Showing 96001 words to 99000 words out of 128353 words

Chapter 33 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

13

babu komai sai bacin rai, ki batan rai sannan wani gardin saurayinki nada shima ya batamin rai.” Yai karasa maganar tare da dan yarfar da fuskarta gefe, saketa ya fara kokarin

yi da sauri tasa hannu ta sake rikeshi, waigowa yai a fusace yadan runkufo saitin fuskarta yace “Abinda na tsana kenan wadannan idanuwan naki da………”

Dan daga kafafunta tai kawai ta sumbaci bakinshi, kallanta yai cikin mamaki, yana kokarin sa hannu ya gog

e bakinsa kawai ta riko wuyansa ta sake kai bakinta cikin nashi, yau ake drama me makon mace ta dan dinga tirjewa namiji na binta yau namijin ke tirjewa matar na kara rikoshi. Ganin ya kasa tirjewa ga dama sha’awa na kansa ya sa yadan lumshe ido nan fa mak

ulin kansa suka kunce, idanunta kyam ta rufesu saboda kar tsanar ta kara tasowa bata yadda ta bude idanunta ba nan fa Aminu ya manta da komai ya dagata ya daurata akan kujera, dayake Allah ya taimakeshi maganin nan sau biyu yasha bayan ana bukatar ya dinga

sha akai akai, sannan Allah ya taimakeshi yana zagaye da mutane masu addu’a a koda yaushe, wannan dalilin yasa yau maganin yai rauni sosai.

Ai fa nan komai ya kwance, Aminu an tafi sama lulayi, ya shiga sarrafa Ibty iya san ransa, itakam sai kawar da ka

i take tana wani irin nishi na tsananin dadin da bata taba ji ba, Aminu kam an mika dan ya dade yana lamari kafin………….

********

Dikowa daga kan karamin gadon tai tadan saki wata kara sannan ta rike bayanta dake amsawa, dakyar tadan mike ta jingina da

jikin gadan ta dan baza tagumi, yanzu itakam menene mafita? Ya zatai ta sa Aminu ya dawo yanda yake da? Ko dai ta lalaba Malam ne ta yarda da abinda yake santa dashi? Inyaso daga sanda Aminu ya dawo hayyacinsa ta ci zarafinsu?

Shiru ta sakeyi tana tunani

, auranta na farko wani dan kasuwa ta aura, asalinsa dan garinsu ne yai kudi yai auransa a birni, ita kuma tunda ta taso batada mashinshini ko kyauta akai da ita sai kiga abu bai yiwu ba, daga nan aka fara mata zargin maita, mahaifinta ya lalaba abokinsa w

ato mahaifin baban Na’ima akan suyi hadin auransu tunda itada yanzu kaf ‘yan garin bamai santa, balle akwai wanda akaso auransu saura kwana biyu ya mutu shikenan ‘yan gari suka tabbatar da maitarta, nan aka lalaba akai hadin aure ta aureshi a matsayin mata

rsa ta hudu, bayan ya kaita gidansa nan fa Hajiya dadin duniya ya fara mata dadi, ta fara zabga makirci da hada husuma iri iri a gidan, bayan ta haifi Na’imah ta hada husumar da har ta jawo ya saki matansa biyu, gasu kowacensu da ‘ya’yanta dayawa, randa as

iri ya tuno kuwa ya saketa ya kuma kwace ‘yarsa, wannan dalili yasa ta koma kauye, gashi lokacin mahaifinta ya rasu, dama mahaifiyarta ta dade da rasuwa.

Na’imah ta taso da tsanar ‘yan uwanta saboda tasan sune silar korar uwarta daga gidan, dan sanda aka

i sakin tana shekara goma sha biyu alokacin Hajiya duk ta gama hure mata kune ta gama sa mata tsanar ‘ya’yan baban.

Ta kuma dau alkawarin auran mai kudi inda zataji dadi. Na’imah sam a fuska bazaka taba gane halinta ba dan irin matan nan ne masu sanyin f

uska gashi batada magana sosai, shiyasa su ‘yan uwan ba wanda yasan tsanar da take musu.

🏌🏻

‍♀

️

[3/26, 9:11 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏ

ʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*n

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004jiki

2083371244

Zenith Bank

40*

Mikewa Hajiya tai ta dan kwantar da kanta

akan gado, lissafi takeyi menene zai ceceta? Ko dai ta yadda da abinda boka yace? Inyaso da zarar ta dan tattara kudi a gunsa sai ta san yanda zatai ta nemi wani babban malamin da zai halaka Ummy da Ibty? Kai ta girgiza da sauri dan itakam bazata yanda ta

zama inji ba.

Yanzu ita kadaice a duniya dole ne ta kwaci ta kanta ta kuma mori duniya iya san ranta yanzu meya dada? Na'imah ta gama saita rayuwarta gashinan bata mori duniya ba? Dole taje taga halinda Umar yake ciki dan ta tabbatar yana nan yana cigiya

rta ta ko ina.

Mikewa tai cikin karfin gwiwa gwara taje ta lalabashi ya sai mata gida a boye da dai ta yarda a dinga lalata da ita haka kamar wata injin taliya.

Fitowa tai sanye da hijabin ta kai kace mutuniyar arziki ce.

Adaidaita ta fada ta nufi umgu

war.

********

Aminu kam bayan ya samu nutsuwa yana daga gefenta ta baya hannunsa sakale a kugunta akan kujerar, ita kuma ta juya baya saboda bataso ya ganta.

Kansa na kan wuyanta sun dade a haka ba wanda yai magana, a hankali yace "Ke ba lafiya ba n

a sake wahalar dake."

Haryanzu bata juyo ba tadan girgiza kai a hankali tace "Indai zaka sauko kamar da wake zancen wahala? Sannan ni ba wahalar ma danasha."

Gyara kansa yai yace "Kema kin fahimci ba kamar da nake ba?"

Saura kadan ta juyo sai tai sauri

n tunawa, murmushi tadanyi tace "Bayan ni kadai ka canzawa? Taya zan kasa sani?"

Saman goshinsa ya shafa yace "Bansan meke damuna ba sam, gashi kasan raina nasan gaskiya amma sai naji kawai wani abu na tasomin kamar garwashi a raina."

"Yaya kaima wasa w

asa kana sakaci da addu'a bance bakayi ba amma dai......"

Meyasa kowa ke cewa ina sakaci da addu'a?

Tadanyi shiru tana tunanin abin cewa kafin tace "addu'a makamin mumuni, inhar kana aikata abinda ba'a san ranka ba kakeyi kaga kuwa kana bukatar dagewa d

a addu'a."

Shiru yadanyi ya matso da labansa kusa da kunnenta yace "Malama an samu bakin magana?"

Dan kasa tai dakai saboda wani yanayi data tsinci kanta a ciki "zaki iya tashi ko na taimaka miki? Dan na tabbatar rannan kinji haushi na daban taimakeki ba

." Yai maganar yana kokarin juyonda ita, kara dukunkunewa tai ya dan kalli saman kanta yace "Kunya? Na dauka daga sanda kika sumbaceni da kanki kin nunamin kin daina kunya ta."

Sake cusa jikinta tai jikin kujera cikin kunyar kalamansa, itakam Ya Aminu bat

asan ya zatai dashi da zarar magana ba.

Mikewa yai yaja vest da wando ya zura ya sa hannu ya dagota cak, kanta tasa a cikin kirjinsa saboda kunyar yanayin da take da kuma rashin san hada ido dashi.

Toilet dinta ya nufa da ita ya sauketa sannan ya ajiye

mata towel yaja kofar ya fita, shower ta kunna tana wanke jikinta kawai ta samu kanta da fashewa da kuka, sai yaushe ne zataji dadin rayuwa? Gashi kiri kiri ta fahimci mijinta ya damu da ita amma an shiga tsakaninsu? An hanasu nunawa juna kulawa? Haka tan

a wanka tana share kwallarta.

Shima Aminu toilet dinsa ya nufa ya sakarwa kansa ruwa yanajin wani nishadi na tasowa daga kasan ransa, tabbas zuciyarsa na san Ibty sosai babu tantama a ciki sannan yana samun nutsuwa tare da ita amma meyasa sam wani sa'in y

akejin tsana da kyamarta?

Dole ya dage da addu'a yana babba amma yarinya ita ke bashi shawara akan abinda ya kamata ya dinga yi?

*****

Acan bangaren Umar kuwa yana isa gida ya wuce bangarensa da niyyar zuwa yajawa Bilkisu kunne akan karta fadawa Abba

komai in ba so take ya bata takardar sakinta ba, me zai gani? Jakar kayansa ya gani a wajen gidan mamaki ya kamashi ya sa hannu zai bude yaji kofa a kulle, cikin zafin rai ya bubuga kofar yana kiranta ransa a matukar bace.

"Idan ka gama bige-bigen ka dau

ko jakarka ka biyoni." Abinda yaji an fada daga bayansa kenan, basai ya duba ba muryar Abba ce, nan fa hankalinsa yai mugun tashi, cikin sanyin jiki ya dau jakarsa yabi bayan Abba har bangarensu.

A falo Abba ya zauna shi kuma yai sum-sum ya zauna a kasa

kai kace mutumin arziki, Abba ya kalleshi yace "Na sa an rufe shagonka dan dama me makon riba kullum kara kankancewa yake na rasa ina kudin suke shiga. Sannan na rufe gidanka na d'auko 'yata dan ba baiwa na baka ba, sai abu na karshe ga takarda nan da biro

ka sauwake mata ka tattara ka koma gida dan na kira Yaya na sanar dashi zaka dawo."

Cikin sauri Umar ya dago yace "Abba!"

Abba ya kalleshi cikin takaici sannan yai murmushin bacin rai yace "Na fahimci nama laifi na baka Bilkisu da take nakashashiya aka

n Ibty da take da lafiya, sai dai wannan ba hujja bace da zaka wahalar da mara lafiya saboda burinka bai cika ba, sannan ka hana ita Ibtyn kwanciyar hankali a zaman aurenta, banda rashin sanin darajar addini a ina ka taba ganin anabin mace mai aure? Wannan

abinda ka aikata ya nunamin bazan iya barinka kacigaba da zama anan ba inhar ina bukatar kwanciyar hankalin Bilkisu da Ibtisam."

Shiru Umar yai sai dan hucin bacin rai da yakeyi, Abba ya kalleshi ya ce "Na kuma tabbatar tunda Aminu ya fadamin ba wannan

bane karanka na farko na bibiyar matarsa."

Cikin fishi ya dago dan ya tsani a dinga cewa matarsa, ganin yanda Abba kenkallansa yasa ya kauda kai gefe kafin yace "Amma Abba ni da kuka cuceni kuka kwacemin abinda nakeso fa? Duk hakurin danai baku gani ba? I

n har tanine wallahi dauke Ibty zanyi muje wani garin muyi rayuwarmu, amma nai haku........."

"Ka rufemin baki ko sai na fasashi? Mahaukacin banza da wofi." Cikin tsawa Abba ya fadi haka tare da katseshi, Umar ya dunkule hannu cikin tsananin bacin rai.

A

bba ya nunashi da yatsa yace "Bansan mahaukaci na raina ba sai yau, sauwake wa Bilkisu ka fitarmin daga gida."

Cikin gadara ya jawo takarda, da sauri Bilkisu ta turo kekenta da alama tana bakin kofa tana jin duk abinda suke cewa, tana hawaye ta karaso.

"

Abba banda saki dan Allah."

Cikin tsawa Abba ya nuna mata ciki yace "Wuce ciki."

Komawa tai tana kuka, Umar ya kalli Abba yace "in rubuta naga kamar inta rabu dani wani hali zata shiga."

Mamaki ya kama Abba ya dake yace "Ko ta shiga ko karta shiga ba da

muwarka bace, kaidai ka sauwake mata.”

Umar ya ajiye biro din yace “Zan sauwake mata in Aminu ya saki Ibty.”

Abba ya bude baki yana mai kallan mamaki yace “Amma bakada hankali ko?”

Umar ya kauda kai sannan ya mike ya dau jakarsa yace “Taita zama da igiy

ar aurena, in har anaso in saketa to nima a saki Ibtisam.” Ya fita yabar Abba da baki a bude.

Yana fita ya duba aljihunsa yaga yanada dubu daya nan ya wuce tasha dan tafiya kauyensu, a ransa yace “Tunda sunasan Bilkisu dayawa na tabbatar zasusa Aminu ya

saki Ibtisam su nemini, dama ban taba kusantar nakashashiyar nan ba balle ta haramta min aure tsakanina da Ibty.”

Nikaina Ayusher mamakin Umar ya hanani magana, lalai wannan kan bakomai sai…….

🏃🏻

‍♀

️

******

Daga can nesa Hajiya tasa aka sauketa, t

akowa tai tana bin bango dan haka kawai bata yadda da Ummy ba, kartaje tasa a dinga kula da zuwanta.

Harta iso kofar gate din ta dan kwallawa Baka kira daga gefe, yana zaune yanajin radio ya dago, ganin Hajiya yasa ya taso da sauri yazo yana gaisheta, ta

na dan yake tace “Bala! Aminu fa?”

Yace “Dazu ya dawo da shi da matarsa suna ciki.”

Gabanta ne ya fadi tace “tare suka dawo?”

Ya daga kai cikin fara’a yace “Kin dawo ne?”

Fuskarta ta tsuke sosai tace “Kana san cemin tare suka shiga mota daya?”

Yace “E

h tana gaba shi da ita, menene?”

“Baisa anyi cigiyar inda nake ba?”

Bala yai dariya yace “Inda kike Hajiya? Na dauka ai tafiya kikai dan shikam tunda ya shiga baifito ba.”

Kai Hajiya ya dafa shikenan magani ya karye, ta ina Aminu zai zauna kusa da Ibty?

Ita ta dauka yana can yana nemanta ashe yana ma tare da matarsa?

Kasa magana tai sai tafiya data fara, Bala yace “Hajiya?”

Daurewa tai ta kalleshi tace “Karka fadawa Aminu nazo dan Allah.”

Kai ya daga cikin rashin damuwa ya juya abinsa.

Wani jir jiri

Hajiya ta fara ji, dakyar ta rike bango tana yafiya, ta hau adaidaita ta wuce gun Malam.

Malam kam ana cemai tazo ya kwashe da dariya dan tabbas yasan dole tabi abinda yake so.

Hajiya ta shiga gaba daya ba laka a jikinta, gwiwowinta tasa a kasa ta hada

hannayenta tace “Malam na rokeka ka taimakeni ka taimakeni ka sa Aminu ya nemini, naji yanzu na hakura da matarsa nidai ya dawo dani gidana.”

Malam yai ‘yan dube dubensa yace “Wannan aikin babba ne dan yanzu rabin ayukanmu sun karye sai mun sake yin koma

i daga farko.”

Hajiya ta jinjina kai tace “Naji dan Allah nidai ka taimakeni.”

“To zaki kawo dubu dari uku in an gama ki kawo dubu dari biyu.”

A zabure ta kalleshi tace “Ina naga wannan uban kudin?”

Yace “To gaskiya ba abinda zan iya miki sai kin kawo

wannan kudin.”

Hakiya ta sake hade hannu tana rokansa, yace “Sai dai in zaki amince da abinda nace in yaso shi sai ya biya kudin, sai ki zauna a gunsa na sati biyu kacal, daga komai ya kammala zaki bargunsa ki koma gun Aminu.”

Shiru tai sai dai yanzu ka

m batada wata mafita, fuskarta ta shafa tace “Shikenan, na amince.”

{Hmmmmmm……..}

[3/28, 7:50 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*To

p Ten! Takun Haske Batch A*n

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004jiki

2083371244

Zenith Bank

41*

Abba yai shiru a falo gaba daya kansa ya dau zafi, koda wasa bai

taba tunanin Umar zai kwabamai magana haka ba. Umma ce ta fito daga dakin fuskarnan tata ba annuri sam, tana daga tsaye tace "Yanzu Abba abinda ka aikata yayi daidai?"

Juyowa yai ya mata kallan mamaki, tacigaba " A wani dalilin zamu yadda Ibtisam ta warga

za rayuwar Bilkisu? Shikenan ita baza'a barta taji da rashin lafiyarta ba sai an kara mata da bakin cikin kanwarta? To in har auran Bilkisu ya mutu itama Ibty a kashe nata susu su zauna tare Allah ya basu wasu mazajen."

Idanu ya ware sosai yana kallant

a dakyar ya daure yace "Me kike cewa?"

Ta kara tsuke fuska tace "Haryanzu ban sauko daga abinda Ibty tawa Bilkisu ba, wani irin san kai kake nunawa? Taya zata ruguza rayuwar 'yar uwarta sannan ita taje tai rayuwar da takeso?"

Kai ya jinjina cike da jima

mi yace "Sai yanzu na fahimci dalilin dayasa yarinyarnan sanda yaran nan yake takura mata ta kasa sanar da uwar data haifeta, to tana kula da wannan uwar tata bata damu da ita ba, bata damu da matsalar ta ba, me zaisa ta tareki? Wani irin rashin hali da ra

shin kirki ne zaisa ki dinga nuna banbanci tsakanin 'ya'yanki?"

"Kai ma ai banbancin kake nunawa, taya zaka manta da halinda Bilkisu take ciki? Da dalilin daya jefata? Haba! Dame yarinyarnan akeso taji? Da rashin lafiyarta ko da abinda ake mata."

Mikew

a yai ya kalleta a fusace, kamar zai cigaba da fada sai kuma ya fasa kawai ya fita daga falan yai ya wuceta ya shiga daki, kana kallan fuskarsa zakasan ransa yayi mugun baci.

Zama yai a bakin gado yana sake takaicin abinda kunnensa suka jiye mai, hankalin

ta daya kuwa? 'Ya'ya duk naki ne amma kiri kiri san kai yasa idanunki su rufe?

Umma kam ko a jikinta, dakin Bilkisu ta wuce cikin kunar rai itama.

Bilkisu na kwance a kan gado kuka kawai takeyi kai kace an rabata da wanda yake tsananin kaunarta ne.

Zam

a tai a kusa da ita tadan bubuga bayanta alamar lalashi tace "Ya isa hakanan, ke kukan me kikeyi? Bakiga Umar ba sanki yake ba? Me zaisa ki cigaba da wahalar da kanki akanshi?"

Kuka kawai takeyi dakyar tadan daure cikin kuka tace "Umma dan Allah ki roki A

bba yai hakuri ni wlh bazan iya zama da wani ba inba Ya Umar ba, na sani ba sona yake ba amma ni ina sanshi kuma a hakan nake sanshi, na kuma tabbatar a hankali shima zai canza zai dawo ya soni ya manta da Ibtisam."

Saman kanta ta shafa tace "Bilkisu hak

a kikeso ki cigaba da rayuwarki da wanda baya sanki?"

Tana kuka tace "Ya Umar fa abin tausayi ne, rana tsaka an rabashi da wacce yakeso na tabbatar shiyasa yake abubuwan nan daga sanda ya fahimci nice matarsa kuma ji ke tare dashi duk runtsi Allah zai dai

na."

Shiru Umma tai tana tsananin tausayinta, itakam bazata yarda a lalatawa yarinyar nan rayuwa ba ga jinya ga bacin rai, ita Ibty a kalla lafiyarta kalau ai.

*******

Ibty kam bayan ta fito daga wanka ta bude drawer dinta, dole fa ta tattaro hanka

lin dan mijinta, ga asiri ga shi tana kunya ai abin sai yai yawa, yanzun ma kamar dazu riga da wando ta saka, sun mata kyau sosai sai dai wannan sun kamata sama da na dazu, ta tufke kanta, ta fesa turare bata ko daura dankwali ba ta fito ta nufi kitchen, m

e zata dafa maidan sauki? Dan haryanzu bata gama ware wa ba gashi dama su biyu ne a gidan.

Farar talliyavta daura tare da miyan cabeji wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login