Showing 18001 words to 21000 words out of 128353 words

Chapter 7 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

9

tsada, kana iya hango vest din jikinsa ta cikin yadin, sanye yake da hula dark

brown kalar takalminsa, yayi kyau kwarai da gaske ga sajen ya kara fito da zatinsa da girmansa.

Motar ya maida ya rufe yana tunanin yaushe rabanshi dayazo zance? Wannan karan kuma Ummy wata samo? Sai murna take kamar ance yaune auransa, shikam yana mama

kin yanda Ummy ke san taga yayi aure.

A hankali ya karasa jikin kofar gidan sannan ya kwankwasa, daga can ciki Iman ta fito sanye da mayafi karami, dama tun dazu take gadi wai a dole ita zata fara ganinshi.

Bude kofar tai, Aminu cikin mamaki ya kalleta

amma dai ba wannan 'yar ficikar bace bako? Katseshi tai da cewa "Sannu da zuwa."

Kai ya daga mata kafin yace "Yauwa."

Shiga yai sannan tai gaba yabita a baya, kofa ta budemai na falo ya shiga. Kamshin turaren wuta ne ya fara dukan hancinsa, a hankali

yadan lumshe ido, sallama yak ta amsa sannan ya shiga ya zauna akan kujera, Iman ta wuce dakin Umma. Tana shiga tace "Umma! Yaya! Ya iso ya iso."

Bata jira me zasuce ba tace "Ammafa ya hadu sai dai Allah babba ne sosai dan cikin sajen daya tara harda fur

fura."

Yatsa Umma ta nuna ta dashi tace "Kinga ki fita idona, koma menene ki tabbatar kin nutsu bansan tsinanen rawar kan nan."

Umma ce ta fito da sauri yadan sauka daga kan kujerar ya gaisheta, cikin fara'a tace "Aminu ya Ummyn taka?" Cikin girmamawa

yace "Tana gaisheku."

Komawa ciki tai, sannan Bilkisu ta fito suka gaisa itama, tausayin yanda take akan keken guragu ne yadan kamashi, nan Iman ta kawomai juice da ruwa sannan tahau sama ta kira Ibty wacce tun farkon jin muryarsa suna gaisawa da Umma ta

ji gabanta ya fara dukan uku uku.

Iman ta shigo tana zolayarta, itadai batace komai ba.

Mayafinta ta dauka ta koma gaban madubi ta zauna tana dan maida ajiyar zuciya, dariya Iman ta saki tace "Ibty karfa kije saboda rikicewa maimakon kice ina wuni kice

ina kwana."

Bata tanka ta ba sai data gama sauke hucin ajiyar zuciyarta sannan ta fito, a hankali ta sauko kasa ta zauna daga can gefen bakin kujera, a hankali cikin dauriya tace "Ina wu..........."

Idanunta ne ya sauka akanshi, shima cikin tsananin m

amaki yake kallanta, kif kif tai da ido kafin tace "Ya Aminu?"

Kansa yadan karkatar kadan sannan yadan sa hannu ya gyara zaman farin glasses din dake kan fuskarsa, murmushi yai yace "Kamar kawar Ainah ko?"

Kai ta daga cikin mamaki sannan tace "Kaine ba

kon?"

Kunya duk ta rufeshi amma lalai Ummy, ta rasa da wacce zata hadashi sai kawar Ainah? Kasa magana yai itama tai kum ta kasa cewa komai.

Can dai ganin zaman nasu bamai cewa komai yasa tace "Amma Ainah bata sani ba ko? Naga munyi waya batace komai b

a."

Kallanta yai sosai yace "Ke saurin me kikeyi?"

Fuskarta dauke da mamaki tace "Saurin me?"

Ya kalleta sosai yace "Yarinyarki dake meyasa kike neman auran namijin da ya taba aure har yake da yara biyu?"

Kai ta girgiza da sauri tace "Ba sauri nake

ba, Abba ne yace zanyi bako."

Ya dan hade hannayensa yace "Baki tambayi girman bakon ba?"

A hankali ta daga kai kafin tace "Umma tacemin kanada yara."

"And?"

"Nace to."

"To kawai? Ya tambayeta yana kallanta."

Kai ta daga alamar eh, sun sake yin

shiru kafin yace "Yanzu sai ki sanar dasu na miki tsufa."

Tai saurin cewa "Ya Aminu sai dai kai ka sanar dasu Ummy ni bazan iya cewa Abba a'a ba……”

Kallan mamaki ya mata hakan yasa ta kasa karasa abinda take shirin cewa, yace "Baki damu da rayuwar ki b

ane? Taya yarinyarki dake zaki auri namiji babba wanda a kalla na baki shekara kusan sha takwas zuwa ashirin, sannan kizo ki fara kuka da yaran da ba naki ba? A shekarunki?"

Haushi yadan fara kamata, duk da ba so take ba itama amma sai wani zancen yarint

a da shekarunki yakeyi kamar irin 'yar shekara goman nan.

Kamar zata maida mai murtani sai kuma ta kasa dan tana shakkarsa sosai balle yanzu daya tattara hankalinsa kanta.

Kanta kawai tai kasa dashi tana wasa da hannunta, shikam ko Ainah bayaji zai bar

i ta auri sa’ansa, mesu Ummy ke tunani?

Shiru falon yai, a hankali tadan mike ta shiga kitchen dan kawomai abincin da aka shirya dominsa, kusa dashi ta dan turo centre table din sannan ta ajiye.

Tana kokarin mikewa yace “Badai sanda kikaje gida kinsan

abinda ake ciki ba?”

Kallansa tai idanunta suka dan canza tace “Allah bansani ba.”

Yace “To Meyasa ranar kikace na ajiyeki a gidan da ba naku ba?”

Da sauri ta kalleshi sai a lokacin ta tuna, cikin wani yanayi tace “Gani nai ga bakin hanya yafi sauki.”



“Saurayin da na gani yana jiranki fa?”

Gabanta ne ya fadi ta kalleshi kafin ta tattaro dauriyarta tace “Yaya nane, a gidan nan yake.”

Kai ya jinjina alamar gamsuwa, dan ya dauka ko auren dole ake shirin mata bayan tanada wanda takeso.

Mikewa tai

a hankali ta koma ta zauna, haryanzu bata dawo daidai ba, Aminu ya kalli abincin a zahirin gaskiya ya koshi kuma yana ganin ba dadi an shirya abu dominsa ya tashi ya tafi ba tare da yaci abincin ba.

Mikewa tai tace “Ya Aminu ko na zuba maka?”

Kai ya g

irgiza alamar a’a sannan ya dan bude kular?”, fried rice ce tasha hanta, ya zuba dan kadan a plate sannan ya zuba hadin salad din a gefe, bai dauke pepper chicken din ba yadan ci kadan sannan ya ajiye plate din, mikewa yai yace “Zai wuce.”

Ta mike itama

tana kokarin sanar da Umma zai tafi, tana kokarin shiga dakin taji yace “Ki sanar dani daga yau zuwa gobe inhar kin janye maganar auren, in kin kasa musu magana ni zan sanar dasu.”

Ta kalleshi tace “In fadawa Ainah?”

“Ainah kuma?”

Tace “Banida numberk

a bansan ta yanda zan fada maka ba.”

Hannu yasa a aljihunsa ya dauko wayarsa ya mika mata, a hankali ta tako tazo inda yake ta amshi wayar.

Hotonshi ne shida Aunty Na’imah a jikin alan wayar, da alama daga jikin hoton takarda aka dau hoton, murmushi ta

i sannan ta saka number tai dialling sannan ta kashe ta mikamai.

Kallansa tai a gabanta taga ya rubuta “Kawar Ainah.”

Samun kanta tai dacewa “Sunana Ibtisam.”

Kai ya daga bayan yasa wayar a aljihu yace “Na sani.”

Juyawa tai ta kira Umma aranta tace

“Ai sai ka canza kasa sunana.” Umma ce ta fito nan sukai sallama, yaba Iman dubu biyar, sannan bayan ya fito mota ya ciro ledar da Ummy ta bashi yaba Iman yace “Ki ba yayarki inji Ummy.”

Nan ya juya ya tafi yana mamakin wannan lamari…….

Ita kanta Ibty d

aki ta wuce ta fada kan gado tana mamakin wannan abu, tana ganin kiran Ainah amma ta kasa dauka yau kam batasan da wacce zatai gulmar ba dan bata isa tayi da Ainah ba da alama ma Ummy bata sanar da ita komai ba.

********

Ganin yanda Abba ke ta murn

a yasa Ibty ta kasa cewa a’a kuma harga Allah dama bata tsani Ya Aminu ba, bata sanshi kuma bata tsaneshi ba.

Shikam Aminu sai jira yake yaga text dinta ko kiranta akan ta fasa ya mata girma sai dai haryau babu ko flashing dinta.

Shi kuma yana ganin yay

i girman da bazai kira yarinya karama yana tambayarta ra’ayinta akanshi ba.

Ganin yanda Ummy keta shirin hada lefe yasa duk ya rasa abin yi, gashi duk wannan abin da ake haryau Ainah bata sani ba.

******

Ibty kam a skul duk yanda Ainah ke binta akan t

a bata labari taki, har ta gaji ta daina tambayarta.

*******

Yau tafiyar Umar kwana biyar, a yau kuma Ummy ta sake turo Aminu yazo zance da daddare, sannan su kuma gobe suke sa ran kai kayan lefen da suka hada cikin gaggawa.

Umar ya gaji da kauyen na

n ko ince ya gaji da rashin Ibty, da safe ya shirya tsaf yana san tahowa, yana shiga dakin mahaifiyarsa ya tadda ita a kwance ba lafiya, ashe tun daren jiya take amai da gudawa. Wannan lamari yasa dole ya fasa tafiya a wannan ranar, haka suka kira likita y

azo ya daura mata drip a cikin gida.

*******

Ummy yau ta samu kanta da samun shawarar data kara kwantar da hankalinta, Baffa na shigowa bayan yaci abinci sunyi sallah tace “me kake tunani in muka katangewa matar can bangarenta? In har bazamu iya korart

a daga gidan ba ai zamu iya raba gidan da take ciki da inda Aminu da Ibtisam zasu zauna.”

Baffa dadin wannan shawarar ya kamashi yace “Ya akai wannan shawarar bata taba gifta mana ba?”

Ummy tace “Da alama alkairi ne yake binmu a wannan auren haka kawai

daren jiya wannan shawara tazomin, ku katangeta a fitar mata da kofarta ta waje, duk masifa da bala’inta ai sai ta shiga cikin gidansu ko? Kuma duk rashin hankalinta bazata dinga afka musu gida ba, dan dama Aminu bai bari tana shigar mai gida

ba kaga in ta

ga an barta ita kadai zata gaji tabar gida, balle in taga Aminu yana rayuwar farinciki da matarsa.”

Wannan shawara ta musu dadi, Baffa ya sanar da Aminu kuma shima bai musa ba dan shi dama damuwarsa bazai iya barinta bane, alkawari ya dauka yana ganin hak

kinsa ce ya kula da ita.

*******

Ibty tayi zugum a daki tana tunanin yanda zasu kwashe yau da daddare in Aminu yazo, gashi Umar ya isheta da kira, number number, kwanciyar hankalinta kawai ta kashe wayarta gaba daya, dan batasan me zatace mai ba bayan

an riga anba yayarta shi, sannan tana sa ran tunda dai Yaya ba fita take ba Umar zai kula da ita……..

Hmmm

Ayusher Ce

🏌🏻

‍♀

️

[1/26, 9:32 PM] Fav

♡♡

:

💫

IBTISAM......

💫

(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i

̝

o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*Free Page*

Ki hanzarta ki mallaki naki dan Free Pages sun kusa karewa

🤸🏻

‍♀

️

*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA

DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*

*SAI YA TURA 500 TA* *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

Page 9

Girgizashi yai yac

e "Umar ka dawo da hankalinka nan, kai baka tambayi yarinyar da aka ce an baka bane? Koni magana ta gaskiya kunnena abinda yajimin kenan auran Umar da Bilkisu."

Fizge jikinshi yai yana huci ya nunashi da yatsa yace "Yaya Naziru karka batamin rai wallahi

in raina ya baci ba abinda bazan iya aikatawa ba, uban waye zai sani auran wata a duniya inba Ibtisam ba Yarinyarnan mata tace tun farko kuma wlh duk wanda ya nemi shiga tsakanina da ita zan iya mai ila."

Shi kanshi Naziru ya tsorata da yanda Umar ke mag

ana, a tsorace ya sakeshi yana kallan yanda yake wani huci, Umar ya kalleshi yace "Bari naje gun Abba ko shi limamin sai ya sanar dani meke faruwa."

Naziru kam ya fahimci lalai akwai matsala da sauri ya juya ya nufi inda Kawunsa yake cikin mutane, shikan

shi Kawun jikinsa duk yai sanyi kawai dai yana yake ne cikin mutane amma yasan tabbas akwai matsala. Yana hango Naziru ya nufoshi da sauri yace "Ina Umar?"

Naziru jiki a sanyaye yace "Ya tafi neman Abba ko Liman."

Shafar fuskarsa Kawun yai yace "kafin y

aran nan ya sa mutane sumana kallan mahaukatan kauye kajashi ya bat gun nan."

Cikin damuwa Naziru yace "Matsalar yaki tsayawa ya saurareni, bansan ya zanyi ba Kawu."

Da sauri Kawun ya shiga neman Umar a cikin mutanen, masallacin ya nufa dan yafi kokont

an can zaije, yana shiga kuwa ya hangoshi a tsaye da alama mutanen dake durkushe kusa da limamin, da sauri Kawu yasa hannu ya rikoshi suka fito.

Umar gaba daya ya firgice yace "Kawu tambayar liman nake san yi me yasa yace ya bada auran Bilkisu gareni? In

ma kuskure yai ya dawo ya kira mutane a sake daura aure."

Kawun ya jashi can gefe yace "Umar bansan meya faru ba tsakaninka da uban rikonka, sai dai tabbas shi Bilkisu ya baka, sai dai in kaine baka tsaya ka fahimceshi ba, bayan an daura aure dakanshi a

masallaci yace "Yaya nikam Umar ya gamamin komai tunda ya amince da auran Bilkisu."

Rai a bace ya nuna kansa yace "Ni? Wlh cutata akai ni ban taba kawo auran nakashashiya ba, Kawu Allah cutata yai, bakuma zan yarda ba, duk bala'in da za'ai sai dai ayi am

ma ba wanda ya isa ya rabani da Ibtisam."

Baiko tsaya jin me Kawu zaice ba ya wuce ya fara tafiya ransa na wani irin kuna, motar da su Aminu ya kalla wacce yaganshi dazu ya iso a ciki, a kufule ya dau dutse ya kalli gefe da gefe ganin gun ba mutane kawai

ya buga gaban motar iya karfinsa sannan ya wuce. Karar glass din motar da mutane sukaji ne yasa suka juya, shikam adaidaita ya tara kawai ya shiga.

Ganibyai mai adaidaitar baya sauri cikin bacin raj yace "Kai Dalla malam kajani da sauri wannan tafiyar k

amar wani dan koyo? In kasan baka iya ba uban wa yace ka fara sana'ar?"

Wannan magana ta batawa mai adaidaita rai gashi shima dama ba hakuri gareshi ba, parking yai a gefen titi yace "Kai bansan hauka da iskancin, tashi sama kake so nai ko me? In shaye s

haye kai kaje can ka sau........" Ai Umar ya gama kaiwa wuya cakumo kwalarsa yai ya daga hannu yana neman kaimai duka, shima mutumin ya cakumo wuyan Umar, ganin baisan bata lokaci yasa ya sakeshi rai a bace ya fito ya tari wata, gaba daya huci kawai yakeyi

.

********

Gida kam ya cika sosai da mutane anata hidimar yin abinci an sauke wasu ana daura wasu, a daki kam Ibty tana zaune ita da kawayenta 'yan uwa sukaji ana

guda ana cewa an daura, sanye take da wani hadaden lace wanda Abba ya dinka musu ita da

Yaya Bilkisu iri daya, sunyi kyau iya kyau ga dinkin ya karbesu, Iman dama ta iya makeup ita ta zane musu fuskarsu, sunyi kyau sosai abinsu.

Bilkisu tana kasa cikin mutane su kuma suna sama anata hira, itakam sam batajin dadi haka kawai takejin jikinta ka

mar mai zazzabi, Ainah ce ta kirata dagawa tai tare da dan matsawa gefe tace "Ainah!"

Ai Ainah bata amsa ba tace "Ibty yau naga abinda ya hanani sukuni, wai yau ake daura auran yayana amma ba wanda ya fadamin?"

Dan idanta Ibty ta runtse tace "Ainah maga

nar gaskiya......."

"Ibty kinsan abin dariyar? Sunanku daya da amaryar."

Yawun bakinta ta hadiya tace "Ainah wai nice amaryar."

Ainah bata fahimci me take nufi ba tace "Kece me?"

Kiran da aka kwalla ma Ibtisam ne yasa tace "Zan kiraki anjima" bata

jira me zatace ba ta kashe wayar, fitowa tai daga dakin, kanwar Umma ce ta kalleta tace "ki sauko mai hoto yazo."

Kai ta daga sannan ta koma ta dauko mayafin kayan sannan ta sauko, sun tsaya kenan ana shi shiryawa za'a dau hoto tundaga wajen harabar gida

n sukaji ana kwallawa Ibtisam kira cikin kakkausar murya, gabanta ne ya yanke yai wani irin faduwa balle dataji muryar Umar, me yake yi hakan? Ta dauka dai yanzu komai ya wuce ko?

Kafafunta ne suka dan fara rawa jin yanda yake kiranta kai tsaye kuma kana

ji kasan muryar bacin rai ce.

Gaba daya mutanen falan mamaki ne ya kamasu, Umma ta mike cikin mamaki tace "Umar lafiya kuwa?"

Suna kokarin fitowa ya shigo cikin falan, ya cire babbar rigar ya rike a hannunsa, bai damu da taron mutanen dake falan ba ci

ki kuwa harda mahaifiyarsa, idanunsa kawai ya sauke kan Ibtisam yace "Ibty meke faruwa?"

Kallansa tai gaba daya ta kasa magana sai rawa da jikinta kawai yakeyi, takowa yai yazo inda take yanayinsa ya canza sosai cikin tsawa yace "Meke faruwa nace?"

Bay

a tadanyi gaba daya jikinta ya kasa daina rawa, cikin fada mahaifiyarsa tace "Umar me kakeyi hakan? Bakaganin manya ne? Ko sallama da gaisuwa bakai ba kazo ka tsareta kamar 'yar cikinka."

Kallan Goggon yai ji yake kamar yai ihu, wani mugun kallo ya zabga

wa Bilkisu sannan ya kalli Ibtisam yace "Wuce muje ki fadawa Abba dani za'a daura miki aure kafin ranki ya baci a cikin gidan nan."

Jin wannan kalmar yasa gaba daya matan dake gun suka sauke salati, Umma cikin tsananin mamaki tace "Mene? Umar me kake cew

a?"

Ibty kam zubewa tai a kasa kawai jikinta na rawa, ta kasa ko magana balle hawaye.

Umar ya kalli Umma yace "Ibtisam nake so kuma ita tafi kowa sanin tsawon lokacin dana dauka ina santa akan me za'a dauramin aure da Bilkisu?"

Nan fa falo ya kara ri

ncabewa gaba daya kowa yahau salati ana kallan ikon Allah, yau meke faruwa a gidan nan? Umma kam ta kasa ko magana sai kallan Umar da takeyi.

Shikam ko a jikinsa ya kalli Ibtisam yace "Bakiji nace ki tashi ba?" Yai maganar yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login