Showing 51001 words to 54000 words out of 128353 words
yai dayin murmushi wanda hakan ba karamin mamaki ya bata ba. Kallansa tai cikin jin dadin da batasani babtace “Ya Aminu? Murmushi kai?”
Fuskarsa a daure yace “Murmushi kuma?” Ya karasa maganar yana ajiye cup din hannunsa,
kallanta yai sosai yace “In murmushin ma nai menene naki na murna?”
Dariya tadanyi tace “Bantaba ganin Kayi Murmushi bane”
Gyaran murya yai yadan mike yace “A kalla naji bakiyi maganar yarinta ba.”
Haushi ya dan turnuke ta, cikin dan takaici da magana
kasa kasa tace “Duk wacce takai lokacin aure ai ba’a kirata yarinya ba.”
Waigowa yai da sauri anan suka hada ido, zaro ido tai dan ta tabbatar yaji me tace, wata guntuwar shakuwa ce ta taso mata, da sauri ta mike tana neman barin gun, harta fara tafiya ta
ji an riko rigarta ta baya, mayafin dake jikinta ne ya sauko.
Sake shakuwa tai sannan tadan bibigi kirjinta, Aminu ya jawota tana tirjewa, dawo da ita gabansa yai yace “Me kikace?”
Sake shakuwa tai da sauri ta rufe bakinta da hannayenta biyu ta girgiza
kai alamar bakomai.
Hannunsa daya yasa ba wanda ya riketa dashi ba ya dauko ruwa faro dake kan dinning din ya mika mata tare da mata alama datasha, amsa tai ta bude sannan tasha sosai.
Kallanta yai haryanzu hannunsa na rike da rigarta yace “Ehen me ki
kace?”
Fuskarta ce tadan shagwabe kamar mai shirin kuka tace “Namanta.”
“Kin manta?”
Kai ta daga da sauri alamar eh “to tuno ko na tuno miki?”
Kai ta girgiza alamar a’a da sauri tace “Allah kaine komai sai kamin zancen girma ni haryanzu banga wasu she
karu dayawa da aka bani ba.”
Mamakin kalamanta ne ya rufeshi ya kalleta sosai sannan ya nuna kanshi da yatsa yace “Me? Ni kike cewa ban baki wasu shekaru ba?”
Kasa tai da kanta tare da dan yin raurau da fuska, Aminu yadan furzar da iskar bakinsa yace “ L
alai kinga gadan bacci na.” Yai maganar tare da saketa yana neman juyawa. Da sauri tasa hannu tadan riko rigarsa ta baya, cikin sanyin murya tace “Yahkuri bawai da raini na fada ba Allah ni banasan kaitacemin yarinya bayan ni ba yarinya bace.”
Wucewa yai
ya zauna akan kujera itakuma tabi bayansa da kallo, komawa tai ta gama cin abincinta tanaci tana kallansa bayan ta gama ta kwashe takai kitchen. Wanke kwanukan tai sannan ta hada turaren wuta ta fito dashi.
Kamshi sosai ne ya baibaye gidan, Aminu nasan
kamshin turaren wuta da alama yarinyar ta iya abubuwan gidan, yayi mamaki dan ya tabbatar Ainah akwai abinci sosai bata iya ba. Yana zaune yana kallanta ta gefen ido harta gama turare falan da dakin bayan ta sake gyara kan gadan sannan ta fito ta maida shi
bangarenta.
Zama tai akan kujera tana dadana wayarta, tai shiru tana tunanin yanda zata bashi hakuri, ita dai Allah tasan ba laifi tai ba amma da alama yaji haushin kalamanta.
Ibty a haka inka ganta zaka dauka batada magana sai dai a zahiri in ta samu
waje to fa sai a hankali, a gidansu sam bata zama sosai ai hira da ita saboda ta tabbatar daga ta zauna Umar zaizo ya kafeta da ido, shiyasa har tafisan ta ganta a daki ita kadai.
Mikewa tai ta nufi falan inda yake ta zauna daga dan gefe tare da daukan
wayarta taba dadanawa. Aminu bai kula ta ba ganin haka yasa tace “Ya Aminu wani satin za’a fara registration na second semester.”
“Okay.” Abinda yace kenan ya cigaba da duba takardunsa, ajiyar zuciya tai ta zauna kawai dan bayasan me zatace ba gashi kamar
aiki yake batasan ya dameshi.
Sunfi minti ashirin a haka, so yake ya tambayeta abinda ke damunta har cikin bacci amma ya rasa ta yanda zaiyi.
Jitai yace “ Ya Ummanku? Kunyi waya?”
Kallansa tai idanunta ne suka dan canza, cikin dauriya tace “Suna nan
lfy na kira Abba dazu da safe.”
Zancen Umma yai amma amsar Abba take bashi, tun suna hotel ya kula da Abba kawai take waya, a iya saninsa mace tafi shakuwa da uwa.
Kansa nakan takardun hannunsa yace “Yayarki fa da akai aure? Tana nan lfy?”
Tadanyi yak
e tace “Lafiya kalau, ai a kusa da gida take.”
Kai yadan daga alamar gamsuwa sannan yace “Meya sameta naga kamar bata tafiya.”
Jiki a sanyaye tace “Sickle cell gareta, SS ce to ciwon yaci karfinta ya taba mata kafa, da tana tafiya daga baya ne tafiyar k
e bata wahala.”
Kallanta yai yace “Kinsan tana da SS shine baki nemi sanin genotype dina ba kika amince ki auren?”
Dagowa tai taga yanda yake kallanta sosai, shiru tadanyi tare da maida kai kasa dan harya dauka batada amsar da zatace sai yaji tace “Na ta
bbatar Abba ya bincika dan yafi kowa damuwa da ciwon.”
Sake kallanta yai baiyi magana ba sai dai ya sake girmama zurfin tunaninta a karo na uku.
Ganin yanda yake kallanta yasa tadanyi murmushin yake tace “Kayi hakuri dazu ba rashin kunya nasoyi ba, bana
so ne kai ta cemin yarinya.”
“So kike a cemiki babba?”
Tadanyi murmushi wanda yasa dimple dinta ya motsa tace “Ba wai acemin babba ba amma bansan aita cemin yarinya ko komai nai ai tamin kallan abin yarinta.”
Yanzun ma baisan sanda yai murmushi ba tare
da girgiza kai yace “Meyasa mu manya in ance mana manya bamajin haushi?”
Ganin yanda yai murmushi yasa tadan fadada fara’arta tace “Yaya tsakani da Allah kai babba ne? Irin babban babba?”
Fuska ya daure sosai tare da yi mata wani kallo, ta dan girgiza h
anayenta da sauri tace “Karka fassara maganata wlh ni dariya abin yake ban in naga kanata zancen girma, na dauka mutanen dasuka kai 50 zuwa sama sune suke zancen girma.”
Sosai ya daure fuska yace “Wato dai so kike kice nima ba babba bane?”
Tana dan gunt
se dariyarta tace “Kai ma ba babba bane nima ba yarinya bace.”
Wani kallo ya mata sannan ya cigaba da aikinsa, ya kula in aka tabata to fa akwai magana, shi kuma bai fiya san magana tai tsayi ba.
Ibty kam samun kanta tai cikin farinciki, a kalla yau su
nyi magana mai tsayi, murmushi tai tayi.
********
Naman cikin farfesun duk ya juye a cikin plate dinsa, kana gani kasan saboda mugunta yai, Bilkisu kam koko tasha ta gutsiri bread tana hadawa dashi, batama taba farfesun da aka aiko musu dashi ba, ji
yai ya koshi duk yanda yake turawa, kallanta yai cikin tsana yace “karki taba roman nan ki juyemin a kwano zan kaiwa abokina.”
A hankali tace to.
Wani haushi ya kara kamashi danshi ladabin nan konamai rai yakeyi, mikewa yai ya shiga daki ya cire kaya ya
watsar a kasa sannan yai wanka, kaya yasa ya fito yana kallanta tanata kokarin gyara falan. Kafa yasa yadan tura keken sannan yace “Dalla ki dinga yi kina kallan hanya, kinso da keke kin cika wannan dan karamin falan, ta ina kikesan mutum ya wuce banda ki
na kokarin sani na fadi?” Yaja wani tsaki tare da daukan ledar datasa kwanan a ciki ya fita yana masifa.
Kwallarta kawai ta share ta cigaba da aikinta.
*****
Abangaren Hajiya kuwa tun bayan dawowarta ta kasa zaune ta kasa tsaye, ganin zaman ba inda za
i kaita kawai ta fito, abin takaici an gama ginin katangar balle ta leka ta gani ko Aminu nanan.
Waje ta fito kawai ta hau adaidaita ta wuce gun malaminta.
Sai daya dade yana dube dubensa sannan yace “Yanzu me kikeso ayi mata? A haukatata ko kuma a mat
a ture ta shiga duniya.”
Hajiya tace “in akai haka kowa zargina zaiyi nidai kawai ka ban abinda zan dinga juyata sai abinda nace sai kuma abinda na tsara, bazata taba kallona tamin musu ba. Sannan ka sake tabbatarwa kar wani abu ya shiga tsakaninsu na aur
atayya. Sannan ka tura mata aljani wanda zai rikitata yasa Aminu ya fara daukarta mahaukaciya ko mara lafiya.”
Dariya ya bushe dashi yace “Wannan layar da kikasa inhar ta kwanta akai to fa ita dashi har abada dan bazai taba sha’awarta ba, sannan zancen yi
miki biyayya wannan abune mai sauki”
Ya miko mata magani yace ki tabbatar kinsa mata a abinci taci, inhar taci sau uku ke da kanki zaki ban labari. Maganar aljani kuma karki damu zan shirya komai, sai dai yau kudin aikin sai kin hada da irinta kwanaki, d
an dole na mika sakon aljani zuwa cikin jikinki.”
Tafahimci me yake nufi sosai dan sanda zata rufe bakin kowa akanta sai data bashi kanta ya isar da sakon aljani jikinta. Bata damu ba haka ta wuce cikin daki shima yabi bayanta…….
{Allah ka mana tsari d
a wannan bala’i da masifar, ace saboda buri duniya mutane basu dauki zina wani laifi ba.}
🏌🏻
♀
️
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! T
akun Haske Batch A*
Ki hanzarta ki mallaki naki
🤸🏻
♀
️
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004
Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
20
🤾
🏻
♂
️
Boka ko nace malam sai daya gama biyawa kansa bukata dan dana umarnin aljanun dayake amfani dasu ne akan inhar yanaso su cigaba da aiki dashi to fa sai dai ya dinga kusantar manyan mata, tsohon jini.
Itakam Hajiya mikewa tai dan dama bawai abinda k
e gabanta ba kenan, burinta ta samu biyan bukatarta, kuma akan wannan zata iya aikata komai, in tace komai tofa lalai tana nufin komai.
Fitowa tai tana tafe tana tunanin yanda zata sa wannan 'yar iskar yarinyar taci abincinta, dan ta kula kallan kitso ash
e takeyiwa rogo.
********
Abangaren Ibty kuwa ganin sha biyu tayi yasa ta nufi kitchen dan daura abincin rana, gaba daya hankalinta nakan mahaifiyarta, ta rasa yanda zatai ta kirata a waya.
Dabara ce ta fado mata da sauri ta dau wayarta ta fara duba
yanda ake boye number in za'a kira waya. Ai nan danan google ya nuno mata, cikin tsananin jin dadi ta saka sannan ta kira Umma, tana ringing tana addu'ar Allah yasa ta dauka. Harta katse ba'a dauka ba, jiki a sanyaye ta sake kiranta, yanzun ma harta cire r
ai akan baza'a daukaba dan harta sauke wayar daga kunnenta sai taji ance "Assalamu Alaikum!"
Cikin tsananin jin dadi da zumudi ta dauka tace "Ummana?"
Aminu daya taso dan ya sanar da ita zai fita daga nan zai taho dasu Islam yaji muryarta da yanda take
magana cikin farinciki.
Umma tace "Ibtisam? Naga number wayar a boye?"
Tana murmushi tace "Kullewa nai, Abba ne yace karna kira ni kuma hankalina ya kasa kwanciya."
Kalamanta sunyi tsananin ba Aminu mamaki, taya mahaifi zaice karta kira mahaifiyarta?
B
ai gama dogon nazari ba yai kamar zai juya sai yaji tace "Umma komai na gida ya dawo daidai? Hankalina yaki kwanciya wlh."
Dan juyowa yai ya kalli kofar kitchen din yana mamakin abinda yake ji. Umma tace "Ibtisam haryanzu ban huce na abinda kika aikata b
a, ko tunowa nai zafinki nakeji, taya zaki bari abu ya rincabe haka? Kina sane da irin farin cikin da mukeyi na ganin munyi hadin auran nan?"
Idanunta ne suka ciciko da kwalla sai jiyai tace "Wallahi Umma bansan abin zai kai haka ba, ban kuma san a dalil
ina abubuwa zasu rikice haka ba, dan Allah Umma ki yafemin ke da Yaya wallahi na kasa samun nutsuwa ina ganin laifin duk nawa ne."
Jiki a sanyaye Aminu ya bar falan yana sake maimaita kalamanta, wayarsa kawai ya dauka ya tura mata sako akan yazo ya sanar
da ita zai fita amma yaga tana waya.
Mota ya shiga yai shiru yana nazarin abinda ke faruwa, tabbas wannan ya nuna a dalilinsa ne take cikin wannan halin, sannan saboda haka ne bata samun nutsuwa ko cikin barcinta.
Bayan mota ya kalla inda littafanta s
uke ya dauko dan ya dawo dasu gaba tunda su Islam zasu zauna a bayan, gefen kujera ne yadan bigi hannunsa hakan yasa ya saki lidar, wasu daga cikin litattafan suka fito.
Hannu yasa ya daukosu yana kokarin maidasu ciki nan wata takarda ta fado daga ciki,
kamar karya bude sai kuma ya samu kansa dadan budewa. Kai ya girgiza da sauri ganin bai kamata ba yana kokarin maidawa ya rufe idanunsa suka kai mai rubutun dake jiki. "Ibtisam ki fito waje karfe 10 na dare, zan daukeki mu tafi sokoto.............."
Mamak
i ne ya rufeshi matuka tare da wani zargi daya darsu a cikin ransa, wanene yakesan daukarta su tafi? Saurayinta kenan? Lalai wannan ya tabbatar mai akwai wanda take so akai karfin hali aka bashi saboda Baffansa yasan Abbanta.
Ganin tunani suna neman yi m
ai yawa kawai yaja mota ya fita daga gidan, yayi mamaki sosai dan yana kokarin shan kwana ya hango Hajiya ta sauka daga kan adaidaita sahu, ina taje? Itada ba lafiya ba? Wucewa yai gida kai tsaye, yaje gidan ya tadda su Ummy sun fita dasu Islam da Baffa, A
inah ce kadai a gida.
Juice ta kawomai bayan sun gaisa tace "Yaya ina Ibtis....." sai kuma tadan rufe baki tana dariya tace "Aunty Ibtisam."
Kallanta yai yace "Tana nan lfy." Mikewa tai tana neman tashi taji yace "Kawarki kamar kawarki ce sosai ko?" Ta
mbayar taso bata dariya yanda yai tambayat ta koma ta zauna tace "Yaya wace tambaya ce wannan?"
Fuska a daure yace "Indai kin gane ba shikenan ba?"
Tace "Kawatace sosai yaya tun secondary school muke tare."
Shiru yai yana tunanin ta yanda zaiyi tambay
ar ba tare da raini ba, yadanyi gyaran murya kafan yace "Ita batada wani saurayi ne ta amince ta auran?"
Gaban Ainah ne yadan fadi kadan badai Umar ya tari yayanta ba?"
Aminu yadan kalleta kadan ganin kamar tana neman tuno amsar da zata bashi ne yasa yai
saurin cewa "Meyasa bata aureshi ba? Bayan tana sanshi?"
Ainah tadanyi ajiyar zuciya tace "Data auri wannan ai wlh gwara ta zauna babu aure."
Zarginsa daya ya tabbata kenan, akan tanada saurayin da take so, yadau juice yadan kurba yace "Dan mutum na t
alaka shikenan sai aki auransa?" Yai maganar cikin alamar bugar ciki, tai saurin girgiza hannu tace "Wallahi Yaya ba haka bane, sanda yake mata ne ya fara zama hauka, ya hanata sukuni, ya hanata rayuwa, makaranta wannan biyota yake fa? Saboda kishinsa na h
auka."
Dan idanunsa ya runtse kadan lalai ba shakka silarsa ce ta rabasu, da alama kuma saurayin na matukar santa.
Kallan Ainah yai yace "In tasan yana santa haka meyasa bata sanar dani ba? Ko ta sanar da iyayenta?"
"Tab! Yaya wlh ita Ibty ba sanshi
take ba, a gidan su ya taso ya bi ya takurawa rayuwata kallo kadai in namiji ya mata wlh sai an kwaceshi a hannunsa, wannan Yaya ai ba so bane hauka ne, bakasan takura da masifar da ta shiga a dalilinsa bane, gashi ta kasa sanarda iyayenta saboda dan yayan
babanta ne kuma a gidansu yake."
Shiru yai kenan yaran daya auri Yayarta ne? Meke faruwa kenan?
Kamar bazaiyi magana ba sai yace "Meyasa ya auri yayarya to?"
Nan Ainah ta sanar dashi abinda Ibty ta fada mata, sannan tace "Ni na bata shawara akan kart
ai magana kila ya hakura da ita ne, bansan me kuma ya faru ba harta aureka ba."
Kallan da Umar ya makamai ya tuno da yanda yanayinsa yake, ya kuma tuno da fasamai glass din mota da akai, da kawota da akai ba tare da shiri ba, lalai Umar baisan ba Ibty a
ka bashi ba kenan sai bayan an daura auran, to amma a ina aka samu matsala? Haka ya zauna sam tunani ya hanashi sukuni, ya daura ya kwance, tabbas tunkararta da maganar shine saukinsa amma matsalar shi baisan ta ina zai fara tambayarta ba, haka ya zauna ha
rsh Ummy suka dawo sannan ya kwaso su Islam suka taho.
Da gudu sukai cikin gida, ya bude musu kofa ta bangarensa, suka shiga ciki suna kiran "Kawar Aunty!"
Da sauri ta fito daga daki sanye da hijab da alama sallar la'asar tai, suna karasowa ta rungumes
u, tace "Kawayena kun dawo?"
Islam cikin murna da tsale tace "Kawar Aunty zo kiga abinda Baffa ya sai mana" tai maganar tana jan hannunta.
Ibty ta biyota tana dariya, Ilham tace "Kawar Aunty na dauka kin koma gida har inajin haushi bazamu nuna miki ba."
Murmushin yake tai tace "Kwantar da hankalinki Ilham zan kwana biyu anan kafin na koma."
Falan Aminu suka nufa inda suka ga katan kwali guda biyu dauke da hoton keke, murmushi tai tace “Inyee lalai yau dole asha murna.”
Kallan Aminu tai cikin girmamaw
a tace “Sannu da dawowa.”
Shiru yai yana kallanta, fuskarsa sauke da alamomin tambaya masu yawa.
Nan fa aka fara murna suka zauna ana bubude kwalin, yana zaune yana kallansu.
Kallanshi tai tace “Ya Aminu taimaka mana mu hada dan nikam na kasa.”
Kam
ar yace bazaiyi ba dan shi ya tsani a dinga kokarin saka shi abu, sai dai baisan dalili ba ya dan sa hannu ya jawo abin gabanshi yana hadawa.
Mikewa tai ta fara kawo abinci shi kuma yana hadawa, sukam su Islam sun kafa sun tare suna jira a gama.
Ibty ta
na murmushi tace “Kofa an gama hadawa sai anci abinci sannan za’a fara hawa.”
Islam ta shagwabe fuska tace “Dady ni yanzu nakesan hawa.”
Bai kalli inda take ba sai Islam daya kalla yace “In kunci abincin sai kuyi.”
Taji dadi sosai na yadda