Showing 15001 words to 18000 words out of 128353 words
take bamai sake maidata gidan jiya.
*****
Ibty tana zaune da daddare
suna ta kallan kayan dasu Iman ke dagawa, jiya akace Aminu zaizo saidai har dare bai zo ba karshe dai Abba aka kira aka sanar dashi aiki yadan rikeshi dole ya tafi Abuja, amma yau inya dawo nan zai fara zuwa.
Itadai tana zaune tana kallansu sam ji take k
amar bada gaske bane, wai ita ce za'a a daurawa aure nanda sati daya, to dama haka ake auren a gurguje? Duk da ance ba tarewa zatai ba amma a kalla ko 'yar waya sa dingayi da wanda zata auran, sai dai har yau ko Hi bai kara hadasu ba. Gashi tanasan yiwa Ai
nah gulma ba dama.
Yaran makotarsu ne yai sallama cikin mamakin ganinsa bayan isha ba tare da sunji an kwankwasa ba, Umma tace "Sani kofar a bude take?"
Ya daga kai yace "Ina turawa naga ta bude."
Da sauri Umma ta kalli Iman tace "Kece karshen shigow
a kina tafe kina latse latsen wayar taki hala kika manta baki rufe ba? Kindai fi kowa sanin halinsa kasar nan tamu take ciki, ka rufe gida ma ya aka kare bare ka bar gida a bude.
Cikin sanyin murya tace "Umma yahkuri."
Sani ya kalli Ibtisam yace "Ana s
allama dake a waje."
Kallansa tai ta nuna kanta dan jin abin tai wani banbarakwai tace "Ni?" Ya daga kai yace "Eh wai inji Yayan kawarki."
Da sauri Umma ta wurga mata wani kallo tace "Waye yake sallama? Bayan an riga an bada ke?"
Cikin dan shagwaba t
ace "To ai shine yayan kawar tawa." Ta mike tai daki cikin takaicin wannan abu, meye zai wani ce yayan kawarta? Harta dau powder zatadan shafa kawainta ajiye ta zari hijab ta zunbula ranta duk a bace. Tana kokarin fita Iman tace "A haka zaki?"
Bata ko t
ankata ba ta fito, Umma tadan guntse dariyarta kafin tace "In borin Ibty ya tashi ai sai a hankali, gwara yasan halinta tun yanzu."
Dariya sukasa dukansu suka cigaba da kallan kaya.
******
Yana zaune a cikin mota ta karasa jikin motar daga gefe ta tsay
a ba tare da tace komai ba, shi kuma yana zaune a mota ya kurawa hoton Na'ima ido a hankali ya maida wayar ya ajiye yana duba agoggon hannunsa, kodai yaran baikai sakon bane? Gashi ya gaji dan daga Abuja yake ko gida bai je ba Ummy ta takura sai ya fara bi
yowa nan.
Fitowa yai da niyyar sake aiken wani yaran, mamaki ne ya kamashi ganinta tsaye daga gefe ta jingina da jikin motar tana kallan mutanen dake wucewa.
Maida kofar yai ya rufe sannan yai dan gyaran murya irinta manta, kallansa tai cikin dan dakew
a tace "Ina wuni?" Cikin mamaki haryanzu yake kallanta yace "Lafiya kalau me kike a tsaye anan?"
Cikin dan kunkune tai magana hakan yasa yace "Me kikace?"
Ta girgiza kai alamar bakomai, ko zaginshi tai? Abinda yazo mai kenan, lalai Ummy tana neman jawo
mai raini shifa sam kunyar ma tsayawa yake da yarinya karama haka.
Shiru sukai kai kace zancen kurame akazo, to wai me zaice? Shifa sam baisan me zai cewa yarinya ba.
Itakam Ibty itama shiru tai tana tunanin ko zai sake tambayarta meyasa ta tsaya anan,
dan yanzu kam so take ta daure ta fadamai dalilin.
Ganin shirun yaki karewa yasa yace “Akwai wani abu da zakiyi da biki ne?”
Kallansa tai kafin ta girgiza kai alamar a’a tace “Komai cikin sauri akeyi sai dai in zan tare.”
Ya jinjina kai yace “Inda w
ani abin sai ki sanar dani na baki kudi.” Yai maganar yana mika mata envelope yace “kiyi amfani da wannan yanzu.” Ta kalleshi bata amsa ba cikin girmamawa tace “Ni Allah ba abinda zanyi da kudi, in ina bukata zan fada maka.”
Kafeta yai da ido haka kawai
ko tanasan rama abinda ya mata ko tanasan maida mai murtani inta kalli idansa sai taji ta kasa, hannu tasa ta amsa sannan tace “Nagode.”
Bai amsa ba sai cewa yai “Inba wani abin ni zan wuce.”
Matsawa tai daga jikin motar yana kokarin shiga tace “Sai ya
ushe Ainah zata sani?”
Kallanta yai ta sauke kanta kasa yace “Sanda Ummy ta sanar da ita, na dauka saboda kawancenku zaki sanar da ita.”
A hankali tace “Gani nai bata sani ba bankuma san meyasa ba’a sanar da ita ba, sai naga kamar banida hurumin fada m
ata.”
Shiru yai yana kallanta, wanda har tadan tsargu ta dago ta kalleshi, bai taba tunanin jin magana ta hankali agun yarinya karama haka ba.
Murmushi yai yace “Zan wuce.”
Kai ta daga sannan tace “Agaida su Ilham.”
Juyawa tai ta shiga ciki duk hau
shin kanta ya isheta, haka za’ai zaman auren bata iya magana daga ta kalleshi? Oh itakam wannan shine gaba kura baya damusa, sai dai duk da haka auranshi yafi mata na Umar.
********
Umar kam a kauye duk yabi ya daga hankalinsa ga kwanan nan tsabar mis
sing din Ibtisam ko gyangyadi yai sai yayi mafarkinta, abin takaici numberta kawai ya hadace sai number Abba shi kuma sunyi waya a wayar Kawunsa, yanzu Abba sirikinsa ne bai isa ya tambayeshi Ibty ba.
Duk abin duniya ya dameshi ga jikin Goggonsa yaki war
warewa, shi so yai ya tafi a haka amma Yayanshi ya hanashi yana ganin taya zai tafi bayan mahaifiyarsa ba lafiya?
Umar har wata rama yai na rashin Ibtisam ya mata text yayi kiran har ya rasa kuma abinyi, yanzu kam kawai jiran sanda zasu barshi ya taho ya
ke dan shikam gaba daya komai ya fita a kansa, hira wannan basanyi yakeyi ba.
******
Akwana a tashi asarar mai rai, Abba ya samu ya kammala gyaran bangaren da Bilkisu zata zauna, ya kuma fara shirye shiryen kayan dakin Ibty dan a san ransa in akai ta
tare bayan wata daya ko sati uku dan baisan ai aure yarinya ta dade sosai a gida balle ita da take karatu.
Gidansu Umma har an cicika ‘yan uwa yau tun safe suka bayyana, shima Umar yau da safe ya iso dan baya azahar ne daurin auren, Abba yasa an mai din
ki ya kuma amso mai, tun a hanya Umar duk ya susuce yanaji kamar yai tsale ya ganshi a gidan, suna isa ya fara kokarin cusa kanshi cikin gidan sai dai abin haushi gidan ya cika da mata anata hidima, ta ina zai nemo Ibty? Gashi sai tsokanaraa ake wai ango a
ngo wai basu yarda yaga amarya ba yanzu sai ya jura sai an daura, haka ya fito kunya duk ta kamashi to shi gaskiya ana daura aure a bashi matarsa su tare tunda dai abin haka ne.
Wanka yai a bangarensa yayansa sai tsokanarsa yake, ya dauko dakakiyar farar
shaddar da Abba ya dinka mai ya saka, ya saka babbar rigar nan fa ya fito cas dashi.
A’a ango kasha kamshi inji Ayusher
🤩
*******
Acan gidansu Ummy kuwa suma yau yayunta sunzo da kannenta, haka kannen Baffa, batai gayya ba su kadai ta sanar tana g
anin a bari in zata tare mutane saji burinta dai a daura auren in dai an daura to komai ya wadatar.
Ainah yau tasha mamaki bayan asuba da Ummy ta sanar da ita za’ai auran Aminu sai dai bata fada kata da wacece ba, duk da haka tayi murna saboda ita kanta
tanasan taga Yaya Aminu yayi aure.
Baffa yasha manyan kanya hakama Aminu yasha fararen kaya, yayi kyau matuka, Ummy kam ta kasa rufe baki sai addu’a take zubgamai.
Haka suka fito suka shiga mota, yan uwan Baffa su daga can zasu wuce, Aminu dama shi ba
abokai gareshi ba balle yai gayya, kuma shi a ganinsa ma da kunya yace zai auri yarinya sa’ar Ainah.
*******
Masallacin ya cika sosai da mutane, anan Umar yaji labarin auren mutum biyu za’ai, bayan zuwansu Aminunya kure mai kallo yana mamakin mutum iri
nsa babban mutum haka dan kana kallansa zakasan kudi ya zauna mai, shi kuwa ya rasa wacce yakeso sai Bilkisu? To ko dai yanada wata lalular ne a boye? Inba haka ba baiga wani dalili ba.
Hannu ya mikawa Aminu sukai musabaha yana mai kallan tausayi tare da
zargin abinda ke damunsa a boye.
Aminu kam bai tsaya wani kallan Umar ba balle yasan wanene shi suna gaisawa ya wuce ya cigaba da gaisawa da mutane, Umar yana jiyo wani mutum abokin Abba yana cewa “Wannan ne mijin Ibtisam din?”
Umar ya matso yana murm
ushi, gani yai mutumin na kallan Aminu, tsaki yadanja yace “matsalar a hada auranka da wasu kenan sai mutane su fara kuskuren fuskokinku.”
Nufar mutumin yai da niyar mai magana, yayansa ya dafashi yace “Kai kuma rashin hakurin na menene? In an daura ai z
ai ganka ko?”
Haka suka shiga cikin masallaci nan fa aka fara addu’oi, gaba daya Umar ji yake kamar a mafarki lalai wannan rana tafi ko wace rana mahimmanci a tattare
dashi, yau zai cika burinsa na auran masoyiyarsa abin begensa abin kuma alfaharinsa.
Sam baiji sanda akace an daura auran Umar da Bilkisu, Aminu da Ibtisam ba, gaba daya kunnensa shidai ya jiyomai Umar da Ibtisam.
Yayansa ne ya dan dafa cinyarsa cikin rada yace “Meke faruwa? Naji ance Umar da Bilkisu?”
Umar ya bude idanunsa yace “Kai w
allahi inaji ka fara tsufa ina nan naji ance Umar da Ibtisam kai mai kake tunani?
Da sauri yace “Ba haka akace ba wlh na tabbatar ji nai ance Umar da Bilkisu.”
Tsaki yadan yi yace “Kai dalla banasan zancen banza ranar farinciki na. Kunnenka yak ta jiye
maka karya.”
Shikam Kawun Umar gaba daya shima jikinsa ne yai sanyi dan tabbas ba haka Umar yace mai ba, meke faruwa? Taya za’a hada dansa da nakashashiya?
Mutane anata musabaha ana rarraba goro, nansu Umar suka fito dan daukan hotona, abokansa da suka
taho daga kauye suka kwashe mai da dariya daya ya dafashi yace “Ha’a na Ibtisam bada kanka a sare kaje gida kace ya fadi, kace da Ibtisam za’ai ya akai ka kare da gurguwa? Wancan babban guy din ya maka dan kafa?”
Kansa ne yaji yayi wani gingiringin, kal
lansu yai idanunsa suka dan kada suka fara jaa yace “Banasan hauka da rashin hankali uban wa kake cewa ya auri wata?”
Kallansa sukai, dayan yana dariya yace “to ko limamin ne yai kuskure? Dan dai aure da Bilkisu aka daurama.”
A zuciye yakai mai wani waw
an naushi ya cakumeshi yana neman sake naushinsa, yayansa ne ya riko hannunsa da sauri ganin mutane harsun fara nufo gun, janshi yai bayan masallacin dashi.
Umar sai huci yake cikin kunar rai yace “Bani dan Allah na fasawa yaran nan jiki banasan dakikanc
i da jahilci.”
Cikin tausayi yake kallansa yanzu kam ya tabbatar abinda yaji gaskiya ne kenan Umar da Bilkisu aka daura mai, lalai in Umar yasan maganar nan gaskiya ne baisan me zai faru a masallacin nan ba dan tabbas Umar bazai taba barin abin nan ba da
n zuwansa kauyen nan kowa ya fahimci mugun san da yake yiwa Ibtisam……
Hmmmm nikam Ayusher a guje nabar masallacin dan nasan in Umar yasani harni za’a yiwa illa haka kawai baza’a karyamin dan kafar da nake ji da ita ba……
Ayusher Ce
🏌🏻
♀
️
[1/26,
9:32 PM] Fav
♡♡
:
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*Wattpad :-AyusherMohd*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*Free Page*
Ki hanzarta ki mallaki
naki dan Free Pages sun kusa karewa
🤸🏻
♀
️
*GA MAI BUKATAR BIYAWA KANSA KO KANWA KO MATA KO YAN UWA YA KASANCEWA DA TAKUN HASKE TOP 10 BATCH A*
*SAI YA TURA 500 TA*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004
07043079282
*Shaida
r biya ta wannan* 07065283730
Page 7
Washegari......
Tun bayan Ummy tayi sallar asuba ta zauna akan sallaya tana addu'oi itakam tasan Allah ne kadai zai kwacesu ya kuma kwaci Aminu daga wannan bala'in, mutanen unguwa sai zundensu akeyi zagi ku
wa da yada habaici har bataso ta shiga taro. Dadinta daya mijinta nada hali sai dai a dinga yada mata habaici, kishiyarta kam cin mutumcin da take mata akan wannan abu ya isheta, addu'a kawai take Allah yasa wannan karan Aminu ya samu abokiyar rayuwa kuma
ya basu ikon korar matarnan data zame musu bala'i da masifa......
****
Itakam Ibtisam bayan sun gama gyaran gida itada Iman, tana shiga daki zatai wanka Iman ta biyota tana dariyar gulma, fuska ta daure tace "Meye hakan zakizo ki sani agaba kina dariya
?"
Iman ta kalli dakin tace "Kai duniya tamin dadi, yanzu dai saman nan ni kadai zan zauna, injuye can in murguda can, bamai sa min ido."
Harara Ibty ta maka mata tace "Dadinta kema mace ce ki gama murgude murguden a hankadaki kema gidan miji."
Iman
ta dan turo baki tace "Ni Autar Umma ce bazata ba kowa ni ba. Ko mijin nake so sai dai ya biyoni."
Tsaki Ibty taja tace "Sanda za'a cilaki gidansa ki tabbatar kin sake maimaita kalaman nan."
Baki Iman ta murguda mata tace "Allah yasa in kin tashi ganin
miji ki ganshi dan lukuti mumuna wanda inya danneki bazaki iya......" Dukan da Ibty ta kawo mata ne yasa ta fita a guje tana cewa "Ki kasa ko motsi."
Kwafa tai tace "Yarinyarnan ta mugun rainani wlh."
Wayarta ce ta fara kara, kallan wayar tai harta ka
tse, wanka ta shiga haka tai wanka tanata tunanin ko ya zataga bakon? In kuma ta Iman ne taga jibgegen
namiji fa? Kallan dan siririn jikinta tai tace "shikenan mai makon na gudarwa Umar sai na samu mai kakaryani." Ajiyar zuciya tai na tausayin kanta, can k
uma tace "in kuma shima masifaffen kishi da zargi gareshi fa?" Haka ta gama wankan tana saka da kwancewa.
Daya daga cikin sabbabin kayanta ta dauka ta saka, material ne an mata gown dark blue ya mata kyau sosai da sosai, zama tai a bakin gado ta dau way
arta ta turawa Ainah text "Ainah akwai labari anjima."
Ai tana ajiye wayar sai ga kiran Ainah, dariya tasa ta daga tace "Kai jama'a wato ke dai bakyasan a barki cikin duhu."
Cikin zumudi Ainah tace "Ya akai? Fesamin dan Allah."
Dariya tai tace "Ki bar
k sai anjima in yazo ya tafi sai muyi gulmar da hujja." Ido Ainah ta zaro ta zauna digirgir akan gado tace "Wanene zaizo?"
Cikin dan kunya Ibty tace "Abba jiya yace min yau zanyi bako, bansan wanene ba tukuna." Wata 'yar kara Ainah tasa na nishadi tace "K
ai amma naji dadi, Ibty ai daga kinga ya miki kiyi wuf kuce gobe a dayra muku aure, dan nikam fargabar dawowar jarababem can nake."
Dariya sosai Ibty tai tace "Dan ni na kawo rashin hankali duniya daga ganin namiji yau sai ince gobe ya zo ya aureni? To ko
tallan kaina nake ai sai haka."
Baki Ainah tadan rufe tace "Na zake dayawa?"
"Zakewar gaske ma." Sako ne ya sake shigowa wayar ta nan sukai sallama tana dubawa taga ansa "Ibty nine Umar ki daga muyi magana, wayata aka sace."
Idanu ta zaro gabanta yai
wani irin faduwa, kashe wayar tai da sauri sannan ta sauka kasa, dole ta sanar da Umma abinda ke faruwa yanzun nan.
A falo taga Yaya Billy sunata kara gyagyara gida ita da Iman, tausayinta ne ya kamata ta dan matso tace "Yaya dan Allah ki bar gyaran nan
ki huta."
Murmushi ta mata tace "Ki barni hankalina yafi kwanciya in nai, in na auri Ya Umar ke zaki dinga zuwa kina min gyara?"
Shiru tai tana kallanta, cikin mamaki tace "Yaya Bilkisu wai da gaske san da kike mai haryakai kina auno zamanku tare?"
Da
n gefen kanta tadan buga kadan tace "Ke wai meyasa kika damu da san da nake mai? Ibty maganar gaskiya ada na hakura amma a yanzu ji nake kamar dashi kadai zan iya rayuwar aure, Yaya shi kadai na sani, zuciyata shi takeso, inaji kamar inba shi ba to ni da a
ure har abada."
Dariya sosai Iman ta kwashe dashi tana tafi tace "Lalai Yaya bansan kin rika agun kalamai ba."
Ibty ta maka mata harara, sannan ta nufi dakin Umma.
Umma tana zaune tana gyara fuskarta a madubi da alama itama wanka tai, kallan Ibty tai
cikin jin dadin shigarta yasa tace "yanzu nake tunani Allah yasa kinyi shiga mai kyau."
Zama tai a bakin gado cikin kunya, Umma tace "Munyi waya da Abbanki yace nan da minti ashirin zai iso, duk da nasan basai na fada miki ba amma ki bashi girmansa a mats
ayinsa na babba."
Kai ta daga a hankali sannan tace "Umma dama maganar Ya Umar da Yaya Bilkisu ce, nikam........"
Katseta tai tace "Kiji da abinda ke gabanki ba maganar nan ba, su sun amince da junansu bansan me yasa ke kika damu ba, Ibty wannan shine b
abban burin mu nida mahaifinki dan haka ki cire komai a ranki ki rungumi abinda muke so kuma suma suke so."
Jikinta ne yai sanyi a hankali ta daga kai alamar to sannan ta mike jiki a sanyaye ta fito daga dakin.
Sama ta koma tai sallar azahar ganin loka
cinta yayi sannan tadan yi kwaliya sama sama dan dama bata iya heavy makeup ba amma ta iya daidai nata wanda kuma yake kara mata kyau.
********
Sanye yake da farin yadi mai