Showing 45001 words to 48000 words out of 128353 words
kwana da ita? Kwanansa nawa kenan raban dayai bacci mai dadi?
Sai wajen asuba sannan
bacci ya daukeshi, cikin bacci taji alamun kiran sallah, idanunta ta bude a hankali, tana neman yin mika.
Ganinta yai a makale a jikin Aminu, ta sakalo hannunta a tsakanin cikinsa da kirjinsa. Idanu ta zaro ta dan janye hannunta a hankali ta shige toile
t.
Brush tai sannan tai alwala tana yi tana tuno yanayin data ganta, oh itakam shikenan zai ce batada kamun kai. Wannan abin kunya dame yai kama?
Fitowa tai daga toilet tana gyara zaman hijab dinta, fitilar wayarsa ya hasketa dashi.
Da sauri ta dan j
uya baya, yace “Kin gama daddaneni kin tashi?”
Juyowa tai tana dan murmushin yake tace “Ya Aminu kasan in mutum yana bacci baya sanin abinda yakeyi.”
Kai kawai ya girgiza sannan ya mike yai toilet, wato yarinyarnan da inta kalleshi bata iya magana yand
a ya kamata amma yau data kwana dashi harta fara? Lalai wannan yana nuna kwana dashi ne yake kara jawo raini.
Alwala yai ya fito, ganinta yai tana lafila, nan yadau wayarsa da carbi ya fito daga dakin.
Harya isa masallaci yana tunanin meke damun yariny
a karama haka? Da ko bacci batayi mai dadi? Ko ya tambayi Ainah? Kai ya girgiza da sauri dan ya tabbatar inya tambayi Ainah zata fada mata ko kuma ta fadawa Ummy.
Harya dawo daga masallaci abin bai bar ransa ba, tunda ya shigo bangarensa yaki jiyo zazzak
ar muryarta tana karatun qur’ani, har ya nufi dakin sai naga ya dawo ya zauna akan kujera ya dan mike kafafunsa ya kwantar da kansa a saman kujera tare da lumshe ido yana juyo karatunta, baisan tanada murya mai dadin sauraro ba haka, sam baisan sanda bacci
yai gaba dashi ba.
Ibty kam sai data kai karshen Suratul Ma’idah sannan ta kalli yanda gari yai haske, lalai karatu rahama ne, kwanan nan bata samu damar yin karatu ba tana tunanin karta takuramai a hotel, jiya kuma batasan ta tashi su Islam, agoggo ta
kalla karfe shida da rabi.
Fitowa tai tana mamakin yanda akai bai dawo ba, akan kujera ga ganshi, jikinta ne yai sanyi da alama saboda baisan shiga daki tana nan ne yasa ya kwanta anan.
Sam jitai zuciyarta ba dadi, a rayuwarta batasan taga ta shiga hak
kin wani, dan karamin murmushi tai sannan ta koma daki ta kalli bargon dake kan gado tace “Wato a film in naga namiji ko mace suna luluba bargo in ana bacci abin naban dariya yau nima da alama zan kwaikwayesu.”
Daukan bargon tai ta nufi falo, a hankali ta
shiga ya ware bargon sannan ta lulubamai, juyawa tai zata koma sai jitai yace “Dadin ki sake taremin gado ko?”
Kallansa tai, mikewa yai tare da daukan bargon yace “Yanzu ai safiyace bakya bukatar kwana dani ko?”
Wannan wani irin mutum ne? Ita a film i
n aka shimfida bargo gani take ana godiya, ko a rungume ka, ko kuma adan kalleka ai murmushin jin dadi, in kuma mutum bai farka ba inya tashi zaiji dadi. To ita gashi tayi abin arziki an bige da fada mata magana.
Dakinsa ya wuce, gani yai ta gyara gadan,
kwanciya yai ya maida idansa ya rufe.
Ibty kam bangarenta ta koma, dakinta ta shiga ta zauna a kan gado tana kallan dakin, kalaman Ummy ke sake dawo mata, itakam gaba daya yanzu komai shakkarsa take a gidan, batasan taganta ita kadai sai taga kamar wani
abin zai sameta.
Wayarta ya dauko kawai ta koma falo ta zauna tana dane dane a haka har bakwai da kwata tai sannan ta wuce kitchen, me zata dafa? Nan fa ta fara hidimar harhada ingredients tana tunanin yau ce rana ta farko da zaici abincin ta dole ta za
ke karya sake ce mata yarinya.
*********
Potato omelette tai sannan tai sauce na hanta, ta dan soya dankali kadan tasa daga gefe, ta dafa tea ta zuba a flask sannan ta shiga tai wanka, lace ta dauko na daya daga cikin lefenta ta saka, tayi kyau sos
ai, ta gyara gashinta duk dabai bamai tsayi bane sosai amma ba gudil bane. Dan kwalinta ta dan daura ta dan yafa mayafi sannan ta dau turare, tana fesawa taji ana knocking din kofar, gabanta ne ya fadi ta fito daga dakin tare da nufa kofar.
Tace “Waye?”
Hajiya tace “Amarya kin tashi?”
Budewa tai cikin dauriya ta kalleta, hannunta dauke da tire na abinci.
Ibty ta gaisheta sannan tace “Ya jiki? Naji ance baki da lafiya?”
Tana murmushi tace “Na samu sauki, ga abincin safenku.”
Kallanta tai, cikin dauriy
a tadan hade hannayenta, tsoro takeji sosai, sai dai inta tuna tsoronta abinda yaja mata a rayuwa sai taji haushin kanta, dan badan tana tsoron Umar ba da tuni ta takamai birki, da ta sanar da iyayenta an dau mataki tun farko.
Bakinta nadan rawa tace “Ha
jiya mun gode amma na riga nayi abinci.”
Hajiya taji abin sama taka, balle a yanda take kallan yarinyar kamar wawiya, cikin dauriya tace “Ke da nace ki barshi shine kima wahalar da kanki?”
Tadan dake tace “In na zauna ba abinyi nima zaman isata zaiyi, k
e da ba lafiya ne dake ba gwara ki huta.”
Lalai kallan kitse nakewa rogo, amma ba tasaka mata laya ba? Badai tare take kwana da Aminu ba?
Kallan zargi tawa Ibtisam wacce ke wasa da yatsun hannunta tana addu’ar tsari a ranta.
Hajiya ta juya hannunta d
auke da tire, cikin tsananin kunar rai ta isa bangarenta, abincin ta juye a cikin bola sannan ta zauna ta daura kafa daya kan daya tana girgizawa lalai da alama yarinyarnan ba wacce ya kamata ta raga mata bace.
{Nikam Ayusher sim sim sim na fito tun ka
fin abu ya ritsa dani
🏃🏻
♀
️
}
🏌🏻
♀
️
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
Ki hanzarta ki mallaki naki
🤸🏻
♀
️
*TU
RA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004
Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
18
🤸🏻
♀
️
Tsaye tai a cikin dakinta tana tunanin yanda zata tunka
ri dakin Aminu, ta zauna a gaban madubi tana kallan kanta. Ajiyar zuciya tadanyi mai sauti sannan ta dan gyara fuskarta ta dau turare tadan fesa, shiru ta sakeyi tana tuno yanda Amare ke dan naku-nuku in tana karanta novel, to ita gashi sai dai takai kanta
? Hijab dinta ta dauka ta zura sannan ta nufi bangarensa.
Agoggon falansa ta kalla wanda ya nuna karfe goma na dare, kwan wutar dakinsa tana kune da alama bayan yaci abinci ciki ya shiga. Gabanta ne ke faduwa akai-akai harta isa kofar dakin, hannu tasa
tana neman bude dakin da sauri ta sauke hannunta. In ya korota fa? Gashi tawa Ummy alkawari? Hannu ta kara sawa cikin shakka ta runtse idanta da karfi sannan ta bude kofar, bakinta dauke da sallama.
Bata kalli inda yake ba dan ta tabbatar suna hada ido z
ata rasa abinyi, tana jinsa sanda ya amsa sallamar amma kanta na kasa ta nufi gado tana kallan kasan dakin.
Aminu dake zaune akan gado ya mike kafa yana dane-dane a computer ne ya tsaya cak yana kallanta. Me takeyi? Tambayar datazo mai kenan. Bai gama tu
nanin me take shirin aikatawa ba kawai yaga ta nufi kan gado inda yake.
Dan idanta ta dago kadan ta hango kafar Aminu a saitin da take kokarin kwanciya, da sauri ta koma baya ta zagaya ta daya bangaren, shikam idanunsa na kanta yana kallan ikon Allah.
Kamar zata zauna a gadan sai kuma ta wuce toilet dinshi, brush dinta data dauko ta ajiye a ciki, sannan ta furzar da wata iska, shafar kirjinta tai sannan ta kara fitowa, kan gadan ta karasa, kawai yaga ta kwanta ta juya baya, tsananin mamakin wannan lamar
i ya hanashi magana.
Jin baice komai ba yasa tadan saki ranta, hannu tasa saboda ta ji sanyi na ratsa kafarta, tana dan laluban bargo, idanunta a rufe sannan ta juya. Kallan hannun yai sannan ya janye bargon daga inda hannunta zai kamo, ganin ta kasa kam
o bargon yasa ta dan takure cikin hijab dinta.
“Me kike anan?”
Abinda taji yace kenan, bakinta nadan rawa tace “Anan zan kwana.”
“Anan zakiyi me?” Yai tambayar yana kara kallan bayanta cikin mamaki, Ibty tai shiru tare da maida idanunta ta rufe ta fara
dan sauke numfashi kadan kadan alamar bacci.
Abin ma dariya yaso bashi, yace “Anan zakiyi me kikace?”
Shiru nan ma ba amsa, ajiye laptop dinsa yai a side bed sannan yasa hannu ya juyo da ita saitinsa, haryanzu idanunta a rufe wai a dole bacci take, sa
keta yai sannan ya zuba mata ido yana ganin sanda zata bude ido. Ibty kam idanunta kam, jin shirun yayi yawa yasa tadan kasa kunne, motsi taji kamar an sauka daga kan gadon, sai kuma taji alamar rufe kofa, idanta daya tadan kyalla kadan tanasan ganin ko ya
na nan, ganin bakowa agun yasa ta danyi fifita da hannunta sannan ta dan mike ta zauna tana sake fitar da wata ‘yar iska.
Gyaran murya taji daga gefen toilet, idanu ta zaro ai bata kalli gun ba tai saurin kwanciya ta runtse idanunta kyam.
Aminu baisan
sanda wani murmushi ya bayyana a fuskarsa ba lalai yarinyarnan.
Karasowa yai ya zauna yace “Tashi ki fadamin me kike a dakin nan? Ko kuma na kinkimeki na maidake dakinki.”
Kin bude ido tai, yace “in irga uku?”
Nan taji yace “Daya, biyu, uku!”
Hannu
nsa taji ya sakalo ta wuyanta da sauri ta bude ido tare da cewa “Ya Aminu dan Allah ka bari, tsoro nakeji, bazan iya kwana ni kadai ba.”
Kallanta yai sosai sannan ya saketa, yace “Kina nufin ni kike cewa tsoro kike?”
Ta jinjina kai da sauri alamar eh tac
e “tsoro ne dani sosai, bakaga jiya a gunsu Islam na kwana ba?”
“Ahhhhhh tsoro ko?” Ta daga kai da sauri. “Oh! Shiyasa naga sanda kike kwana a daki ke kadai a hotel cikin dare ihu kikeyi kina dawowa inda nake.”
Ganin ya kamota yasa tadan hada labanta bi
yu ta rufe tace “Na kwana ni kadai ko?”
Bai amsa mata ba sai kallanta dayai, tadanyi murmushin yake tace “To koma dai na kwana da yanzu tsoro nake.”
“Tsoro?”
Ta daga kai yace “Tsoro shine bazaki kwana a kasa yanda kika kwana a dakinsu Islam ba sai ak
an gadona?”
Saman goshinta tadan sosa kadan tace “Jiya dana kwana a kasa ne bayana yake ciwo.” Tai maganar tana dan taba bayanta dayin alamar zafi.
Dan kallansa tai kadan taga yanda ya kafeta da ido, da alama yanzun ma bai kama karyar ba.
“In nace mik
i yarinya kiji haushi, yanzu wasu tatsuniyoyin kike jeromin?”
Tadan turo baki cikin jin haushin kalamansa, kallan yanda ta wani turomai baki yai yace “Badai zagina kike a ranki ba ko?”
Kallansa tai cikin wani yanayi na shagwaba da sakalci da batasan tay
i ba tace “Nawa Ummy alkawarin kwana a dakin nan daga yau ne shiyasa. Sannan Allah ni ba yarinya bace.” Tana fadar haka yaga ta ja bargo ta sake kwanciya, a zaune ta barshi da baki bude eh lalai yarinyarnan taga gadan baccinsa, shi takewa magana haka?
Sh
i dama yasan akwai abinda suka tattauna da Ummy wato akan kwana tare ne?
Kallanta yai yace “Kina nufin daga yau anan zaki dinga kwana?”
Gani yai ta daga kai alamar eh, yace “In kuma naki yadda fa? Ko kin manta daki nane?”
“Sai na fadawa Ummy tasan abi
nda kace” Baiyi tunanin jin wannan amsar ba sam. Kasa magana yai sai kallanta dayai, eh lalai Ummy ta kara bari yarinyar nan ta rainashi.
Ko ya sauka ya bar mata dakin? Tunowa yai da kwanciyar kujera dayai a hotel yanda ya dinga tashi da ciwon baya, abin
ka da shekaru sun dan fara kamawa.
Yanzu haka zai dinga kwana da yarinya a gado daya? Bai kwanta da ita bama ta rainashi balle sun kwana gado daya?
Aikin sam kasa karasawa yai haka yanayi yana kallanta cikin takaici ya kashe wuta ya kwanta, ya dade ya
na juye-juye kafin bacci ya daukeshi.
***
Wajen karfe biyu da rabi na dare mumunan mafarki ta farayi, wai gatanan Umar ya rufeta a wani daki a daji, abinci ma ta window yake cila mata. Sam saboda tsoro batasan ta shigo jikin Aminu ba, cikin bacci yaji a
n rikeshi sosai, idanu ya bude sannan yasa hannu ya kuna fitilar wayarsa, mamaki ne ya kamashi ganinta a jikinsa sosai ta rikeshi. Hannu yasa yana kokarin janyeta daga jikinsa, hawayen dayake gangarowa a idanunta ne yasashi tsayawa yana kallanta, wannan ya
rinyar tabbas akwai abinda ke cinta, to shi bata fadamai ba taya zai tambayeta? Ko saboda batasanshi ne kullum take mafarki da koke koke cikin bacci? Saman goshinsa ya shafa yana sake kallanta, harya sake kai hannu zai tureta sai kuma ya fasa.
Hannunsa y
a daura a saman goshinsa kawai ya rufe idansa, da alama yanzu da take jikinsa bacci take shikam sam ya kasa komawa bacci, a haka zai cigaba da kwana da ita? Kwanansa nawa kenan raban dayai bacci mai dadi?
Sai wajen asuba sannan bacci ya daukeshi, cikin
bacci taji alamun kiran sallah, idanunta ta bude a hankali, tana neman yin mika.
Ganinta yai a makale a jikin Aminu, ta sakalo hannunta a tsakanin cikinsa da kirjinsa. Idanu ta zaro ta dan janye hannunta a hankali ta shige toilet.
Brush tai sannan tai
alwala tana yi tana tuno yanayin data ganta, oh itakam shikenan zai ce batada kamun kai. Wannan abin kunya dame yai kama?
Fitowa tai daga toilet tana gyara zaman hijab dinta, fitilar wayarsa ya hasketa dashi.
Da sauri ta dan juya baya, yace “Kin gama d
addaneni kin tashi?”
Juyowa tai tana dan murmushin yake tace “Ya Aminu kasan in mutum yana bacci baya sanin abinda yakeyi.”
Kai kawai ya girgiza sannan ya mike yai toilet, wato yarinyarnan da inta kalleshi bata iya magana yanda ya kamata amma yau data
kwana dashi harta fara? Lalai wannan yana nuna kwana dashi ne yake kara jawo raini.
Alwala yai ya fito, ganinta yai tana lafila, nan yadau wayarsa da carbi ya fito daga dakin.
Harya isa masallaci yana tunanin meke damun yarinya karama haka? Da ko bacci
batayi mai dadi? Ko ya tambayi Ainah? Kai ya girgiza da sauri dan ya tabbatar inya tambayi Ainah zata fada mata ko kuma ta fadawa Ummy.
Harya dawo daga masallaci abin bai bar ransa ba, tunda ya shigo bangarensa yaki jiyo zazzakar muryarta tana karatun q
ur’ani, har ya nufi dakin sai naga ya dawo ya zauna akan kujera ya dan mike kafafunsa ya kwantar da kansa a saman kujera tare da lumshe ido yana juyo karatunta, baisan tanada murya mai dadin sauraro ba haka, sam baisan sanda bacci yai gaba dashi ba.
Ibty
kam sai data kai karshen Suratul Ma’idah sannan ta kalli yanda gari yai haske, lalai karatu rahama ne, kwanan nan bata samu damar yin karatu ba tana tunanin karta takuramai a hotel, jiya kuma batasan ta tashi su Islam, agoggo ta kalla karfe shida da rabi.
Fitowa tai tana mamakin yanda akai bai dawo ba, akan kujera ga ganshi, jikinta ne yai sanyi da alama saboda baisan shiga daki tana nan ne yasa ya kwanta anan.
Sam jitai zuciyarta ba dadi, a rayuwarta batasan taga ta shiga hakkin wani, dan karamin murm
ushi tai sannan ta koma daki ta kalli bargon dake kan gado tace “Wato a film in naga namiji ko mace suna luluba bargo in ana bacci abin naban dariya yau nima da alama zan kwaikwayesu.”
Daukan bargon tai ta nufi falo, a hankali ta shiga ya ware bargon sann
an ta lulubamai, juyawa tai zata koma sai jitai yace “Dadin ki sake taremin gado ko?”
Kallansa tai, mikewa yai tare da daukan bargon yace “Yanzu ai safiyace bakya bukatar kwana dani ko?”
Wannan wani irin mutum ne? Ita a film in aka shimfida bargo gani
take ana godiya, ko a rungume ka, ko kuma adan kalleka ai murmushin jin dadi, in kuma mutum bai farka ba inya tashi zaiji dadi. To ita gashi tayi abin arziki an bige da fada mata magana.
Dakinsa ya wuce, gani yai ta gyara gadan, kwanciya yai ya maida ida
nsa ya rufe.
Ibty kam bangarenta ta koma, dakinta ta shiga ta zauna a kan gado tana kallan dakin, kalaman Ummy ke sake dawo mata, itakam gaba daya yanzu komai shakkarsa take a gidan, batasan taganta ita kadai sai taga kamar wani abin zai sameta.
Wayart
a ya dauko kawai ta koma falo ta zauna tana dane dane a haka har bakwai da kwata tai sannan ta wuce kitchen, me zata dafa? Nan fa ta fara hidimar harhada ingredients tana tunanin yau ce rana ta farko da zaici abincin ta dole ta zake karya sake ce mata yari
nya.
*********
Potato omelette tai sannan tai sauce na hanta, ta dan soya dankali kadan tasa daga gefe, ta dafa tea ta zuba a flask sannan ta shiga tai wanka, lace ta dauko na daya daga cikin lefenta ta saka, tayi kyau sosai, ta gyara gashinta duk
dabai bamai tsayi bane sosai amma ba gudil bane. Dan kwalinta ta dan