Showing 3001 words to 6000 words out of 128353 words
/>
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*Free Page*
*Na Kudine ki Bada 500 ki cafki garabasar novel bakwai da program Uku*
*Shafi na Biyu.*
Umma ce ta fito daga daki, ko karasowa cikin falan batai ba Iman ta ruga a guje ta boye a bayanta, Ibtisam ta biya da gudu tana, "Wallahi Umma yau wannan autar taki sai ta gamu dani."
Umma ta kalli Iman ta baya sannan tace "Yahkuri Ibty na kinsan kanw
ar taki akwai tsokana, karki biyeta kinji? Ke ai mai hakuri ce.”
Tsayawa tai tare da hararar Iman kamar zatai kuka tace "Allah Umma shiyasa takemin haka, taga duk sanda kika sa baki bana iya yi mata komai."
Cikin murmushi Umma tace "Nan gaba in ta kuma
dakaina zan zane miki ita kinji?"
Juyowa Ibtisam tai a take suka hada ido da Umar wanda ya kafeta da ido yana kallo kai kace xai lashe ta, dauke kai tai da sauri ta hau sama tana yan kunkunin abinda Iman ta mata.
Umma ta kalli Iman ta kamo kunnenta da
ya tace "Na dauka na hanaki daukarwa Ibty kaya?"
'Yar kara tai tace "Nadaina Ummana."
Umar ne ya kalli sama yace "Umma bari na amso sakona agun Ibtisam, da alama tahau dashi sama."
Tana kokarin cemai ai basai ya hau ba ya bari Iman ta amsomai ko a kira
Ibty ta kawomai kawai taga harya haye, itakam halinsa na bata mamaki, duk da a gidan ya taso ya kamata yasan shifa saurayine su kuma 'yan mata ne, inda yayi yanzu ai bai kamata ba.
Umar kai tsaye ya tura kofar dakinsu Ibtisam, tana ta ninke kayanta sam b
ata kawo shi bane ta dauka Iman ce, dan har ta mita, “Allah Iman kinyi na karshe ya isa hakanan kuma.”
Jin ansa key a kofar dakin yasa ta juyo da sauri, cikin tsananin faduwar gaba ta kalleshi bakinta nadan rawa tace "Ya Umar meye hakan?"
Takowa yai zuw
a inda take idanunsa duk sun canza, hannu yasa ya dagota iya karfinsa, jikinta ne ya fara rawa tace "Me kakeyi hakan?"
Jikin bango ya kaita ya matse hannunta biyu wanda zafi da zugi sukasa tadan runtse ido kadan, cikin kakkausar murya yace "Me kikace daz
u a makaranta?"
Wani irin bugawa zuciyarta take da karfi tace "Ya Umar wai dan Allah ana so dole ne? wannan wace irin soyayya ce? Dan Allah na rokeka da Allah ka......."
Hannu ya daga kamar zai wanka mata mari ne yasa tai dif, idanunta ta runtse da ka
rfin gaske, jikinta ya kara daukan rawa, sauke hannu yai sannan ya nunata da yatsa yace "Wallahi inkikai gaggawar sake furtamin wannan kalmar ki shirya fuskantar tashin hankali a rayuwarki, na sanar dake ba yau ba bakuma jiya ba, ke tawa ce ni kadai duk du
niya ba wanda ya isa ya rabamu. Aurena dake wajibi ne
yanda kike sallah biyar a rana haka aurena yazama wajibi, ko da wasa karki kuskura ki karamin maganar nan wannan umarni ne na baki." Yana kaiwa nan ya saketa ya juya ya fita daga dakin tare da banko kof
ar da tsananin karfi.
Haryanzu jikinta bai dawo daidai ba, tsugunawa kawai tai ta fara wasu hawaye masu tsananin zafi da kuna, itakam ya zatai ta kwace kanta daga wannan bala'in da masifar? Ko zuwa zatai tace Abba ya mata aure da wanda yake so? Dan aure n
e kawai zai sa wannan mahaukacin ya kyaleta. Da sauri ta girgiza kai in kuma Abba ya zaba mata Umar fa? In ta fadi abinda yake mata ba lalai su Abba su yarda ba dan Abba ya yarda dashi dari bisa dari kuma batasan adalilinta Abba ya rabu da yayanshi wanda s
hikadai Allah ya barmai a duniya, duk ‘yan uwansa sun rasu daga shi sai mahaifin Umar. Fuskarta ta shafa tana kokarin mikewa wayarta tai kara.
Idanunta cike da hawaye ta jawo wayar tare da zama a bakin gado, ganin sunan Ainah a alan wayar ne yasa ta dan
share kwallarta cikin sanyin murya tace "Ainah!"
Daga can bangaren Ainah cikin zumudi tace "Ibty albishir?" Bata jira me zatace ba tacigaba "Anyi mutumin naki a gidanmu yau, in kawo miki?"
Murmushin yake tai tace "Oh ni Ainah yanzu haka kawai dan ni na k
awo san sinasir duniya sai ai abinci a gidanku ki taso ki kawomin?”
Dariya Ainah tai tace "Ke dai me ya dameki? Sannan sinasir din sadaka ne, yau matar Ya Aminu ta cika shekara biyar da rasuwa.”
Cikin sanyin jiki tace “Oh ikon Allah! Yaushe yaushe ki
ka kawomin na shekara hudunta a makaranta?”
Ainah tace “Duniyar ce gudu kawai take, yanzu tunda kinji na sadaka ne in kawo miki?”
Kai ta girgiza tace “Ki barshi dan Allah, nima jiya naci a gida.”
Yanayin maganar Ainah ne ya canza da alama taji ba dad
i tace “Shikenan.”
Kamar zata kashe Ibtisam tai saurin cewa “Haushi kikaji? Kiyi hakuri gobe kya tahomin dashi skul to, shikenan?”
Dariya tai da alama ta sauko nan sukaci gaba da hira wanda rabinshi na Umar ne, itakam Ainah sai kara bata shawara take aka
n tasan yanda tai ta yakice wannan abin.
********
Yarane ‘yan kanana guda biyu mata ‘yan shekara biyar, kallo daya zaka musu kasan yan biyu ne wato tagwaye saboda kamaninsu da tsayinsu, sanye suke da riga doguwa ta lace sunyi kyau sosai, abin sha’aw
a.
Da gudu suka taho suka rungume Aminu wanda yadan motsa lebe kadan sam babu fara’a a fuskarsa, in da sabo sun saba, cikin zakin baki daya tace “Dady ka taho mana da chocolate?”
Kallan wacce tai maganar yai yace “Islam na dauka na fada miki banasan sh
an zakin nan? Nace zan siyo sau daya a sati ba kullum ba. Okay?”
Ya karasa maganar yana mika ma dayar ledar hannunsa “Ilham kaiwa Hajiya maganinta.”
Abinda yace kenan ya wuce dakinsa, dakin Hajiya suka shiga tana zaune tana irga kudi, tanajinsu ta maid
a kasan pillow da sauri ta kwanta a kan gado tana wani fitarda numfashi, da gudu suka fada kanta.
Ta shafi kansu tace “Ilham kin fadawa Dady dinki ina kwance ba lafiya haryanzu?”
Da sauri ta rufe baki tace “namanta Hajiya, bari na je na fadamai.”
Rik
ota tai tace “bashi kya fadamai anjima.”
Magani ta mika mata, ta amsa tai dan shiru alamar tunani sai kuma ta baza tagumi ta mike dakyar ta kwaso kaya daga cikin drawer tana kokarin sawa a akwati, Islam tace “Hajiya ina zaki?”
Tadan shafi kanta tace “Is
lam kinga Ummy batasan na cigaba da zama anan, shiyasa nake jiran babanku yazo dan na samu na mai sallama……”
Ai basu tsaya jin karshe ba suka rushe da kuka, fitowa sukai daga dakin sunata kuka Islam harda zunduma ihu, da sauri ya fito daga dakinshi jin ku
kan da suke rusawa, suna ganinshi suka karaso suka rike rigarsa Ilham tace “Dady dan Allah karku kori Hajiya! Ka roki Ummy tabar mana ita.”
Islam ma tana kuka tace “Dady inta tafi wazai dinga mana wanka? Yana shiryamu yana mana abinci?”
Idanu yadan runts
e kadan yace “Ya isa hakanan, ba inda zataje zan mata magana yanzu.”
Fuskarsu suka share suka hau murna harda tsale.
Bangaren Hajiya ya nufa wanda dan karamin corridor ne tsakaninsu, tana zaune ta saka hoton Na’imah a gaba, gefe kuma kayayakin da taketa
hadawa ne a gefe, sallama yai ya shiga ciki.
Hajiya tana ganinshi ta ajiye hoton tana share kwalla, jikinsa ne ya sake wani irin sanyi jikinsa yai ya zauna a kasa tare da lankwashe kafa yace “Hajiya meyasa kike haka dan Allah? Da jikinki zakiji ko kuma d
a tunani?”
Cikin muryar kuka tace “Aminu yazanyi? Rashin Na’imah a kullum dawomin yake sabo? Barin gidan nan shine abinda ya cancanta, taya zakai aure ina gidan nan? Na fahimci dalilin Ummynka nasan taga na bar gidan, haka zakaci gaba da zama? Kaifa d’ana
ne bazanzo abinda zai ma ila ba a rayuwa.”
Ajiyar zuciya yai yace “Wai dan Allah menene na tilastawa sai nayi aure? Nace ba yanzu ba dan Allah Hajiya ku barni tukuna.”
Tace “Aminu bafa zai yiwu ba, shekara biyar? Ai Ummynka tayi hakuri, dan Allah kabi
umarninta.”
Shiru yai shikansa ya gaji da batawa Ummy raj akan maganar aure, Hajiya bata auno abinda zaice ba sai jitai yace “Naji zan yiwa Ummy magana ta samo yarinyar data kwanta mata, amma wannan bazai sa ki bar gidan nan ba, ke amanace a gareni, zan k
uma kula dake har karshen rayuwata.”
Gabanta ne ya fadi, tadan hadiyi wani abu tare da yin yake tace “Nagode Aminu daka fahimceni.”
Mikewa yai ya bar dakin, yana fita ta dafa kanta, itafa ba auransa bane matsalarta, matar da za’a kawo wacce zata hanata j
in dadi ne bazata yarda ba, haka kawai yaran da ‘yarta ta taimaka gun bunkasar arzikinsa wata can tazo ta mori jin dadi ta barsu? In ‘yarta bataji dadin daya kamata taji ba ita da jikokinta dolene suji, kauye kuma ta barshi kenan har abada.
*******
D
uk yanda Ibtisam taso tai bacci ta kasa, wannan bala’i dame yai kama? Mikewa tai ta sauko daga kan gado, sauka kasa tai inda dakin yayarsu yake wacce Allah ya jarabceta da ciwo na sickle cell, mahaifinsu fa mahaifiyarsu basu san As da AS bane harsai bayan
an haifeta, da harsun so hakura da haihuwar sai Allah ya
kawo cikin Ibtisam, damuwa da tashin hankali ya bayyana a gunsu suna tsoron kar su sake samun SS sai dai cikin godiyar Allah ita sai aka samu mai lafiya, daga nan sukace sun hakura, sai dai zuciya da
san abu yasa Umma ta sake rokar Abba akan su gwada na karshe, Alhamdulila Iman itama tazo da lafiya daga nan suka hakura balle a lokacin damuwa da rashin lafiyar Bilkisu ya damesu, kusan koda yaushe suna asibiti, wannan ciwo ya taba kafarta daya wanda tafi
ya take wahalar da ita, dole sai keken guragu aka nemar mata.
Bude dakin tai a hankali ta shiga ta kwanta a bayanta, tana tsananin san yayarnan, idanunta ta rufe tana tattaro idea din abinda ya kamata tai wanda zai rabata da wannan jarabar.
*********
Washegari…….
Yauma sanye take da abaya sai dai yau mayafin kanta brown ne kalar jakarta, tunda dadewa ya hanata yawo da mayafi, bata isa ko kofar gida ta fito da mayafi ba, da hijab yasa ta dinga sawa dan har dinko mata dogaye yai tace ita kuma bazata
sa hijab kullum ba, nan sukai ta fada a karshe dai ya hakura da abaya.
Cikin murna ta tari adaidaita sahu ganin yau bai biyota ba, lalai yau tayi sa’a, tana shiga adaidaita kawai taganshi ya shigo.
Jitai kamar an kwara mata ruwan xafi, kai ta kauda
gefe suka fara tafiya, ba wanda yace wa wani kala. Kallan mai adaidaitar yai cikin masifa yace “Inka sake kallanta ta madubi wlh sai na faffasa maka jiki, wannan ai iskancin banza ne.”
Baki mai adaida ya bude yace “bawan Allah nida adaidaita ta akan me z
a’a hanani kallan madubi?”
Cikin bacin rai yace “Ka sake kaga yanda ake hauka wallahi daga kai har adaidaitar sai na muku ila.”
Ibtisam ta sa hannu a saman goshinta itakam anya mutumin nan baya shaye shaye? Ko dai yanada tabin hankali ne? Wannan wani iri
n jaraba da masifa ne? Suna isa makaranta ta sauka bata ko mai magana ba tai ciki, sai dayaga ta wuce sannan shima ya wuce.
Motar datasha gabanta ne yasa tadan matsa kadan, tana kallan motar, glass din motar aka zuge ta gefe ta kalli motar, a daidainan
idanunta suka sauka akan matashin dake zaune akan kujerar bayan mota, hannunsa dauke da jarida ya sa medical glasses fari a idanunsa, jitai ance “Yaya bari na sauka anan, zamu wuce da kawata.”
Ganin Ainah yasa ta saki murmushi sannan ta gane Ya Aminu ne,
a hankali tace “Ina kwana?”
Kalan sakan daya ya mata kawai yace “Lafiya.”
Ainah na fita Mamman yaja motar suka tafi, kallanta tai tace “Can na hango chewing gum dinki yana lekenki yaga ko aji kika wuce.”
Tsaki tai tace “Yau dakar sa’a kikai Ya Aminu ya
kawoki?”
Tadan yi huci suka fara tafiya tace “gida yazo yiwa Ummy magana danaga zai wuce na rokeshi ya saukeni, dakyar ya amince sai da Baffah yasa baki.”
Tadan girgiza kai, Ainah tadan daga mata gira tace “nafa taho miki dashi.”
Ibtisam ta saki fuska
tace “Thank you Ainah kinsan ko breakfast banba? Wai ina sauri dan na gudu kafin ya fito?
Ayusher Ce
🏌🏻
♀
️
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą
Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*Free Page*
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA KUDINSA TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
*Se
ka tura shedar biyan kud'inka zuwaga wannan lambar*
+447894142004
*Ko kuma tura katin waya na MTN ta wannan number
👇🏼👇🏼
*
07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*DUK AKAN 500NAIRA ONLY MACCEN DA TA'ISA TA SAN KANTA BAZATA BAR DAMA
R NAN TA WUCETA BA!*
*ƳAN NIGER
🇳🇪
, ZAKU IYA TURA KUƊINKU 550F TA NITA, AMANA, AL'IZZA, BENIF KO ZEINA GA WANNAN LAMBAR* +227 96 91 36 36 *SUNA* RAHINA daga Niamey.
Page 3
Suna shiga class Ainah ta ajiye kayanta tace “Ibty ina zuwa.” Ko minti biy
u da fita batai ba wayarta data bari a kusa da Ibtisam ta fara kara, kallan wayar tai ganin My bro a jikin allan wayar dauke da hotonsa yasa ta kara kallan wayar da sauri, tare da wawaigawa ko zata hangota, ganin wayar na kokarin katsewa yasa ta daga tare
da karawa a kunnenta, haka kawai ta samu kanta da kasa magana.
Aminu yanaji an daga yace “Ki fito ki dau wallet dinki, kin barshi a mota in kuma bakya bukata na wuce.” Tana kokarin mai magana taji an kashe wayar.
Kallan wayar tai cikin mamaki tace “Iko
n Allah sai kallo, ai ka bari kaji amsarta kafin ka kashe wayar ko?”
Mikewa tai ta fito waje rike da wayar Ainah sai dai sam bata hangota ba, zuciyarta ce ta bata gwara kawai taje ta amso dan da alama Ya Aminun nan bashida hakuri.
Tayi tafiya maidan ya
wa kafin ta hango motar dazu, karasawa tai a hankali tadan kwankwasa glass din motar, cikin mamaki yake kallanta, shifa matsalar yaran zamani yana bashi mamaki, sam mata yanzu basuda kamun kai.
Bai sauke glass din ba sai kallanta da ya sakeyi tana tsaye
tana jira, sake kwankwasawa tai, cikin kulluwa da takaicin halin matan yanzu, yarinyar da batafi kanwarsa ba tana neman mai mota ya kulata, kai yadan girgiza dan ya saba fuskantar wannan takaicin, ransa a bace ya sauke glass din.
Bai jira tace wani abu b
a kawai ya hau magana cikin bacin rai “ Motar kice? Ko kuwa mai motar dan uwanki ne?”
Zati da girman shekarunsa yasa Ibtisam tai shiru haka kawai shakkarsa ta kamata, dan Aminu nada kwarjini da cikar zati balle gashi babba, bakinta nadan rawa tace “Ya Am
inu wallet……”
Jin ta kira sunansa yasa ya kara kallanta cikin mamaki yace “Ikon Allah! You even know my name?”
Tadan sake motsa baki kokarin maida glass din ya farayi cikin hanzari tasa hannunta a saman, kallanta yai cikin matukar mamaki, yanzu kam kall
an da yake mata na kyamar rashin kamun kai ne, yace “Me kike hakan?”
Hannunta ta zare da sauri idanunta sundan ciciko tace “Ya Aminu ni kawar Ainah ce, wallet dinta nazo amsar mata tadan fita ne.” Ta dan kunna wayar Ainah dake hannunta tana nunamai.
Tsa
nanin kunya da haushin abinda ya aikata ne yasa ya kalleta, lalai idansa ne ya rufe tabbas muryarta ce dazu wacce ta gaisheshi. Burin kunya da kokarin danne laifinsa ya fara yi yace , “Oh! Why didn’t you said it earlier?” Yai maganar yana miko mata wallet
din.
Amsa tai kafin tace, “Ina na samu damar magana? Ka rufeni da fada?” Abinda tace kenan ta juya ta fara tafiya, baki ya dan bude kadan tare da komawa ya zauna sosai yace “Mamman kaga sanda na rufeta da fada?”
Mamman ya shafi kansa yace “Yallabai ai t
ana zuwa baka bata damar magana ba ka hau fada”
Ya dan kalli wajen window inda take tafiya yace “Amma dai ba bakinta na rufe bako? Kawai dai bataso yin magana bane.”
Mamman yadan guntse dariyarsa dan karyai laifi.
Ya kara kallanta daga yanda take taf
iya ya tabbatar zaginsa takeyi, in ba zagi ba rashin kunya take na abinda ya mata.
Kanshi ya kawar daga kallan gun a ransa yace me yasa tana zuwa bata sanar da kanta ba? Su yaran yanzu sai kwarewa gun neman magana.
Itakam Ibtisam tana tafe tana mita,
“ Su manyan nan sai suyi abu suki daukan laifinsu, insukai abu sai su nuna ba laifi sukai ba. Ai sai ya bata hakuri amma tsinanen san girma irin na mutane da san rike girmansu bazai taba bari ya bata ba.”
Aji ta shiga lokacin har lecturer dinsu ya shigo,
kusa da Ainah ta zauna ta ajiye mata wallet da wayarta, cikin muryar rada tace “Ina kikaje?”
Harararta tai tace “Gun Yayanki mai masifa.”
Dan zaro ido tai batasan sanda tadan daga murya ba tace “Ya Aminu?”
Ganin kallan da aka mata yasa ta gyara zaman t
a da sauri tare da guntse baki, Ibty ta harareta tare da mata alama datai shiru.
Ai Ainah