Showing 126001 words to 128353 words out of 128353 words

Chapter 43 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

31

ita ba zataci ba.

Yau aka samu matsala Ummy sun tafi gaisuwar wata yar aminiyarta ta rasu, ibty na gida kamar zataci babu saboda yunwa. Aminu ya shiga dakinta ya tarar da ita sai juyi take

akan gado, cikin sauri ya isa wajanta ya dagota zuwa jikinsa.

"Habibty ya akai? Me yake damunki?" Hannu ta saka ta riko shi tasa idanunta cikin nashi kamar zata fashe tace “Ummy bata gida, gashi yunwa nakeji wallahi kamar zan mutu haka nakeji." Gyara zama

nsa yai tare da kwantar da ita saman kirjinsa, bayanta da gashin kanta ya shiga shafawa cikin lallashi yace “To ko ni zan zake dantse na daure na dafa miki ko indomie ce kici? da kaina ma zan dafa miki, am sure zakiji dadinta."

Kallan mamaki tamai tace “K

ai din?”

Ya dan hadiyi yawon bakinsa shi kansa fada kawai yai dan bai san ma ya ake ba, kawai dan zolayarnan ne.

Mamaki ne ya kamashi dayaji tace “Banacin indomie, taliya ma bana so sai dai kaimin danwake." Aminu ya zaro ido yana kallanta yace “Danwake?”

Tadan shagwabe tana daga kai, yanzu ne lokacin da zaki dan moreshi ko ruwan tea tunda akai aurensu bataga ya dafa ba, Aminu fa an shiga tunani. Yanzu ina yasan yadda ake danwake? Abu daya ya sani ana saka kuka itama besan a wane lokaci ake amfani da ita

ba. Ibty da taji yayi shiru sai ta juyo ta kalleshi, ya sakar mata murmushi kamar gaske, cikin wasa kai yace.

"Wanda zan miki sai yafi na Ummy dadi, zaki sha mamakin dadinsa, kwanta ina zuwa." Ya kwantar da ita shi kuma ya fice daga dakin. Yana shiga daki

nsa ya sauke numfashi yana furzar da isa daga bakinsa. Kodai ya kira Aina ne ya sata ta dafa sai ya amso ya kai mata? Amman kuma idan ya kirata shi kuma cikin yace baya so dole fa shi din ne zai yi ko? To idan shima yayi cikin yace baya so fa?

"Kai ya sub

ahanallahi." Ya fada yana dafa bango. Wayarsa ya janyo ya kunna data, YouTube ya shiga ya nemo yadda ake danwaken, cikin sauri ya tashi ya nufi kitchen din duk abinda yaga an fada a hadin sai da ya dakko a ajiye a gefe, wanda be gani ba zaije ya tambayota

inda ta ajiye, Allah-Allah yake ya gama tun kafin yara suzo su ganshi dan baisan me zai ce musu ba.

Ta YouTube video Aminu ya kalla yai mata danwaken, shi kansa sai da ya burge kanshi ganin yadda komai ya kammala, sai dai fa ya bata kwanuka sunfi nawa g

aba daya kitchen din yayi kacha kacha ko ina flour da kuka.

Ya zubo a cikin dan bowl ya dakko tire ya dora yaji da mai da ruwan sha ya dauka ya nufi dakin. Lalai Aminu wai mantawa kake da shekarunka? Abinda zuciyarsa tace kenan, ya dan yi murmushi in bany

i ba yanzu sai na tsufa zanyi? Da wannan ya shiga dakin, ya tarar da ita ta fito daga wanka saboda tunda cikin nan ya sameta buni-buni tayi wanka ta zama tamkar wata kifi. Sai da ya ajiye tire din a kan gado sannan ya karasa ya taho da ita ta zauna.

Kalla

n bowl din tayi mamaki ya bayyana saman fuskarta dan ta dauka ma wata hidimar ya shiga ko kuma kila fita zaiyi ya siyo mata ya kawo mata, daga karshe ta yanke tunani akan lalai Ainah zai turawa tayi yaje ya dauko, dan Ummy tace zatasa a yi amma ita Ibtyn t

ace a barshi tanada ragowar, sam batasan daurawa su Ummy wahalar nan.

Baki ta saki tana ta kalleshi kafin ta kuma kallan danwaken ta janyo shi gabanta tasa yaji da mai tana cewa.

"Wai dagaske Habiby kaine kayi wannan?”

Hanaye yasa a aljihunsa ya dan zau

na tare da harde kafa yace “Ce miki akai shekarun danai a banza nai?”

Ta sake kallanshi cike da mamaki, ya dan daure fuska yace “Wai ke kin dauka ban iya ba?" Ya fada cike da kuri.

"Wallahi nasha mamaki, Ummy fa tace bata taba ganin ka soya koda kwai ba

bare abinci. A gida in an ganka a kitchen to tea ka shiga hadawa.”

"Af yo komai nawa ta sani ne an gaya miki? Kinga yanzu sai kije ki basu labarina." Tana motsawa tace dashi “A’a fa karfa ka cika baki, ka bari baki ne zai bada amsar girkin naka ba wai ido

ba." Ta diba shi kuma yai saurin rintsa ido yana shafa tafukan hannayensa kamar mai shafa mai. In baiyi dadi ba ai ya bada kanshi.

Shiru beji tace komai ba hakan yasa shi kuma rintsa ido yasan an samu matsala.

Ya juyo cikin dakewa da rashin san nuna abi

nda ke ransa yace “ya akai?" Ya tambayeta yana bin yanayinta da kallo.

"Me aka yi?" Ta fada tana kallanshi tana kokarin boye abinda ke ranta.

Ido ya kankance yana mata wani kallo, fork tasa ta sake dauka takai bakinta, bata ko sake magana ba sai dataci s

poon hudu, ai Aminu besan lokacin da ya saki murmushi dan ya tabbata komai yayi.

"Habiby gaskiya ka iya wallahi, ni daga yanzu ma kai zaka dinga yi min yafi na Ummy dadi."

"Ke! Me zan dinga yi?" Kallanshi tayi cike da marairaicewa tace masa.

"Danwaken."

Aminu yace.

"Tab kin maidani kuku? Hajiya sorry bazanyi karya ba dan bazan iya ba.”

"Allah ba ruwana babyn ciki na ne yake so bani ba.”

Suna ‘yar hirar nan ta cinye tas da yake waya yake yi sai ta tashi ta kai kayan kitchen anan ta tarar da aika-aikar

da yayi.

Goshinta ta dafe lalai taci dan wake da wahala, dan dacin wannan dan waken da wannan uban aiki ai gwara ba’aci ba.

Nan ta shiga tattare kwanukan da aka bata sannan ta shiga wanke-wanke, sai datai wajen rabi ya shigo tare da kamo kugunta ya rike

sannan ya kwantar da kansa a kafadarta yace “yaushe aka tara kwanuka haka? Dazu fa da na shigo babu kwanukan wanke-wanke.”

Kallansa tadanyi kadan tace “Dan wake ne ya tara mana.”

Baki yadan bude yace “Wai nine na tara kenan?”

Murmushi tadanyi “Madam ka

rfa kice in tayaki dan bansan ya akeyi ba. Nadaiyi sanda ina karatu a kasar waje amma ban iya ba.”

Ta dan yi kasa dakai tanayi yana tsaye a jikinta suna ‘yar hira kafin daga baya ya tayata kifa kwanuka har suka gama.

Yadan kalleta yace “Sai muje yanzu ku

ma a bani ladan aiki." Ya fada yana jan hannunta ya nufi dakinsa.

Suna shiga daki tana dariya tace “Nawa ne kudin?" Ta cigaba da dariya kasa kasa.

"A'a wallahi ni bana kudi nai miki ba, zuwa zaki nan gurin." Ya nuna kusa dashi yana gyara mata filo.

"Yay

a an kusa kiran sallah fa." Ya shafa kai saboda gabaki daya yasawa ransa dan haka ya mike ya kamota.

"Dama ance ‘yan yaran nan sufi jan aji gurin shimfida.”

Suka saki dariya tare da hawa kan gadon. Daga nan fa suka ci gaba da farantawa juna rai, Aminu ga

ba daya yayi laushi a hannun ‘yar yarinyar da ya raina, a koda yaushe in suna tare har mamakin kansa yake, sai dai fa in suna cikin mutane yana nuna fa shi namiji ne babba, ita abin ma dariya yake bata wani sa’in in gaga ya daure a gaban mutane.

Lalai ba

shakka su Hajiya ne suka juyar mai da hankali dan mutum ne mai saukin kai da yiwa mutum uzuri in yai laifi.

***********

Dawowarta daga makaranta kenan ta baje a parlor ta kwanta tana ta bacci, gajiyar da tayi ne ya hanata ko cire hijabi bare ta nemi

abinci. Cikin bacci taji tamkar ana sallama amman ta kasa tashi, duk a tunaninta ma mafarki takeyi.

"Ibtisam." Umma ta kira sunanta tana bugun kafarta. Ibty ta bude ido a hankali, wa zata gaji? Ai da sauri ta tashi ta rungume ta tana murna.

"Umma sannunk

u da zuwa, Yaya Bilkisu hardake?"

Umma ta girgiza kai tace “Yanzu in barawo ne ya shigo har sata sai yai kina baje kina bacci.”

Sai a lokacin ta dan rufe baki tace “A bude nabar kofar?”

Umma ta harareta hakan yasata yin murmushi tace “Zan kula nan gaba.

”

Bilkisu tadan tura kekenta bayan ta gama dan zagaya falan dan yau ne zuwanta na farko tace “Ke kuma a haka kike sha'awar kwanciya? Kinga a yadda muka tarar dake kuwa? Ke a takure babynmu a takure?”

Kai ta sunkuyar dakai cike da jin kunyar Umma yanzu fa

kowa yasan mai tai ta samu cikin ko?

Bata san ana magana akan cikin nan saboda kunya takeji sosai.

"Nima dawowata daga makaranta kenan na kwanta sai bacci, bari na kawo muku ruwa."

"A'a bashi wucewa zamuyi Iman ta dage sai mun biyo." Cewar Umma tana sa

ke kallan Ibty.

"Ina kukaje?"

"Asibiti." Iman ta fada tana shiga kitchen.

"Waye ba lafiya Umma?"

"Ba kowa Bilkisu muka kai, tunda tai barin nan take ciwon mara shine mukaje saboda ina tunanin ko be gama ficewa ba, munje kuma an duba lafiya lau."

Suka

hada ido da Bilkisu, nan da nan na mata sannu. Hira suka taba dan Umma yanzu tana ta kokarin jan Ibty ta fahimci lalai duk abinda ya faru itace sila da ta ja Ibty a jiki to fa da duk hakan bata faru ba.

(Iyaye dan Allah mu dinga kokarin jan ‘ya’yan mu a j

iki especially ‘ya’ya mata dan sai kin jasu a jiki ne zasu iya sanar dake matsalarsu.)

Bayan sun gama hira ne su Umma suka tashi suka tafi ita kuma taje tai wanka.

Assignment din da aka basu tai shiga yin browsing tana yi Aminu ya dawo, ya zauna sukayi

a tare ta rakashi dakinsa yai wanka sannan suka fito falo.

******

A bangaren Umar kuwa gaba daya yanzu Allah ya jarabceshi da mugun san Bilkisu, ga sha’awa dake damunsa kullum in zai kwanta, tabbas yaji dadin saduwa da ita gashi yanzu duk yanda ya ba

ta hakuri ta kafe ta tsare tace a’a.

Gaba daya ba wanda yake kulashi yanzu a gidan, abinci wannan a bakin kofarsa Iman ke ajiyemai tai tafiyarta, Abba kuma ya hanashi shiga cikin gidanshi.

Rayuwa tamai zafi yanzu har letters yake rubutawa Bilkisu ya sa a

kwanon dayaci abinci, text kuwa kullum sai ya mata amma ba reply, gaba daya ya canza ya maida hankalinsa gun aiki dan ba wanda ke kulashi, kauye ma Kawunsa yace in har zaizo ta ya tabbatar ya daidaita da matarsa, ita kanta Goggo taki kulashi.

Wannan abu

yamai yawa abokan ma yanzu duk sun daina harka dashi.

Watansu biyar da rabuwa zazzabi ya kamashi cikin dare, ya turawa Bilkisu sako tare da sanar da ita halin da yake ciki, kamar bazata kula ba sai kuma ta tuna halin data shiga a dalilin kin zuwan dayai,

haka ta fito va tare da sanin kowa ba ta nufi bangarensa, a hankali tadan kwankwasa yana daga ciki ya mike dakyar dan ko abincin rana baici ba, yana tafe yana fatan Allah yasa itace, a hankali ya bude kofar nan suka hada ido, fuska ta daure tana neman juy

awa, da sauri ya rikota yana cewa “Billy ki yafemin dan Allah!”

Tsayawa tai bata juyo ba, hannu yasa a kan kafadarta zafin dataji ne yasa tadan juyo, bakinta nadan rawa tace “Da gaske bazaka rubuta takarda ta ba?”

Ya girgiza kai yace “Ko a haka zamu dawa

mma bazan sakeki ba, ki tuna ni mijinki ne, nayi iya kokarina na ganin kin hakura, to amma tunda kinki zan umarceki a matsayina na mijinki ki koma dakinki gobe.”

Yanayinta ne ya canza ya dawo gabanta ya tsuguna yace “Billy please…….”

Tausayinshi ne ya ka

mata ta rike hannunsa tace “Kasha magani?”

Ai bai jira komai ba ya rungumeta yace “Dan Allah ki dawo, wallahi Allah bazan sake wulakantaki ba in har na kuma duk hukuncin da kika ga dama ki dauka.”

Nan suka daidaita washegari ta sanar dasu Abba ta koma da

kinta.

Umar gaba daya ya canza, tunsanda yaji Ibtisam nada ciki ya tsani kanshi, ita gata can tana rainon cikinta amma shi dan asara ya jawo sanadiyar zubar da cikin datai.

Wannan dalili yasa ya kara kaimi gun kula da Bilkisu yana kuma fatan Allah ya bas

u wani cikin.

Hankalinsu Abba yanzu ya kwanta dan Umar ya canza banda zafin rai wanda haryanzu yake dashi.

*****

Cikin Ibty yakai wata tara haihuwa yau ko gobe, ta ajiye karatunta a level 3 akan in ta haihu zata dawo ta cigaba, Aminu da kanshi ya nemi

alfarma aka kawo Iman gidan ta zauna da ita, sannan duk weekend Ainah na zuwa tai kwana biyu sai ta koma.

Kulawa ta ko ina tana samu sau da dama takan yi kuka sai taga anya ta cancanci wannan farincikin kuwa? Ilham da Islam na tsananin santa ita ma tana

iya kacin kokarin ta, har addu’a take a ranta akan kada Allah ya bata damar nuna banbanci tsakaninsu da ‘ya’yan da zata haifa nan gaba.

Alhamdulila nakuda ta zo mata suka nufi asibiti inda ta haifi danta namiji, Aminu ya sa mashi sunan Abdullahi dan yana

san sunan.

Aminu bai kara waiwayar zuri’ar Hajiya ba bai kuma sake bi takansu ba, mahaifin Na’imah dai suna gaisawa wani sa’in har gida yake zuwa ya gaisheshi banda shi bai bi takan kowa a cikinsu, a koda yaushe yana godewa Allah daya kawo Ibtisam cikin

rayuwarsa, yanzu hankalinsa a kwance yake sai dan abinda ba’a rasa ba wanda dukanmu dani da ke mai karantawa munsan rayuwar aure dole in ana tare wani sa’in za’a samu matsala…..

Allah ya kara daidaita rayuwar auranmu da mazajenmu, wanda basuyi ba kuma

Allah ya kawo miji na gari.

****

Alhamdulila ina godiya ga duk wanda ya sai novel dinnan ya karanta, wadanda kuma suke san siya su min magana ta number dake sama

☝

🏻

Ku biyoni a cikin wani saban littafin kar ku damu free zanyi

🤪

Ayusher Ce



Documented by H.M.G

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login