Showing 60001 words to 63000 words out of 128353 words
Ibty ta bude kwalayen ta dauko cup na shan juice din sannan ta kalleshi tace "Ya Aminu sauko."
Kallan mamaki ya mata yace "In sauko?"
Ta kalli su Islam tace "Eh mana, gwara ka sauko aci gaba daya."
Tab shi bayan Baffansa akwai wanda yakecin abinci dashi ne? Sai matarsa data rasu.
Ibtu ce ta katseshi jin tana cewa "Ilham matso nan, kinga Dady zai zauna agun."
Kallan yaran yai sannan ya kalleta, kamar yace bazai sauko ba sai dai kar yaransa suji ba
dadi yasa ya sauko fuskarsa a daure sosai.
Gutsira tai ta mikawa yaran sannan ta turamai wani gabansa, hannu yasa ya dauka tare da jawo wayarsa yana daddanawa, fuskarnan a hade sosai yakeci kai kace cin dole aka sakashi, yana gama ci ya mike ya wuce dak
i.
Sukam bayan sun gama ta gyara gun sannan sukai sallar isha’i kafin ta kai su daki ta musu addu’a suka kwanta.
*****
Dakinta ta koma ta dauko d’aya daga cikin kayan baccinta wani mai shara shara, ita kanta kunyar ganin kayan tai da sauri ta maida ta
sake dauko wani shima da sauri ta maida, jawo wata riga tai 'yar doguwa ce kadan bata kai gwiwa ba, kallan rigar tai tana tunanin ta yanda zata iya kwana da ita a gaban namijin da ko fuska bai sakar mata ba.
Dakewa tai ta saka rigar ta shafa turaruka sa
nnan ta daura zani a kasa ta zura hijab. Dan itakam kunyar ma fita daga dakin take da wannan rigar.
Haka ta zauna a falo tai dan kallo tanata lissafin yanda zata shawo kan Aminu ya so ta, har internet ta shiga tanata dube dube, kunya da haushin kanta ne
ya kamata tace “Wai duk yanda nakejin labarin soyayya a gidan amarya da ango ni nawa nice mai neman yanda zan sa a soni?” Jitai idanunta sun ciko da kwalla nan gidan da zaman aurenta shine dahir dinta dole koma menene tayi. Haka ta mike ta duba su Islam sa
nnan ta wuce dakin Aminu hannunta dauke da tire na tea data dafamai wanda yasha kayan kamshi.
Kwankwasa kofar tai daga ciki ya amsa sannan ta shiga da sallama, yana zaune yana duba abu a laptop dinsa ta karasa ta ajiye akan side bed dinsa, dagowa tai ta
kalleshi tare da cewa “Aiki kake?”
Tambayar tazomai a banbarakwai dan bai tabaji ta tambayeshi haka ba, kai ya daga sannan ta wuce ta inda take kwanciya, tunani ta fara ta yanda zata zare zanin ta kuma zare hijab gashi kwan wutar dakin a kunne.
Gaba da
ya gani tai bazata iya wannan abin kunyar ba, haka ta kwanta tadan ja bargo, daga cikin bargon ta dan zare zanin jikinta ta dan janye hijab din, shikam bai ma san tanayi ba, sai dai gaba daya hankalinsa na kanta. Ta hakura kenan? Da alama tunda dai yaga ta
sauko. Ya zaiyi ya gane komai ya wuce?
Dan gyaran murya yai hankalinsa nakan laptop din yace “Me kike gani akan kije ziyara gida kafin ki koma school?”
Sam ta manta shigarta ai cikin wani irin zumudi da yanayi ta yayi bargo ta juyo gaba dayanta tace “G
ida?”
Yanda tai maganar cikin zumudi yasa ya juyo ya kalleta, mamaki ne ya kamashi ganin shigar dake jikinta, gashi rigar irin mai hannun vest din nan ce, itakam sam ta manta ta sake kallanshi tace “Yaya da gaske?”
Sake gyaran murya yai ya kasa sake kal
lanta yace “Eh ya kamata nima na gaishesu sannan su Ilham ma su je.”
Wani irin dadi ne ya kamata, duk ta rikice tace “Yaya yaushe kake ganin ya kamata? Gobe? Ko jibi?”
Juyowa yai jin lalai zumudin nata da gaske take, idanunsa ne suka sauka akan jikinta
, da sauri ya dauke idanunsa.
Ganin yanayinsa yasa ta tuna shigar dake jikinta, da sauri taja bargo ta lulube jikinta sannan ta sulale a hankali ta kwanta, kunya duk ta gama kamata.
Haryayi shiru sai taji yace “Badai cewa zakiyi kunya kike bako?”
Juyow
a tai haryanzu tana cikin bargo tace “Allah na manta abinda ke jikina.”
Wani murmushi yai wanda iya kacinsa lebensa yace “Hmm.”
Da sauri tace “Allah dagaske na manta.”
Kallanta yai yace “Taya mutum zaisa abinda yake kunya? Kedai kawai kice kinsa dan k
ija ra’ayina.”
Haushi ne ya turnuketa, ta kalleshi cikin dan sakalci tace “Koma hakan ne Ya Aminu ba sai kai shiru ba? Sai ka fada?”
Duk yanda yaso ya dane kasawa yai baisan sanda yai wata ‘yar karamar dariya ba, kallan mamaki tamai, bai bi takan dariy
ar dayai ba yace “Yanzu da na fada kinji kunya?”
Ta dan shige bargo tare da dan fito da idanunta kadai tace “Allah ba sai kai shiru ba? Kuma ni wlh na manta, amma sai dai ka fadan sannan.”
Kai yadan girgiza yana murmushi yace “Ranar juma’a insun dawo da
ga skul zan samu nazo lokacin sallah sai na kaiku can na gaishesu, in yaso sai na barku sai dare.”
Dadi ne ya kara kamata tadan bubuga kafa ta cikin bargo tare da juya baya tana murna, zataje taga Ummanta, dasu Abba.
Aminu ganin yanda taketa murna yasa
wani abu yazomai, ta gefen ido ya kalleta yace “Kin tabbatar ya kamata kiyi murna sosai?”
Sake juyowa tai cikin mamaki take kallansa dan bata gane me yake nufi ba.
Kafada yadan daga yace “Dama ina jiye miki ne karkije wannan mutumin ya dan balla kafar
da kike murnar da ita.”
Sam ta manta da Umar, yanayinta ne ya canja ya dan guntse dariyarsa fuskarsa a daure yace “Gaki da tsoro? Ni karma yaje yayiwa su Ilham illa.”
Kifta ido tai, lalai tasan haukan Umar tsaf zai nakasata, shi Aminu da alama wasa ya
dauki abin ita kuwa tasan tsaf zai aikata.
Hannu tasa tadan riko hannunsa, hakan yasa ya kalleta sosai, cikin dan damuwa tace “Yaya dan Allah muje tare ka zauna acan bar lokacin da zamu dawo.”
Yace “Ni? Inje gidan surukaina na zauna har sai kin gama y
ini sannan na daukoki?”
Kai ta daga da sauri, kallanta yai sosai yace “A ina aka taba haka? Kuma ko an taba ma cemiki nai ni zan iya? Duk tsoron ne?”
Tadan hadiyi yawon bakinta tace “Bawai tsoro bane, gudun magana ne.”
Gudun magana?
Ta daga kai tace “
Kaga mijin yayata ne bai kamata ayi husuma ba.”
“Ohhhhh! Husuma ko?”
⛹
🏻
♀
️
[3/1, 7:16 PM] Hauwa Galadima:
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*To
p Ten! Takun Haske Batch A*
Ki hanzarta ki mallaki naki
🤸🏻
♀
️
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004
Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
24
Ganin yayi shiru yasa tai shiru tana tunani, juyawa tai cikin ranta tana cewa “In har na danne tsoron tsohuwar nan dan me zan zauna Umar na ban tsoro?” Jan idanunsa ta tuno da yanda yake tsareta a daki, hala tai ta tunane tunane har bacci ya dauket
a. A bangaren Aminu kuwa abinda ya shekara biyar baiji ba shine ya taso mai yau, dan wata irin muguwar sha’awa ce ta rufeshi, haka yai ta juyi shima kafin baccin ya daukeshi.
****
Ran Juma’a suna tafiya school ta hau aikin gida tai wanka ta dauko wani
dankakareren lace mai tsada ta saka, dinkin an mata shi mai kyau dan asali dama shi ta ajiye zata saka washe garin daurin aure to sai kuma aka samu matsala, tayi kwalliya sosai dan dama ba laifi ta iya kwalliya, Ibty ta fito das da ita kai kace ranar auran
ta ne, turaren wuta ta kunna wanda ya kara kama kayanta.
Sha biyu da rabi yara suka dawo daga skul nan suka ci abinci sannan ta musu wanka suma ta dauko kaya iri daya mai kyau ta saka suma lace sukasha an musu doguwar riga, tana daura musu dankwalli suk
aji alamar bude gate. Wani irin dadi ne ya kamata yau dai xata gida taga Ummanta.
Fitowa falo sukai, shi kuma ya shigo kenan hannunsa dauke da leda, tunda ta shigo falan yake kallanta a sace, tayi kyau sosai da sosai gashi tun ranar da sha’awa ta tasomai
abu kadan kesa yaji yana bukatarta. Har ta karaso yana tsaye yana dan satar kallanta, cikin murmushi tace “Sannu da dawowa.” Tai maganar tare da sa hannu tana kokarin amsar ledar, hannunsu ne ya tabu a hankali ta dago ta kalleshi, shikam kasa janye hannun
sa yai yanda ya saba, amsar ledar tai sannan ta juya ciki, ajiyewa tai a kitchen sannan ta dauko abincinsa, haka kawai takejin tunda ta tabashi bai janye hannunsa ba yanda ya saba ba ta samu kanta da murmushi a cikin ranta.
Ajiyemai tai a dinning sannan
ta nufi dakinsa dan sanar dashi, ya cire rigarsa kenan tai sallama, juyowa yai ya kalleta, ta dauka zai maida rigar sai taga ya karasa cire ta daga jikinsa tare da kallanta. Ibty tai kasa dakai tare da yin shiru tana dan wasa da hannunta.
Sam batasan ya
tako ba sai ganin kafafunsa tai yana nufo ta, gabanta ne yadan fadi kadan bata matsa ba haka kuma bata dago ba, daf ya matso da ita tana juyo numfashinsa, hannayenta tadan matse saboda yanda ta tsinci kanta, idanunta ta lumshe dan ta dauka rumgumeta zaiyi,
ganin jikinsu ya hadu da juna, hannu yasa bayan ya matsota suna gogan juna, kofar data bari a bude yasa hannu ya rufe, sannan yadan kalleta, gefen kunnenta ya matso yace “A dinga rufe kofa saboda akwai yara a gidan, in kika shigo kika manta dasu su kuma s
uka taho nan fa? So kike suka babansu a haka?”
A hankali tadan bude idanta daya tare da dan rike kunnenta tace “Sorry!”
Matsawa yai daga jikinta sannan ya bude wardrobe ya dauko wasu kayan, tace “Dama kiranka nazoyi kazo kaci abinci.”
Kai ya daga alamar
to, juyawa tai kamar zata tafi sai taji yace “Duk kwalliya da zumudin zuwa gidan ne?”
Tadan rufe fuska saboda kunya, murmushi yai yadau towel ya nufi bandaki, haryaje zai shiga yace “In Umar yaga kwalliya kuma ya hanaki dawowa to.”
Yanayin fuskarta ne
ya canza, kamar mai shirin kuka tace “Yaya baza dai ka daina ba ko?”
Juyowa yai ya kalleta yace “Sai randa kika bar tsoron sa.”
Tana kokarin magana taga ya shigo toilet baki tadan turo kafin tadan rufe fuskarta alamar kunya sannan ta fita.
Aminu kam a t
oilet shiru yai yana hadiyar wani abu, shikam meke damunsa? Taya zai bari sha’awar yarinya ta fara damunsa? Dan tabbas dazu rungumeta yaso yi ya wayance, iska yadan furzar lalai inya biya zuciyarsa tofa zai gabza abin kunya.
Haka ya fito yasa yadi fari s
un mai kyau sosai sannan ya fito falo. A waje ya jiyo muryarsu da alama su Ilham ana keke ne, zama yai ya bude abincin, kamshin butter ne ya dan bigi hancinsa, vegetable soup ne wanda akai amfani da butter a maimakon mai, abinci yasa yana ci yana dan murmu
shi dan yana juyo hirarsu daga waje. Ba shakka Ibty tasan takan yara, har mamakin yanda ta shaku dasu daga zuwa yakeyi.
Yana gamawa suna shigowa, nan ta kwashe kwanuka suka kara gyarawa kafin su fito. Suna shiga tadan kalli bangaren Hajiya sannab ta tuno
leken dataga tanayi ranar, cikin murmushi tace “ Yaya ko zamu shiga muyima Hajiya barka da juma’a kafin mu wuce.”
Cikin jin dadi ya kalleta, wanda har ita kanta ta fahimci yaji dadin maganarta, nan yai parking a waje suka fito.
Hajiya kam tana kishingid
e a falo takaici duk ya isheta, tana juyo muryarsu Islam dazu suna wasa, yau kwana biyu kenan ko keyarsu bata gani ba.
Wata ajiyar zuciya ta bakin ciki ta saki sanda taji ana bude gate din gidan. Mamaki ne ya kamata dataji kwankwasa kofa yanzu, kafin ta m
ike har tajuyo murya da gudunsu Ilham.
Da sauri ta bude kofar ashe ba tare zasu fita ba? Da alama kawo mata su zaiyi ya fita. Kofa ta bude da sauri tana dariya tare da tafa hannu.
Da gudu suka karaso suka rungumeta, dadi ne ya kamata. Jin alamun bude k
ofa yasa tadan dago, Aminu ne ya shigo, haba wani irin dadi ya sake rufeta, ta bude baki zatai magana kawai taga Ibty ta biyo bayanshi.
Yanayin fuskarta ne ya canza lokaci daya, daurewa tai ta fara lale lale.
Nan suka koma ciki, suma suka karaso, Aminu
ne ya zauna a kasa daga gefe, ga mamakinsa yaga Ibty ta karaso ta zauna gefensa, Hajiya ta kalleta ta dau wanka, wata tsana ce ta sake turnuke ta, lalai itakam mutuwa ta cuceta, banda mutuwa ina Aminu ya isa ya kawo mata wannan karamar karuwar?
Gaisheta
sukai ta amsa, tana kallan Ibty tace “Amarya irin wannan kwalliya? Ina za’a haka?”
Aminu yai dan murmushi yace “Gida zata ta ziyara saboda makaranta da zata koma.”
Takaicin amsarsa ne ya kamata, wato harya fara bada amsa a maimakon ta? Ko batada baki ne?
Kallansu Islam yai yace “Ku tashi mu wuce saboda inaso na saukeku na wuce gun aiki.”
Hajiya na kokarin magana taga harsun mike, Ibty ce ta kalleta tace “Hajiya mu mun wuce sai anjima.”
Murmushin yake tai sannan ta rakosu, haka tana tsaye a kofa taga s
un shiga mota, suna tafiya ta kwararo wani dogon ashar ta zabgawa Ibtisam tare da maimaita kalamanta, Hajiya mu mun wuce? Ko ubanwa ya tambayeta oho. Da karfi ta makonkofa sannan ta koma ciki, zama tai ta baza tagumi tana tunani kodai ta canza malami ne? D
an da alama wannan malamin ya fara sanyi, ba abinda yai aiki tun bayan auran nan.
********
A kofar gidansu yai parking, mamaki ne ya kamata ganin ya bude boat ya dauko ledoji guda biyu, karasowa tai tace “Yaya na menene?”
Mika mata daya yai yace “Hak
a ake zuwa gidan da ba komai?”
Amsa tai ta bude, turaruka ne ne da irin body wash din nan na kwali, ya mika mata daya shi kuma kayan kwalliya ne, yace “Kya rabawa su Iman ko?”
Tayi mamakin jin yanda ya rike sunan Iman, kallansa tai tare da cewa “Angode A
llah ya kara budi, Yaya ni sai yaushe zaka kira nawa sunan?”
Boat din ya maida ya rufe yace “Randa kika bar tsoro?” Ya kamo hannun Ilham sannan ya mata alama dakai akan su shiga.
Baki tadan turo tanasan yin magana gashi a gaban yara ne, ganin yanda ta m
aida maganarta yasa yadanyi murmushi kasa kasa.
Shiga sukai, ba kowa a harabar gidan, har saida suka isa ciki.
Kwankwasawa tai daga cikin aka amsa sannan Iman ta karaso ta bude, idanu ta zaro ta saki wani wawan ihu tare da rungumo Ibty iya karfinta, sam
Ibty bata kawo irin rungumar nan ba ga hannunta dauke da ledoji, baya tai tana neman faduwa, da sauri Aminu yasa hannu daya ya taro bayanta, Iman sai a lokacin ta kula da abinda ta aikata, saketa tai tana dariya tare da yin alamun kunya na Aminu tace “Yay
a kayi hakuri ai bankula tare kuke ba.”
Ibty ta juyo ta kalleshi a hankali wani murmushi ya bayyana a fuskarta, hannunsa ya zare sannan yai gyaran murya yace “Da alama batada karfi ne shiyasa ta kusa faduwa.”
Iman tai dariya tace “Ah to mutum kullum jiy
a iyau ai dole ya fadi.”
Nan suka shiga ciki Ibty tana yima Iman rada na masifa a kunne.
Zama yai kafin Umma ta fito suka gaisa, farinciki ne a fuskarta sosai tace “Yanzu shine zakuzo Ibty bazaki sanar min na shirya tarbar siriki ba?”
Kallanshi tai tar
e damai alama ya taimaka yai magana, kai ya kauda yanaji Umma na cewa “Kedai wlh naga randa zaki daina wannan zurfin ciki? Da kunzo bama nan kuma fa?” Ibty ta sake kallansa kamar mai shirin kuka, daurewa tai tana neman abin cewa taji yace “Ninace karta fad
a saboda banasan daura muku wahala.”
Wani irin dadi ne ya kamata dan da ta dauka bazai kula ba, nan aka kawomai juice da ruwa, itakam tana makale kusa da Ummanta.
Iman ta fita da sauri dan sanar da Yaya Bilkisu.
Umar na mimike a falo yana kallan TV yan
ayi yanacin dubulan din ta na gara, dama duk sanda zai zauna a falo to fa ita sai dai ta koma daki, haka ya kafa mata doka dan yace ganinta kusa dashi tasar mai zuciya yake.
Iman kam cikin zumudi tana shiga falan cikin daga murya tace “Yaya Bilkisu kizo
ku gaisa da mijin Yaya Ibty, sunzo tare yanzun nan.”
Ai garin durowa daga kan kujera baisan sanda ya fado ba, mikewa yai da sauri ya matso kusa da Iman yace “Da gaske?”
Kallansa tai cikin mamakin yanda ya fado, badai haryanzu bai hakura ba?
Bilkisu ce
ta turo keke tace “Iman da gaske?”
Jikin Iman ne yai sanyi dan idanun Umar kadai zaka kalla kasan a rikice yake, daki ya koma ya canza kaya ya dau turare ya fefesa, sukam tare suka fito bayan Bilkisu ta rufa mayafi.
Comb ya dauka yana taje kansa yana wa
kar Babe ina kwana yanayi yana dan takawa. Fitowa yai yana cewa “Da alama daga nan bina zatai muyi wucewarmu.”
Falon ya nufa, suna zaune duka anata hira, yana isa yai sallama, gaban Ibty ne ya fadi da sauri ta kalli Aminu. Shima kallanta yai tare da yi ma
ta magana mara sauri yace “Uwar tsoro.”
Baki tadan turo tare da dakewa ta dauke kai