Showing 12001 words to 15000 words out of 128353 words
Ibty tai wacce tai shiru da alama tunanin abinda zatace mata takeyi, hannu tasa tadan bigi kafadarta tace "Tell me,
meke faruwa?"
Juyowa tai ta kalleta sosai, tasa hannu ta kamo hannun Ainah tace "Ainah bansan meke faruwa ba, jiya da daddare bayan na dawo daga gidanku Abba ya sanar dani wai zaiyi hadin aure tsakanin Yaya da Ya Umar."
Cikin matukar mamaki Ainah tace
"What?"
Ibty tadan girgiza kai kafin tace "Bansan meke faruwa ba, kwakwalwata ta kasa tunanin komai, kuma abin mamakin wai Ya Umar shi ya fara yarda da wannan hadin. Gashi itama Yayan sanshi take ashe bansani ba."
Ainah kanta tadan kama alamar damuwa t
ace "Yau naga ikon Allah! Kin tambayi Ya Umar din?" Tace "Yayi tafiya kauyensu, so nake yanzu ko in an tashi ma kirashi a waya naji meke faruwa."
Yanzun ma shiru Ainah tai da alama batasan me zatace ba itama, Ibty ta sake kallanta tace "Ainah kodai na s
amu Umma na sanar da ita halin Ya Umar? Tsoro nake kar a dalilina Yaya ta shiga cikin kangin rayuwa, gashi ita ba lafiya ba dame zataji?" Tai maganar cikin rauni da alama kuka ke neman kamata.
Ainah ta jinjina kai alamar gamsuwa tace "ina ganin ki sanar
da itan gaskiya, duk da dai ina tunanin wani abu, kodai ya amince da Yaya ne saboda yaga batada lafiya? Ina take zuwa? Yanada wani hali ne bayan kishi da wannan zargin?"
Ibty tai shiru kafin ta girgiza kai alamar a'a tace, "A iya sanina wannan halin ne n
ashi mara kyau banda shi yanada kirki ga taimako."
Ainah tace "to ko shiyasa ya hakura dake? Yana ganin gwara Yaya wacce zata zauna a gida kullum? Hankalinsa a kwance?"
Alamar tunani ta tafi kafin tace "Ko?"
Kai ga jinjina tace "Nidai haka nake gani,
inba haka ba meyasa yanda yake haukar sanki zai yadda ya auri Ya Billy?"
Wannan maganar ita ta gamsar da Ibty ta kuma sa aranta lalai haka ne dalili da alama ya hakura da ita ne shiyasa jiya bai rufeta da masifa ba dayaga taje gidansu Ainah. Amma alkawa
rin dayace ta dauka fa? Kodan dai ya saba ne? Haka taita sake sake a ranta har suka koma class.
********
Kiran Baffa ne yasa Ummy ta dan gyara zamanta tare da kara wayar a kunnenta tace "Alhaji har ka kirashi?"
"Asma'u kin tabbatar number nan itac
e ta Baban yarinyar?"
Cikin mamakin kalamansa tace "Eh Ainah tana turomin na tura maka ai."
"Number Audu mai kwari ne fa? Kina san cemin 'yarsa ce kenan?"
Mikewa tai zaune sosai tace "Audu dai Audu abokinka da kuka hadu a Saudia?"
Yace "Shifa, na gam
a saka number kawai sunanshi ya bayyana a jikin wayata, sannan address din gidan ma ai gidanshi ne."
"Ikon Allah! To ko kasan ma yarinyar? Tunda naga kana zuwa shima yana zuwa."
Baffa ya jinjina kai yace "Yaranshi uku mata, daya kinsan batada lfy, sai t
a tsakiyan wacce nake zatan itace dan sa'ar Ainah ce."
Ummy tai murmushi tace "Da alama wannan hadin daga Allah yake, sannan itace matar da muka dade muna fatan Aminu ya samu."
Baffa yai dan shiru kafin yace "Ki bari dai mu hadu dashi muyi magana, kar
inje an mata miji."
Kai ta jinjina sannan tace "Dan Allah yanda kukai ka kirani ka sanar dani dan damuwa bazata barni na kwantar da hankali na ba."
Dariya yadanyi yace "In matarsa ce komai zaizo da sauki in kuma ba matarsa bace sai kiyi hakuri tunda dai
kinsan wani baya auran matar wani."
Kashe wayar yai kai tsaye ya kira Abba, shikam yana zaune a babban shagonsa yanata lissafin kudin da zai kashe na kayan daki, da gyaran gidan da akeyi. Ganin sunan Sulaiman a jikin alan wayarsa yasa ya dauka cikin fara
'a yace "Lalai ka tari numfashi na, ina san kiranka na sanar dakai babban al'amari ashe kai zaka riga kirana."
Baffa yai dariya yace "Kana shago? Inaso zanzo yanzu mu tattauna akwai maganar da nake so muyi."
Abba yace "ina shago in kuma kana ganin ni n
azo office dinka to?"
Baffa yai saurin cewa "A'a ai ni na fara cewa zanzo ko?"
Suna dariya sukai sallama akan Baffa zaizo nan da minti ashirin.
Haka ya wuce kai tsaye zuwa kasuwa yana tafe yana tuno haduwarsu a saudia da yanda suka zama abokai, daki
n Abba na kusa dana Baffa a hotel dinsu, komai tare suka yishi, ko sarin kaya da Abba zaiyi shi ya rakashi sukaje, bayan sun dawo
sun cigaba da zumuncinsu, duk dadai zumuncin maza sai lokaci zuwa lokaci amma duk da haka suna kokarin haduwa.
Abba cikin t
sananin murna ya tarbeshi ya zauna akan kujera yana kallan katan shagon, wasu laces ya kalla yace "Da alama ya kamata kafin na tafi na saiwa Uwar gida da Amarya tsarabar zuwa kasuwa."
Abba yana dariya yace "In baka siya ba ma duk sanda naje gidanka zaiyi
gulmar kazo bakasainmusu komai ba."
A tare sukai dariya kafin Baffa yace "Me kake san kirana ka fadamin?"
Abba ya fadada murmushinsa yace "Sulaiman nan din shirin auran 'yata nakeyi, ina sa ran nan da sati biyu a daura, tunda 'yar gida zanyi a hankali
a karasa gyara da wasu abubuwan."
Jikin Baffa ne yai sanyi a ransa yace "Ba rabanmu bace."
Abba ne ya katsemai tunaninsa yace "Kasan Umar ai ko? Yaron da na rike? Wanda yake zaune da a shagon nan?"
Baffa yace "Umar? Na ganeshi ko ba yaran yayanka ba?"
Cikin jin dadi yace "shi! Shine zan hadasu da Bilkisu."
Fuskar Baffa ce ta bayyana da fara'a yace "Kai masha Allah! Amma na tayaka murna, ita ta tsakiyar fa?" Da saninsa yaki fadan sunan Ibtisam saboda yana san tabbatarwa kansa itace wacce Ummy ke mag
ana.
Abba yana murmushi yace "Ibtisam?" Baffa fara'arsa ya fadada yace "Eh!"
Kai yadan girgiza yace "A'a sai fatan Allah ya kawo nagari."
Baffa yadan gyara zamansa yace "Audu bansan ya zaka dauki abin ba, na kuma san Aminuna ya mata girma amma me kake
ganin in muka hadasu aure?"
Abba yai dan shiru kafin ya kalleshi yace "Aminu?"
Baffa ya daga kai, Abba ya danyi dariya wacce ta dan kwantar da hankalin Baffa yace "Aminu dai Aminu?"
Tambayar tadansa jikin Baffa yin sanyi, jiyai yace "Sulaiman kasan y
anda nake san hada zuri'a dakai? Balle Aminu wanda a koda yaushe nake kainar hankali da nutsuwarsa, tunda na ganshi nasan lalai kayi dacen d'a ga tausayinsa da nake daka sanar dani rasuwar matarsa da halin da ya shiga na rashinta."
Baffa dadi ne yasa ya
rasa abin cewa sai hanun Abba kawai daya kamo.
Abba cikin jin dadi yace "Da alama kwanciyar hankali ce tazomin, ban taba tunanin Umar zai yarda kai tsaye da auran Bilkisu ba gashi ya yarda sannan ban taba kawo Ibtisam zata samu miji kamar Aminu nan kusa
ba sai gashi ta samu. Sulaiman Allah ne kadai yasan dadin da nakeji."
Baffa dadi ya kamashi yace "Amma kana ganin yarinyar zata amince?"
Cikin sauri ya daga kansa alamar eh yace "Ibtisam yarinyace mai biyayya da hakuri, ban taba ganinta da ko saurayi ba
, ita ba zuwa gidan kawaye take ba, batada rawar kai irin na yaran zamani, na tabbatar bazata taba kin namiji kamar Aminu ba."
Hamdala Baffa ya fara ji yake dadi duk ya rufeshi, Abba ya kalleshi yace "In har na sanar da ita ta amince ka kuma sanar da Ami
nu shima ya amince me kake gani in muka daura musu aure tare a ranar da za'a daura na Umar? Banasan sai an gama a sake taso mutane wani auran, amma in anyi auran sai ta jira a gida kafin na gama hada kayan daki da sauransu."
Baffa cikin tsananin gamsuwa y
ace "Kai amma naji dadi, hakan yayi sosai wannan abu yamin dadin da bansan me zan ce ba. Ji nake kamar a mafarki"
Lamarin ya musu dadi nan suka zauna sunata tattaunawa cikin nishadi da farinciki.
******
Ummy kam duk hankalinta yaki kwanciya sai kallan
wayarta takeyi, tunanin yanda zatai ta kori waccen matar inhar abin ya tabbata takeyi, ta tabbatar matarnan magani ta musu dan duk sanda ta yunkuro zata mata korar kare daga taje gidan sai ta kasa, wannan bala'i ya isheta mutane sai zaginsu ake aka magana
akan wannan rashin tunanin, 'yan uwanta sunyi fada harsun gaji kowa ya zuba masu ido, gashi Aminu sam abin bai damunshi itakam ta rasa ta inda zata shawo kan wannan bala'i da masifar.
Kamar daga sama taji sallamarta, gabanta ne ya fadi tai saurin fara a
ddu'a a cikin ranta tana neman tsari daga sharrin wannan matar.
Juyowa tai bayan ta gama addu'oin sannan ta kalleta tadanyi yake tace "Yau kece a gidan? Na dauka baki da lafiya tunda inata aikawa kizo kin kasa zuwa."
Hajiya tai dan murmushi ta zauna ak
an kujera kai kace mutuniyar kwarai tace "Asma’u ai kya bari mu gaisa dai ko?"
Ummy ta koma ta zauna akan kujera nan suka gaisa, kallanta tai tace “Kwanaki dana miki magana kikace zaki wuce a satin, ko?”
Kallan Ummy tai sosai, wanda har ranta ya fara b
aci, gani tai ta saki murmushi wanda ya kara dagawa Ummy hankali.
Tace “Aminu bai sanar dake bane? Har kayana na hada shine ya hanani tafiya?”
Yanda ta yiwa Ummy maganar haka kawai ta samu kanta da kasa cewa wani abin, sai tsananin faduwar gaba kawai d
a Ummy ta fara fuskanta. Addu’a ta fara cikin sauri.
Hajiya ta sake murmushi tace “Sannan kinsan ni na saka Aminu ya amince da auran da kike san yimai ko?”
Ummy kam duk yanda taso ta daure ta mata magana ta kasa, yawun bakinta ta hadiya ta daure sosai
tace “Ba maganar aure ba, Yanzu yaushe zaki tafi? Wai dan Allah bakya jin kunyar zama a gidan sirikinki? Ni tunda nake ko a labarai ban taba jin wannan abin ba, mu ba a garin maguzawa ba bare garin gala galu? Ai na tabbatar kudin da kike tarawa ya isheki y
anzu haka nan.” Dakyar Ummy ta daure tai wadannan kalaman dan ji take zuciyarta kamar zata fito saboda bugawar da take.
Murmushi ta sake yi tace “To ya kikeso nayi? Ni kaina yanzu so nake na tafi. Danki ne ya dage sai na zauna, in ke baki daukeni a matsa
yin wani abu ba shi a matsayin uwa ko ince sama da matsayinki ya daukeni.”
Kallanta kawai Ummy take cikin tsananin mamaki, Hajiya ganin tabbas Ummy bata samu matar da zata aurawa Aminu ba dan yanda ta watsa mata maganganu ta tabbatar da ta maida mata mur
tani yasa ta mike tace “Dama dai gaisheki nazo yi bari na wuce zan dauko jikokina.”
Fita tai ba tare da ta sake neman jin ta bakin Ummy ba.
Tana fita ta kalli gidan tace “Daga ke har Aminu a tafin hannuna kuke.”
Ummy kam harta fita gabanta bai daina fa
duwa ba, wayarta ce tai kara cikin tsoro da firgici ta dauko wayar dakyar ta danna ta kara a kunnenta.
Baffa cikin jin dadi ya sanar da ita abinda ke faruwa, hamdala ta shiga yi sannan tace “Alhaji karka fadawa kowa maganar auran nan dan Allah, shi kansh
i Aminu zan ce karya sanar da kowa, in aka daura auran koma menene aji.”
Yasan tanada dalilinta na fadar haka, shi kanshi abin na damunshi ya rasa me yasa suka kasa korar matarnan, sannan duk matar da Aminu zai aura sai wani tangarda ya taso.
********
*
Umar kam can cikin zumudinshi a motar haya, yana kwance ya rufe ido yana hango ana shafa fatihar auransa da Ibty bai san an sace masa wayarsa ba, sam bai kula ba harsai da ya isa kauyensu, takaici ya isheshi gashi yanasan ya kirata video call dan har
ya fara missing dinta.
A kauye kuwa ya sanar da kowa maganar auransa da Ibtisam. Murna kam kowa ya shiga tayashi dan Ibtisam irin matan nan ne masu ban sha’awa da birgewa.
Kawunsa yace ai kuwa anan kauyensu zai zauna kafin aure dan tunda ya koma birn
i shekara sama da goma kenan bai taba zuwa ya kwana ba, sun kuma tabbatar yanzu in yai aure shikenan sai dai yazo ya wuce.
Bai musa ba dan yanzu ji yake rayuwar sa tana cikin kan hanyar da yake so, yace zaiyi sati daya inyaso sai ya koma ana saura sati d
aya biki.
Rashin wayarsa ya dagamai hankali, haka ya ari wayar abokansa yai ta kiranta ita kuma taki dauka, dan ita sam bata daukan number da bata sani ba, ganin Umar bai kirata ba yasa ta tabbatar da lalai yanzu ya juya akalarsa zuwa kan Yayarta, sai da
i duk da haka zata sanar da Umma halinsa.
Umar kullum ya kwanta bashida aiki sai mafarkin yana saduwa da Ibtisam shikenan da yin wanka, wannan sha’awa data tasomai kwanan nan ta isheshi, lalai in akai aure zai kwashi gara dan tabbas a rana sai ya sauke
sha’awarsa iya san ransa, shi ji yake sau hudu ma bazai gamsar dashi ba. Wani irin mugun santa yakeji bai taba yini bai ganta ba lalai sati dayan nan sai ya jure in ba haka ba tabbas za’a tashi cikin dare a nemeshi a rasa, matsalar daya yayiwa mahaifansa a
lkawarin zama harna sati daya.
Nikam nace Hmmmm
😆
su sha’awa manya……
*******
A hankali ta sauko daga saman dakinsu ta kwankwasa kofar dakin Umma, daga ciki ta amsa tare da bata izini, a tunaninta Abba bai dawo ba dan bataji alamun motarsa ba, tana
bude kofa ta ganshi a zaune yana shan tea.
Gaisheshi tai sannan ta tsuguna, ita datazo yiwa Umma zancen Umar yanzu kam ina zata iya a gaban Abba?
Abba cikin jin dadi yace “Ibtisam dama yanzu zan sa a kiraki.”
Kallansa tai a ranta tace “Shikenan Ya Um
ar ya canza ya dawo yace ita yake so” Idanunta tadan sadda kasa takaicin duniya ya isheta.
Abba cikin jin dadi yace “Akwai bako da zakiyi gobe in Allah ya kaimu, naga gobe asabar kina gida ko?”
Kallansa tai a hankali tace “Eh ina gida Abba, amma wani b
akon?”
Ya dan sake shan tea din yace “Yaran abokina ne bazaki gane babanshi ba amma sau biyu yana zuwa gidan nan, daya kun gaisa lokacin daya kuma kina makaranta yazo. Dazu Ummanki ke fadamin dan na dauka ma kinsanshi sosai tace bazaki ganeshi ba.”
Bat
a ce komai ba sai daga kai kawai datai tana mamakin wani yaran abokin?
Abba ya sake murmushi yace “ Ibtisam ki kalli abin nan da fuska mai kyau, wannan hadin ina matukar sanshi ina kuma fatan kema zaki soshi. A koda yaushe burin iyaye bai wuce su aurar d
asu gidan da zasu samu kwanciyar hankali da nutsuwa ba.”
Kanta yana kasa a hankali tace “Hakane Abba.”
Jin kalamanta yasa Abba ya mike ya shiga toilet yana murmushi shi dama yasan bazai samu matsala daga gunta ba.
Umma cikin jin dadi tace “Ibty ko akwai
wanda kikeso? Naga bamu tambayeki ba.”
Da sauri ta girgiza kai alamar a’a, Umma tai murmushi tace “Ya taba aure amma matarsa ta rasu, sannan yanada yara biyu mata ‘yan biyu ne shekararsu biyar.”
Kallan Umma tai tace “Yara?”
Umma ta daga kai alamar eh
tace “Bakyasan mai yara?”
Kai ya girgiza alamar a’a itakam ai koma wanene indai zai barta da rayuwarta ya barta tai karatunta zata amince, sannan in har zai rabata da kusa da Umar dan ta tabbatar barinta gidan shine zai sa ya maida hankali gun kula da y
ayarta.
Umma ta dan dafata tace “Allah ya muku albarka, yau cikin farinciki nake, ban taba tunanin auranki zaizo nan kusa ba.”
Kunya ta kama Ibty ta mike da sauri ta wuce daki.
Tana shiga wata number na sake kiranta, kashe wayartai gaba daya ta zauna
a bakin gado tana tunani, tunda take bata taba kula wani saurayi ba da sunan so saboda takurar Umar, gobe ko me zatace? Sannan gobe dole ta sanar da Umma tunda yau bata samu dama ba.
Ayusher Ce
🏌🏻
♀
️
[1/26, 9:32 PM] Fav
♡♡
:
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*Free Page*
Ki hanzarta ki mallaki naki dan Free Pages sun kusa karewa
🤸🏻
♀
️
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA 500 TA* *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004
0704307928
2
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
Page 8
Yau ankai laifi duk da ba'ai karya ba amma kaya kam anyisu masu kyau da tsada, Yayar Ummy da kanwar Baffa ne suka kai, a cewarsu tunda abin na gaggawane basu samu damar yin gayyata ba, sai dai a zahi
ri sunyi haka ne dan kar labari yakaiwa Hajiya, haka kawai ta tashi taga ana gini a gidanta, tasan sarai abinda Ummy ke shirinyi sai dai a ganin ta a banza, dafarko dai su Ilham a gunta suke, a kuma gunta suke kwana, duk wani abu na Ummy sai dai tayi ga ga
ma gida ne duk duniyar nan bataga mai rabata dashi ba, ita kadai tasan wahalar datasha a kauye bayan auranta ya mutu, har mayya sai da akacemata, yanzu kuwa da Allah ya kwaceta gani