Showing 99001 words to 102000 words out of 128353 words
yasha kayan hadi. Kamshi ne kawai yake tashi, har dinning ta kawo sannan ta nufi dakinshi ganin baya falan.
Amin
u kam yana zaune hannunsa rike da waya yayi shiru yana kallo, sai dai a zahiri addu'oi ya bude yaketa karantawa a ciki.
Sallama tai kanta na kasa bakinta dauke da addu'ar neman tsari, dagowa yai ya kalleta da sauri ya juya kansa gefe yana maida wani abu d
ake taso mai, tabbas ya kula abin baya tashi sai ya kalleta.
Gaban madubi ta dan tsaya, ta juya baya tace "Abinci Yaya."
Jikinsa ne yai sanyi badai itama ta fahimci baya san kallanta ba? Da bai kula ba amma yanzu yaga alama tabbas ganinta ne bayasonyi.
To kawai yace taje juyawa ta fita hannunta ya bigi hotonsu wanda yake kan madubi shida Na'imah.
Ji kake rasss glass din hoton ya fashe, gaba daya hankalinta ne ya tashi ta dago ta kalleshi, a tsorace take dan ta gama shirya fadan da zatasha yanzun nan.
Saman kansa yadan dafa da yaji kamar baya gani sosai, hannunsa ya murza a idanunsa yadan lumshesu, magana yakesanyi amma sam ya kasa saboda dum din dayaji a kanshi.
Da kyar ya mike tana nan tsaye ya wuce ya nufi bandaki, Ibty kam gaba daya dana sani da h
aushin kanta ya isheta, haka ta dauko abin shara, tana daga takardar hoton wani abu ya fado a jiki, kamar takardace sai dai an yi mata wani nadi mai kama da la ya, kamshin da dakin yakeyi wanda ta dauka daya daga cikin turarensa ne shine taji yana tashi da
ga jikin wannan takardar.
Mamaki ne ya dan kamata ta bude takardar tare da kallan wani rubutu a jiki duk ya dan koke baka ganin abinda aka rubuta sosai, sai dai rubutu ne mai kamada na larabci, sannan kamshin har hawa kan mutum yakeyi, tsoro ne yadan shi
ga ranta nan ta fara addu’a tana kallan takardar sosai, sake hude ta ciki tai shima rubutu ne a jiki sai dai wannan karan kamar da biro akai shima ba’a gani sosai.
Ido ta kura tana san ganin me aka rubuta sai dai bata gane komai ba sai sunan Aminu da haku
ri dataga ansa a jiki.
Shiru tai tana kallan takardar tabbas wannan takardar tayi shekaru anan, sannan bataji Hajiya tana shiga dakin Aminu balle hartai wannan ajiyar, badai Na’imah……
Kai ta girgiza da sauri tare da cewa zato zunubi sannan Na’imah banaj
i irin mahaifiyarta ce.
Dauko abin shara tai ta gyara gun sannan ta kalli toilet wanda haryanzu Aminu bai fito daga ciki ba, kamar zata nufi toilet din sai tace “in kuma bayan gida yake ba?”
Nan ta fita daga dakin ta tafi bangarenta dauke da takardar t
ana ta sake kura ido dan san karanta me aka rubuta.
Ganin har magrib Aminu shiru yasa ta nufi dakin, mamaki da tsoro ne ya kamata ganin haryanzu baya dakin, cikin dan hanzari ta nufi bandakun ta tsaya tare da kwankwasawa.
“Ya Aminu?”
Shiru kakeji ba ma
gana, “Ya Aminu?”
Nan ma shiru, cikin tsoro tadan bude kofar, zabura tai tare da sakin wani ihu ganin Aminu a kwance a kasan bandaki, da gudu ta karasa ciki ta dan dadage karfinta ta dago kanshi, dan jijigashi tai cikin tashin hankali take kiran sunansa s
ai dai sam baya motsi.
Wayarta ta fito ta dauka ta kira Ummy tana kuka ta sanar da ita, dan itakam ta dauka ma mutuwa yai ganin ko motsi bayayi.
Ummy tashin hankalin data shiga mara musaltuwa ne, nan ta fito sanye da hijab din datai magrib, Baffa na fal
o ta tasoshi suka fito cikin tsananin tashin hankali.
Tun a hanya kawai addu’a takeyi duk tsoro ya gama kamata, gani take kamar abinda ya faru ne Hajiya tamai wani abin ko kuma raine yai halinsa, gashi basu daidaita da d’an nata ba.
Ibty kam kuma kawai
take tana xaune a bandaki sam ta manta a inda suke, kuka kawai take tana jijigashi.
Gaba daya tama rasa me akewa mutum a cikin wannan yanayi, buga kofa taji cikin rawar jiki ta mike ta nufi kofa, tana budewa Ummy da Baffa suka shigo duk a rikice, nan suka
dungume bandaki, Baffa ya dagoshi ya dawo dashi daki sannan yace ta kawo ruwa.
Sai a lokacin ma kwakwalwarta ta bata ashe ana suma, itakam tsabar tsoro sam ta manta da komai.
Abba ya sawa Aminu ruwa sai dayai sau uku sannan yaja wani dogon numfashi ya b
ude idanunsa a zabure yana salatin annabi kai kace mumunan mafarki yai.
Ibty tayi shabe shabe tanata hawaye ya sauke idanunsa a kanta. Kallan ta yai sosai sannan ya kalli Ummy da Baffa sannan yasan akwai abinda ya faru.
Shiru sukai Ummy ta daure tace “Me
ya faru Aminu?”
Kai yadan girgiza yace “ Yana yana na fara gani a idona sai naga bana gani sosai, na shiga bandaki ina wanke fuskata daga nan bansan meya faru ba.”
Ummy cikin damuwa tace “Inalilahi wa ina ilaihi raji’un Allah dai yasa ba wani ciwon bane?
”
Yadanyi yake yace “Dazu fa da safe naje ganin likita ba komai da alama kawai abin ne yazo.”
Ummy tai shiru sannan ta kalli Ibty dake hawaye tace “Ibtisam kefa? Ba abinda ya faru?”
Tadanyi shiru hakan yasa Ummy tace “fadamin.”
Kallan Aminu tai shima k
allanta taga yayi, sai dai yanzu ba kallan tsana tagani a idansa ba, ta daure tace “Hotoncan ne ya fado ya fashe daga nan ya shiga toilet.”
“Hoto? Me zaisa dan hoto ya fadi ya suma?”
Aminu yadan girgiza kai yace “Nima nasan da faduwan hoton amma me zai s
ameni saboda hoto?”
Kallan Ummy tai idanunta sunyi raurau dama gasu sunsha kuka, tace “Akwai abinda ya fado a bayan hoton. Duk da dai zargi nane.”
Ummy ta kalleta tace “Daukomin na gani.”
Nan Ibty tai bangarenta ta dauko takardar nan ta mikawa Ummy, kal
lan takardar Ummy tai sannan ta mikawa Baffa shima ya duba ya mikawa Aminu gaba daya hankalinsu ya tashi sai dainahi Aminu cewa yai “To me nene hadin takardar nan da faduwa ta?”
******
Hajiya ganin kiran Malam sau biyu yasa ta dane zuciyarta ta dauka
dan dama itama zata kirashi sai dai ganin kiransa yasa tsoron rayuwar da zata jefa kanta ya shige ta.
Tana dauka taji yace “Kina ina? Komai na Aminu ya wargaje?”
Da sauri ta mike tsaye tace “Mene?”
Yai wani dogon tsaki yace “Ina nasan meke faruwa nima?
Sai dai kwalbar da muka kulle komai nashi a ciki itace ta fashe, aikin da akamai tun daga shekarun baya an budeshi sannan duk wanda muka mai yanzu komai ya tafi dama abinda yasa muke samun sauki gun mai magani saboda mun riga mun rike gudan tsorkar dake zu
ciyarsa ne to yanzu komai ya bale.”
Jikinta ne yahau rawa tace “Yaushe akai wannan aikin?”
Yace “Aikin dai da aka faramai tun na farko ai samun nasara a kanshi shine yasa muke komai cikin sauki.”
Batasan sanda tasa farcenta a baki ba saboda tsoro tace “
Nashiga uku yanzu ya za’ai?”
Ya girgiza kai kamar tana ganinsa yace “Ai wannan aikin banaji yanzu zai sake yiwuwa kedai ki gaggauta amincewa da abinda muka nemeki dashi kila in mukai sa’a a saku dacewa.”
Tana kokarin magana taji ya kashe wayar, zama t
ai dabas a kan gado gaba daga jikinta yahau rawa, sai gutsirar farce kawai takeyi, shikenan taga ta kanta, shikenan itakam ta gama yawo. Rayuwa tana neman juya mata baya…..
[5/4, 3:44 PM] Hauwa Galadima:
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Betwe
en)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*n
Ki hanzarta ki mallaki naki
🤸🏻
♀
️
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*
+447894142004
2083371
244
Zenith Bank
42*
Cikin sanyin jiki ta shigo dakin bakinta da sallama, ta kalli inda suke zaune taga idanun Aminu a kanta. Da sauri ta mayar da kai kasa taje ta durkusa kusa da Ummy tare da mika mata takardar dake hannunta.
Jiki a sanyaye
Ummy ta amsa sannan tai bismillah, bude tarardar tai wacce ta fara yin wani kaushi-kaushi sakamakon danshin jikinta da ya fara bushewa.
Duk yadda Ummy takaiga san gane rubutun kasawa tayi, ta dinga kankance idanuwa dan ta karanta amman ta kasa. Baffa ta
kalla wanda ke rike da Aminu ta sauke numfashi tana cewa. "Sai dai ka duba dan ni bana gane komai wallahi." Baffa yasa hannu ya karba, yana sake kai takardar wajan haske sannan ya zaro glass dinsa dake aljihu ya saka, shiru yai yana sake bin takardar da ka
llo a hankali.
A hankali suka ga yanayinsa ya fara canzawa, gani sukai jikinsa ya fara rawa, jijiyoyin goshinsa suna tashi sai wani cicije lebe yake yi, ransa ne a matukar bace, ya kalli Aminu tare da cewa "Inalilahi wa ina ilaihi raji'un! Wannan wace
irin jaraba ce?" Ummy dake gefe a zaune tace dashi. "Jaraba kuma?" Yaja numfashi cikin wani yanayi yace "Kinsan me yake jikin takardar nan?" Yai maganar tare da runtse idanunsa, ya zare glasses din cikin wani yanayi yace "Haba mana shi yasa yaro gabaki day
a ya kasa karawa kansa yanci, wannan hoton da akaga takardar nan tun yaushe yake a gurinka?" Cewar Baffa yana kallon Aminu cikin huci. Aminu ya kalli ibty dake tsaye wacce itama shi din take kallo dan jin abinda zai fada. "Ya dade Baffa tun aure na da Na'i
ma." "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun kaji wata masifa." Duk sukayi shiru suna sauraran Baffa na fada kafin yace.
"Zuciyar Na'ima da Aminu ta kasance tamkar ta rai da mutuwa da ikon n..nai..n." Bansan me suka rubuta a gurin ba saboda ya dan goge." C
ewar Baffa da ya gama karanta abinda ya gani. "Kenan anyi wannan aikin da sanin Na'ima?" Ummy ta tambaya tana kallan Aminu wanda gabaki daya jikinsa yai sanyi ji yake kamar mafarki yakeyi. "Waye ya sani. " sannan ya sake kallan Ummy yace "Asma'u Ina Uwar N
a'iman take?" Ya tambaya yana kallan Ummy wace gaba daya kanta yai gingirin ta daure tace "Ni tun da na sauketa ban sake bi ta kanta ba.
Baffa ya shafi saman goshinsa yace " Da ansani ba'a koreta ba sai yanzu dole mu nemo Hajiya ta sanar damu abinda yake
faruwa." Ummy ta tabe baki kafin tace "Wannan munafukar matar ce zata gaya maka gaskiya? Kasan sharrin matar nan kuwa? Kila ma ita tasa akai wannan asirin."
Ibty kam gaba daya jikinta ya gama sanyi, hawaye ne kawai suke zubo mata. Dakin yayi tsit Duk su
nyi shiru, Ummy ta janyo ibty zuwa kusa da ita, lallashinta ta shiga yi. Aminu kam yana tsaye yanayinsa kadai zaka kalla kasan yana cikin mumunan tashin hankali, idanunsa sunyi ja sosai, lebensa ya ciza kawai ya juya baya. Kukan da yaji tana yi har cikin r
ansa yake jin abin kamar ya janyota ya lallashi abarsa.
"Babban aikin da zamuyi yanzu shine neman inda Hajiya take, duk inda take a kawo ta dan sai nayi maganinta wallahi, sai ta sanwa ta tabo." Ummy ta tabe baki dan tasan da kamar wuya Baffa ya dauki h
ukunci, amman dai tasa a ranta koda kowa beyi hukunci akan Hajiya ba, ita kam sai tayi. Baffa ne ya kalli Ummy yana cewa.
"Mu tafi gida, ina san yin wani aiki." kallon Ibty Ummy tayi tare da cewa. "Allah yai miki albarka Ibtisam, inai muku fatan alkairi.
Insha Allahu komai zai daidaita kuci gaba da addu'a." Ibty ta rintsa ido tana jin wani iri, ita kam da zata iya da tace a sake musu gidan da suke a ciki. Amman ba zata iya magana ba saboda nauyin baki da kuma kunya, Aminu ma batajin zata iya gaya masa bal
lanta kuma su Ummy.
Aminu befito rakasu ba, Ibty ce kawai Ummy ta rike hannunta cike da karfafa mata guiwa tace.
"Ibtisam ke rahama ce a gurin Aminu, Allah shi kadai yasan dalilin yin auranku tare. Kici gaba da kulawa da kanki da kuma mijinki, karki ku
ma barin wata bakuwar fuska tazo miki, wannan Hajiyar dai ta cuce mu da yawa. Tsakaninmu dasu sai dai Allah." Ibty gyada kai kawai tayi ba tare da tayi magana ba, har suka shiga mota suka tafi.
Rasa abin yi tayi, sai kuma ta kalli ƙofar shiga falo, gani
n babu kowa yasa ta kalli bakin gate, Bala ta hango taji tana son zuwa gurinsa amman tana tsoron kar Aminu ya fito. da wane kwarin guiwa zai iya tashi? Kawai kije kiyi abinda zakiyi' ibty taji zuciyarta na bata kwarin guiwa.
"Allah yasa kisamu abinda za
ki tambaya" taji zuciyarta na taya ta addu'a. Bala na zaune yana wankin kayansa, ganin ibty yasa shi saurin mikewa ya isa wajanta.
"Ai da kin kirani daga can ranki ya dade zanzo ba sai kinzo da kanki ba." Ibty tayi dan guntun murmushi tana sake duba bay
anta, ganin Aminu befito ba yasa ta kalli Bala tana cewa.
"Bala kasan inda Hajiya ta koma?" Yayi dan jim kadan kamar yana nazari, sannan yaja numfashi. Ibty na sake ware kunne dan jin inda Hajiya take. "Ranki ya dade har yanzu bansan inda ta koma ba." Y
a sake yin jimm tare da kallan ibty yace "Kwanaki dai tazo." Da sauri Ibtyn ta ware ido, cike da tsoro tace. "Kwanaki kuma? Yaushe ne kwanaki Bala?" Bala ya shiga tunanin tare da rike baki alamar wanda ya manta abu. "Ka gaya min yaushe Hajiya tazo gidan na
n?" Yana kame da baki yace. "Wallahi na manta ne tace karna gaya muku." Ibty na jin haka ta samu kanta cikin hade rai, harar Bala tayi kamar zata shake shi tace. "Bala! kana aiki a karkashin mai gidan nan, tsawon shekaru be taba yi maka kwangen albashi ba,
ashe zaka iya munafuntarsa?"
Hankalin Bala ya tashi ganin yadda Ibty ke magana shi daya ke ganinta kullum cikin sanyi, ya shiga rantse-rantse yana cewa. "Wallahi ranki ya dade ban taba bada kofar cutar da yallabai ba, ina jin ko shekaran jiya ne, ko ra
nnan ne na manta ranar, tazo kofar nan take tambaya yallabai ya dawo? Nace Eh, tace shida waye a cikin gidan nace shidake." Yayi shiru, Ibty da kirjinta ke bugawa ta kalleshi. "Sai tace me?" Yaja numfashi yana kifta idanu. "Da na tambayeta nace kin dawo ne
? Sai tace a'a za dai ta dawo. Nace to yanzu tana ina sai tace min karna damu, daga nan kuma ta juya ta tafi."
Ibty taja numfashi tare da dafe goshi, wannan wacce irin masifaffiyar tsohuwa ce? Lallai Aminu ya dade a cikin masifa. Ta sake juyawa tana kal
lon bayanta, babu kowa ta kalli Bala. "Idan Hajiya ta sake zuwa, in ta tambayeka Aminu yana ciki? Kace mata eh, idan tace nifa? Sai kace bana nan. Ka kuma barta ta shigo indai ta bukaci ganinsa kaji?" Cikin ladabi yace. "Angama ranki ya dade." ibty ta juya
, har ta fara tafiya sai kuma tace. "Bala."
Da sauri ya amsa, tana rike da hannayenta tace dashi. "Sai ina gidan sannan zakace mata bana nan, idan shi kadai ne a gidan tazo karka bari ta shiga." Yace. "To ranki ya dade." taja numfashi sannan ta juya z
uwa cikin gidan. Sai dai kuma mene? Tsaye taga Aminu a bakin kofa ya hade rai, kasa tayi da kanta tana wasa da hijab din jikinta. Aminu ganin yadda tai kasa da kanta ne ya kuma bashi haushi, takowa yayi har inda take, ibty ta rintsa ido tana jiran tasha ma
ri. Hannu Aminu yasa ya kamo kafadunta murya a sanyaye yace.
"Meya hadaki da Bala? Kinje gabansa kin tsaya hira kukeyi?" Ibty tai saurin kallansa kafin ta maida kanta kasa da sauri, ya sake wurga mata harara. "Nayi karya ne?" shiru batace komai ba. "wa
to saboda ni bana yin hira dake shine kika fara zuwa gurin Bala? Daman kila wannan mahaukacin saurayin naki kila shike hira dake, gashi na hanashi kulaki." Ibty ta fara hada hawaye ta rintsa ido tana cewa, "Yaya." Aminu ya kuma matse mata kafadunta ta saki
yar kara tana turo baki.
"Gaya min abinda kikayi wajan Bala, dan nasan da wane ido zan ringa kallansa." Ibty ta kasa gane abinda yake nufi, ta kawar da fuska gefe tace. "Kana zargina ne?" Yai saurin dago mata da fuska, tana dagowa su ka hada ido. Kant
a ta maida kasa tana sake mamakin kalamansa.
"Kin bani abinci ma kuwa?" Ya canza maganar dan yaga tamkar taji haushinsa. Bude ido tai ta kalleshi. Aminu ya kifta mata idanuwa, "Naji ina jin yunwa shi yasa nake ganin kamar baki bani komai naci ba."
Ib
ty ta kuma kawar da kai. "Nace kazo kaci abinci, a lokacin ne kuma hoton nan ya fadi, idan ka shiryaci yanzu gashi can akan dining." Tayi maganar muryarta na
ɗ
an rawa. Sam bata gane meke faruwa ba, taya zai jefeta da wannan kalmar? Bayan yanzu ta gama hawa
yen taysaya mai? Sannan shi da baya san ganinta me yake shirin yi yanzu?
Aminu ya juya kai yana kallo saman table din, ji tai ya janyo hannunta suka nufi gurin. "Kina so naci sosai?" Kallan mamaki kawai takemai, mafarki take? Dan yanda yai tambayar kana
ji kasan ba cikin bacin rai bane, zolaya ce wace ya saba yi amma a da.
Cikin sanyin jiki ta daga kai, ya dan sakar mata hannun yana cewa. "Sai ki bani da kanki." saurin bude ido tai tana kallansa. "Idan bakya sonaci sai ki tafi kawai." Ya fada cikin daga
kafada. Ibty a ranta tace 'lallai mutumin nan' kallanta ya cigaba dayi hakan kawai yakeji kamar an saukemai wani gagarumin abu daga zuciyarsa, ji yake kamar ba shi bane, san da yake jinsa sama sama yanzu jinsa yake da karfi, sai