Showing 81001 words to 84000 words out of 128353 words

Chapter 28 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

18

yi kasa dashi tace "Ummy to ya zanyi?"

Tausayinta ne ya kamata tace "Allah dai ya mik

i albarka, nasa anata sauka insha Allahu duk wani kadarin matarnan ya kusa zuwa karshe, kedai ki kara hakuri ki kuma rungumi mijinki."

Cikin girmamawa ta amsa da to sannan sukai dan hira sukai sallama.

Kallan wayar tai tare da sauke ajiyar zuciya, dole

fa ta mike tsaye da alama kamar yanda kowa ke sanar mata.

*****

Aminu kam lokacin tashi yanayi ya mike bai kara lokaci ba kamar yanda ya saba, gaba daya hankalinsa yau yini yai yana tunanin Ibty, sam ya kasa manta yanayin daya shiga daren jiya, anya ba

dan ya dade bai kusanci mace bane? Dan ji yake kamar bai taba jin dadin mace ba irin jiya.

In wannan tunanin yazo mai da sauri yake kawar dashi da cewar ya manta saboda shekararshi biyar da rasuwar Naimah.

Jakarsa ya dauko da flask din Hajiya kasan ran

sa murmushi ne fal, shikam yanzu yanaji bazai iya hakuri da Ibty ba dole zai ajiye duk wani girmansa ya koya mata sanshi, dan shikam yanzu ji yake yana bukatarta a kusa dashi.

Da wannan tunani ya shiga mota, yana tafe yana dan murmushi shi kansa har mamak

in kanshi yakeyi, yana kokarin shan layin gidansu yaga samari guda biyar a tsaye kamar jiransa sukeyi, yana neman wucesu yaga sun nunamai sanda daidai saitin glass din motarsa ta gaba. Ja yai tare da yin parking, nan idanunsa suka sauka akan Umar wanda yak

e sanye da riga da wando na jeans, saman goshinsa yadan shafa lalai mutumin nan kanshi ba daya ba, glass din motarsa yada zuge sannan ya dan sa hannu yamai alamar yazo irin kiran da akewa yara.

Umar ya kalleshi sannan ya kalli abokansa, ya nuna kansa da y

atsa yace “Kana nufin ni nazo?”

Kai Aminu ya daga mai tare da sake mai alamar da hannunsa, Umar wani irin zazzafan takaici da zuciya ne ya debeshi a fusace ya amshi sadar goraf sake hannun abokinsa ya daga sama zai makawa motar, “Kana sauke gorar nan ka t

abbatar zakai kwana cell.”

Juyowa yai ya bugawa Aminu wani kallo yace “Kana tunanin ina tsoro?”

Wayarsa ya fito dashi ya danna kiran wani dake jiki an rubusa DPO nunawa Umar yai yace “Bismillah.”

Umar a fusace ya sake dagawa zai maka wani abokinsa daga

ciki ya rike gorar yace “Kai nifa wlh inada yaro karami a gida bazaka sani zuwa jail ba.”

Umar ya kalleshi tare da fincike jikinsa cikin bacin rai, Aminu ya kalli abokan yace “Nawa ya baku kuka zo aikata abu haka? Duk wanda ya bar wannan wasan shirmen za

n bashi dubu ashirin.”

Ai kallan juna sukai basu tsaya yin wani tunani ba suka matso suna dan rusunawa Aminu, “Yallabai tuba muke wlh muma ba’a san ranmu ya kwaso mu ba.”

Aminu ya kalli Umar wanda ke wani irin huci, cikin fishi ya daga gorar nan zai sake

makawa ai nan abokansa suka hankadashi gefe iya karfinsu ya fadi kasa, ga dama kafarsa haryanzu a kumbure take, idanunsa sukai jaaa ya kafesu da ido yana muzurai yama kasa magana, yana tsaye Aminu ya turawa kowa kudi sannan yasa sumai alkawari akan bazasu

kara aikata hakan ba, nan suka juya suka tafi suna tafi suna murna.

Aminu ya kalli Umar dake yashe a cikin kasa, kai ya girgiza yace “Yauma kana san bashin na motar ne?”

Umar ya mike cikin zafi yace “Na rantse da Allah in baka shiga hankalinka ba zan yi

aika aika.”

“Aika aika? Wadanda suka aikata bakaga ya karshen rayuwarsu ta kasance ba? Wai kai in tambayeka, aikin yi ne bakadashi ko kuma gaba daya rayuwarka akan matata ka daurata.”

A zabure yace “Matarka?”

“Taka ce da?”

Huci ya fara yi cikin kunar

rai, “Ka koma gida ka kula da matarka kabar cusa hanci gun matar wani wacce ko sunanka basanji take ba.”

Kafin Umar yai magana Aminu yaja motarsa, kai ya girgiza cikin bacin rai, yana murnar zuwa gun matarsa wacen dakikin na neman batamai rai.

******

A can gida kuwa Ibty yau ta dage tai kwalliya sosai cikin riga da skirt na atamfa, dinkin ya kamata sosai, yauce rana ta farko datasa kaya ba ko dan karamin mayafi a gidan, ta gyara gashinta tadan daura dankwalli irin wanda ake yayin nan, bayan kanta gashi

nta ya kwanta tayi kyau sosai.

Kallan kanta tai anya zata iya fita a haka? Su Islam suna Islamiya ga Iman ta fita wai zata gidan kawarta, jin alamun motar Aminu yasa tadan sauke ajiyar zuciya dolefa ta jajirce ita ba kidahuma ba bakuma mara ilimi ba gwar

a ta nuna wayewarta.

Fitowa tai daga dakin ta nufi falanshi, shima cikin jin dadi ya fito daga mota, duk da ya boye jin dadin amma tabbas zaka fahimci farinciki a ransa.

Kofarsa ya bude tana tsaye, kallanta yai daga sama har kasa, wani irin sanyi da k

wanciyar hankali ne ya ratsashi, itama kallansa tai cikin jin dadi tace “Sannu da dawowa.”

Karasowa ciki yai yace “ Yauwa.”

Tana tsaye harya karaso inda take, hannu tasa za ta amshi kayan hannunsa “Kin warke ne da kike neman daukan kaya?” Tambayar daya m

ata kenan, cikin maganar rada.

Kanta tai kasa dashi tace “Tun dazu nacema na warke ai.”

“Taka na gani.”

Dagowa tai cikin murmushi zatai magana, idanunsu suka hadu da juna, bakinsa ya motsa yanaso yace tayi kyau sai dai baisan taya zaice mata ba.

Kanta

tadan sauke tare da cewa “Allah Yaya nidai zolayata kawai kakesanyi.”

Kayan ya mika mata yace “Ungo tunda wahala kikeso.”

Hannunta ta maida baya tace “Aikuma yanzu na tuna ashe banda lafiya.”

Murmushi yai yace “Yanzu?”

Kai ta daga tace “Kaifa ka tuna

min.”

Murmushi taga ya sakeyi, wani irin dadi ne ya kamata, tabbas tanaso taga Aminu na murmushi, shikam ji yake kamar ya rungumota jikinsa amma taya zai jawota? Kartai tunanin wani abin daban.

Idanunsa yadan rufe ya bude, ayi komai a hankali Malam kark

a tsoratata lokaci daya.

Abinda yazo mai kenan ya wuce ciki bayan ya ajiye flask din, kallan flask din tai da alana shine wanda Hajiya ta bashi, budewabtai ta leka ciki, kunu ne, cikin kunar rai tace “Wannan matar in an bibiya abu ta hada a kunun nan.” Ad

du’a ta shiga yi akan Allah ya tsaresu ita da Aminu daga sharrin matarnan.

Kai flask din kitchen tai ta zubarda ragowar kunun sannan ta fito ta nufi dakinsa bayan ta jeramai abinci akan dining.

Ya sa riga kenan ta shiga, “Kinyi missing dan na kula buri

nki ki shigo ina sa kaya.”

Da sauri tadan juya baya tace “Nidai Allah bance ba.”

“Kingama kunyar tawa?”

Tadan kalleshi kadan ta dauka bazaiyi zancen jiya ba, “Ba kunya ta kike ba tun safe?”

“Kaima ai kunyata kake yanzu ne ka ware.”

Kallanta yai ya tak

o zuwa inda take, tadan sauke kanta harya matso inda take, daf da kunnenta ya matso jitai numfashinta na neman daukewa “Yaushe nace ina kunyarki?”

Tadan dago tanasan yin magana sai dai yanda ya matso daf da ita yasa ta kasa magana sai dan kif kif da ido

datai, jiyai kansa yadan wani sara kadan da sauri yadan matsa kadan daga inda take.

Matsowa tai tadan rike hannunsa cikin kulawa, kallan hannun yai jiyai kamar an doramai garwashin wuta, da sauri ya fizge hannunsa daga hannunta, sannan ya xauna a bakin g

ado.

Mamaki ya sake kamata tace “Ya Aminu?”

Kansa yadan dafe ya dan daure yace “Karki damu, bani paracetamol, da sauri ta mikomai ya amsa ta bashi ruwa, ya hadiya.

Dan kishingida yai yace “Jeki zan dan huta maybe zai lafa.”

Gaba daya jikinta ne yai

sanyi matsowa tai tadan dauko pillow ta dan fara kokarin daga kansa, jiyai yanzun ma kamar garwashi na tabashi, bai san sanda yadan tureta ba, baya ta danyi mamaki ya hanata ko magana, shikanshi mamaki ne ya kamashi, kallanta yai jiki a sanyaye “Sorry bans

an hanuna ya tureki ba.”

Kallansa tai jikinta duk yai sanyi ta fito daga dakin, yanzun nan suke hira kamar gaske me kuma ya faru?

Jitai gabanta na faduwa da sauri ta zauna akan kujera tana addu’a itakam meya samu Ya Aminu?

Abinda yabashi mamaki tana fi

ta daga dakin kansa ya daina ciwo, meyasa ya tureta? Bayan tun safe yake kewarta? Meyasa inta tabashi yakeji kamar garwashin wuta?

Idanunsa yadan rufe da alama aikin dayai ne ko kuma bacin ran Umar ne yasa yakejin ba dadi, dan da in Umar yayi abu a hauka

yake daukanshi.

********

A bangaren Hajiya kuwa deban maganin nan tai tana tunanin intai kunu gobe dashi tabbas batasan ta yanda zata bashi ba, to meya kamata tai? Tea ya kamata ta hada dashi sai ta nemi yazo suyi magana da daddare inyaso sai tasan y

anda tai tasashi yasha.

To amma maganar me zasuyi?

Ko tamai maganar tsohon mijinta mahaifin Na’imah? Tamai sharri akan yanasan ta bashi kudi? Kenan intai haka ta daki tsuntsu da dutse biyu gashi zata samu kudi ga kuma ta bashi tea.

Dariyar mugunta tai

, tabbas duk abinda kake nema a duniya indai da kudi da kuma Malam to komai mai yiwuwa ne, wannan maganar ita Na’imah ta fara fada mata sanda ta daukota daga kauye, murmushi tai tace “Kin tafi kin barni ganinan inata amfani da shawarwarinki.”

*****

{Hm

mm nikam wannan tsinaniyar matar ta isheni

🤧

}

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004

2083371244

Zenith Bankima

34

Ibty gaba daya ta kasa gane meke damun Aminu, yanzun ma da yake zaune yanacin abinci a dinning ko kai yaki dagawa ya kalleta, hankalin

ta ya tashi ko dai shigar datai ne baisan kalla? Amma ai ba haka ya nunaba farko daya ganta, mikewa tai tadan matso kusa dashi tace “in karama salad din?”

Yana dagowa suka hada ido yaji kansa ya wani sara, cikin dan zafin murya yace “Please dan kyaleni, i

n inaso zan kara da kaina.”

Kallansa tai jitai gaba daya idanunta na neman kawo ruwa, jiki a sanyaye ta matsa daga gun ta wuce bangarenta.

Zama tai akan kujera tana tunanin abinda ke faruwa, menene wannan? Canji lokaci daya?

Wayarta ce ta fara kara, ja

wota tai tana kallan sunan Yaya Bilkisu a jikin wayar, ba shakka Iman ko Umma ne wani ya bata number dan dai itakam sanda taje bata ba taba.

Dauka tai tare da yin sallama.

“Ibtisam na rokeki da Allah ki dawo gareni, wallahi in har na rasaki gaba daya ray

uwata zata iya salwanta, ni na amince mu gudu daga garin koma ina ne na baki xabi ki zaba……”

Gabanta ne yai wani irin faduwa jin muryar Umar na wannan sharhin, cikin fada tace “Ya Umar bakada hankali ne? Ka amshi wayar matarka ka kirani? Sannan ka dingami

n zancen hauka na marasa tunani?”

Abinda tace kenan ta fara kokarin zare wayar daga kunnenta zata kashe, “Wallahi inhar baki dawo gareni ba ki shirya ganin ‘yar uwarki a gadan asibiti, in nan ma bakiji ba to ki shirya ganin ta a kabari.”

Kamshin turaren

data juyo ne yasa tai sauri sauke wayar ta kashe, tana maida wani irin numfashi na ban tsoro, dagowa tai tace “Ya Aminu, nikam inaji Ya Umar ba kalau yake ba, tsoro nake karya yiwa Yyata wani abin.”

Yanda taga Aminu na kallanta ne yasa tadanyi shiru, gaba

nta ya fara wani irin faduwa, dan kallan daya mata kallo ne na wanda bai taba yi mata ba a iya xamansu, tsanarta ce karara a idanunsa.

“Dama ni nayi mamakin tareni dayai, da alama ke kika sanar dashi lokacin dawowa ta.”

Cikin rashin fahimtar kalamansa ta

ce “Wana sanar?” Dan ita batamasan sun hadu da Umar ba. Matsowa taga yayi cikin karfi yasa hannu ya finciki wayarta ya kalli sunan Yayarta, ya cila mata wayar yace “Bravo! Kenan sunan yayarki ko ince a wayar yayarki kuke waya dashi?”

Mikewa tadanyi tace “

Yaya nikam meya sameka lokaci daya? Wace irin magana kakeyi?”

Yatsa ya nuna mata cikin matukar bacin rai, idanunsa sunyi wani irin jaa “in kika kuskura kika kusamin wallahi zaki fuskanci tsananin bacin raina. In har mijin yayarki kikeso ki tafi gunshi man

a.”

Baki ta bude sam kwakwalwarta ta kasa daukan kalaman da Aminu ke jefanta dashi, juyawa taga yayi. Aminu kam yana shiga dakinsa ya dafe saman goshinsa, meke damunshi? Hakuri fa yaje ya bata na abinda ya aikata mata yaji tana waya, taya zai zargi alakar

ta da Umar bayan yasan komai, bayan shine yake zolayarta dan kawai yaga bacin ranta? Gefen kansa yasan buga, Aminu kanka daya kuwa? Meya sameka lokaci kankani? Yanzu gashican na tabbatar kasa yarinyar nan kuka.

Mikewa yai da sauri dan jiyai bazai jure gan

in tana kuka akan abinda ya aikata ba, dan har hangota yai tana kuka da shesheka.

Yana daf da shiga falan yajuyo kukanta, jiyai zuciyarsa na tafasa da tsananin tausayinta, kofa ya bude ya shiga a durkushe ya ganta a kasa tana kuka sosaj, da alama kalamans

a sunyi matukar kona mata rai, haryasa kafa zai shiga yaji sam baisan ganin ta, juyawa yai da sauri tare da komawa dakinsa.

Ibty kam kalaman Aminu sun tsaya mata a kwakwalwa, da ace zolayarta yake bazataji haushi ba amma wannan yanayin nashi har ransa yak

e magana.

Haka ta gaji da kukanta ta daure ta mike, wayarta ta kashe gaba daya ta wuce kitchen kawai ta hau yin wanke wanke.

Sai daf da magrib Iman ta dawo tare dasu Islam, kallo daya ta mata tasan tayi kuka sai dai a cewar Ibty ciwon kaine yake damunta.

Har dare yai yara suka kwanta tai wanka tasa kayan bacci ta nufi bangaren Aminu dauke da kayan tea dinsa, zataje in laifi tamai ma ta bashi hakuri dan bazata iya jure bacin ran nan ba, hartakai bakin kofa tace “Kodai dama budurcinta kawai yakeso? Ya gama

yanzu baya bukatarta?”

Kai ta girgiza da sauri dan Aminu ba irin mazan nan bane, sannan jiya soyayya tsantsa ya nuna mata bawai kawai saduwa yake so ba.

Shiga tai jiki a sanyaye bakinta dauke da sallama, lumshe ido yai cikin jin dadi a zuciyarsa, da ala

ma ta ware dan sam hankalinsa yaki kwanciya.

Yana juyowa zai amsa sallama yaji kansa ya dan sara, wata irin muguwar tsanar ganinta ne ya shigeshi, kai ya kauda cikin kunar rai ya amsa sallamar kamar bayaso.

A hankali ta karasa ta ajiye tire din tace “Yay

a in laifi na maka dan Allah ka……..”

Hannu yasa a saman kunnensa ya kalleta yace “Can you please leave me alone? I just hate it! Dan Allah ki kyaleni naji da abinda ke damuna.”

Kallansa tai a hankali ta mike kamar wacce kwai ya fashewa a ciki, tana nema

n kwanciya yace “Please fita daga dakin nan.”

Juyowa tai da sauri tana share hawaye tace “Yaya na fadamaka nawa Ummy alkawari akan kwana anan kullum.”

“Okay! Ki zauna ni zan barmiki dakin.”

Kallansa tai mamaki ya hanata magana, Inalilahi wa ina ilaihi r

aji’un ya Allah ka dubeni, meke faruwa?

Bata gama tunani ba kawai taga yabar dakin, zama tai a bakin gado kawai ta fara hawaye, can ta share tace “Koma menene am sure in aka tashi daga bacci zai huce, sai na bashi hakuri.”

Aminu kam falo ya fito ya zauna

ya fara aikinsa, wajen karfe goma Hajiya tamai waya akan wai maganinta batasan ya kare ba sai yanzu datazo sha.

Hankali a tashe ya fito ya shiga mota, Ibty sai jin alamun fita da mota ta fito a guje, kafin ta karaso ya fita, ina zaije a daren nan? Baiko

fada mata ba? Bayan ko masallaci zaije yana ce mata ya wuce masallaci? Zama tai a bakin gado ta zuba uban tagumi, yau itakam meke faruwa? Jiya sunsha soyayya yau kuma kiyayya?

****

Hajiya kuwa mikewa tai ta dafa tea da maganin nan ta ajiye a falo da cup.

Tana jin sallamar Aminu tadan mike a hankali tace “Aminu kai hakuri na tasoka da daddare.”

Ajiye ledar maganin yai yace “Haba Hajiya! Ko tsakar dare ne bana tashi na siyo ba balle yanzu?”

Murmushi tai ta amsa tana godiya, kallansa tai tace “Kasha tea d

an nasan kaunarka da shan tea.”

“Kinsan bansha ba yau, dazu Ib…..” sai kuma yai shiru jin bama yasan ya ambaci sunanta, ita kuwa dama so take ta tabbatar da iya aikin da maganin yai, tace “Lafiyarta dai kalau ko?”

Kai yadan girgiza ya zuba tea yace “Aure

n yarinya ko bacin rai, nidai banaji zanyi sa’ar mace bayan rasuwar Na’imah.”

Wani sanyin dadi ne ya rufeta tace “Ka daure kasha tea din, sannan ka dinga mata uzuri kaga yarinyace sai hakuri.”

Tea ya hada ya fara sha yace “Bazaki gane bane Hajiya.”

Itak

am wani dadi ne yake kamata ganin yana shan tea din nanfa ta far janshi da ‘yar hira harya shanye sannan tace “Kayan abinci nama sun danyi kasa.”

“Subhanallah Hajiya kiyi hakuri yanzu zan tura miki kudi.”

Nan ya tura mata 100k yace “Kiyi hakuri gaba daya

bansan meke damuna ba harna manta.”

Murmushi tai tace “Karka damu ai sai ana uzuri.”

Haka ya taso ya nufi gida, yana shiga falo itama ta bude kofar ta fito daga daki dan dama tunda taji motsinsa ta mike, yanzu ta zare hijab dinta sanye take da rigar bac

i mai hannun vest da wando three quater, ta dan sa hula a kanta. Tayi shiga najan ra’ayi sosai.

Idanunsa ya runtse dan sam bai kaunar ganinta ji yake kamar yaga wani dodo mai mumunan halitta. Kansa ya dauke da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login