Showing 24001 words to 27000 words out of 128353 words
hotel, me zasuyi anan? Kallansa tai tana neman magana sai dai jitai batada bakin magana.
Aminu ya dau tissue
ya mika mata yace "Goge fuskarki kafin mutane su dauka satoki nai."
Ansa tai ta goge fuskarta sannan ta fito sam ta manta da jakarta.
Aminu ya kalli jakar lalai wannan yarinyar, badai da saninta tabarmai jakar ya daukar mata ba?
Kallanta yai kamar za
i mata magana sai kuma ya fasa, dauka yai sannan yai gaba, wuceta yai ta bi bayansa.
Babban daki ya kama musu, ta zauna akan kujera, ko sallah batai ba, mikewa tai ta kalli falan ba kowa sai ita, nufar daki tai da niyar tai alwala shi kuma daidainan ya c
ire manyan kayansa yana sanye da vest da wandan shaddar, kokarin yin wanka da alwala yakeyi.
Idanu ta zaro da sauri ta koma falo, bakijta nadan rawa tace "Yahkuri."
Aminu kam da sauri ya maida kayansa sannan ya zauna akan gado cikin dakewa yace "Shigo
ko ba toilet zaki ba?"
Shiga tai kanta a kasa wai dan karta kalleshi, tana kokarin kuma kanta da bango taji yace "Me kikeyi hakan?"
Tsayawa tai sannan ta kalleshi da sauri, ganin saura kiris ta make kanta yasa ta sake kallansa tace "Yahkuri na dauka bak
a gama shiryawa bane."
Tai maganar tare da wucewa toilet da sauri, alwala tai sannan ta fito ta koma falo tai sallah, ya dade akan sallaya tana kuka tana kaiwa Allah kukanta, shikam Aminu duk kunnensa ya gaji dajin wannan kukan, wai haka amaren yanzu suk
e? Shi ko dan suna kaunar junansu da Na'ima ne? Dan kuka kadan tai, wannan anya ko abinci ma taci?
Yadan kauda kai ai wannan ra’ayinta ne. Harya gama abinda yake ya kwanta bata shigo ba, yanzu ya daina jin sheshekar kukanta.
Ibty kam tun tana kuka har
bacci ya dauketa, dan ta rasa yanda zatai gashi Abba ya kwace wayarta yace “Ko an sai mata waya karta kira kowa saishi, itakam tanasan tasan halinda su Umma kw ciki. A haka bacci ya dauketa a durkushe.
Tun Aminu na lissafi hardai ya kasa kwantar da hank
ali ya mike, falon ya fito a zaune take inda tai salla ta hada kai da gwiwa, kallanta yai sannan a fili yace “Ba dole bacci ya daukeki ba, kinata kuka kamar ba gobe, kinfi awa hudu kina abu daya.
Kamar zai juya sai kuma tausayin kwanciyar datai yadan kam
ashi, ko ya sata a daki shi ya kwanta anan?
Hannu yasa yadan tabata yace “Tashi ki koma daki.”
Sam bataji ba saboda nannauyan baccin daya tafi da ita, dan tabata ya sake yi da dan karfi, ita kuma daidainan tayi mafarkin Umar na janta a daji tana turjew
a.
Cikin firgici ta rike hannun Aminu iya karfinta tana wani irin kuka, tana cewa “Kayi hakuri dan Allah! Na tuba!”
Yanda ta matsemai hannu da kalamanta ne yasa yadan sunkuyo hannu yasa yadan daga kanta yace “Tashi!”
Bude ido tai gabanta na faduwa, t
a zubasu akanshi, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata, mamaki ya kamashi yace “Sakemin hannu ko?”
Kallan hannun tai sannan ta sakeshi da sauri, ya dan gyara zamanta, mikewa yai cikin dakewa yace “Ki wuce ciki ki kwanta, in kuma kinajin yunwa a kawo mik
i abinci.”
Kai kawai ta girgiza sannan ta mike a hankali tace “Nagode Ya Aminu, banajin yunwa.”
Abinda tace kenan ta wuce ciki, kafada yadan daga kadan sannan ya zauna ya jawo wayars ayana dube dube, kallan dakin yai yace “Tunda batajin yunwa ai tasan
cikinta.”
**********
Umar kam ya gama saitawa ta yanda zai je gida ya sato Ibtisam, ya kuma samu abokansa biyu wadanda zasu taimaka mai, sai dai abin tambayar “Inane gidan?” Taya zaisan gidan? Wannan abu yasa sun rasa yanda zasuyi shi kuma yasha alwa
shin bazai kwana ba sai da Ibty…….
*******
Wayyo
🤭
Kinaso kisan yanda rayuwar Aminu da Ibty zasu kasance? Ga kuma Hajiya a gefen hagu? Sannan ga Umar a gefen dama?
Yi maza ki mallaki naki domin free pages sun kare
😔
Ayusher Ce
🏌🏻
♀
️
💫
IB
💫
(.........In Between)
*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*
*ŋą Ä̤
ʏʊ
ֆ
ɦɛʀ
ʍʊɦɖ
🏌🏻
♀
️
*
*Top Ten! Takun Haske Batch A*
*Dan Allah in baki siya ba karki karanta, kudi kalilan zaki biya ki samu wannan garabasar*
*11*
Duk yanda Aminu yaso yai bacci ya kasa, sai juye yake akan kujera, ajiyar zuciyar da take tayi irin na wacce taci kuka ta gaji shine duk ya hanashi bacci. Kamar ya jawo dakin ya rufe sai dai yana ganin hakan bai kamata ba in wani abin ya sameta cikin da
re fa? Ganin dare natayi gashi yanasan zuwa aiki gobe yasa ya mike ya nufi dakin. Tana kwance ta dukunkune ko bargo bata rufa ba, ta dukunkune jikin hijab dinta, shiru yai yana kallanta yanda take bacci tanata sauke ajiyar zuciya.
A fili yace "In kinsan
bakyasan auren meyasa baki bi shawarata ba? Bayan na sanar dake kice bakyaso?" Ganin dai shikadai ke maganarsa ba amsa yasa yai kamar zai juya, haryayi taku biyo sai kuma naga yadawo yaja bargon dake kan gadan ya luluba mata, cikin baccinta taji alamun han
nu ana sa mata abu. A hankali ta bude idanunta ta saukesu akanshi.
Da sauri ya saki bargon tare da mikewa sosai yai gyaran murya, kafin yace "Meye amfanin bargon in kinajin sanyi?"
Bakinta tadan motsa a hankali kafin tace "Ya Aminu karfe nawa?"
Agogg
on hannunsa ya kalla kafin yace "karfe biyu na dare."
Wani abu tadan hadiya a bakinta kafin tace "Nasan sun kwanta yanzo, amma Yaya dan Allah bani aran wayarka ko text nayiwa Abba."
"Yanzun?" Abinda ya tambayeta kenan tadan mike zaune fuskarta da idanu
nta duk sun kumbura, shi dama haka amaren suke?
Wayarsa ya dauko ya bude sannan ya mika mata, kafin ya juya ya fita. Zama yai a falo yana mamakin yanda yanayinta duk ya canza, ji yai tausayinta ya kamashi, shifa abinda bayaso kenan azo ana auren dana sa
ni bayan shi ba shine ya tilastata ba.
Ibtisam kam daga daki sako ta turawa Abba tana tambayar ko gida kowa lafiya, ganin anfi miti biyar ba reply yasa tasan bacci yake.
Saukowa tai daga kan gadan a hankali, jitai jiri jiri na yunwa na neman yarda ita,
rabanta fa da abinci ashe tun safe ko? Tazo zataci akace tai wanka ta shirya tukunna, bayan ta shirya kuma tayi sallah akace ta fito daukan hoto, daga nan kuma shikenan komai ya rikice, gashi da safen kosai taci kawai tasha dan tea.
Bango ta dan dafa ta
re da takawa a hankali zuwa falan, kusa dashi taje yana zaune akan kujera ta mikamai wayar da hannu biyu, kallanta yai bai amsa ba yace "Kingama?" Kai ta daga a hankalin sannan tace "Nagode!"
"Wayarki a gida kika barta? Ko kwacewa akai?" Kai tadan girgi
za a hankali kafin tace "Mantawa nai da akace na fito bansamu damar daukowa ba."
Kai ya daga sannan yasa hannu ya amshi wayar, juyawa tai, tai dan gefe kadan tana neman faduwa, da sauri ta rike kujerar dake gefe, mamaki ne ya kamashi ya mike ya tako zuw
a inda take, hannu yasa akan saman goshinta, wanda hakan yasa ta dawo ta kalleshi, samun kanta tai da saukar da idanta da sauri saboda wani kwarjini daya mata.
Hannunsa ya dauke daga saman goshinta sannan yasa a kan wuyanta, jitai numfashinta na neman da
ukewa na wucin gadi, ta kasa ko kwakwaran motsi, muryarsa taji yace "Baki da lafiya?"
Bakinta nadan rawa tace "A'a kawai kaina ke ciwo sai dan jiri da nakeji."
"Abinci fa? Yaushe rabanki dashi? Tunda naji ba zazzabi bane.”
Yanzun ma kanta na kasa a h
ankali tace "Da safe nasha tea da kosai."
Wani kallo ya mata na bacin rai da alama yarinta na damun yarinyar nan, tun abincin safe bataci komai ba ta zauna kuma tanata uban kuka? Kamar wacce akayiwa rasuwa?
Cikin dan zafi yace "Shiga daki ki zauna."
Bata ko musa ba ta wuce tana tafiya a hankali tana dan bin bango, da kallo ya bita sannan yadan girgiza kai, saman fridge ya kalla kayan tea ne kawai a gun, ya kuna kettle ya dafa ruwan zafi sannan ya hada mata tea, bacci yakeji dan har wata doguwar hamma
yai, daukan cup din yai ya nufi daki, harta dan fara gyangyadi, gyaran murya yai yana daga tsaye. Bude idanunta tai tare da gyara zama, mika mata cup din yai yace "Sha kafin ki kwanta"
Hannu tasa ta amsa, idanunta suka dan ciciko a hankali tace "Nagode."
Bai amsa ta ba ya koma falo, kwanciya yai kankace me yanzu kam bacci yayi gaba dashi.
Ibty kam tana gama sha tai alwala tai saloli wanda haryanzu babu karfi sam a jikinta, da kyar ta koma kan gado ta kwanta kafin bacci yai gaba da ita, yanzu kam bacci n
e mai nauyi ya dauketa.
********
A can bangaren Umar kuwa yayi sintiri harya gaji, ganin bashida wata hanyar dazai sa yasan inda aka kai Ibtisam yasa ya dawo gida.
Yan Uwa yanzu kam ana zaune a falo duk kowa yayi jugum 'yar hirar ma duk kowa ya daina
, wasu ma sun tafi sun kwanta bacci.
Shiga yai da sallama kansa a kasa kai bakace shine na dazu ba.
Ganin haka yasa kowa hankalinsa yadan kwanta, tsugunawa yai sannan ya bada hakuri kafin ya nemi shiga dakin Bilkisu wai dan ya bata hakuri.
Wannan abu
ya kwantar da hankalin kowa nan fa ya wuce dakinta su kuma kowa ya saki hamdalla.
Bilkisu tana zaune akan gado tana cin abincin da aka kawo mata, da taki ci sai dai Umma da kanta ta zauna ta tilastata sannan ta mata fada, jin sallar Umar yasa Umma ta kal
li kofa cikin mamaki sannan ta amsa.
Umar ya shiga ya tsuguna a kasa sannan yaba Umma hakuri, wani dadi ne ya ziyarci zuciyarta, ta fito daga dakin cikin jin dadi tana godiya ga Allah.
Zama yai a kan gadan kafin ya watsa mata wani kallo, Bilkisu gabant
a ne ya fadi ganin yanda ya canza, cokalin hannunta ta ajiye cikin tsoro tace "Ya Umar?"
Wayarsa ya mika mata yace "Saka sabuwar number Ibtisam."
Da sauri ta kalleshi kafin ta girgiza kai tace "Ibtisam ai bata canza number ba." Cikin zafi ya nunata da
yatsa yace "Kinsan Allah? In har bakyasan na baki saki uku a daren nan ki fadamin gaskiya."
Hawaye ne suka zubo mata tace "Wallahi bansan wata number ba bayan wacce take da ita."
Fuskarsa a daure ya maida wayarsa yace "Wace unguwa aka kaita?"
Nan ma
kai ta girgiza tana haways tace "Wallahi shima bansani ba, kaga ko jere ba'a mata ba balle asan wace unguwar ce."
Fuskarsa takai matuka gun baci, hannu ya sa ya fizgo wuyan rigarta, samun kanta tai da numfashi dakyar ya saketa yana hucin bacin rai, yace
"ki tabbatar kin binciko inda aka kai ta kafin gobe da safe, kuma karki kuskura ki fadawa kowa ni na sakaki, in kuma takardarki kike nema ni a yanzu ma sai na mika miki."
Yana kaiwa nan ya mike ya fito, da kallo ta bishi tana wasu zafafan hawaye masu zaf
i.
Umar kam sai shimai albarka su Goggo suke dan tabbas yanzu kam hankalinsu ya kwanta, shikam waje ya fita zuciyarsa na wani irin tafasa, ranar haka ya kwana ko gyangyadi baiyi ba, ko idanunsa ya rufe hango Ibty yake a kusa da wannan sokon mutumin suna
mai dariya.
*********
Har akai kiran assalatu dukansu ba wanda ya farka, sai karfe bakwai na safe Aminu ya bude idanunshi, yana ganin agoggo a zabure ya mike tsaye gashi 8 ya kamata ya shiga office, wayarsa ya dauka yana kokarin sanar dasu zaiyi late
kadan, sakon Baffa ne ya shigo "Na sanar yau bazaka samu zuwa aiki ba, ina kuma sa ran ka kula da matarka"
"Baffa!" Abinda ya fada kenan tare da ajiyar zuciya, sakon Abba ya gani hakan yasa ya ajiye wayar tunda sakon ba shi akayiwa ba.
A hankali ya sh
igo dakin ya bude jakanya kwashi kayan dazai saka, shikam ai a toilet ma zai shirya dan bayasan raini, ina girma ace kanasa kaya yarinya sa'ar kanwar kanwarka ta ganka?
A hankali ya kwashi duk abinda zai saka sannan ya nufi toilet yana tafiya a hankali,
kamar daga sama yaji ance "Ya Aminu ka yadda abu."
Runtse ido yai sannan ya mike sosai ya kalleta fuskarsa a daure sannan ya kalli kasa, jiyai kamar zai nutse ganin boxers dinsa, wannan wani irin abin kunya ne? Cikin takaici ya dauka bai ko kalleta ba y
a wuce toilet.
Ibtisam kam batama kula da menene ba, ta danji motsi ne ta bude idanunta ganin abu ya fado yasa tamai magana.
Aminu kam haka yai wanka ya shirya a bandaki duk ji yake raini ya gama shiga tunda har taga boxers dinshi. Fitowa yai fuskarsa
a hade yana kokarin komawa falo.
Ita kuma ta yashi ta gama gyara gado kenan tana jiran ya fito ta shiga tai alwala.
Ganin ya fito yasa tace “Ina kwana?”
Dan kallanta yai na dan second sannan ya maida kansa gefe yace “Ya jikin naki?”
A hankali tace
“Na warki.”
Harya fara tafiya tace “Ya Aminu? Abba yayi reply?”
Tsayawa yai sannan ya dauko wayarsa ya bude, mika mata yai bai bari ta kalli cikin idansa ba. Itakam a hankali ta karaso ta amsa ta duba sakon daya bude mata “Ibtisam ki kwantar da hankali
nki nan komai ya daidaita, ki kula da mijinki.”
Idanu ta runtse sannan ta sauke wata ajiyar zuciya wacce yasashi kallanta, daidainan idanunsu suka hadu da juna.
Dauke idanu yai itama ta sauke nata kasa, mika mai wayar tai ya amsa yasa a aljihu, kafin
yace “Me zakici? Zan je nai order a restaurant dinsu.”
Tace “Koma menene ba matsala.”
Okay kawai yace sannan ya fita daga dakin, falo ya nufa ya tada sallar asuba.
Ibtisam wani ajiyar zuciyar ta sake saukewa yanzu kam najin dadi ne dan da alama komai y
a daidaita a gida.
Toilet ta shiga tai wanka tai alwala sannan ta fito tai sallah, jakartata ta bude ta dauko wata doguwar eigar lace wanda bayan an gama dinkin, akazo akai kwalliya da stones wanda ya fito da kyan dinkin sosai, ganin yanda kayan yadan ka
mata yasa ta dauko mayafin lace din ta ajiye akan gado sannan ta dau hijab ta tada sallah, ta dade tana kai kukanta gun Allah tana addu’ar Allah yasa kar sanadiyarta rayuwar Yayarta ta kara shiga cikin bala’i.
Kallan dakin hotel din tai dan sai yanzu ta
kurewa dakin kallo, hijab din jikinta ta ninke ta maida akwatin sannan ta fito falo tana dan tasan bayanan saboda taji alamun fitarsa tana sallah, a ranta tace “Da alama ansha kudi dan tasan babban daki irin wannan mai kyau dole a kashe kudi, jikinta ne ya
i sanyi cikin takaici tace “Duk laifinane da badan anyi haka ba ai ba yanda za’ai Abba ya sa a kaita cikin gaggawa haka.”
Zama tai a kan kujera tana mamakin wai ashe Umar shi ya dauka ita zai aura? Itakam ta kasa gane meke faruwa ta kuma kasa fahimtar kw
antar da hankalinta ya kamata tai ko kuma kuka? Batasan auran Umar sai dai bazataso dalilinta yayarta ta shiga cikin bala’i da masifa ba.
Ta tafi tunani sam bataji alamun bude kofarsa ba, doguwar rigarnan ce kawai a jikinta ko dankwali bata daura ba sabo
da ta leko taga falan ne ta koma ta daura dankwali ta sa babban mayafin data fito dashi.
Aminu kam kallanta yai cikin mamaki, a ransa yace “Har ta gama kukan amarcin?”
Kamar yanda ya saba gyaran murya yai hakan yasa ta kalli gun, idanu ta zaro a tsorace
sannan ta mike cikin sauri, samun kanta tai da sa hannu a saman kirjinta, duk kunya ta rufeta tai daki cikin sauri har tana neman faduwa.
Baki yadan bude cikin mamaki, me take rufewa? Lalai yaran zamani dauka tai kallan kirjinta yai ko me?
Itakam daki
ta shiga da sauri ta dauko mayafi ta yafa sannan ta zauna akan bakin gado tace “Wannan ai sai ya dauka banida kunya, jiya na kwan ina kuka yau nazo nunamai kaina.” Fuskarta ta rufe da hannayenta tace “Dama yana min kallan sai a hankali yanzu na nunamai ba
nda kunya.” Tadan bubuga kafa a kasa tare da sake rufe fuskarta cikin jin haushin kanta.
Aminu dake tsaye inda ta barshi duk yana kallan abinda take a daki, saboda a bude tabar kofar, kuma yana tsaye daga falan ta inda zai iya hango cikin dakin.
“Me ku
ma takeyi hakan?” Tambayar datazo mai kenan, Ibty ta bude ido cikin kunyar kanta kawai suka sake hada ido, sam ta manta bata kule dakin ba, shikenan itakam yau ta mutu, wannan abin kunyar har ina?
Sandarewa tai a zaune ta kasa ko motsi shikam komawa yai
ya zauna akan kujera tare da girgiza kai, wato yarinyarnan dasu Islam da alama banbancinsu kadan ne, waya ya dauko yana danawa yana jiran su kawo musu abinci.
*********
An fito da kadan daga cikin kayan da aka riga aka siya na kayan dakin Ibtisam, n
an wasu daga ciki suka taho dan fara shirin gida, su Umma kuma suka tafi kasuwa dan siyo ragowar, haryanzu Umma bata sauko akan abinda Ibty tai ba sai dai