Showing 114001 words to 117000 words out of 128353 words
tabi bayansa. Tunda ya hangot
a tana tahowa ya kasa dauke ido daga kanta har sai da ta iso wajan, yasa hannu ya bude mata kofar ta shiga ta rufe sannan yaja suka fice. Sai da suka dauki hanya sosai yaga bata kallansa sannan yai murmushi dan abin nata dariya yake bashi yace
"Baby Wai d
uk fushin na menene?"
"Ni ba fushi nayi ba." Ya dan kalleta.
"Kikai shiru kuma?"
"Me zance to?"
"Labari zaki bani."
"Kai Yaya ni fa banda labari." Ibty ta fada tana sake turo baki.
"Yaya? Wa kenan?"
Baki ta sake turowa batace komai ba.
"Ahhh sai y
anzu na tuna ashe dazu abu biyu nazo fada miki kika sa na manta."
Dan kallansa tai kadan, ya dan gyara zaman glass dinsa yace "Tunda fishi ake dani banaji akwai anfanin fadar."
Kamar bazatai magana ba sai kuma tace "Ni fa ba fishi nake ba."
Murmushi yai
kadan yace "to me?"
"Habibty...."
Tai maganar cikin wata murya wacce tasashi kunshe dariyarsa.
Aminu yaci gaba da tuki jefi jefi ya kan kalleta a haka har suka karasa asibiti. Ya samu guri ya ajiye motar suka kalli juna yayi murmushi, itakam kallan asi
bitin take tana tunani waye ba lafiya?
"Fito muje." Babu musu ta fito ya rufe suka jera. Tun daga bakin dakin din suke jiyo ihun Hajiya, hakan yasa Aminu saurin murda kofar yaga nurses suna ta kokarin riketa gashi tayi kaca-kaca da gurin da kashi da fitsa
ri. Su kansu a dole suke ajiye da ita a asibitin kowa ya tsani zamanta, gashi da alama kudi ake bawa mai asibitin shiyasa shi ko haushin abin basuga yanaji ba.
Ibty jikinta ne ya fara rawa ganin Hajiya a cikin wannan yanayin, babban abinda yazo mata shi
ne meke faruwa? Menene yake damunta? Wannan wane irin ciwo ne yasa duk ta fige ta lalace? Kallo daya zaka mata kasan lalai tana cikin tashin hankali mara misaltuwa.
Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, cikin sauri Aminu yace da ita ta koma waje. Hankali a
tashe ta fita, jikinta na wani irin rawa, tsugunawa tai a jikin bango tana addu'a dan gaba daya kwakwarata ta kasa fahimtar abinda ta gani.
Wayarta ce tai kara hakan yasa ta zarota, nunber Ainah ce hakan yasa tazaro wayar ta daga gaba dwya jikinta rawa
yake "Ibty wato miji dadi ko? Shiyasa kika gudu kika barni a skul ko?"
Shiru Ibty tai dan batama san me zata ce mata ba, Ummy dake zaune kusa da ita ta dan bige kafadarta tace "Auntyn taki kikewa magana haka? Sannan ba Aunty sai wani Ibty gatsai?"
Baki
ta turo tace "Kawatace fa akan me...."
Ummy ce ta amshi wayar tasa a kunnenta tace "Ibtisam."
Dakyar ta daure tace "Ummy!"
Jin muryarta yasa tace "Lafiya?"
Bakinta na rawa tace "Hajiya ba lafiya, ciwon ba dadi......"
Hankalin Ummy ne yadan tashi tace
"kuna ina?"
Babu bata lokaci kuwa sai ga Ummy da Aina, mamaki ya kama Aminu ya kalli Ibty wacce ke gefe tare da Ainah wacce ta rike hannunta ganin yanda yanayinta duk ya canza.
Hankalin Ummy ya tashi itama ganin halin da take ciki "Fadamin meke damunta
haka?" Yayi shiru yana neman abin cewa.
"Da alama karya kake son yi min ko?"
"A'a Ummy."
"Kai nake sauraro, kar kuma kayi min karya kasan dai matsayina a wajanka. Sannan nan asibiti ne zan iya neman likitan ya sanar dani."
Aminu ya dafe kai shi gas
kiya besan asan abinda yake damun Hajiya, gashi yanzu sunce masa har tana dauke da cutar nan mai karya garkuwar jiki wato HIV ga kuma ciwon koda wanda da alama shi kuma girma ne ya jawo mata shi. Kai ya sunkuyar kasa yana tunanin abin cewa.
Cikin dan dag
a murya tace "jiranka nake ko?"
Badan yaso ba haka ya bawa Ummy labarin abinda ya faru da Hajiya. Ba karamin tashin hankali ita kanta ta shiga ba, tasan matar shaidaniya ce amma batasan shaidancinta yakai haka ba.
Inalilahi wa ina ilaihi raji'un abinda U
mmy ta fada kenan sannan ta kalli Aminu cikin fada ta fara magana.
"Wai a ina ka hadu da Na'ima ne har ka jajibowa kanka wannan masifaffiyar matar? Wannan wace irin jaraba ce? Tunda nake a rayuwata ban taba cin karo da bala'i irin na mutanen nan ba."
Ta
sauke wani huce tacigaba "Duk saboda su mallake min kai shine har takai kanta wajan sabawa ubangiji? Zanji matukar kunya a nuna wannan matar a ce surukatace, gashi harda zuri 'a a tsakanin mu da ita."
Ta kalli Hajiya dake runkufe akan gado an mata allurar
bacci tace "Ka bude kunnanka da kyau kaji ni, duk yadda za'ai sai matar nan ta koma kauyensu, taje can su samar mata lafiya."
"Amman Ummy k..." Da sauri ta dakatar dashi.
"Umarni ne ba shawara ba, kayi yadda nace maka, ban hana ka bada abinda za'a kula
da ita ba, amman dai bana bukatar ka sake kusantar inda take indai ba da sani na ba."
Ummy na kaiwa nan ta juya ta kalli Aina tace "wuce mu tafi, zuciyata bazata dauki ganin wannan matar ba."
Suna fita Ibty ta karasa wajan Aminu wanda yake dafe da gosh
i ya rasa ma abinda zai yi.
"Yaya!"
Kallanta yai cikin dan bacin rai yace "Meyasa zaki kira min Ummy? Tunda kikaga ban kawo ta ba ai nasan abinda nakeyi." Yai maganar ba tare da ya kalleta ba.
Ita kanta batasan mai ya kaita fadawa Ummyn ba, cikin dana s
ani da sanyin jiki tace "Kayi hakuri."
Yayi shiru kafin ya dago su hada ido, Ibty tai saurin maida nata gefe saboda kwarjinin da yai mata.
Sake waigowa tai ta sake kallensa yanzun ma kallanta yai, a hankali ta daura hannu ta dan rike kunnenta alamar tay
i laifi, idanunta sukai jaa tana neman yin kuka, kai ya girgiza mata da sauri alamar kartamai kuka, ta kallo Hajiya wacce tausayinta duk ya rufeta, kara kallansa tai ta dan rike rigarsa, dan murmushi ya mata hakan yasa hankalinta ya kwanta.
Tana kusa da
Hajiya aka turo kofa, Ummy ce ta kuma dawowa wannan karan da wasu maza suna bin bayanta, ta kalli Aminu.
"Ga bus nan na taro shata, kaje ka karbo sallama yau ba sai gobe ba matar nan zata koma kauye."
Mamaki ya rufe Aminu yace " Amma Ummy......"
Ummy t
ai saurin katse shi tare da dagamai hannu
"Karka sake ka rokeni, wallahi matar nan sai ta koma kauye kaji na rantse. Sanda take yawon badalarta ta tuna dakai? Ta tuna da darajar jikokinta?"
Ido yadan runtse "Tun kafin asan me ta aikata ayiwa 'ya'yanka la
mba matarnan zata koma inda ta fito."
Babu yadda zai yi dole yabi umarninta yaje ya karbo takardar sallama, ma'aikatan gun sai dadi sukeji dan damw sun gaji da ita. Nan aka janyo Hajiya har mota aka sanya ta Ummy ta bawa masu bus din kudinsu sannan Ami
nu ya kwatanta musu garin da unguwar da zasu kai Hajiya.
Sai da Ummy ta gama tabbatar da cewa sun tafi sannan ta tasa keyar su Aminu suka tafi. Ibty kam gabaki daya ta dinga baya-baya da Aminu dan tasan tabbas haushinta yakeji, da ya sauko amma abinda Umm
y tai ta tabbatar ya kara hawa.
Suna isa gida yai hanyar daki fuskarsa a daure, dan tunda suka shiga mota ba wanda yai magana, da sauri ta karasa da gudu ta rike rigarsa ta baya, bai waigo ba yace "Dan sakeni toilet zan shiga."
Jikinta a sanyaye ta sake
shi tana kallo ya wuce, tabi bayansa da kallo.....
******
A can kauye kuwa ana kai Hajiya gidan sukace fir bazasu amsheta ba, wai mayya ce da alama kuruwar wani taci aka kamata, sukam masu bus suka ajiyeta a waje sukai tafiyarsu.
Kan kace me? An cika
taf a kofar gidan ana kallanta, Kawu wato yayanta ne ya dawo daga gona cikin sauri saboda wayar da Aminu yamai sannan ya turo kudi masu yawa akan a kula da ita.
Nan ya shiga da ita ciki a ka gyara kata dakin awakai aka sakata a ciki, gaba daya bata gane k
anta sai ihu kawai take tana cewa "Amaidata gun Aminu...."
Yau Kwana hudu kenan da maida Hajiya kauye aka turo musu sakon cewa jikin nata ya matsa kuma babu sunan da take ambata irin na Aminu. Da kyar Ummy ta barshi suka tafi shi,Ibty,Aina dasu Islam.
Koda suka isa Hajiya suka tarar cikin wani daki dako kare basu tsammanin zai iya zama a cikinsa, tana ganin Aminu tayi murmushi mai zafi.
Dazun nan jikinta yai dan sauki tadan sa a taimaka mata ta gyara jikinta jinsu Aminu na hanya, bayan sun gaisa ne y
a kalleta yace "Hajiya ya naga bakya shan magungunan?" Ganin da yai musu a ajiye da alama tunda ta dawo kauyen bata sha su ba.
"Babu komai Aminu, bana iya sha." Islam ce tace"Sannu Hajiya."
Ilham ta matso gunta tace "Hajiya in kika warke da kaina zan k
awo miki chocolate dayawa dayawa/"
Hajiya ta kalleta tare da yin murmushi, kallan Ibtisam tai kamar zatace wani abu sai kuma tayi shiru.
"Kuje waje ina zuwa." Suka hada ido da ibty ya jijiga mata kai, babu yadda zatai dole ta fita ta basu waje.
"Aminu."
"Na'am Hajiya." Suka yi shiru na dan lokaci.
"San zuciya ya kawoni wannan yanayin da nake ciki, kayi min komai amman na kasa hakura gashi inda na kai kaine. Aminu ka yafewa Na'ima dake kwance a cikin kabari. Allah ne kadai yasan azabar datake sha a dali
lin abinda ta aikata. Nima ka yafe min dan Allah."
Aminu yai shiru yana sauraranta harta gama, ya sauke numfashi.
"Allah ya yafe mana baki daya. Amman ya kamata ki dinga shan maganin saboda wahalar ciwo ake gudu bawai mutuwa ba."
Hajiya tayi shiru ita k
adai tasan halin da take shiga idan tana shan magungunan, shi yasa kwatakwata ta dena shansu.
Ayusher
🏌🏻
♀
️
[5/10, 3:11 PM] Hauwa Galadima:
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą A
̤̈
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*mg's skincare*
Shin Ina matan suke
🗣
️
🗣
️
🗣
️
maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi
😃🤩
Hakika tabbas duk mace
n data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's organic prod
ucts ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum
👌
hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata
ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar
❣
️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki t
ana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki
😫
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana wa
lwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy
🤗
ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student pac
kage:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg's skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa
🤝
Do you guys wanna achie
ve that milky skin that turns head wherever you go
🤩
Then @mgs skincare gat you covered
💯
Now is time to glow
😍
Pamper ur skin
🦵
Shine like bride
👰🏻
♀
Glow
🧖
♀
️
💯
tested nd trusted
🤝
Guarantee
*47*
Dakin yadanyi shiru kafin Hajiya cikin
sheshekar kuka tace “Duk abinda ta aikata nice sila, tun tana karama nake hure mata kunne nake nuna mata ‘ya’yan kishiyoyina ba ‘yan uwanta bane, kudi sunw gatanta da darajarta. A haka aurena ya rabu da mai gidana saboda ya gaji da mugayen halayena, da s
harrin da nake yiwa kishiyoyina ina hadasu husuma.”
Aminu ya kalleta sosai yace “Ni kuma mai na muku? Mai na muku daga ke har ‘yarki kuka tarwatsa min rayuwa?”
Hajiya ta girgiza kai da sauri tace “San zuciya ne kawai irin namu amma ba abinda ka mana, aha
salima bamu sanka ba mu muka bincikoka da kanmu.”
Kallanta yai mai tattare da alamar tambaya, ta share kwallarta tace “Mahaifinka ne yake san ‘yar kishiyata Zainab da aure, Na’imah tunda taga kudin mahaifinka ta rikice, balle ita duk samarin dake santa ba
bu mai ko mashin, ita kuwa gashi mai jibgegiyar mota yazo yana santa. Nan ta bazama neman samari masu kudi sai dai kowa yai amfani da ita sai yace bazai turo ba.”
Kan Aminu ne yai wani ginginrin jin wannan kalmar, ko kallan Hajiyar ya kasa saboda nauyin d
a zuciyarsa tai, Hajiya tai kasa dakai tace “Allah ne kadai yasan yanda akai ta shiga gun malami taje ne akan a juyo da hankalin mahaifinka kanta, ya bata umarni ta kawo hotonsa ta kuma yi bincike a kansa, anan ne tasan yanada babba ‘ya wanda ya isa aure,
bata sanka ba saboda baka kasar, nan malamin yai maka asiri wanda ya karkato da hankalinka ka dawo Nigeria.”
Gaba daya kallan Hajiya yake yanzu yana mamakin wai matar dayai shekara uku da ita ashe duk zaman karya tai dashi?
“Tundaga lokacin take ma asiri
harka mato akanta wanda babu wanda kake gani sai ita, a haka kuma tasa ka daukoni nan muka kara shiga dan rufe bakin ka dana mutane…….”
Hannu ya daga mata da sauri yace “Ya isheni haka, to daga ke har Na’iman ribar mai kuka ci? Ita ta rasu ba tare da ta
moreni ba yanda ta shirya ke kuma kalli yanda Allah yai dake.”
Kuka ta fashe dashi sosai, nan danan tari ya riketa, Aminu ya kalleta cikin takaici yace “Ni duk abinda kukamin na yafe muku sai ku shirye gamuwarku da wanda ya haliceku, ‘ya’yana bazasuzo nan
garin da sunan ganinki ko wani naki ba, wannan shine hukuncin dazan muku daga ke har ‘yarki. Basu da dangin uwa daga yau na musu iyaka daku.”
Yana kaiwa nan ya mike ya fito daga dakin wanda ba abinda ke tashi sai warin kashi na dabobi da kuma warin tusar
Hajiya.
Hajiya kuka take sosai tana rokar yafiya tana kiran Aminu, daga baya ta koma kiran Ibtisam sai dai Aminu kallo daya ya mata tasan bai amince ta shiga ba.
Kafin su tafi Aminu ya bawa wata mata kudi yace ta dinga kula da Hajiya, daga haka suka ta
fi.
Kwanan su biyu da zuwa kauyen suka sake samun mummunan labari na rasuwar Hajiya, tun dare ta mutu dayake tana xaune ne a bangare guda basuma san ta cika ba, sai da safe anzo kawo mata dumame akaga ta mutu.
Babu wanda yaje gaisuwa daga Kano sai Aminu
, gaba daya gidan kamar ba gidan mutuwa ba, mutane ana zaune anata hira da shewa, ana sanar dasu labarin zuwan Aminu kowa yai kasa dakai wasu harda dauko carbi, ya shigo ya ajiye musu kudi bayan kayan abinci da aka shigo dashi, yana zuwa ya dawo ko minti t
alatin baiyi ba ya juyo.
Abin mamaki tunda Hajiya ta rasu sai yaji tamkar an cire masa kaya a cikin zuciyar shi, kamar yau aka haife shi haka yakejinsa cikin walwala da nishadi, dama yana tsoran yadda zai yi rayuwa bayan Hajiya na da manyan tabbuna a jiki
nta, duk da yaji mutuwarta sai dai ga yaransa yan mata da in har mutane suka san sirrin kakarsu aure zai yi musu wahala.
(Allah yasa mu cika da imani ka kuma mana kyakyawan karshe)
****
Yana shiga karin kano ya wuce ta wani mall, bangaren kayan mata y
a nufa, english wears yadan dauka gaba daya kamar wanda ke sata haka yakeyi saboda kunyar kar aganshi da girmansa yana daukan kaya irin wannan, wata rigar bacci ya gani irin mai net din nan shara-shara, ta gefe ya dinga kallan rigar yana tunanin yanda zata
zauna a jikin Ibtisam, gefe da gefe ya kalla ganin ba mai kallansa yasa yadan zaro rigar ya dukunkune yasakata a kasan cart din ya rurufeta da wasu kaya, shi a dole baisan a gani.
Gun mai biyan kudi ya nufa, gaba daya kunya ce ta rufeshi, da aka daga rig
ar, wayarsa kawai ya dauka ya kira kaninsa dake kasar waje suka fara waya, kallan mai biyan kudin yai yace “Eh duk na sai maka abinda kake bukata.”
Cikin mamaki kanin nasa yace “Me nake bukata?”
Bai tankashi ba ya kalli mai biyan kudin yana murmushi ya k
ashe wayar yace “Haka nan suke, sune yara amma ba dama suji zaka shiga siyayya sai su fara cewa sunasan kaza da kaza.”
Shidai dariya kawai yai dan baisan me zaice ba, haka Aminu ya fito ya shige mota yana hawa kan titi kawai ya girgiza kai tare da sa dari
ya, lalai Aminu yaushe ka zama haka?
(Ni kaina abinda nake san sani kenan
🤪
)
******
Da wani irin farin ciki Aminu ya shiga gidan, hannunsa dauke da kayan shopping din da yai, yau bayan tayi wanka ta saka wani lace dinta da aka mata dinkin buba, ya m
ata kyau sosai, tayi dan makeup kadan sannan ta daura dankwallinta nan fa ta kara fitowa fes, dama kwanakin nan wani kyau da fresh take karawa, ba shakka kana ganinta