Showing 84001 words to 87000 words out of 128353 words

Chapter 29 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

41

sauri ya wuce doguwar kujera ya mike, tare da

sa kansa akan throw pillow din kan kujerar.

Dan kusa dashi taje, kamshin turaren datasa mai dadi sai dai a gunsa ji yake yafi komai wari, tace “Yaya dan Allah ka shiga ka kwanta, kar tsautsayi ya kawo Iman…..”

“Dan Allah matsa daga kaina.”

Abinda yace

kenan ya rufe idanunsa, matsawa tai kamar zata juya sai kuma ta dawo tasa hannu a cikin sumarsa, ai a zabure yasa hannu ya hankade hannunta yace “Ke wai ana dole ne? Meke damunki ne?”

Bakinta tadan motsa tana sanyin magana sai dai hawayen dake kokarin fi

towa ya hanata, juyawa tai jiki a sanyaye ta koma daki.

Duk yandabtaso bacci ya dauketa ta kasa, sai juyi kawai takeyi, ganin ba dama kawai ta mike tai alwala ta fara kai kukanta gun Allah, dan itakam batasan metayi ba bakuma ta fahimci me ke damun Aminu

ba.

Sqi wajen karfe biyu tadan kwanta akan sallayar anan bacci ya dauketa. Harya shigo yin alwala bataji motsinsa ba, tsayawa yai a jikin kofa yana kallanta cikin dan hasken dake shigowa ta window kadan, tausayinta ne ya kamashi, haushi da tsanar kansa ne

suka rufeshi, ji yake kamar yaje ya rungumeta ya fara aika mata da sakonin so da kaunar daya tabbatar yana mata, to amma an taba so da tsanar mutum lokaci daya? Meke damunshi?

Kusa da ita ya karasa yana tunanin maidata kan gado, idanunsa ne suka sauka ak

an fuskarta da sauri ya dauke kansa ransa a bace ya tsallaketa ya wuce toilet.

Yana fitowa ya sake tsallaketa ya wuce masallaci.

Ibty kam tunda ya shiga toilet ta farka, tana kallansa ya tsallaketa ya tafi masallaci, jitai wasu zafafan hawaye sun sake zu

bo mata.

*******

Har sukai breakfast in kaji yayi magana to dasu Islam ne, ko kallanta baiyi ba, kallansa tai tace “Yau zamu makarantar da Ainah.”

Ai kamar ta taboshi, “kije kiyi me? Banace ki jira ba? Keni meyasa sam bakida hakuri ne? Ko kuwa so ki

ke kije ku hadu da wancan sha sha shan mijin yayar taki?”

Kallansa tai tanasan magana sai dai a gabansu Islam? Shiru tai, nan taji yace “To ni nace ki jira koma menene ba yanzu ba.”

Haka suka fito tana kallanshi ya wuce ko bi takanta baiyi ba.

Ainah ce

tai waya akan zatazo anjima, jin muryar Ibty yasa tace “Ibty lafiya?”

Jiki a sanyaye tace “Ainah kije kawai ni zanje daga baya.”

Mamaki ya kamata tace “Yau ma bazaki ba kike nufi?”

Murmushin yake tai tace “Banajin dadi ne shiyasa, kije ni in na warke za

ni.”

“Meya sameki?”

Zazzabi ne kawai na tabbatar zuwa gobe insha Allahu zan samu sauki.”

Sam Ainah bata yarda ba dan muryarta ta nuna kamar wacce tai kuma ta gaji.

Kashe wayar tai ta nufi falo ta sanar da Ummy akan Ibty wai batada lafiya, hankalin Ummy

ne ya tashi tace “Subhanallah! Bari Mamman ya dawo sainya kaimu mu dubata, ke kuma kibar zuwa makarantar zuwa jibi inta warke sai kuje tare.”

*******

Sam Aminu ya rasa abinda ke mai dadi yau aiki har mistake yai sai da aka dawomai dashi ya sake, abin

da tun shekararsa ta farko a aiki ba’a taba dawomai da aiki ba inya gama.

Gaba daya hankalinsa nakan Ibtisam ya rasa meke damunsa, ji yake gaba daya so yake ya ganta kusa dashi ya lalasheta akan abinda yai, sau hudu yana daukan wayarsa yana ajiyewa.

Tab

bas wannan laifin daya mata ya wuce waya dolene ya bata hakuri sosai, taya zai yi mata haka bayan yanzu ya tabbatar yana san yarinyar? Ya kuma sha alwashin koyar da ita kaunarsa, to me kuma yakeyi haka? Me makon kauna kuma yana koya mata tsanarsa?

Yauma

ana tashi ya fito, yana kokarin shiga mota Baffa ya fito, da sauri ya karasa suka gaisa, Baffa ya kalleshi yace “Aminu yau kaine da wuri haka zaka wuce?”

Dan bayan kansa ya sosa yace “Inada abin yi ne a gida shiyasa.”

Dadi ya kama Baffa yace “Ya kamata k

am, ai tunda kai ango ne sai anamaka uzuri.”

Mota ya shiga dan yasan halin Baffa sarai da tsokana.

Yana kallansa harya wuce dadi ya kama Baffa da alama Aminu yanzu yana kaunar matarsa, dolene yanzu su cigaba da addu’a akan Allah ya kara hada kansu.

**

****

Tsayawa yai a shago yasai wani turare mai tsada wanda yake hade da lotion dinsa, aka saka mai a gift bag, murmushi yai wai yau shine yake abinda samari keyi? Dan birge budurwa? Dan yanzun ma sai daya shiga internet yaga yanda ake ba mace hakuri, nan

yaga wai asai gift akai mata sannan a bata hakuri.

Kai ya girgiza lalai Aminu kayi nisa.

A gida iyakam Ibty zazzabin gaske ne ya rufeta tsabar damuwa, dakyar ta daure tai abinci sannan ta koma dakinta ta kwanta.

Bayan su Islam sun dawo ta fito ta tabb

atar sunci abinci sannan Iman ta kaisu Islamiya ita kuma ta koma daki ta kwanta. Da Iman ta dawo itama ta shige dakinta tana latse latsen wayarta har bacci ya dauketa.

Harya shigo gidan ba motsin kowa, murmushi yadanyi ai ba laifi da alama nunamai taji h

aushi tai, bangarenta ya nufa ya rike jakar a bayansa da hannun hagu.

Yana bude kofar dakinta tana zaune agaban madubi tana gyara fuskarta dan ta tabbatar ya kusa dawowa.

Juyowa tai nanfa suka hada ido jiyai gaba daya tsana da kyamarta sun tasomai, fuska

rsa ce ta canza lokaci daya.

Ibty kam ganin yanayinsa yasa tadan runtse ido da alama haryanzu ana gidan jiya, mikewa tai jiki a sanyaye ga zazzabi tace “Yaya sannu da……”

“Kun shigo ciki kun zauna gida ba kowa, in sata ma ko wani mugun abin akazoyi har ay

i a tafi bakusani ba.”

“Nasa key a kofofin gida ai.”

“Musu kedai kullum musu bakya taba daukan laifinki, sam bazakiyi abu ace kinyi ba? Wannan wani irin taurin kaine?”

Kanta kawai tai kasa dashi, juyawa yai rai a bace, dakinsa ya shiga ya cila jakar cik

in wardrobe, tsaki yaja, laifinane ko wanaso birgewa?

Yaja wani tsaki tare da dafa kansa.

Ibty kam da kyar ta fito daga daki, dan tun ruwan tea datasha da safe haryanzu ta kasa cin komai, saboda zazzabi da bacin ran dake damunta.

******

Ummy ta dau

ko mayafi ta yafa tana kwallawa Ainah kira, “Kin fito munje munga jikin Ibtisam ko so kike dare yai? Dama gashi Mamman bai samu zuwa ba sai yanzu ke kuma kin tsaya kalula.”

Fitowa tai tana gyara dankwalinta Ummy kefa kikace nai mata abinci? Da ace masu ai

ki ne sukai da yanzu nima na shirya.”

“Sai kace wacce aka saki sirfe, dan abincin da kikai nawa yake?”

Ainah tana dariya suka fito, “Sai san jiki kamar mage.” Ummy ta fada.

*****

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e

̝

W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004

2083371244

Zenith Bankima

35

Haka su Ummy suka fito suka shiga mota, a dan shago suka tsaya suka sai drinks sannan suka dau hanya, Ummy a ranta tana ta fatan Allah yasa ciki ne?m, can kuma sai tace amma ciki ya fara wahalar da ita tun yanzu? In wannan tunanin yazo mata sai tace

ai kuma ko wace mace da yanda take laulayin cikinta, itadai ta tabbatar ciki ne kadai zai tabbatar mata da kusantuwar Aminu da Ibtisam, abinda kullum ke ranta take kuma addu'a akai kenan.

****

Ibtisam kam tana kwance a daki dan dakyar ta iya kaiwa Ami

nu abinci, gudun samun matsala ga ciwon kai da zazzabi dake damunta yasa tabar falan ta koma daki ta kwanta, tana juyo sanda su Islam suka dawo amma sam ta kasa mikewa, haka suka shigo dakin da Iman ganin yanda take yasa sukasan batada lafiya, murmushin ya

ke tai tace "Kaina ne ke ciwo daga nadan huta zan warke."

Haka Iman ta jawosu dakinsu suka cire kaya ta zuba musu abinci sannan ta nufi dakin da Ibty ke kwance, kusa da ita ta zauna tace “Ya Ibty dazu matsala kuka samu da Ya Aminu?”

Gabanta ne yai dan k

aramin faduwa ta bude ido ta kalleta, Iman ta kara kallanta tace “Dazu ina kwance a daki am sure naji muryar Ya Aminu a sama kamar yana fada, to na mike zan fito naga kamar bai dace ba.”

Murmushin dauriya tai tace “Kawai dan kinji muryar mutum a sama sai

akacemiki fada ne? Yana daga bakin kofa ne ina daki shine yake magana, yaji gidan shiru.”

Wata nannauyiyar ajiyar zuciya ta saki tare da danyin dariya tace “Kai Alhamdulila har hankalina ya tashi wlh na dauka har kun fara samun sabani.”

Maida idanunta ta

i ta rufe tace “Shine kika wani damu?”

Mikewa tai tana dariya tace “Harda na fara tsoron aure dan ganin Ya Aminu yasa yanzu naji inasan aure inhar naga ko wata ba’aiba ya canza ai kinga ba kanta.”

Ibty bata tanka mata ba dan kanta dake ciwo sosai, tasha

magani amma kamar batai ba.

Ana kiran sallar magrib taji ihun yara sun fita waje a guje, gashi ba karfi jikinta sam balle ta musu magana tace magrib tayi su dawo ciki, wayarta ta jawo tana kokarin kiran Iman taji kamar daga sama kuryar Ainah tana cewa “In

a Kalbin tawa?”

Dakyar ta mike zaune ta dan ja mayafi ta yafa ta fara kokarin mikewa, kofar dakin aka bude Islam sai tsalle take, ta kalleta tace “Aunty kinga??”

Ainah ce ta tsaya bakin kofar ta dan daga mata gira sannan ta karaso da sauri ta rungumeta,

tana “Wayyo kalbina ashe file dinki aka binciko.”

Ibty tadan tureta kadan tace “Ba wata kalbi kina magana kina dariya?”

Hannunta tasa akan kuncinta, kallanta tai da sauri tace “Zazzabi haka?”

Jin muryar Ummy a falo yasa ta mike da sauri, bata ko kula Ai

nah ba.

Ummy dake kokarin zama ta hango Ibty na tahowa, cikin kulawa ta mike da sauri, Ainah ta dan rike Ibty dan tafiyarta kadai zaka kalla kasan ba karfi a jikinta, tana kokarin zama a kasa Ummy tace “Zauna kan kujera” nan Ainah ta zaunar da ita, karaso

wa tai ta zauna kusa da ita tare da taba jikinta, cikin tsananin damuwa wanda ya bayyana kiri-kiri a fuskarta tace “Ibtisam? Kinsha magani kuwa? Zazzabi haka?”

Dan gyara zamanta tai tana tattaro dauriyarta tace “Nasha Ummy! Sannan bawai sosai yake wahala

r dani ba.”

Sallamar Aminu ce ta dan katseta dan Islam yanzu ta sanar dashi zuwan su Ummy, yana daki baiji ba.

Fuskarsa dauke da fara’a sosai yace “Ummy! Irin wannan zuwa ba sanarwa?”

Kallansa tai tadanyi murmushi tace “Ba dole nazo na dubiya ba, banm

asan zazzabin ya kamata haka ba.”

Bai kawo komai ba yace “Wani ne ba lafiya?”

Yai tambayar yana kallan mutanen falan, Ummy ta daure fuska sosai, mamaki ya rufe kowa na falan banda Ibty da batama dago ba, Ainah ta kalla tace “Keda Ummy ku shiga dasu daki.

”

Nan yaga anja su Islam cikin mamaki ya karaso ya zauna yana gaisheta tare da cewa “Wanene ba lafiya?” Ya karasa maganar yana kallan Ibty, da sauri ya dauke idansa dan sam ji yai bayasan ko ganinta.

“Kanasan cemin bakasan matarka batada lafiya ba kenan

ko me?”

Kallan Ibty ya sakeyi da sauri, nan fa wata kiyayga ta sake ruruwa yai murmushin takaici yace “Karya kika koma kuma? Ko kuwa neman hadani da iyayena kike?”

Mamakin kalamansa ne ya rufe Ummy baki a bude tace “Mene?”

Ya kalli Ummy rai a bace yace

“Banda munafurci Ummy ina zaune da ita a gida bata fadamin batada lafiya ba amma gashi can tana sanar dake batada lafiya?”

“Munafurci? Aminu? Kanka daya kuwa? Kai dana sani baka fadar munanan kalamai yau hankalinka daya kake abu haka?”

Wani banzan kall

onya mata ya kalli Ummy tare da dafa goshinsa yace “Ummy yarinyarnan ta isheni wlh, shiyasa tun farko nace muku banasan auren nan, sam ko ganinta banasanyi.”

Gaban Ummy ne ya fadi, tabbas Aminu ba kalau yake ba, nan fa ta fara Inalilahi wa ina ilaihi raji

’un a ranta, anya batai sake ba?

Cikin dakewa tace “Fadamin menene laifinta?”

“Batada kunya sam, gashi ta iya musu bazaka taba fada mata abu tace to ba, sannan ga karya na kamata tana abu amma sam tabure batasan zance ba.”

Ba shakka Aminu ba’a hayyaci

nsa yake ba, uta ta haifeshi a cikinta ko a mafarki tasan idansa bazai rufe ya dinga kushe mutum haka ba.

Kallan Ibty tai wacce hawaye kawai ke gudu akan kuncinta, tsananin tausayinta ya kamata. Maida idanunta kan Aminu tai tace “Naji na kuma fahimta yan

zu fadamin kalma daya datai na rashin kunya?”

Shiru yai da alama wai tunani yakeyi, sai can yace “Batadai da kunya Ummy, tamin rashin kunya ta kuma yiwa Hajiya, in ni ta rainani ai ita uwa ce.”

Idanunta tadan runtse, ta fara addu’oi a ranta tace “To yau

yau cikin daren nan matarnan zata bar gidan nan.”

Fuskarsa dauke da murmushi yace “Gwara ta koma gidansu inda wannan mahaukacin dake jiranta yake.”

Dagowa Ibty tai da sauri tana hawaye rabuwar aure ko wata da aure ba’ai ba? Itakam ta shiga uku.

“Ba mat

arka nake nufi ba wacce bakada hadi da ita nake nufi. Yau ko me zai faru kafata kafarta a gidan nan.”

Wani dan zabura yai yace “Wai Hajiya ce zata bar gidan? Ummy sai yaushe zaki fahimci matarnan amana ce a gareni?”

Yanayin fuskar Ummy ne ya canza zuwa d

amuwa sosai, da alama zurfin ciki gareta tunda har take kokarin boye abinda ke faruwa.

Tai wani banzan dariya tace “Amana? Ta wuce ni dana dauki cikinka na wata bakwai na kuma haifa?”

Fuskarsa a hade sosai yace “Saboda wannan ta zugaki yasa kika fadi hak

a Ummy?”

“Ya Allah! Na rokeka ka kwatomin d’ana daga wannan bala’in.”

A fusace Ummy ta mike ta fito daga falan, biyota yai da sauri yana bata hakuri akan kar ta kore Hajiya, ai bata tsaya ta kanshi ba tana tafe tana addu’oi akan yau Allah ya bata nasara.

Kai tsaye ta bude kofa ta nufi ciki tana bubuga koga.

Aminu na kusa da ita yana bata hakuri, Hajiya daga ciki duniya ta mata dadi dan tsire ma ta gama ci tasha yoghurt tana kallo a tv.

Tana bude kofa sukai ido hudu da Ummy, hankalinta ne yai mugun tash

i gashi batasa kwallinta ba wanda ke hana Ummy yi mata musu.

Ummy ta cusa kai cikin falan, kallan ledar dake kan centre table tai ta danyi murmushi tace “Duniya ta miki dadi, sai dai am sorry to say yanzu zata juya miki baya.”

Hajiya ta dake tace “Nikam

Asma’u mena tsare miki a rayuwa? A iya sanina ban miki komai ba, Aminu shiyasa a koda yaushe nake ce maka mahaifiyarka batasan zamana a nan……” ta karasa maganar tana wani matsar kwalla, aifa nan hankalin Aminu ya tashi ya kalli Ummy yace “Ummy wai dan All

ah meyasa kike haka? Ga wacce ya kamata kiwa fada can kinzo kina yiwa Hajiya? Menene laifinta?”

“Laifinta kake tambaya? Ina uwar arziki zata zauna a karkashin mijin ‘yarta? Bayan rasuwarta? Ki tashi tun muna mu biyu ki tattara kayanki mu wuce dake goben n

an ki tarkata ki koma kauyenku, gidan da nake neman a sai miki ma yanzu na fasa, tunda babban burinki a rayuwa bai wuce ki hana Aminu zama cikin kwanciyar hankali da matarsa ba.”

Kuka ta fashe dashi tace “Aminu na taba magana akan matarka? Nikam bazan iya

wannan bakin cikin ba ka barni kawai na tafi.”

Aminu yakai karshe gun bacin rai, yace “Inhar Hajiya tabar gidan nan to itama yarinyarcan yau auranta xai mutu zata koma gidan su.”

Mamaki ne ya rufe Ummy tace “Ni kake fadawa haka Aminu?”

Ya dan kauda kai

yace “Ummy na kasa gane meke damunki, akan me zaki dinga bin bayan yarinyarcan kina wulakanta Hajiya?”

Bacin rai ne karara a fuskar Ummy tace “Ni kakewa magana haka?”

Shiru yai baice komai ba, Ummy tace “To sai ta bar gidan nan yau, Ibtisam ni na kawota

ko? To zan tafi da ita yanzun nan.”

Hajiya ta dauka zataji Ummy ta sauko sai dai jin kalamanta yasa ta dago a zabure, ya zatayi tasa kwallinta? Wannan tsinaniyar mata me take shirin yi mata tana murna komai ya fara tafiya daidai?

Aminu ya zubawa Ummy i

do yace “Wai Ummy…….”

Hannu ta dagamai, yau kam sai godiyar Allah bata taba tunanin zata samu damar magana haka ba, dan haka dole ta tabbatar matarnan ta fita daga gidan nan kafin ta kasa komai.

“Idan ka sake magana wallahi sai ka fuskanci bacin raina. M

alama ke kuma tashi ko? Muje zan biya miki kudin hotel ki kwana yau gobe ki dau hanya. Sannan kar kiyi tunanin dawowa gidan nan domin a goben nan zan nemo masu zama a ciki koda kuwa kyauta zan basu gun zama.”

Gaba daya Hajiya ta sususuce, zubewa tai a k

asa ta dan hade hannaye tace “Asma’u naji koma menene zanyi amma ki bari sai zuwa gobe yanzu dare yayi.”

Ummy tai wani banzan murmushi tace “Dame dame kikayi kafin ki cimma burin raba Aminu da matarsa?”

Hajiya tadan dafe kirji tace “Wani saban sharri ne

wannan? Nikam mena miki kike min kazafi haka?”

Ibty dake waje dan ta biyosu ganin maganar ta dau zafi yasa ta tsaya a waje, jin kalaman Ummy yasa hankalinta yakai kunun da akaba Aminu, tabbas daga shan kunun nan ne ya fara canzawa, lalai matarnan bala’i c

e.

Aminu ya dan dafa goshi wata tsanar Ibty na sake tasomai, tabbas komai saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login