Showing 69001 words to 72000 words out of 128353 words

Chapter 24 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

33

inya gaji ha zauna ya huta sannan ya tashi ya cigaba da tafiya, tun daga kundila haka ya karasa cikin Tara

uni da kafa, kallo daya zakamai ka san lalai yasha wahalar da ya dade baisha ba a duniyar nan, tsinuwa kuwa Aminu yashata harya gaji, ya dau alwashin tattaro abokansa sumai tsinanen duka inya warke. Dan wallahi bazai bar wannan cin kashin ba, a kwace mai I

bty a wahalar dashi haka ba.

🏌🏻

‍♀

️

[3/7, 6:19 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki

mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

28

Hartai bacci bai daina shan tea yana ka

llanta ba, shikansa har mamakin kansa yake a 'yan kwanaki kalilan yana neman canzawa daga Aminunsa zuwa wani Aminun? Bayan ya gama abinda yakeyi yazo ya kwanta, hannu yasa yana neman gyara mata bargon data luluba dashi, idanunsa ne suka kai kan shigar dake

jikinta, wani abu ne ya sake dan tasomai da sauri ya maida mata bargon ya rufe sannan ya mike yadan fara tafiya a cikin dakin alamar dan karamin exercise, yafi minti sha biyar yanayi sannan ya samu ya kwanta tare da juya mata baya, dan shikam kwanan nan b

aisan meke kansa ba.

*******

A bangaren Hajiya kuwa jiya tana shiga gida ta zauna a falo ta baza uban tagumi, can ta miki tana huci tace "Kamar ni? Yarinya karama ta kirani mai aiki sannan ta shanyani a waje?" Kwafa tai tace "Kin taimakamin dan dama in

a neman hanyar da zan wulakanta yayarki, kin bani dama kin kuma kawo min abu ta sauki." Duk yanda bacci yaso ya dauketa taki yarda, haka tasa gishiri a ruwa ta hau kwankwada, ranar haka ta kwana cir ba bacci, kafin asuba kuwa kanta yayi gingirim saboda uba

n ciwo na rashin bacci datai, ana sallar asuba ta fito waje dakyar tana tafe kanta na uban ciwo ta nufi gun Bala dake zaune a waje yadan kunna radio. Tana kama bango ta karaso, kasancewar rana bata fito ba sai data zo kusa dashi sannan ya gane ta, da sauri

ya mike yana gaisheta. Cikin hakki da magana irinta marasa lafiya tace "Bala! Taimaka ka taremin adaidaita saho in sun fito ina san naje asibiti."

Hankalinsa a tashe yace "Hajiya ba lafiya?"

Tadan daga kai cikin irin yanayin nan na tsananin jin jiki tac

e "Da alama dadewar danai a waje jiya da daddare ne yasa jinina yahau. Ga sanyi daya sake shiga jikina."

Cikin rashin jin dadi da tausayi yace "Ki koma ciki Hajiya zan samo adaidaita sai na miki magana."

Haka ta juya tana tafiya dakyar, a kuma hankali t

akeyi dan tanaso Aminu ya sameta.

Cikin sa'a kuwa sai gashinan ya dawo daga masallaci, daga nan nesa ya hangota sanda ta shiga ciki, da sauri ya karasa gun Bala yace "Kamar Hajiya ce na gani ta shiga ciki yanzu ko?"

Bala cikin hausarsa yace "Eh itace,

adaidaita tace na tsaidamata zata asibiti."

Hankali a tashe yace "Batajin dadi ne?"

Hajiya dake bakin gate tanajin muryar Aminu sama sama saboda safiya, da sauri ta koma ciki ta dauko tire din abincin jiya ta ajiye akan table sannan tai saurin sa kwallin

maganinta ta dawo falo ta kwanta a irin galabaican nan.

Aminu ya kalli Bala rai a bace yace "Ba tambayarka nake ba? Meya faru?"

Nan Bala yace "Jiya ta shigo bayan kun dawo da alama abinci ta kawo to awaje aka barta dan tafi minti talatin a waje tana ji

ran a barta ta shiga kafin daga baya ta fito tana share kwalla, ina ganin shine ya tada mata ciwo."

Yanayin Aminu ne yai matukar canzawa, fuskarsa ta canza sosai haka idanunsa suka canza kala, bangaren Hajiya ya nufa cikin sauri, tana kwance a falo tana r

ike da kanta dake ciwo, kallan abincin yai, cikin tsananin takaici yace "Hajiya tashi ki shirya zan dauko mota mu tafi asibiti yanzu."

Tunda ya shiga gidan kamshin turaren ke kara hasaso bacin ransa, zuciyarsa na sake tafasa. Kallansa tai tace "Aminu kark

a damu, zanje da kaina, banaso a adalilina kai da matarka ku dinga samun matsala."

Fuska a daure yace "Matar da batasan darajarki ba nima bazata samu matsayi a gurina ba, ki shirya zanzo yanzu."

Fitowa yai a fusace ya shiga cikin gida, tana zaune tana ka

ratun qur'ani, idanunsa ya runtse yace "A haka kamar matar arziki" kofar dakinsa ya bude tana kai aya ta tsaya sannan ta kalleshi tace "Yaya Ina kwana?"

Wani kallo ya mata ya wuce ya dau key sannan yasa a aljihun jallabiyarsa, mamaki ne karara ya bayyana

a fuskar Ibty ganin jiya ana raha da tsokana sukai bacci, da sauri ta mike ganin yana kokarin fita, hannu tasa ta riko rigarsa ta baya. Juyowa yai ya kalleta, yanda yake kallanta kadai tasan wani babban laifin tai. Bakinta nadan rawa tace “Yaya wani abin n

ai?”

Yatsa ya nunata dashi kamar zaiyi fada, dan har jikinta ga gama yin sanyi ta tsorata da yanda ya nunata da yatsa, idanunta ne suka dan fara neman canzawa ya sauke hannunsa yace “Why are you pretending?”

Kallansa tai tace “Pretending?”

Rigarsa ya

dan janye daga hannunta yace “The worse people I despite are those with two face, a gabanka su nuna maka wani hali a bayan idanka su nuna maka wani.”

Bata gane meyake nufi ba, ganin ya fito daga dakin yasa tabi bayanshi da sauri tace “In laifi nai a mats

ayinka na babba yaya fadamin zakai menai sai kamin fada ko?”

Bai kalleta ba sai gani tai ya fita daga gidan, da sauri tabi bayansa tana kallo ya shiga mota ya fita, hawaye ne suka gangaro saman idanunta, jiya da farinciki ta kwana yau kuma meke faruwa hak

a?

Tunowa da Hajiya tai, idanu ta zaro da sauri ta bi gate, Bala wanda yake sa kwado a gate din bayan fitan Aminu ta kalla tace “Bala? Ina Ya Aminu yai?”

Ya gaisheta sannan yace “Hajiya yaje kaiwa asibiti.”

Idanunta ta runtse sannan ta furzar da wata is

ka, Alhamdulila matsalar ta Hajiya ce dan ta dauka wani abin ne ya sake bullowa, indai Hajiya ce Allah na tare da ita kuma insha Allahu sai yanda taso hadata da Aminu kwanaki yanzu bata isa ba.

Bala ta kalla tace “Ciwon nata sosai ne?”

Yace “Dazu dai da

kanta ta fito da alama bawai ya hanata motsi bane.”

Jin haka yasa ta juya ciki, zama tai a dakin Aminu tana kallan hotonsa wanda sukai shida Na’imah dake kan madubin dakin, ko tunanin ya kamata ya dauke hoton bayan auransu baiyi ba.

Ta dade ta a tunanin

abinda ya kamata tai, ca. ta mike kawai ta shiga kitchen ta hau yin abinci, kasancewar weekend ne su Islam anata bacci, Iman ma dasan baccin safe tana can tanata baccinta.

Ta dade tana shirya abinci kafin ta gama, wanke wanke tai sannan ta fito ta shiga

toilet. Wanka tak ta dauko wani doguwar material ta saka, dinkin ya mata kyau haka kalar material din ta amsheta. Batai wani kwalliya ba ta dau wayarta ta duba lokaci. Karfe tara na safe.

Saman goshinta ta dafa tana tunanin abinyi, can ta kira wayar Ain

ah.

Ainah na cikin bacci taji vibration, cikin abin bacci ta dauka. Ibty tace “Ainah taimaka ki turon number Hajiya.”

Ainah jin muryar Ibty yasa tadan bude ido sosai tace “Ibty?”

Murmushi tai tace “Turomin yanzu dan Allah, sai ki koma kiyi ta bacci har

sai Ummy ta gaji ta watsa miki ruwa.”

Ainah tai dariya sannan tace “Me zakiyi da numberta?”

“Kawai dai gani nai banida numberta gashi muna daf da juna.”

Ainah tadan tabe baki tace “Kardai ki sakewa matarnan dayawa wlh bazaki iya yakiceta ba.”

Murmushi

tai na yake tace “Turon please.”

Ainah tana turo mata number ta kashe sannan ta kira number Hajiya.

*****

Kwance take akan gadan da aka bata ba’a dade da fara saka mata ruwa ba, Aminu na zaune yana tunanin hukuncin daya kamata ya dauka, tabbas Ibtisam t

a bashi kunya, wancan karan yaji harda laifinsa amma wannan fa? Ai Hajiya uwa ce taya zata barta a waje?

Wayar Hajiya ce ta fara kara, mikewa yai ya karaso kan saman drawer ya dau wayar, ganin number ne ya kalleta yace “Number ce.”

Gabanta ne ya fadi ko

dai malamin ta ne? Wani irin faduwar gaba ne ya kamata, tana kokarin cewa ya kashe kawai taji yace “Assalamu Alaikum!”

Idanu Hajiya ta runtse shikenan in yaji muryar namiji zai yi zargin wani abin, ita kuma da saninta taki yin saving din numbersa saboda t

sautsayi, gashi ba karatu tai ba bataso asa abinda zai rikitata.

Ibty kam jin muryar Aminu yasa tadan runtse ido, tace “Yaya! Nayi mata abincin safe ne shine nake so naji jikinta? Sannan na kiraka naji ko zaku dawo yanzu ko kuma zaka turo Mamman yaxo ya

dauka?”

Duk da akwai jin haushinta mai karfi a ransa sai dai bayanda zaiyi, zai hana Hajiya cin abinci ne saboda bacin ransa?

Kallan Hajiya yai ya sanar da ita sakon Ibty, mamaki ne ya rufe Hajiya wato yarinyar nan makirace? Murmushi tai tace “Allah sa

rki mun sata wahala, ka duba abinda kake gani ni duk daya ne.”

Aminu fuska a daure yace “Zanzo na dauka yanzu, Mamman sun fita da Baffa.”

Tana kokarin sake magana taji ya kashe. Kallan Hajiya yai yace “Ki kwanta ki huta ance harda rashin bacci, bari naje

na dauko.”

Haka ya fita daga dakin, gida ya wuce kai tsaye.

Su Islam sun tashi daga bacci, Iman ta kamasu ta musu wanka, Ibty tana dakin Aminu tana gyarawa taji motsin motarsa, turaren wutan data sa a dakin ta fito dashi zuwa falo, daidai nan shima ya s

higo falansa.

Kallan juna sukai da sauri tace “Sannu da zuwa.”

Bai amsa ba ya fara kokarin wucewa daki, da kallo ta bishi harya shiga ciki, ajiye kaskon tak ta nufi dakinsa, ya zare jallabiya sanye yake da vest da gajeren wando hannunsa dauke da towel da

alama wanka zaiyi.

Har tana neman juyawa sai kuma ta koma tace “Ya jikin nata?”

Yadan rufa towel a saman kafadarsa yace “Kin damu da lafiyarta ne kika barta a waje jiya?”

Ibty tadan sadda kai kasa tace “Haka kawai sai na barta a waje? Bayan nasan mat

sayinta a gunka? Ko wace bansani ba nayiwa wannan wulakancin bazakai mamakin dalili na nayin hakan ba?”

Wani abu yadan hadiya yace “Sometimes I feel like wannan face din nake akwai abinda kike boyewa, yanzu kinasan cemin akwai hujjarki na barin babbar ma

ce a waje? Da daddare? Sannan cikin sanyi?”

Hawayenta tadan share tace “I thought mun fara fahimtar juna, kasan abinda zan aikata da wanda baxan aikata ba, at least ko bakasan duka ba na dauka xaka fahimci bazan wulakanta babba ba……”

Hawaye ne suka dan

fara neman cin karfinta, da saninta tadan rufe fuskarta tana kuka sosai, me makon tai hanyar kofa sai ta nufi bango wai a dole batasan ina take nufa ba.

Cikin hanzari yasa hannu ya rikota hakan yasa ta dan fada kirjinsa, yana neman dagata kawai yaji tana

kuka harda shesheka. Idanu ya runtse dan sam bayasan a dalilinsa mutum ya dinga kuka haka, kamar ya zareta ta karfi sai kuma ya kasa, samun kansa yai da dan shafa bayanta, can ya tuna abinda tai yadan dagota yana neman yin magana yaga yanda hawaye duk suk

a bata mata fuska, idanu yadan runtse sannan yadan juya baya, Ibty ta dan riko hannunsa da sauri, juyowa yai ya kalleta. Kwarjini da shakkarsa fal take a zuciyarta, ga rashin riga yasa saman kirjinsa a bude, kashin dake kirjinsa ya bayyana. Dakewa tai tana

hawaye tace “Wlh bansan tana waje ba, ina wanka sanda tazo, kafi kowa sanin girman gidan nan in mutum yana toilet ba yanda za’ai yaji. Yau Hajiya ta fara zuwa ko jiya? Meyasa ban taba kin budewa ba? Sannan dana fito nai sallah muka zauna a falo banji kwan

kwasawa ba balle na bude, daga nan kuma na taho gunka”

Idanunta ya kalla dake zubar da hawaye, da alama gaskiya ta fada, dan koshi baiji kwankwasa kofa ba.

Shiru yai yana tunani, muryarta ce ta katseshi, Hajiya mahaifiyar matarka ce data rasu, batada ha

kkin zama dakai, ba muharramarka bace, ba kuma aikinka bane kula da ita, nice matarka nice hakkinka, amma na taba nuna maka banasan xamanta dakai? Duk kuwa da bansan da zamanta ba sai bayan aurena?”

Jikinsa ne ya sake yin sanyi, kara matsowa tai tana hawa

ye tadan kwantar da kanta a saman hannunsa tace “Kayi hakuri in har na bata maka rai.”

Lalai san Ibty ya fara shiga jikinsa, dan tabbas ji yake kamar ya jawota sosai ya rungumeta, sannam ji yake kamar ya bata hakurin fishin dayai da ita.

Shiru suka dan

yi, can yace “Kin tabbatar ba kirana kikai dama ki kwanta a jikina ba?”

Dagowa tai tace “Ni?”

Yace “Umm humm kalli, tunda na shigo kike ta wayan ririkeni.”

Badai ya gano yau kisisina tadan yi bajintar yi ba?

Sakeshi tak da sauri tace “Allah Yaya ka da

ina min haka kaifa ka jawoni jikinka.”

“Ya akai ban tuna ba?”

Tace “Allah kaine, naji bigewa ka jawoni……”

Then?

Kunya tadan kamata, sai dai wani irin dadi ne yake kasan ranta yau ta tabbatarwa kanta inhar tanasan jin dadin aure to dole ta cire kunya t

a kwaci mijinta da kisisina.

Aminu ya wuce toilet har zai rufe bandakin sai taji yace “Rainane ya baci jin an barta a waje, banyi tunanin baki sani ba.”

Kallansa tai ya maida kofar ya rufe, murmushi tai tare da dan rufe fuskarta, dole ta sa Iman ta siyo

mata littatafai na kisisina a kasuwa, sannan ta tabbatar akwai wasu online, tunda Aminu nada saukin kai da rauni, da alama dashi Hajiya take amfani.

******

A bangaren Umar kuwa dakyar ya shiga bangarensu, a kwance a falo yaga bilkisu tana bacci da ala

ma jiransa take. Wani dogon tsaki yaja sannan yasa kafa ya zunguri kafarta iya karfinsa, a razane ta farka, dayake ba wuta fitila suka kunna, ta kalleshi tana kokarin mikewa duk ta rikece, garin sauko da kafafunta ta fado daga kan kujerar, kafa yasa ya kar

a hankadata da karfin gaske, wani irin azaba ce ta ratsata tadan saki kara tare da rike kafafunta, tsugunowa yai yadan shako wuyanta yace “Wato na tafi kinajin dadi har bacci kike kina sakin munshari ko?”

Kai ta girgiza da sauri tana hawaye, hankadata bay

a yai ta sake faduwa yasa kafa ya tsallaketa sannan ya wuce kitchen, fitowa yai yace “Tashi kiban abinci kafin ranki yai mugun baci.”

Dakyar ta mike ta nufi kitchen shi kuma ya wuce daki. Man zafi ya shafa a kafarsa sannan ya dau wayarsa, tabbas sai Aminu

yasan shiya wulakanta wlh.

Abinci ta kawo ta ajiyemai, hannunta ya matse da karfi, ya kalli kafarsa yace “Kinga menene nan?”

Idanu ta firfito dashi tace “meya sameka? Ko bigewar dazu ce?”

Ya yarfar da hannunta yace “Ba sai kinji ba sai dai ina sanar mi

ki duk sanda aka kai wani asibiti akan an kusa kasheshi ki tabbatar kin sanar da iyayenki shine ya fara bani ba.”

Bata gane me yake nufi ba sai dai babu fuskar sake tambaya.

Nan fa yasa abinci a gaba sai daya cinye tas ya saki wata katuwar gyatsa sannan

yasha ruwa.

******

🏌🏻

‍♀

️

[3/8, 11:27 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki ma

llaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

29

Tana tafe tana dan waka a ranta nadan nisha

di, bangarenta ta wuce daga falo ta juyo musun Islam da Ilham nan ta karasa dakin fuskarta duk alamun tayi kuka amma farinciki ne karara a bayyane a fuskar.

Iman dake zaune tana zabga dariya saboda itace ta jawo musun daga tambayarsu wanene babba. Ganin I

bty ta shigo yasa ta guntse dariyarta. Ibty da sauri ta karaso ciki jin muryar Islam harta fara canzawa tana neman yin kuka. Kusa da ita ta karasa ta kalli Iman tace "Allah kece."

Iman ta dan dafa kirjinta da hannu tace "Ni nai me? Kina dai kallo na a zau

ne."

Harara ta maka mata tace "Ko a kwance kike nasan kece, duk da nasan suna fada tsakaninsu amma tunda har musu ya nemi sa Islam kuka nasan kece."

Iman ta kalli Ilham tace "Ilham daga cewa wanene babba na sake magana?"

Da sauri Ilham ta girgiza kai al

amar a'a, sannan ta daura da cewa "Itafa Islam neman kuma take dama, Kawar Aunty ba itace karama ba? Wanene ke fitsarin kwance? Wanene bai iya homework dinsa ba? Wanene inzai sa kaya sai an tayashi?"

Ai nan Islam ta harzuka tace "Kema ai baki da wayau kum

a duk mara wayau shine karami."

"Surutu shine wayau?"

Ibty ta kalli Ilham tace "Ilham ya isa haka nan kinji?" Nan ta fara rarrashi tare da dauke musu hankali akan insuka shirya zasuyi keke.

Fitowa tai daga dakin, Iman ta biyota tana dariya. Dakin Ibty s

uka shiga, kallanta Iman tai yanzu ta daina dariyar tace "Ya Ibty wani abin ya faru ne? Naga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login