Showing 48001 words to 51000 words out of 128353 words
daura ta dan yafa mayafi sannan ta dau turare, tana fesawa taji ana knocking din kofar, gabanta ne ya fadi ta fito daga dakin tare da nufa kofar.
Tace “Waye?”
Hajiya tace “Amarya kin t
ashi?”
Budewa tai cikin dauriya ta kalleta, hannunta dauke da tire na abinci.
Ibty ta gaisheta sannan tace “Ya jiki? Naji ance baki da lafiya?”
Tana murmushi tace “Na samu sauki, ga abincin safenku.”
Kallanta tai, cikin dauriya tadan hade hannayenta, t
soro takeji sosai, sai dai inta tuna tsoronta abinda yaja mata a rayuwa sai taji haushin kanta, dan badan tana tsoron Umar ba da tuni ta takamai birki, da ta sanar da iyayenta an dau mataki tun farko.
Bakinta nadan rawa tace “Hajiya mun gode amma na riga
nayi abinci.”
Hajiya taji abin sama taka, balle a yanda take kallan yarinyar kamar wawiya, cikin dauriya tace “Ke da nace ki barshi shine kima wahalar da kanki?”
Tadan dake tace “In na zauna ba abinyi nima zaman isata zaiyi, ke da ba lafiya ne dake ba
gwara ki huta.”
Lalai kallan kitse nakewa rogo, amma ba tasaka mata laya ba? Badai tare take kwana da Aminu ba?
Kallan zargi tawa Ibtisam wacce ke wasa da yatsun hannunta tana addu’ar tsari a ranta.
Hajiya ta juya hannunta dauke da tire, cikin tsanan
in kunar rai ta isa bangarenta, abincin ta juye a cikin bola sannan ta zauna ta daura kafa daya kan daya tana girgizawa lalai da alama yarinyarnan ba wacce ya kamata ta raga mata bace.
{Nikam Ayusher sim sim sim na fito tun kafin abu ya ritsa dani
🏃🏻
♀
️
}
🏌🏻
♀
️
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
Ki hanzarta ki mallaki naki
🤸🏻
♀
️
*TURA 500 TA* *Ka samu rahus
ar novel bakwai tare da shirye shirye*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004
Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
19
🤸🏻
♀
️
Tana rufe kofa ta jingina da jikin kofar ta ciki tana addu’a tare da rike kafarta
datake rawa. Batasan meyasa take tsananin tsoron matarnan ba, tafi minti biyar agun kafin ta daure ta koma ciki.
Bangaren Aminu tayi, tana shiga yana fitowa daga dakinsa, kamshin turaren daya saka ne ya cika falan, jitai kamar ita batasa turare ba bayan
sai da ta saka sannan ta fito. Kallansa tai yayi kyau sosai cikin shadda light blue, Aminu nada kyau ita kanta tasan kudi da kyansa sunfi karfin ta, samun kanta tai kawai da zubamai ido ta kasa daukewa.
Aminu daya fito yana gyara zaman hularsa, ya kallet
a tana tsaye tana kallansa.
Gyaran murya yai hakan yasa tai saurin cewa “Yaya ka fito?”
“A’a ina ciki.” Ya fada yana shigowa cikin falan.
Aranta tace “oh daga tambaya?”
Komawa tai ta dauko kayan abinci ta jera akan dinning yana zaune yana duba wasu t
akardu dake gefen kujera. Kallanta yai yana mamakin yaushe harta gyara falan haka?
Sake gyaran murya yai yace “Ko zaki nemo mai aiki? Dan ni dama mai gadi ke shigowa yadan shashare gidan bayan kwana biyu, to yanzu tunda kina gidan inaga ki nemo mai taya
ki.”
Ajiye plate din hannunta tai tace “Bari mugani in na koma makaranta naga abubuwan sunmin yawa sai muyi shawara, amma yanzu ba wani aiki tunda ba ko ina bane yake datti.”
Kafada yadan daga alamar yanda ta gani, Ibty ta dan kalleshi tace “Yaya abinc
i.”
Ajiyewa yai ya dawo ya zauna akan kujera, ganin abin yake wani banbarakwai dan raban da ya zauna shikadai da mace haka an dade. Plate tasa a gabansa sannan ta bude flask din, kamshin abincin kadai sai sayasa ya kalli flask din, dake wa yai tare da cig
aba da dan dana wayarsa. Ganin yanda take ta zubawa yasa yai saurin rike hannunta. A hankali ta dago ta kalleshi, bai kula da hannunta daya rike ba yace “Abincin mutane nawa kike zubawa?”
Kallan abincin tai tace “Yanzu hakan dayawa na zuba?”
“A’a dan ka
dan kika sa kamar cikin Islam.”
Dan baki ta turo itafa batasan wasan fadar bakar magana.
“Mikomin cup na hada tea”
Hannunta daya rike ta kalla tace “Ta yaya?”
Saketa yai yadan sake gyaran murya yace “keda hannunki bazaki kwace ba?”
Kamar zatai maga
na kawai ta fasa, cup ta mika mai sannan ta zauna a daya kujerar, tare da mikamai kayan tea.
Hadawa yai sannan yai Bismillah ya fara ci, magana ta gaskiya yaji dadin abincin nan dan ba shakka da badan karta rainashi ba daya yabi girkin, yaci sosai dan sa
i daya cinye wanda ta zubamai, tea ya kurba sannan yace “Gashinan kin cikamin abinci kinsa ina nishi dakyar.”
Aranta tace “Sai kaci ka rage.”
Ya dan sake shan tea yace “Amma Hajiya tasan kinyi abinci? Dan na tabbatar inba jikinta ne ya matsa ba zatai ab
inci damu tunda ta saba.”
Jin yace Hajiya yasa hankalinta yadan tashi kadan, murmushi tai tace “Na fada mata zan dinga girki sa kaina, sannan ta girma bai kamata mu daura mata wahala ba.”
Yayi mamakin jin kalaman nan daga bakinta, samun kansa yai dayin m
urmushi wanda hakan ba karamin mamaki ya bata ba. Kallansa tai cikin jin dadin da batasani babtace “Ya Aminu? Murmushi kai?”
Fuskarsa a daure yace “Murmushi kuma?” Ya karasa maganar yana ajiye cup din hannunsa, kallanta yai sosai yace “In murmushin ma na
i menene naki na murna?”
Dariya tadanyi tace “Bantaba ganin Kayi Murmushi bane”
Gyaran murya yai yadan mike yace “A kalla naji bakiyi maganar yarinta ba.”
Haushi ya dan turnuke ta, cikin dan takaici da magana kasa kasa tace “Duk wacce takai lokacin aure
ai ba’a kirata yarinya ba.”
Waigowa yai da sauri anan suka hada ido, zaro ido tai dan ta tabbatar yaji me tace, wata guntuwar shakuwa ce ta taso mata, da sauri ta mike tana neman barin gun, harta fara tafiya taji an riko rigarta ta baya, mayafin dake jik
inta ne ya sauko.
Sake shakuwa tai sannan tadan bibigi kirjinta, Aminu ya jawota tana tirjewa, dawo da ita gabansa yai yace “Me kikace?”
Sake shakuwa tai da sauri ta rufe bakinta da hannayenta biyu ta girgiza kai alamar bakomai.
Hannunsa daya yasa ba
wanda ya riketa dashi ba ya dauko ruwa faro dake kan dinning din ya mika mata tare da mata alama datasha, amsa tai ta bude sannan tasha sosai.
Kallanta yai haryanzu hannunsa na rike da rigarta yace “Ehen me kikace?”
Fuskarta ce tadan shagwabe kamar mai
shirin kuka tace “Namanta.”
“Kin manta?”
Kai ta daga da sauri alamar eh “to tuno ko na tuno miki?”
Kai ta girgiza alamar a’a da sauri tace “Allah kaine komai sai kamin zancen girma ni haryanzu banga wasu shekaru dayawa da aka bani ba.”
Mamakin kalama
nta ne ya rufeshi ya kalleta sosai sannan ya nuna kanshi da yatsa yace “Me? Ni kike cewa ban baki wasu shekaru ba?”
Kasa tai da kanta tare da dan yin raurau da fuska, Aminu yadan furzar da iskar bakinsa yace “ Lalai kinga gadan bacci na.” Yai maganar tare
da saketa yana neman juyawa. Da sauri tasa hannu tadan riko rigarsa ta baya, cikin sanyin murya tace “Yahkuri bawai da raini na fada ba Allah ni banasan kaitacemin yarinya bayan ni ba yarinya bace.”
Wucewa yai ya zauna akan kujera itakuma tabi bayansa d
a kallo, komawa tai ta gama cin abincinta tanaci tana kallansa bayan ta gama ta kwashe takai kitchen. Wanke kwanukan tai sannan ta hada turaren wuta ta fito dashi.
Kamshi sosai ne ya baibaye gidan, Aminu nasan kamshin turaren wuta da alama yarinyar ta iy
a abubuwan gidan, yayi mamaki dan ya tabbatar Ainah akwai abinci sosai bata iya ba. Yana zaune yana kallanta ta gefen ido harta gama turare falan da dakin bayan ta sake gyara kan gadan sannan ta fito ta maida shi bangarenta.
Zama tai akan kujera tana dad
ana wayarta, tai shiru tana tunanin yanda zata bashi hakuri, ita dai Allah tasan ba laifi tai ba amma da alama yaji haushin kalamanta.
Ibty a haka inka ganta zaka dauka batada magana sai dai a zahiri in ta samu waje to fa sai a hankali, a gidansu sam bat
a zama sosai ai hira da ita saboda ta tabbatar daga ta zauna Umar zaizo ya kafeta da ido, shiyasa har tafisan ta ganta a daki ita kadai.
Mikewa tai ta nufi falan inda yake ta zauna daga dan gefe tare da daukan wayarta taba dadanawa. Aminu bai kula ta ba
ganin haka yasa tace “Ya Aminu wani satin za’a fara registration na second semester.”
“Okay.” Abinda yace kenan ya cigaba da duba takardunsa, ajiyar zuciya tai ta zauna kawai dan bayasan me zatace ba gashi kamar aiki yake batasan ya dameshi.
Sunfi minti
ashirin a haka, so yake ya tambayeta abinda ke damunta har cikin bacci amma ya rasa ta yanda zaiyi.
Jitai yace “ Ya Ummanku? Kunyi waya?”
Kallansa tai idanunta ne suka dan canza, cikin dauriya tace “Suna nan lfy na kira Abba dazu da safe.”
Zancen Umm
a yai amma amsar Abba take bashi, tun suna hotel ya kula da Abba kawai take waya, a iya saninsa mace tafi shakuwa da uwa.
Kansa nakan takardun hannunsa yace “Yayarki fa da akai aure? Tana nan lfy?”
Tadanyi yake tace “Lafiya kalau, ai a kusa da gida take
.”
Kai yadan daga alamar gamsuwa sannan yace “Meya sameta naga kamar bata tafiya.”
Jiki a sanyaye tace “Sickle cell gareta, SS ce to ciwon yaci karfinta ya taba mata kafa, da tana tafiya daga baya ne tafiyar ke bata wahala.”
Kallanta yai yace “Kinsan t
ana da SS shine baki nemi sanin genotype dina ba kika amince ki auren?”
Dagowa tai taga yanda yake kallanta sosai, shiru tadanyi tare da maida kai kasa dan harya dauka batada amsar da zatace sai yaji tace “Na tabbatar Abba ya bincika dan yafi kowa damuwa
da ciwon.”
Sake kallanta yai baiyi magana ba sai dai ya sake girmama zurfin tunaninta a karo na uku.
Ganin yanda yake kallanta yasa tadanyi murmushin yake tace “Kayi hakuri dazu ba rashin kunya nasoyi ba, banaso ne kai ta cemin yarinya.”
“So kike a ce
miki babba?”
Tadanyi murmushi wanda yasa dimple dinta ya motsa tace “Ba wai acemin babba ba amma bansan aita cemin yarinya ko komai nai ai tamin kallan abin yarinta.”
Yanzun ma baisan sanda yai murmushi ba tare da girgiza kai yace “Meyasa mu manya in anc
e mana manya bamajin haushi?”
Ganin yanda yai murmushi yasa tadan fadada fara’arta tace “Yaya tsakani da Allah kai babba ne? Irin babban babba?”
Fuska ya daure sosai tare da yi mata wani kallo, ta dan girgiza hanayenta da sauri tace “Karka fassara magana
ta wlh ni dariya abin yake ban in naga kanata zancen girma, na dauka mutanen dasuka kai 50 zuwa sama sune suke zancen girma.”
Sosai ya daure fuska yace “Wato dai so kike kice nima ba babba bane?”
Tana dan guntse dariyarta tace “Kai ma ba babba bane nima
ba yarinya bace.”
Wani kallo ya mata sannan ya cigaba da aikinsa, ya kula in aka tabata to fa akwai magana, shi kuma bai fiya san magana tai tsayi ba.
Ibty kam samun kanta tai cikin farinciki, a kalla yau sunyi magana mai tsayi, murmushi tai tayi.
********
Naman cikin farfesun duk ya juye a cikin plate dinsa, kana gani kasan saboda mugunta yai, Bilkisu kam koko tasha ta gutsiri bread tana hadawa dashi, batama taba farfesun da aka aiko musu dashi ba, jiyai ya koshi duk yanda yake turawa, kallanta
yai cikin tsana yace “karki taba roman nan ki juyemin a kwano zan kaiwa abokina.”
A hankali tace to.
Wani haushi ya kara kamashi danshi ladabin nan konamai rai yakeyi, mikewa yai ya shiga daki ya cire kaya ya watsar a kasa sannan yai wanka, kaya yasa y
a fito yana kallanta tanata kokarin gyara falan. Kafa yasa yadan tura keken sannan yace “Dalla ki dinga yi kina kallan hanya, kinso da keke kin cika wannan dan karamin falan, ta ina kikesan mutum ya wuce banda kina kokarin sani na fadi?” Yaja wani tsaki ta
re da daukan ledar datasa kwanan a ciki ya fita yana masifa.
Kwallarta kawai ta share ta cigaba da aikinta.
*****
Abangaren Hajiya kuwa tun bayan dawowarta ta kasa zaune ta kasa tsaye, ganin zaman ba inda zai kaita kawai ta fito, abin takaici an gama
ginin katangar balle ta leka ta gani ko Aminu nanan.
Waje ta fito kawai ta hau adaidaita ta wuce gun malaminta.
Sai daya dade yana dube dubensa sannan yace “Yanzu me kikeso ayi mata? A haukatata ko kuma a mata ture ta shiga duniya.”
Hajiya tace “in ak
ai haka kowa zargina zaiyi nidai kawai ka ban abinda zan dinga juyata sai abinda nace sai kuma abinda na tsara, bazata taba kallona tamin musu ba. Sannan ka sake tabbatarwa kar wani abu ya shiga tsakaninsu na auratayya. Sannan ka tura mata aljani wanda zai
rikitata yasa Aminu ya fara daukarta mahaukaciya ko mara lafiya.”
Dariya ya bushe dashi yace “Wannan layar da kikasa inhar ta kwanta akai to fa ita dashi har abada dan bazai taba sha’awarta ba, sannan zancen yi miki biyayya wannan abune mai sauki”
Ya mi
ko mata magani yace ki tabbatar kinsa mata a abinci taci, inhar taci sau uku ke da kanki zaki ban labari. Maganar aljani kuma karki damu zan shirya komai, sai dai yau kudin aikin sai kin hada da irinta kwanaki, dan dole na mika sakon aljani zuwa cikin jiki
nki.”
Tafahimci me yake nufi sosai dan sanda zata rufe bakin kowa akanta sai data bashi kanta ya isar da sakon aljani jikinta. Bata damu ba haka ta wuce cikin daki shima yabi bayanta…….
{Allah ka mana tsari da wannan bala’i da masifar, ace saboda buri
duniya mutane basu dauki zina wani laifi ba.}
🏌🏻
♀
️
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
Ki hanzarta ki mallak
i naki
🤸🏻
♀
️
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004
Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
19
🤸🏻
♀
️
Tana rufe kofa ta jingina da jikin kof
ar ta ciki tana addu’a tare da rike kafarta datake rawa. Batasan meyasa take tsananin tsoron matarnan ba, tafi minti biyar agun kafin ta daure ta koma ciki.
Bangaren Aminu tayi, tana shiga yana fitowa daga dakinsa, kamshin turaren daya saka ne ya cika fa
lan, jitai kamar ita batasa turare ba bayan sai da ta saka sannan ta fito. Kallansa tai yayi kyau sosai cikin shadda light blue, Aminu nada kyau ita kanta tasan kudi da kyansa sunfi karfin ta, samun kanta tai kawai da zubamai ido ta kasa daukewa.
Aminu d
aya fito yana gyara zaman hularsa, ya kalleta tana tsaye tana kallansa.
Gyaran murya yai hakan yasa tai saurin cewa “Yaya ka fito?”
“A’a ina ciki.” Ya fada yana shigowa cikin falan.
Aranta tace “oh daga tambaya?”
Komawa tai ta dauko kayan abinci ta j
era akan dinning yana zaune yana duba wasu takardu dake gefen kujera. Kallanta yai yana mamakin yaushe harta gyara falan haka?
Sake gyaran murya yai yace “Ko zaki nemo mai aiki? Dan ni dama mai gadi ke shigowa yadan shashare gidan bayan kwana biyu, to y
anzu tunda kina gidan inaga ki nemo mai tayaki.”
Ajiye plate din hannunta tai tace “Bari mugani in na koma makaranta naga abubuwan sunmin yawa sai muyi shawara, amma yanzu ba wani aiki tunda ba ko ina bane yake datti.”
Kafada yadan daga alamar yanda ta
gani, Ibty ta dan kalleshi tace “Yaya abinci.”
Ajiyewa yai ya dawo ya zauna akan kujera, ganin abin yake wani banbarakwai dan raban da ya zauna shikadai da mace haka an dade. Plate tasa a gabansa sannan ta bude flask din, kamshin abincin kadai sai sayasa
ya kalli flask din, dake wa yai tare da cigaba da dan dana wayarsa. Ganin yanda take ta zubawa yasa yai saurin rike hannunta. A hankali ta dago ta kalleshi, bai kula da hannunta daya rike ba yace “Abincin mutane nawa kike zubawa?”
Kallan abincin tai tac
e “Yanzu hakan dayawa na zuba?”
“A’a dan kadan kika sa kamar cikin Islam.”
Dan baki ta turo itafa batasan wasan fadar bakar magana.
“Mikomin cup na hada tea”
Hannunta daya rike ta kalla tace “Ta yaya?”
Saketa yai yadan sake gyaran murya yace “keda h
annunki bazaki kwace ba?”
Kamar zatai magana kawai ta fasa, cup ta mika mai sannan ta zauna a daya kujerar, tare da mikamai kayan tea.
Hadawa yai sannan yai Bismillah ya fara ci, magana ta gaskiya yaji dadin abincin nan dan ba shakka da badan karta rai
nashi ba daya yabi girkin, yaci sosai dan sai daya cinye wanda ta zubamai, tea ya kurba sannan yace “Gashinan kin cikamin abinci kinsa ina nishi dakyar.”
Aranta tace “Sai kaci ka rage.”
Ya dan sake shan tea yace “Amma Hajiya tasan kinyi abinci? Dan na t
abbatar inba jikinta ne ya matsa ba zatai abinci damu tunda ta saba.”
Jin yace Hajiya yasa hankalinta yadan tashi kadan, murmushi tai tace “Na fada mata zan dinga girki sa kaina, sannan ta girma bai kamata mu daura mata wahala ba.”
Yayi mamakin jin kalam
an nan daga bakinta, samun kansa