyayenta ke lalabashi suna kashemai kudi saboda ita, kuma duk da hakan babu alamun so a tattare da shi y

asa taji ko zata mutu yanzu kam zata hakura dashi, ta tabbatar iyayenta basa farinciki da wannan auran, gashi a dalilinta ta rasa ‘dan cikinta.

Cikin mamaki Abba ya kira Umma wacce ke zaune a bakin gado rai a matukar bace.

Fitowa tai cikin kunar rai, sai

dai jin kalaman Abba yasa gaba daya ta tattare hankalinta kan Bilkisy.

Cikin dauriya ta kalli Umma sannan ta kalli Umar tace “Ya Umar dan Allah ka bada takardata kafin ka fita, in kuma kana bukatar biro da paper ne yanzu Iman sai ta kawo maka.”

Ta maida

kallanta kan Abba tace “Abba dan Allah in ya rubuta aba Iman ta kawomin.”

Bata jira mai zasu ce ba ta shiga daki ta kulle, kuka kawai tasa tana dukan kirjinta ita kadai tasan irin masifar san da takewa Umar a rayuwarta.

Gaba daya falan yayi tsir kowa ma

makin abinda ya faru yake, Umar a firgice ya sa gwiwowinsa a kasa ya hade hannaye yace “Abba wallahi Allah na tuba dan Allah ku yafemin.”

Mikewa Abba yai ya nufi daki, Umma tabi bayanshi.

Hankalin Umar yayi mugun tashi tabbas yanzu abin ba wasa bane, ya

shiga uku? Ya zaiyi?

Duk yanda yai magiya Bilkisu taki yarda, gashi Abba ya kule bangarensu, dakyar Abba ya yarda ya koma dakinshi nada, haka kullum zaizo yana bada hakuri amma Bilkisu ta dage tace sun gama zaman aure, ita kanta duk ta canza ta rame amma

ta kafe tace bataso.

********

IBTISAM kuwa a nasu bangaren cikin yazo mata da laulayi sosai, Aminu kuma ya sake zurmawa cikin shafin kaunarta, gaba daya ya kasa sukuni saboda rashin lafiyarta, in ya tafi aiki yana kira sama da sau biyar ya dinga jin

ya jikinta da sauransu.

Ibty gaba daya ba ta iya cin abincin da ta dafa sai na gurin Ummi shima daga danwake sai tuwo da kunun gyada. Kullum driver yana hanyar gidan Aminu kai abinci, idan sukaji shiru kuma sai Aminu yaje da kanshi ya amso mata in yana gi

da, ita kuma takan jure wajan yiwa Aminu da su Islam girki amman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login