Showing 42001 words to 45000 words out of 128353 words
shigowa ta fizgo hannunta sukai dakinta.
Rufewa tai ta kara rike kugu tace “Sannu Aminiya wacce bata boye
min sirri.”
Ibty ta dafata tace “Wannan daurin fa? Bansan kin iya irinshi ba ai da tuni nazo kin koyamun.”
Ainah ta maze tace “Wai dagaske ke kika auri Ya Aminu? Ni wlh koda Ummy ta fadamin shekaranjiya na dauka karya ne.”
Ibty ta dan ture dankwalin ka
nta tace “ To yanzu me kikeso ayi? Ko muje gun Ummy ta shiryamu?”
Aina tadan shako wuyanta kadan tace “Allah kinci amanata.”
Dariya sukai sosai, kafin su zauna a bakin gado.
Ibty ta kalli dankwalinta daya fadi sannan tace “Banje na gaida Ummy ba kin tu
ren dankwali.” Gaban madubi ta koma ta fara gyara dankwalinta, Ainah ta matso tace “Wai ya akai wannan abu ya faru? Sannan ina Ya Umar? Allah dai yasa karya kashe min yayana.”
Ibty tadan waigo tace “Hmm Ainah nikaina abubuwan dasuka faru jinake kamar a m
afarki, ki barni naje na gaida Ummy koma menene zan fada miki ai kinsan bana iya boye miki abu.”
Tare suka fito suka nufi falan Ummy, su Islam ana zaune kan cinyarta anata zuba.
Ummy kam kallan Ibty kawai take tana hamdallah a ranta, sauke Islam tai san
nan tace “Ibtisam muje ciki mu gaisa.”
Tai maganar tare da nufar dakinta, Aminu na zaune a kasa yana daddana wayarsa, Ainah ta karaso ta tsuguna tana gaisheshi.
Fuska a hade yace “Dazu gidan dambe kike shirin zuwa?”
Tace “A’a Yaya haushi naji Ibtisam b
ata fadamin komai ba gameda aurenta.”
“Sannu Yaya babba, dolene dan kuna kawaye sai kinsan komai?”
Cikin dan shagwaba tace “Nifa ya kamata na mata babbar kawa.”
Kai yadan girgiza ya maida hankalinsa kan wayarsa yace “Yanzun ma ai sai kiyi bata baci b
a.”
Tasan magana ya fada mata, ta dan waske ta fara yiwa su Islam magana.
*****
A daki kuwa Ummy bayan Ibtisam ta shigo taga ta mike tasa ma dakin makuli, mamaki ne ya kamata sai dai bata nunaba, zama tai a kasa cikin girmamawa tare da sauke kanta kasa
.
Ummy tagani ta zauna kusa da ita, sannan suka sake gaisawa, hannunta da take wasa dasu taji Ummy ta riko, kallanta tai sannan ta maida kanta kasa.
Ummy tace “Ibtisam mun miki laifi ko?”
Dagowa tai idanunta suka danyi raurau kafin ta girgiza kai tac
e “A’a!”
Itama kai ta girgiza tai tace “Bamu sanar dake babbar matsalar dake tattare da auranki ba, Mun rufe miki abu mafi mahimmanci wanda ya kamata ki sani.”
Shiru tai a hankali hawaye suka taru a cikin idanunta, Ummy ta dan dago da kanta tace “Bansan
meke faruwa ba Ibty, munyi iyayinmu munyi addu’a munyi sadaka sai dai matarnan taki fita daga gidan nan, abin tashin hankalin shine yanzu hartakai ta kawo bama iya mata magana a gabanta, wanda na tabbatar abu ta mana, ga magana a bakina amma ina ganinta b
ana iya zafafawa.”
Mamaki sosai kalaman Ummy suka bata, habawa shiyasa dan dama itakam ta tabbatar ba kalau ba, ina aka taba wannan kwanacalar?
Ummy ta kara rike hannunta tace “Da Allah muka dogara sai fatan Allah ya baki ikon cetomu daga cikin wannan
bala’in.”
Bakinta na rawa tace “Ni?”
Kai ta daga tace “Aminu mijinki ne, kinfi kowa hakki akansa, bayan ‘ya’yansa, Ibtisam ki taimakemu ki kwato mana yaran nan daga bala’in dayake ciki.”
Kallan Ummy take a tsorace, ita me zata iya? Inhar su manya sun k
asa?
Hannun Ummy taji a kafadarta tace “Kada ki kuskura kisha ko ruwa daga gun matarnan.”
Ibty a tsorace take kallan Ummy, “Kada ki bari ta shigar miki dakinki, kitchen ko toilet, duk inda zata zauna to karya wuce falo. Ki taimakemu karki sake bari Ami
nu yaci abincin matarnan.”
Ibty gaba daya jitai kanta ya fara nauyi, “Sannan kija mijinki a jiki, Aminu nada saukin kai inhar kika fahimceshi, na sani sarai yanzu bakya gabansa sai dai a matsayinki na mace dole ki mike tsaye ki shawo kan mijinki, kada ki
bari kunya ko kuma shakkarsa dan ya girmeki sosai yasa ki kasa kwato mijinki.”
Ta kasa ko firta kalma daya sai shiru kawai datai tana kallan Ummy.
“Tare kuke kwana?”
Kunya ce ta rufeta da sauri tai kasa dakai, Ummy ta jinjina kai tace “Nayi tunanin hak
a, sai dai Ibtisam inaso kimin alkawari daga daren jiya bazaki sake bari ku kwana daki daban daban ba, inhar ba uzuri bane ya kama.”
Kanta na kasa ta daga kai alamar to.
Ummy ta cigaba da yi mata bayani akan Hajiya wanda gaba daya kanta ya gama kullewa
lalai itakam tayi aure a wahale, wannan yaki akeso tayi a gidan miji ko me? Haka suka fito tare itadai gaba daya jikinta ba laka, anan sukaci abincin rana sannan aka hada musu abinci a kula wanda zasu tafi dashi na dare.
Ainah kam tayi mamaki sosai jin y
anda auransu ya kasance, tausayin Ibty ya kara kamata dan ta tabbatar Ya Aminu haryanzu matarsa ce a ransa.
*********
Da karfi ya hankada keken saura kiris ta fadi kasa, tai saurin rike bango.
Kallansa tai idanunta na zubar da kwalla, ya matso yas
a hannu ya shako wuyan rigarta. Tun jiya ciwonta ya tashi, amma ta rasa wa zata fadawa, sai daurewa kawai takeyi.
Idanun Umar yayi jaa kamar gauta yace “Munafukar banza da wofi daga ke har iyayenki munafukai ne kuma azzalumai ne.”
Bilkisu ta share kwal
larta tace “Ya Umar kayi hakuri dan Allah.”
Ya kara rikota sosai yace “Wallahi sai na wahalar dake wahalar da saikinyi dana sani, ‘yancinki daya shine abinda nake shiri yau ya tabbata amma wlh in wani abu ya kawo cikas to wallahi ki shirya haduwa da bala
’i da masifa.”
Ya hankadata yai ciki, hawaye ta shiga gogewa, tana tsananin san Ya Umar gani take kome zai mata indai har suna tare to fa zata jure.
Anayin Isha’i ya fito dana ya hada kayansa yakai gidan wani abokinsa.
Kai tsaye yawuce unguwar su Ibt
y.
*****
Hajiya yau dakyar ta iya cin abinci, ta hanke shawarar kwanciya kawai tace batada lafiya dan ta tabbatar Aminu zai dawo hayyacinsa inyaji ciwonta ya tashi.
Sai dai tunani ya hanata iya kwanciyar, sako ta turamai akan ya taho mata da magani.
Ai yana gani ya tattaro su Ibty suka fito duk ya rikice, mamaki sosai ya kama Ibty yanzu kam ta tabbatar da kalaman Ummy wannan ba’a hayyacinsa yake ba, yana zuwa ko kofar motarsa bai rufe ba ya nufi bangarenta.
Ibtisam ta wuce ciki bayan ta debi wasu k
aya, dan Ummy tace abarsu Islam sai gobe lahadi sai su dawo.
Sam ta manta da litattafan da Umar ya kawo mata, da a kusa da ita ta ajiye batasan ya akai ba taga an maidasu bayan mota, ta tabbatar Aminu ne tunda shikadai ne ya shiga motar.
Shiru tai baya
n ta shiga daki, kalaman Ummy ne keta mata yawo akai, gaskiya bazata zauna kamar mace mara ilimi ba, ko yaran kauye yanzu sunzan yanda ake tafiya da namiji, balle ita.
Mikewa tai ta farayin wanka sannan ta dauko kayan bacci daya daga cikin na lefen ta da
n an kawo mata kayan lefenta, maidashi tai da sauri tana dan dadiya kadan tace “Wannan in na saka ai daukata zaiyi ‘yar iska.”
Haka tai ya dubawa sai can ta samo wata doguwar riga ta zura sannan ta saka hijab dinta, falo ta fito tana dan sake gyarawa, ta
na yi tana kallan window sai yaushe zai dawo? Itakam da gun kishiya yaje ma a kalla tasan inda yaje amma wannan dame zata kirata?
Haka ta shiga kitchen ta karasa wanke kufunan safe sannan ta jera abincin da suka taho dashi daga gidan Ummy.
Aminu kam s
ai dayaga tasha magani sannan ya mike yana shirin fitowa.
Kuka tasa wanda ya daga mai hankali, tace “Aminu nikam komawa kauye zanyi kwanan nan tunanin Na’ima ya hanani sukuni, tunda kai aure nake ganin shikenan rayuwar Na’ima ta kare.”
Dawowa yai ya tsu
guna yace “Hajiya meyasa kike fadan haka? Ko da wasa bazan iya mantawa da Na’imah ba sannan ga ‘ya’yanta nan wanda a koda yaushe inka kallesu zaga tuna da ita.”
Ta sake sa kuka tace “Na tabbatar matarka ma bazataso zamana a gidan nan ba, dama mahaifiyarka
baso take ba, Aminu ka maidani kauye dan Allah.”
Tausayinta ya kara kamashi yace “Hajiya ki kwanta ki huta, da safe mayi magana.”
Haka ya fito duk zuciyarshi ba dadi, da alama auren nan ne yasa duk abin duniya ya dameta, tana ganin wata ta maye gurbin
Na’imah.
Mota ya karasa ya shiga da ragowar manyan kayan abincin, tana kitchen tana wanke sink ya shigo, kallansa tai tace “Hajiyar batada lafiya ne?”
Ya kalleta sosai yace “Me Ummy tace miki da kuka shiga daki?”
Kallan mamaki tamai tace “Hirar duniy
a mukai tamin nasiha.”
Kamar zaiyi magana sai taga yana neman fita da sauri tace “Wani abin akace?”
Ya juyo sosai yana kallanta yace “Hajiya tace kema basan zamanta kike ba, so na dauka Ummy ta miki zancenta ne.” Abinda yace kenan ya fita, da kallo ta
bishi baki a bude.
Ibty kinga ta kanki, yaki yana gabanki, dole na maido da hankalin Aminu kaina kafin na san yanda zanyi na sallami matarnan.
To amma ta ina? Abinda iyayensa suka kasa na isa nayi?
*******
Yayi sintiri harya gaji ga uban sanyi
da akeyi, ji yake kamar gabobin jikinsa sun daina aiki.
Karfe sha biyu da rabi? Lalai Ibtisam ta nunamai inda ta ajiyeshi shima kuma yanzu ya dau alkawarin nuna mata wulakantashi datai ba abinda zai jawo mata sai dana sani.
Haka ya koma gida, ya shiga b
argo kankace me zazzabin soyayya da rashin Ibty ya rufeshi, wasu zafaffan kwala ne suka zubomai, lalai anci amanarsa kuma wlh bazai yafe ba. Tun yarinyarnan tana yarinya yake santa yake tanadinta yake ajiyarta, sannan wani katan banza yazo ya dauketa? Inya
tuna haka jiyake zuciyarsa na wani irin tafasa.
******
🏌🏻
♀
️
💫
IBTISAM......
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
Ki hanzarta k
i mallaki naki
🤸🏻
♀
️
*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*
2083371244
Zenith Bank
Aisha M.Salis
+447894142004
Ko kati a 07043079282
*Shaidar biya ta wannan* 07065283730
18
🤸🏻
♀
️
Tsaye tai a cikin dakinta tan
a tunanin yanda zata tunkari dakin Aminu, ta zauna a gaban madubi tana kallan kanta. Ajiyar zuciya tadanyi mai sauti sannan ta dan gyara fuskarta ta dau turare tadan fesa, shiru ta sakeyi tana tuno yanda Amare ke dan naku-nuku in tana karanta novel, to ita
gashi sai dai takai kanta? Hijab dinta ta dauka ta zura sannan ta nufi bangarensa.
Agoggon falansa ta kalla wanda ya nuna karfe goma na dare, kwan wutar dakinsa tana kune da alama bayan yaci abinci ciki ya shiga. Gabanta ne ke faduwa akai-akai harta is
a kofar dakin, hannu tasa tana neman bude dakin da sauri ta sauke hannunta. In ya korota fa? Gashi tawa Ummy alkawari? Hannu ta kara sawa cikin shakka ta runtse idanta da karfi sannan ta bude kofar, bakinta dauke da sallama.
Bata kalli inda yake ba dan t
a tabbatar suna hada ido zata rasa abinyi, tana jinsa sanda ya amsa sallamar amma kanta na kasa ta nufi gado tana kallan kasan dakin.
Aminu dake zaune akan gado ya mike kafa yana dane-dane a computer ne ya tsaya cak yana kallanta. Me takeyi? Tambayar dat
azo mai kenan. Bai gama tunanin me take shirin aikatawa ba kawai yaga ta nufi kan gado inda yake.
Dan idanta ta dago kadan ta hango kafar Aminu a saitin da take kokarin kwanciya, da sauri ta koma baya ta zagaya ta daya bangaren, shikam idanunsa na kanta
yana kallan ikon Allah.
Kamar zata zauna a gadan sai kuma ta wuce toilet dinshi, brush dinta data dauko ta ajiye a ciki, sannan ta furzar da wata iska, shafar kirjinta tai sannan ta kara fitowa, kan gadan ta karasa, kawai yaga ta kwanta ta juya baya, tsa
nanin mamakin wannan lamari ya hanashi magana.
Jin baice komai ba yasa tadan saki ranta, hannu tasa saboda ta ji sanyi na ratsa kafarta, tana dan laluban bargo, idanunta a rufe sannan ta juya. Kallan hannun yai sannan ya janye bargon daga inda hannunta z
ai kamo, ganin ta kasa kamo bargon yasa ta dan takure cikin hijab dinta.
“Me kike anan?”
Abinda taji yace kenan, bakinta nadan rawa tace “Anan zan kwana.”
“Anan zakiyi me?” Yai tambayar yana kara kallan bayanta cikin mamaki, Ibty tai shiru tare da maid
a idanunta ta rufe ta fara dan sauke numfashi kadan kadan alamar bacci.
Abin ma dariya yaso bashi, yace “Anan zakiyi me kikace?”
Shiru nan ma ba amsa, ajiye laptop dinsa yai a side bed sannan yasa hannu ya juyo da ita saitinsa, haryanzu idanunta a rufe
wai a dole bacci take, saketa yai sannan ya zuba mata ido yana ganin sanda zata bude ido. Ibty kam idanunta kam, jin shirun yayi yawa yasa tadan kasa kunne, motsi taji kamar an sauka daga kan gadon, sai kuma taji alamar rufe kofa, idanta daya tadan kyalla
kadan tanasan ganin ko yana nan, ganin bakowa agun yasa ta danyi fifita da hannunta sannan ta dan mike ta zauna tana sake fitar da wata ‘yar iska.
Gyaran murya taji daga gefen toilet, idanu ta zaro ai bata kalli gun ba tai saurin kwanciya ta runtse idan
unta kyam.
Aminu baisan sanda wani murmushi ya bayyana a fuskarsa ba lalai yarinyarnan.
Karasowa yai ya zauna yace “Tashi ki fadamin me kike a dakin nan? Ko kuma na kinkimeki na maidake dakinki.”
Kin bude ido tai, yace “in irga uku?”
Nan taji yace
“Daya, biyu, uku!”
Hannunsa taji ya sakalo ta wuyanta da sauri ta bude ido tare da cewa “Ya Aminu dan Allah ka bari, tsoro nakeji, bazan iya kwana ni kadai ba.”
Kallanta yai sosai sannan ya saketa, yace “Kina nufin ni kike cewa tsoro kike?”
Ta jinjina
kai da sauri alamar eh tace “tsoro ne dani sosai, bakaga jiya a gunsu Islam na kwana ba?”
“Ahhhhhh tsoro ko?” Ta daga kai da sauri. “Oh! Shiyasa naga sanda kike kwana a daki ke kadai a hotel cikin dare ihu kikeyi kina dawowa inda nake.”
Ganin ya kamota
yasa tadan hada labanta biyu ta rufe tace “Na kwana ni kadai ko?”
Bai amsa mata ba sai kallanta dayai, tadanyi murmushin yake tace “To koma dai na kwana da yanzu tsoro nake.”
“Tsoro?”
Ta daga kai yace “Tsoro shine bazaki kwana a kasa yanda kika kwana
a dakinsu Islam ba sai akan gadona?”
Saman goshinta tadan sosa kadan tace “Jiya dana kwana a kasa ne bayana yake ciwo.” Tai maganar tana dan taba bayanta dayin alamar zafi.
Dan kallansa tai kadan taga yanda ya kafeta da ido, da alama yanzun ma bai kama
karyar ba.
“In nace miki yarinya kiji haushi, yanzu wasu tatsuniyoyin kike jeromin?”
Tadan turo baki cikin jin haushin kalamansa, kallan yanda ta wani turomai baki yai yace “Badai zagina kike a ranki ba ko?”
Kallansa tai cikin wani yanayi na shagwaba
da sakalci da batasan tayi ba tace “Nawa Ummy alkawarin kwana a dakin nan daga yau ne shiyasa. Sannan Allah ni ba yarinya bace.” Tana fadar haka yaga ta ja bargo ta sake kwanciya, a zaune ta barshi da baki bude eh lalai yarinyarnan taga gadan baccinsa, sh
i takewa magana haka?
Shi dama yasan akwai abinda suka tattauna da Ummy wato akan kwana tare ne?
Kallanta yai yace “Kina nufin daga yau anan zaki dinga kwana?”
Gani yai ta daga kai alamar eh, yace “In kuma naki yadda fa? Ko kin manta daki nane?”
“Sa
i na fadawa Ummy tasan abinda kace” Baiyi tunanin jin wannan amsar ba sam. Kasa magana yai sai kallanta dayai, eh lalai Ummy ta kara bari yarinyar nan ta rainashi.
Ko ya sauka ya bar mata dakin? Tunowa yai da kwanciyar kujera dayai a hotel yanda ya dinga
tashi da ciwon baya, abinka da shekaru sun dan fara kamawa.
Yanzu haka zai dinga kwana da yarinya a gado daya? Bai kwanta da ita bama ta rainashi balle sun kwana gado daya?
Aikin sam kasa karasawa yai haka yanayi yana kallanta cikin takaici ya kashe
wuta ya kwanta, ya dade yana juye-juye kafin bacci ya daukeshi.
***
Wajen karfe biyu da rabi na dare mumunan mafarki ta farayi, wai gatanan Umar ya rufeta a wani daki a daji, abinci ma ta window yake cila mata. Sam saboda tsoro batasan ta shigo jikin Am
inu ba, cikin bacci yaji an rikeshi sosai, idanu ya bude sannan yasa hannu ya kuna fitilar wayarsa, mamaki ne ya kamashi ganinta a jikinsa sosai ta rikeshi. Hannu yasa yana kokarin janyeta daga jikinsa, hawayen dayake gangarowa a idanunta ne yasashi tsayaw
a yana kallanta, wannan yarinyar tabbas akwai abinda ke cinta, to shi bata fadamai ba taya zai tambayeta? Ko saboda batasanshi ne kullum take mafarki da koke koke cikin bacci? Saman goshinsa ya shafa yana sake kallanta, harya sake kai hannu zai tureta sai
kuma ya fasa.
Hannunsa ya daura a saman goshinsa kawai ya rufe idansa, da alama yanzu da take jikinsa bacci take shikam sam ya kasa komawa bacci, a haka zai cigaba da