Showing 108001 words to 111000 words out of 128353 words
haka ma Iman to anyi sa'a ita Iman da kanta take nemawa kanta abinda takeso ba kamar Ibty ba.
Daga haka suka sa
mu Bilkisu taci abincin sannan suka samu ta fara walwala ana ta hira da ita sama-sama, duk da haka zuciyarta na wajan Umar da kuma ina zashi? Wannan abun yana damunta sosai, tana so tasan yana wane wajan ko hankalin da yake ciki.
*******
A kwana a tash
i asarar mai rai.....
Yau sati biyu kenan Hajiya na zaune cikin wannan dakin kwani irin ciwon ciki take fama dashi wanda in har ya motsa mata duk irin maganin da zai bata batajin dadi har sai mutumin nan yazo yayi mu'amala da ita ta baya kamar yadda ya sa
ba yi.
Kwananta goma a gurinsa saboda ciwon da yake damunta yasa bata tafi ba, kuma ko ya bartama bata da wajan zuwa. Hajiya kwance tana ta faman murkususu abin har ya fara bawa bokanta tsoro, yace ta shirya zata bar musu gida saboda yana tsoran ta mutu
a gurin shi ace ai shine ya kasheta tunda kowa yasan wannan dakin da take nashi ne. Cikin azabar ciwo tun abun na cinta a hankali yanzu ko zama bata iya yi saboda wajan ciwo yake sai dai tayi goho. Babban tashin hankali mutumin da yake zuwa safe da rana d
a daddare yau kwana biyu kenan ko lekota baiyi ba, dan kayan dadin dayake kawo mata suma duk sun kare, ga yunwa ga azaba ga babu kudi.
**
Tana kishingide gun sai uban zugi yake mata amma duk da haka dan bala'i neman mutumin nan takeyi ko shi ko boka wa
ni yazo ya biya mata bukata.
A fusace ya bude labulen dakin da take a kwance ya kalleta cikin jin haushi. "Dama da nace ki shirya zaki barmin guri ashe bakiji ba?" Cikin wahalar ciwo Hajiya tace. "Ina zanje?" Ya rike baki "Da ina kike zaune? Koda a karkas
hina kike? Ni da ba mahaifinki ba bakuma mijinki ba ina zan dauki nauyin muhalinki?"
Cikin zafin rai Hajiya tace " To kai in bazaka kula dani ba ka sanar da wanda yake bukatata ai yanada kudi tunda har gida yaso sai min, ka fadamai ya sai min gida na kom
a, a wannan matsiyacin gidan naka kake cin zarafina?"
Dariyace ta kusa kwacemai lalai batasan har mutumin da take magana ya gama aiki ya manta ma da ita ba? Dan harya samu wata?
Jiyai tace " Wai ma naga ai yanzu aiki kake min ko har an gama? Dan banga Am
inu ya susuce yana nemana ba?" Ta fada tana sake cije lebe saboda azabar da takeji. Wayarta ya hango yaje ya dauka ya fice tana ta kiransa Amman yaki kulata.
Lambar Aminu ya nemo, jikinsa har rawa yakeyi saboda san ya kirashi. Dan shikam tsoro yake gashi
har an fara gulmar sa akan ya ajiye babbar mace yana bushasha, kenan kiris zai sa ace shiya kasheta.
Acan bangaren Aminu kuwa Ibty na zaune kusa dashi lokacin suna zaune a falo wai kafadarsa ke ciwo ta ce zatamai tausa, tana farawa ya jawota ya dawo da
ita kan cinyarsa sannan ya kalleta yace "Shikenan kafada na ciwo itama kafar neman karyamin ita ake san yi."
Baki tadan bude tace "Yaya kaifa ka jawoni."
Ya danyi shiru sannan yadan girgiza kai yana dan kane ido irin mamakin nan yace "Oh ni yaran yanzu,
ba kunya in su Islam suka shigo suka ganki a haka kuma kice musu me?"
A firgice ta nemi mikewa yasa hannu ya riko kasan cikinta, kallansa tai tace "Yaya Allah karsu shigo su ganmu a haka."
Kafada yadan daga yace "Wannan kuma laifinki tunda kece kikai fit
sarar zama a jikina."
Zatai magana wayarsa tai kara.....
Bugu biyu ya daga tare da yin sallama, dama ya dauke kai akanta ne yana jira har duniya ta koya mata hankali sannan ya sata a gaba ta sanar dashi duk abinda ke faruwa.
A rayuwarsa bayasan zargi sh
iyasa gaba daya yake kokari kauda kai akan abinda ke faruwa, a koda yaushe ya tuna ji yake kamar zaiyi kwalla, ya yarda da Na'imah iya yarda bai taba tunanin zata aikata mai haka ba, har zama yake yana san yai tunanin wai wani irin so ya mata? Sai dai baya
iya tunawa, wanda hakan ya sake tabbatar mai lalai wannan san bana Allah bane.
Sabanin muryar da yake tsammani sai yaji ta namiji.
A dan zabure ya mike yace "Lafiya dai ko? Ina mai wayar?" Yadda Aminu yai magana ne yasa boka zaro ido, sosai yaji tsoran
su hadu a zahiri dan daga ji zai yi matuƙar kwarjini.
"Batada lafiya munga sunanka ne na karshe wanda sukai waya da ita shi yasa muka kira mu sanar dakai." Aminu ya shiga mamaki kafin yace " Batada lafiya?"
Cikin dauriya yace "Ina Hajiyar yanzu?" Bokan
yaja numfashi, yamai kwatancen can wani guri sannan ya katse.
****
Kallansa Ibty tai cike da sanjin bayani, riko mata hannu Aminu yai yana dan matsawa yace.
"Babu komai." Ibty ta kalleshi sosai, ganin kamar tana masa kallan makaryaci ne yasa shi yin
murmushi tare da cewa "Hajiya ce wai bata da lafiya." Cikin sauri tace "And?" Yaja numfashi ya sauke tare da cewa. "Ana jiran naje inda take."
"Bazaka ba, trap ne, wannan matar Allah akwai abinda ta shir......."
Labanta ta hade saboda tuna kalaman da ta
keyi, a cikin ranta tace Banda rainin hankali meyasa tun lokacin da ka kirata ba'a ce kaje ba sai yau? Bazakaje. Yanda ta dage kan cewa bazai je ba ne ya bashi mugun mamaki ta dauke tace "Allah nidai A'a haka kawai su sake rikita ka, daga rashin kallo a ko
ma tsana mai karfi, dan Allah ni nasan kunun da aka baka ne yaja ka tsaneni lokacin, yanzu wa yasan me za'a baka?"
Kallanta kawai yake tana fada yace
"Madam calm down! Zanje ne saboda su Islam." Zuciyar Ibty tayi sanyi amman dai bata san yaje gani take
tamkar munafuncin Hajiya ne. "Karki damu Insha Allahu babu abinda zai samu mijinki kinji?" Sunkuyar da kai tayi tana wasa da gefen rigarta da hannunta.
Tashi Aminu yai tsaye yana gyara maballin riga. Ganin ya dauki mukullin mota yasa Ibty tai saurin tashi
ta dauki hijab dinta tana turo baki. Aminu ya kalleta da mamaki yace. "Yah?" Sai da ta kawar da kai sannan tace dashi "To nidai muje tare, ni gaskiya bazan bari kaje gurin wannan matar kai kadai ba."
Aminu ya janyota a hankali ya sanya ta a jikinsa, ya
dan sumbaci goshinta tare da bubbugawa bayanta alamar lalashi tabbas ta damu dashi tana kuma san kare masa lafiyarsa, daidai kunnan ta yai maganar cewa. "Karki damu, kici ba da min addu'a Insha zanje lafiya na dawo." Babu yadda ta iya dole ta kyaleshi ya
fita ya shiga mota.....
Da kallo ta bishi idanunta kamar zasu kawo kwalla, nan danan ta koma ciki tai alwala tadau Qur'ani, bataso wani abu ya sake shiga tsakaninsu, dan yanzu rayuwa suke mai cike da sha'awa tana san Aminu har cikin ranta ji take kamar ba
zata iya rayuwa yanzu babu shi ba.
*Ayusher ce
🏌
️
♀
️
*
[5/7, 10:15 AM] Hauwa Galadima:
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske
Batch A*
Ki hanzarta ki mallaki naki
🤸🏻
♀
️
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004
Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
*45*
Bok
an Hajiya na gama waya da Aminu ya koma dakin da take ciki tana ta kurmusu tana kuka, Hajiya najin shigowarsa da sauri ta janyo kafarsa jikinta sai rawa yakeyi tace dashi.
"Kazo kayi ko ka gama min aiki na, ina so na tafi nabar gidan nan naka." Ya kallet
a shek'ek'e yana cewa.
"Yau zaki bar min gida, sam aikinki yaki yi wannan karan bansan kuma dalili ba. Aljanun da suke miki aikin ma yanzu sun dena, saboda haka kizo muje na kaiki inda zaki samu abinda kike so ba tare da kinsha wahala ba." Hajiya ta sake
rike ciki kamar wacce ke ciwon nakuda, ta dinga rokanshi akan yazo ya kusanceta kamar yadda ya saba saboda ji take kamar ta mutu amman sam yaki yadda yai "Saka mayafinki muje." Cikin karfin hali Hajiya tace.
"Ina zamu ina cikin wannan halin?"
Tsaki yaja
domin tunda ta fara wannan ciwoce-ciwocen yaji duk ta fitar masa a rai, bashi da buri irin yaga ta bar masa gurin sana'arsa dama ya samu makudan kudi gun wancan Alhajin a dalilinta to shi yanzu batada wata amfani a gunshi.
"Idan mukaje zaki gani." Hajiya
ta rufe ido hawaye na zuba tace. "Babu inda zanje, yanzu ko aikin bana bukata irin yadda nake son kazo kayi abinda ka sabar min." A fusace ya kalleta yana nuna ta da yatsa yace.
"Karki min rashin kunya idan ba haka ba yanzu sai na tozartaki wallahi. Kind
aiji na fada miki."
"Tun yaushe ka gama? Ai karasawa kawai zakai dan ka dade da gama cutar dani. Tozarci kuma na nawa? Wallahi Allah ya isa tsakanina dakai mugu azallumi, banda kadara da masifa ma lokacin ina gidan Aminu ai ko dan wanke wankena bazan dauk
eka ba, kai ko a kauye wlh kallo baka isheni ba......"
"Tashi to muje dan ni ko magana banasanyi dake." Ya katseta yana wani muzurai.
"Wai ina zamuje ne?"
"Gurin da zaki debo kasar maganin Aminu, wannan itace hanya ta karshe da zamuyi, dakyar aljanu su
ka bani wannan satar amsar, bayan ita babu wata hanya data rage." Hajiya naji haka ta mike da kyar, ga azaba da gurin fitar kashin keyi mata. Tasa mayafinta ya sata a gaba suka fito. Mai adaidaita da ya saba shiga ne ya karaso n vn, sai da sukaje inda yace
wa Aminu yazo sannan suka sauka, ya zare mata mayafin ya shimfida ta kwanta sannan ya kalleta.
"Ki zauna anan ina zuwa, zan yi magana da aljanu inji inane daidai gun daya kamata ki tsaya." Hajiya ta ware ido sai dai kuma ta kasa magana saboda azabar da t
ake ciki. Adaidaitar ya kuma hayewa suka barta a gurin.
Hajiya na kwance na juyi ta rasa yadda zatai har almajirai suka fara yi mata layi tana ta kuka, lokacin ne Aminu ya tsaida motarsa, yana zaune a ciki yake lekowa ko zai hango Hajiya.
Mutanen da ya
gani sun yi cincirindo daga can tsalleken yasa shi bude murfin motar ya fito ya nufi gurin yana tunanin ko wani abin ne ke faruwa.
Ganin mutum mai cike da kamala yasa mutane fara matsawa daga gun har Aminu ya karasa inda Hajiya ke kwance. Sam bai kawo i
ta bace ganin mace tayi goho yasa cikin kulawa yace "Baiwar Allah lafiya?" Danshi ya dauka ko mara lafiya ko mai lalura ce.
Gabansa ya fadi hankalinshi yai mugun tashi da sauri ya matsa kusa da ita yana kallanta. Hajiya kam kamshin turaren dake dukan hanc
inta ne da muryarsa yasa ta bude ido da kyar, karaf suka hada dana Aminu dake tsugunne a saitin ta.
Tasa hannu da sauri ta kamo nashi tana matse cinyoyi, baki na fitar da farar kumfa tace.
"Aminu?"
"Hajiya."
"Kaine? Dagaske kaine kazo wajena?"
"Ni n
e Hajiya, me yake faruwa haka?"
Ya fa
ɗ
a yana san zare hannunsa daga cikin nata.
"Ka taimaka min Aminu, ka rufa min asiri dan Allah."
Kallanta yai ya rasa haushinta zaiji ko kuma wulakanci zai mata ko kuwa tozartata zai yi? Gefen zuciyar shi na sanar
masa da cewa akwai Islam da Ilham a tsakanin ku, karka wulakantata saboda albarkacin su.
"Hajiya daga ina kike yanzu? A ina kike kwana? Me ya janyo miki wannan lalacewar ta lokaci guda?" Wadannan tambayoyi ne suka rinjayeshi.
Ta sakar masa hannu da sau
ri ta mayar kan cikinta tana matsawa. Ganin haka yasa Aminu kallan wasu matasa guda biyu yace su taimaka masa a sakata cikin mota. Hajiya naji ta dinga murna tasan gidan shi zai maida ita, aikin boka yayi kyau, idan har ta samu ta koma wannan karan ba zata
i wasa da damarta ba wajan ganin ya sai mata gida da mota, sai yanzu ta fahimci lalai gidanta na kanta shine mutuncinta.
Baya suka sankata, ta kwanta kan kujera ji tai kamar ana tsunkurenta dole ta koma tai goho dan shine kadai mutuncinta, ya zaro dari b
iyar ya basu suka tafi snw murna, shi kuma ya shiga bai kalleta ba yaja motar suka fara tafiya, kai tsaye ya nufi asibiti da ita ba tare da ta sani ba kasancewar a kanta na kasa idanunta taf da kwalla to dadinta ma aikin yaci akan Aminu kuma menene tasan s
hi zai nemo mata maganinsa.
Suna zuwa nurses suka zo suka karbeta, Hajiya ta kalli Aminu sosai amman ta kasa yi masa magana dan tana da bukatar ganin likita itama. Ita kadai tasan azabar datakeji ta kasanta, gani take kamar Aminu yasan me ta aikata shiy
asa ta maida kanta kasa.
Aminu ya ciro wayarsa ya kira Ibty wacce ke zaune tana koyawa Ilham assignment sai dai gaba daya hankalinta na kan abinda ke faruwa tsakanin Aminu da Hajiya, bugu daya ta dauka kamar daman jira takeyi sam ta manta da sallama da sa
uri tace "Yaya Kana ina?"
"Asibiti."
"Innalillahi, meya faru? Badai wani abin suka maka ba?"
Ibty ta tambaya cikin tashin hankali.
Wani irin murmushi yai yace "Wai me yasa kika damu dani haka? Anya tunda na tafi kinyi kwakwaran numfashi kuwa?" Aminu ya
jefa mata tambayar.
Kamar ibty na gabansa ta zaro ido, hannu tasa ta toshe bakinta.
"Uhmmm?"
Ya fada cike da san jin amsa.
"Nidai Yaya ka fada min mekaje yi asibiti? Bawai wancan zancen ba, Allah kai sai ana magana kaita maidashi zolaya." Aminu ya l
umshe ido, yarinyar nan fa tana gab da rikita masa duk wani lissafi nashi, damuwarta akan shi ta fara tasiri cikin ransa. Ya samu kanshi da rashin boye mata komai kamar yadda yai niyya.
"Hajiya ce batajin dadi shine na kawo ta."
Ibty tayi shiru, tunani t
akeyi anya ba makircin Hajiya bane? Tunda ta dade tana karyar ciwo ai dama.
Itafa tsoran lamarin matar takeyi, gashi taga Aminu ba mutum bane mai zafi bare tayi zaton zai nunawa Hajiyan kuskurenta. Shi kuma jin tayi shiru yasa shi maida kai jikin kujerar
mota ya lumshe ido.
"Kina tunanin rashina a kusa dake ne?"
Ibty ta ciji kasan lebenta tare da cewa.
"Nidai Allah tsoro nake, naji amma dan Allah nidai karta baka wani abu kaci ko kasha dan Allah."
"Babu abinda zata bani, bakisan a yadda na dakkota bane
." Sam maganarsa bata yi tasiri akan ta ba, dan ta riga tasan sharrin Hajiya yawa ne dasu.
Wata nurse ce tazo ta kirashi, yace "Shikenan bari naje ana kirana, in nafito zan kiraki." Yai magana tare da katsewa ya nufi wajan nurse din da ta kira shi.
Kalla
nsa nurse din tai sannan tace "Akwai gwaje-gwajen da muke son ayi mata, idan da hali ma harda scanning saboda tafi yin kuka da ciwon cikin da yake damunta kuma dole sai anyi scanning mu sannan zamusan abinda ke damunta tunda ita kanta bata sani ba."
Amin
u ya daga kai alamar gansuwa sannan ya duba aljihunsa, jin ATM card dinsa yasa hankalinshi kwanciya, ya nufi inda Hajiyan take da kanshi ya turata suka isa wajen da za'a dibi jini, duk da haka ta kasa zama sai murkusu take kamar mai nakuda. Suna nan tare h
ar result ya fito, Aminu ya gungurata suka koma wajan scanning shima aka yi ya biya, result na fitowa yaja ta suka isa wajan nurse ita kuma taje ta kaiwa likita. Yanzu hankalinta ya fara kwanciya ta tabbatar aikinta ne yai aiki akan Aminu inba haka ba baya
nda za'ai yasan abinda tai amma ya dinga wahala da ita haka.
Ofive likitan suka nufa ya mika takardun aka shiga mai dasu, tunda likita yaga sakamakon hankalinsa ya tashi, tashin hankali da bacin rai ne karara ya bayyana a fuskarsa, cikin bacin rai yasa ak
a shiga dasu Aminu, da yaso kaita asibitin abokinsa amma sai yai rashin sa'a abokin nasa baya nan, likitan ya kalla bayan ya xauna ganin yanayin fuskar likitan yasa Aminu shima ya hade rai yana tunanin meye zai dinga mai wannan kallan?
"Ina san sanin wa
nnan mahaifiyarka ce?" Jin tambayar yai ta daki kunnensa, Aminu ya kalli likita sannan ya maida ido yana kallon Hajiya tare da tunanin abin cewa.
Kowanne dan adam yakan so a nuna abin kwarai ace nashi ne, taya zai cewa likita Hajiya mahaifiyarsa? Kila ya
taba ganinta a wani gurin wanda be kamata ba dan yanzu bazai taba shaidarta ba, kila shi yasa yai masa wannan tambayar.
Aminu ya shafa kyakkyawar fuskarsa mai tattare da annuri ya kalli likitan.
"Surukata ce, wani abin ya faru ne?"
Likitan ya tsaya yan
a shan mamaki ta hanyar karewa Aminu kallo, Hajiya ta saki wani gigitaccen ihu wanda yasa ta fadowa daga kan kujerar keken da take kai. Cikin azama likitan yasa aka kaita dakin taimakon gaggawa, gaba daya hankalinsu ya tashi sau zunduma ihu takeyi, staffs
din asibiti dayawa sunzo jin yanda take ihu. Haka aka fita da ita sannan ya kalli Aminu cikin wani yanayi yace "A bisa dukan alamu da binciken da akayi Muna zargin saduwar da akeyi da ita ta baya shine ya haifar mata da taruwar wasu cucututa wanda..." Ciki
n razana Aminu ya buga tebur din likitan yana aika masa da wani banzan kallo, rai a bace Aminu yace "Banasan wulakanci da rashin mutunci, matar da ta dade babu aure