Showing 117001 words to 120000 words out of 128353 words

Chapter 40 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

12

zakasan hankalinta a kwance yake, dan a skul ma kawayenta tsokanarta sukeyi Ainah sai tai

dariya tace “Yayana ne da alama ya iya kiwo.

Tana zaune a falo tana juyawa su Islam taliya wacce tai fara da vegetable soup yasha kayan ciki sai kamshi hake, nan sukaji sallamarsa. Atare duk suka waiga ganinsa yasa Islam da Ilham rugawa da gudu suka rung

ume shi, yana murmushi yana kallansu, ya kasa shafa kansu saboda kayan da ya riko. Ibty ta karaso ta karbi na hannu daya, tana neman zame hannunta taji ya rike hannun, cikin kunya tamai alamar su Ilham da ido, saketa yai tare da shafar saman kan su.

"Inye

ee me za'aci haka.?"

"Taliya." Ilham ta fada tana dariya.

"Uhmmm da alama kuna so ko?"

"Mune mukace a dafa mana, Dady daga yanzu wannan shine best abinci na.” Ilham ta fada tana dariya.

Ya kalli Ibty yace “Da alama Mumy ta iya abinci ko?”

Kallan sa su

kai sannan suka kalli Ibtisam da sauri.

Mumy? Suka tambaya

Ya kalli Ibtisam yace “Bakwa santa a matsayin Mumy dinku?”

Kallan juna sukai, yace “shikenan bari ta koma gidansu inyaso ku sai ku cigaba da zama daga ku sai ni.”

Kai suka girgiza da sauri suk

a karaso suka rungume Ibty, Islam tace “A’a dan Allah Dady.”

Yace “Gashinan ku zaba in ba Mumy bace ta bar muku gidan.”

Ilham ta kara kankameta tace “Mumy!”

Idanun Ibty ne suka danyi raurau ta sunkuyo ta rungumesu a jikinta tace “Ilham!”

Itama Islam ta

dago tace “Mumy!”

Kam ta rikesu a jikinta bata fargaba sai kwalla taji, Aminu ya kallesu cike da sha’a.

Mikewa tai suka kalli juna sosai kowanne da abinda yake ransa.

"Sannu." Cewar Ibty tana kallansa cikin wani yanayi.

"Maza kuje kucigaba dacin abinc

inku, bari na kai kayan nan kitchen." Ibty ta sake daukar ledar kan table tayi kitchen, shi kuma ya nufi dakinsa da dayar ledar, ganin haka yasa batace zata karba ba tasan kayan bana kitchen bane. Sai da ta gama ware komai tasa a inda ya dace kafin ta dakk

o wanda zata bawa yaran ta aje gefensu sannan ta nufi dakin Aminu.

Bata ganshi ba sai dai taji alamun zubar ruwa a cikin toilet, ta dinga baza idanu ko zataga inda ya ajiye ledar amman babu, ta daga kafadu ta fice da nufin ta dawo bayan yan mintuna.

Ami

nu yana fitowa jallabiya ya janyo maroon yasa, sannan ya hau kan sallaya yagabar da sallar la'asar, yana addu’a yaji sallamarta yana kallanta ta sake shigowa ta zauna a bakin gado tana jiransa har ya shafa sannan ya juyo ya kalleta.

"Ban rokar miki kishiy

a ba dan naga kinki shafa addu'ar da nai." Zaro ido tai tace “Ni cewa nayi ka roki kishiya? Kuma ko ita ka roka ai bana tsoranta tazo mana." Aminu ya tashi daga kan sallayar ya karasa inda take ya zauna gefenta.

"Ina da budurwoyi fa karki cika baki naje n

a zabo daya." Nan da nan ta hade rai ta kauda kanta gefe, hannunsa ya shiga irgawa kafin yace “Acikinsu na tambatar kowace nawa magana……

Yanda ta sake kallansa fuskarta kamar wacce aka turowa sakon mutuwa ne yasa shi yai murmushi yana kamo mata hannu tare

da lankwasa yatsun ta, tadan daure dan batasan magana, jin zafin yana ratsata yasa ta fara yar kara.

"Ashh! Ahhh!! Washhh...!!!" Hannu yasa ya janyota jikinsa yana cewa.

"Kina ihu sai yaranki sunji? Kuma idan suka ganki anan ai ni zasu zarga, ko suce n

a bugar musu Mumynsu.”

"Gaya musu kuma zanyi ba." Ibty ta fada cikin shagwaba tare da yar harara.

"Kice musu mene?"

"Zance zaneni kayi mana, ince ma da bulala…”

Ido ya zaro yana kallanta, nan ta juyar da kai tana dariya a hankali.

"Shikenan tunda shar

ri zaki min, yanzu anyi abincin dani ko kuwa naje naci a waje? Dan naga yau fitina akeji.”

Juyowa tai tare da turo baki tace. "Salan kaja min zagi, ace kana da mata amman kana fita waje cin abinci?"

"To ai gani nayi baki min tayi ba, shi yasa na kama ka

fa biyu nace in babu na fita waje."

"Taya zanyi abinci bakai?” Cewar Ibty cike da jin haushi.

"A falo za’a bani? Konan zaki zo ki ban?" Kasa cewa komai tai sai tashi da take kokarin yi, hannunsa ne a sakale a kugunta, tadan sake yunkurawa nan ma ta kasa

kwacewa. Ganin yanda take fizgewa yasa shi sakinta ta fita shi kuma ya dafe goshi. Kodai be iya soyayya bane? Shin menene ya fada na rashin jin dadi a maganarsa? Sai ya tuna Na'ima itama haka take fushi idan yace zaije gidan Ummy yaci abinci bayan kuma yas

an tana dashi a gurinta, amma shi ai zolayarta yake.

Tashi yai tsaye ya cire jallabiyar yabar singlet da three quater a jikinsa, gefen gado ya zauna bayan ya dakko laptop ya kunna. Ibty ta shigo rike da tary kallo daya tai masa ta dauke kai sakamakon yadd

a taji zuciyarta ta harba, wani irin yanayi na bazata yai mata. Sosai ta lura da cewa tsarin halitar Aminu kadai kan iya sanya mace fadawa tarkonsa musamman irinta da take da feeling akanshi.

Fuskarta a tsuke tace “Yaya ga abincin nan." ya kalleta shim

a sai ya tsuke fuska yace.

"Nan zanzo naci ko kawo min kusa dani zaki yi?" tayi shiru kamar mai nazari, sai kuma ta dauka ta karasa kusa dashi ta ajiye “Yaya…..."Ta kira sunanshi tana dauke hannunta daga kan tire din, yana ji yai mata banza saboda yaga al

amar zata fara rainashi, haka kawai daga dan zolaya sai wani hade rai take? So take hala yai ta lalabata tana wulakantashi.

"Yaya." Ta sake kiranshi, Aminu ya dago daradaran idanunsa ya zuba mata su, tai saurin dauke nata ta maidasu kan gado.

"Wai ni me

nai maka kake fushi dani?” Mamaki ya kamashi, lallai yarinyar nan ta mugun raina masa wayo, har ta manta ita ta fara yin fushi ya gani.

"Yaya nidai to ka ajiye aikin kaci sai ka karasa idan ka gama."

Ya rufe laptop din ya tsaya yana kallanta. Matsawa ta

yi sosai ta zuba a plate sannan ta fara bashi a baki, yana ci yana kare mata kallo, ita dai tunda ta fuskanci idanunsa yana kanta sai taki bari su hada ido har yazo spoon din karshe sannan ya rike hannun ya juyar dashi saitin bakinta yace.

"Cinye shi." Da

yake sulhu take so sai batai gaddama ba ta bude bakin yasa mata.

Cikin dan shagwaba tace “Ka huce?”

“Shiru yai kamar mai nazari sannan ya nuna kansa sannan ya nunata yace “Nine nake fishi ko kece kike fishi?”

Tadan rufe ido sannan ta bude idonta daya g

anin yana kallanta yasa tace “To ai kaine wai zakaje kaci a waje.”

“Kinga dai kece mai fishin bani bako?”

“To ai na sauko.”

“Aka ce min Yaya?”

Labanta ta rufe a tare tace “Sry Habiby Allah mantawa nake saboda su Islam, ni dai dan Allah kabarninnace ma

Yaya.”

Kuncinsa ya nuna fuskarsa a daure ajiyar zuciya tadanyi sannan ta sumbaci kuncin nasa, tana kokarin zama ya nuna mata daya kuncin, sake dawowa tai ta sumbata, zata sake zama ya nuna kan lebansa, kamar zatai kuka ta sumbata, gani yai ta tsaya bata

xauna ba, ya kunshe dariyarsa ya dau glass dinsa ya saka yana neman shan ruwa.

“Aikin soja kika koma?”

Ta xauna tace “Wai shi wannan punishment din sai nazo zan zauna ake yinsa?”

Ajiyar zuciya yai yadan kalli glass din hannunsa yace “Dazu kin kusa karya

min hannu gaba daya banajin hannun nan na aiki.”

Tasan ruwa hannunsa yakeso ta amsa, amsa tai sannan tace “Yaushe na taba maka hannu amma?”

Kin manta sanda kika sani lankwasa miki yatsu?”

Dariya ta kwashe dashi tace “Kenan ai hannuna ne zaiyi ciwo ko?”

Kai ya girgiza yace “Nawa dai da nai aikin.”

Tana kallansa tace “ Kaifa kai bani na saka ba?”

“Still dai….”

Yaya kenan, shi gaba daya zamansa zolaya ne, shiyasa yanzu gaba daya ya gama shiga zuciyarta sam intana tare dashi bata tunanin komai……

*Ayusher ce*

🏌

️

‍♀

️

💫

IBTISAM......

💫

(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

*mg's skincare*

Shin Ina matan suke

🗣

️

🗣

️

🗣

️

maza

kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi

😃🤩

Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da i

ngantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum

👌

haki

ka duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbat

ar

❣

️

Shin kinafama da

Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?

Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki

😫

Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister

's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy

🤗

ga amare uk wnd yy using bridal se

t dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind

Bridal kit:18k

Beauty kit:11k

Student package:7k

Herbal whitening soap:3k

Chat

08062991549

07046881166

07067210195

Call 08064532391

Facebook: mg

's skincare

Instagram:glow_with_mgs

Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa

🤝

Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go

🤩

Then @mgs skincare gat you covered

💯

Now is time to glo

w

😍

Pamper ur skin

🦵

Shine like bride

👰🏻

‍♀

Glow

🧖

‍♀

️

💯

tested nd trusted

🤝

Guarantee

*48*

Ajiyar zuciya tai ganin yadan mike tsaye, ina zaka?

Yadan dau glass dinsa dake gefenta yace “Gida zanje, amma bazan dade ba.”

“Muma zamuje dan Allah

!”

Kallanta yai yadauko riga yana sawa yace “Yawo ko?" Ibty ta sunkuyar da ido.

"A'a ba yawo bane ba rakiya zamuyi please." Aminu ya juyo tare da sa hannu yadan dagota, samun kanshi yai da rungumeta, yau jinsa yake tamkar wani sabon ango, ga wata muguwar

sha'awa da take bijiro masa tamkar be taba kusantar mace ba.

"Ku shirya amman ba gidan Ummy ba." Kallansa tai tare da lumshe ido.

"Jeki shirya su Islam kema kisa hijabi." Ya saketa ita kuma ta fito tana hadawa da gudu dan tasan idanunsa yana kanta.

"Ki

ds maza kuzo na shirya ku." ta fada tana tattare gun da suka ci abinci.

"Aunty Ina zamu?” Ilham ta tambaya cikin zumudi.

Kallan Ilham tai tare da dan yin wani iri da fuskarta, dariya tasa tace “Mumy ina zamu?”

Cikin jin dadi tace “Idanunku zasu gane muk

u, oya ku tashi muje daki, kafin ace an fasa zuwa damu.”

Da gudu suka tashi da sauri tabi bayansu. Kaya ta zabo musu iri daya riga da skirt masu kyau, ta saka musu ta gyara musu fuska kowacce ta dauki handbag din ta sannan tace su jira itama taje ta shir

ya. Doguwar riga tasa purple ta zauna a jikinta das sai tai wani irin kyau na musamman. Mayafin rigar tasa akanta ta yafa sannan ta janyo farar jaka tasa abubuwanta, ta dakko sneekars tasa tayi kyau sosai.

Tunda ta fito Aminu yake kallanta, shi kansa yasa

yanzu ne yai aure ya matsa kusa da ita yana jin kamar ya sakata a cikinsa.

"Watabarakallahu ahasanil kalik." Aminu ya fada, Ibty ta kalleshi.

"Yaya! Magana kayi?" Hancinta yaja tare da girgiza kai.

"Nace duk wannan kwalliyar fitar ce?”

Tadan yi raurau

tace “Ace nayi kyau ne ba’a san fada?”

Hannayensa biyu yasa a aljihu yace “Muje ko?"

Su Ilham ta kira suka fito tare, baya ta bude suka shiga ita kuma ta koma gaba, Aminu ya shiga yaja mota suka wuce.

Gani tayi sun dauki hanyar gidan su, tai saurin ka

llan Aminu cike da farin ciki ta dafa cinyarsa.

"Gida?”

Kai ya rangwafar yana tukinsa, dadi ya kara rufeta tace “Wayyo dadi yau zanga Umma."

"Is for you."

Kunya tadan kamata tace “Nagode”

Tadan rage magana cikin alamar rada tace “Habiby.”

Sun isa gid

an yai parking farinciki ya kasa boyewa a fuskarta.

Umar ya fito da alama fita zaiyi ya hango mota, basai an fada ba yasan motar waye, yana tsaye yana kallansu har sukai parking. Shi kuma Amin tunda ya hango Umar sai ya hana Ibty fita, ya kalli su Islam y

ace su shiga ciki, shi kuma ya fito ba tare da ya kalli inda Umar yake ba.

Kofa ya budewa mata tare da mika hannunsa alamar ta kama, sarai tasan saboda Umar yai hakan, kunshe dariyarta tai a hankali itama ta dora hannunta saman tafin hannun Aminu ta fito

cike da takama da kasaita. Umar na ganin haka ya zabura a fusace zai nufi inda suke yaji ya dunkule hannu kamar mai shirin dambe, ya nufo gub kai kace an taba matarsa.

Daga gefensa yajiyo muryar Abba, da sauri ya fara dan fifita da hannunsa alamar zafi d

a alama so yai yaje ya naushi Aminu.

"Juya min mota zan fita." Abba ya fada yana mika masa key din hannunsa.

Hannu yasa ya amsa cikin ladabi kamar gaske, Abba ne ya hada ido dasu Ibty nan danan ya fadada murmushinsa, da sauri Aminu ya saki hannun Ibty ta

re da san matsawa daga jikinta yana shafa bayan kansa, murmushi tai dan yanda yai ya bata dariya sosai, Abba ne ya karaso ya mikawa Aminu hannu suka gaisa, Ibty itama ta gaisheshi.

"Kushiga ciki mana? sannunku da zuwa." Umar ganin yanda Abba yake kishi ya

kara kamashi, tahowa yai kamar yana waya ya bugi kafadar Aminu ya wuce. Abba na gani sai dai be ce komai ba hakan kuma ya tabbatar masa da cewa Umar na rike da Ibty a ransa sabannin abinda yace masa.

Bayan sun shiga sun sake gaisawa Abba yai musu sallama

yana sane yace da Umar ya tuka shi su fita tare, dan yasan indai ya barshi za'a samu matsala a gidan.

Aminu kam a gidan ya barsu, sai da akai sallar isha sannan yaje ya dakko su suka koma gida. Da yake sunci sun koshi hakan yasa yaran yin bacci da wuri.



Tunda suka dawo ya kule a daki yana kallan youtube da karatu akan yanda ake soyayya, duk abinda ya gani sai ya girgiza kai yace Da girmana? Wannan abin yara ne, sai ya canza ya fara duba wani. Ganin dai bazai iya ba kawai ya kashe wayar ya dauko ledar d

azu ya fito.

Bayan tayi shirin kwanciya sai kawai taga Aminu ya shigo rike da leda, mika mata yai ta karba tana jiran karin bayani taji yace

"Kisa fararen kizo bedroom dina." Yana fada mata yabar dakin. Ibty tai saurin zazzage ledar ta fara daga kayan

a hankali, duk na bacci ne kuma babu na mutunci a ciki.

"Wayyo Allah na wannan zansa? Nashiga uku." Ta fada tana zama a bakin gado. Taya zata iya zuwa ya ganta cikin wannan arnayen kayan? Waye ya bashi wannan shawarar ta siyan su? Wayyo ita kam kunya tak

eji.

Ta dade tana shawara ganin lokacin yana korewa dare yana kuma yi yasa ta ritsa ido ta dauki fararen tasa, riga ce half vest da dan mitsitsin skirt wanda ko mazaunanta ba zasu rufe ba, tana gama sawa ta isa wajan madubi yadda kasan kareena Kapoor a be

ach ko ince irin ‘yan duniyan nan ansha bikini.

Zani ta janyo ta daura akai tasa hijabi ta nufi dakin nashi.

Tana murdawa ta ganshi a tsaye a bakin kofar, sai dai yana ganinta ya tsuke fuska, fuskarsa a hade yace

"Islamiya zaki?" Tai saurin kallansa ta

ga yana mata up and down.

Tace “Islamiya?”

Juyawa yai ya wuce gado ya kwanta tare da janyo laptop da alama ta bata masa rai. Ibty ta hadiyi yawu a hankali ta kashe wutar dakin tabar wutar dake kunne a gefen gado, ta rufe ido tare da cire hijab din tana

kiransa.

"Yaya.." Aminu yai mata banza, ta bude ido taga ko kallanta bayayi idanunsa ma a rufe suke kamar mai bacci.

Zanin ta cire tare da fashewa da kuka ta tsugunna a kasa ta rike kafa.

"Habiby please..." Jin sautin kukanta yasa shi saurin mikewa ya n

ufo inda take riketa yai cikin tsananin kulawa zaiyi magana yaga tana kallansa tana dan murmushi, kallanta yai sosai nan ya ganta cikin kayan. Saurin kawar da fuska yai sakamakon wani irin abu da yaji yayi masa yawo lokaci guda.

Daurewa yai a hankali ya d

ago fuskarta, idanunta a lumshe taji yayi mata wata kyakkyawar runguma a faffadan kirjinsa. Sake dagota yai yana kallanta kafin ya maida fuskarsa saman kirjinta, luf tai, tanajinsa ya daga ta ya kawota kan gado kafin a hankali ya sa fuskarsa kan hancinsa,

nan ya karaso ya kai bakinsa cikin nata……

(Mukam daga nan mukai waje

🤸🏼

‍♂

️

🤸🏼

‍♂

️

🤸🏼

‍♂

️

)

******

A can gidansu Umar kuwa basu dawo ba sai magrib lokacin har Ibty ta tafi, haushi duk ya kamashi dan ko kwakwaren kallo bai mata ba.

Bangarensa ya nufa, ya

na shiga yaga Bilkisu akan kekenta tana zaune a falo tana kallo, tana ganinshi ta fadada fara’a wani takaici ne ya kamashi amma ya zaiyi? Haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login