Showing 120001 words to 123000 words out of 128353 words

Chapter 41 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

16

ya washe baki kamar gaske yace “Amarya.”

Murmushin jin dadi tai ta jawo keken tana cewa “Dazu su Ibtisam sukazo

sun dade anan.”

Ya waske yace “Haba dai? Ba raban zamu gaisa.”

Jin haka yasa Bilkisu jin wani dadi lalai Ya Umar ya canza.

Abinci ta kawomai ya shiga daki ya fito ya zauna, yau kuma me muka samu?

Ya tambaya yana lankwashe kafa, bude kular yai, fried ri

ce tai da soyayyen naman kaza, dadi ya kamashi, tabbas ko saboda wannan dole zai lalaba nakashashiyarnan, gashi daga gidansu ake kawo kayan abinci ba ruwanshi dayin cefene sai dai yaci ya koshi, wani sa’in ma daga gidansu akeyin abincin.

Nan fa ya cika ka

tan plate ya juye duka naman, ya hau ci.

Wannan abin ne haryanzu bai mata dadi yanda in yazo baya tambayarta ko taci ko bataci ba kawai juye naka yake ya cinye. Sai dai gani take zai daina daga baya.

Sai daya cinye tas sannan ya nufi daki ita kuma ta gya

ra gun, sallar isha’i yai dan yanda ya koshi ko masallaci bayajin zai iya zuwa, danewa kan gadan yai ya bubude kafa yana tuno yanda yaga su Ibty sun wani rike hannu.

Kwafa yai ya runtse ido jin alamun hannu yai akan nashi hannun, ya dauka mafarki yake, ya

danyi murmushi tare da rike hannun, lalai yanasan Ibty wato ma mafarkinta yake shima ya rike hannun da akamai gori dazu.

Hannu ya jawo yadan sumbata yadan bude idanunsa cikin sha’awa.

Idanunsa ne suka sauka akan Bilkisu tana murmushin kunya.

Wani abu ne

ya tsaya mai a rai, ya daure yadan saketa a hankali yace “Banasan takura miki ne tunda ba lafiya gareki ba.”

Matsowa tai ta riko hannunsa tace “Yaya dan Allah ka daina fadar haka, matsalar kafar nan bawai ta hanani rayuwa bane, taya zanki baka hakkinka b

ayan zan iya?”

Yanda yake rike da sha’awar Ibth gaskiya dole ya huceta akan yarinyarnan.

Nan fa ya rikota babu soyayya babu wani lalabawa ya biya bukatarsa, itakam tasha kuka sai dai gani take haka akeyi tunda dai ba sanin kan abin tai ba.

Kasa ko zama

tai gashi shi babu alamar yana da niyyar taimaka mata, ya wuce dakinta wai ya barta ta shirya shi bari yadan kwanta, nan fa ya baje ya shari baccinsa hankali a kwance, lalai yau ya rage abinda ke ransa.

Itakam ta kasa tashi duk yanda taso hakanan ta kwana

, da safe ma tayi tayi ta mike ta kasa wayarta ta dauko ta saka a gaba tana tunanin wanda zata kira, duk wanda ta kira ta tabbatar zaisan sirrinsu, haka tai ta jan jiki tana kwalla harta wuce toilet, dakyar tadan gasa jikinta taba rike da bango ta dawo dak

i.

Haka taja kekenta ta leka dakinta, yana ta sharar baccinsa, jitai hawaye sun zubo mata, anya wannan auren zai yiwu kuwa? Abu babu tausayi sam? Kusa dashi taje, dan tabashi tai tana kwalla.

Cikin zafin rai ya bude ido zaiyi masifa sai kuma ya wayance,

“Amarya ya akai?”

Ta goge kwallarta tace “Ya Umar jiya bakasan a yanayin dana kwana ba?”

“Yanayi? Ohhhh ai nasan zakiji daban tunda abinmu na farko, badai yanzun ma so kike a kara ba?”

Sai yai dariya yace “Ba laifi abinka da sabun shiga daga ni har ke.”

Fuskarta a hade take sosai dan bata taba tunanin abinda zaice mata kenan ba, lalai wannan na nuna rashin so da yake mata.

Hawayenta ta goge, mamaki ne ya kamashi badai yayi laifi ba? Karfa su koreshi dan Kawunsa yace “Inhar Abba ya koroshi tofa ya nemi

wani gidan” banda wahalar dayasha zuwan dayai, Goggo ta dinga dannamai tuwo ba ruwanta da abinda yake so.

Da sauri ya riko kafadarta cikin sanyin murya yace “Wani abin na miki?”

Ta girgiza kai kawai tana neman fita, sake rikowa yai cikin sauri yadan run

gumeta yace “Amarya kiyi hakuri kinga ni sabin shiga ne ba komai nake ganewa ba, in banyi daidai ba ki dinga hakuri dani.”

Tausayinsa ne ya kamata ta girgiza kai cikin jin haushin kanta, ai ta tabbatar baisan ya abin yake ba shiyasa inba haka ba mezaisa y

a barta.

Cikin sanyi tace “Kayi hakuri Ya Umar bansan me ya sameni bane.”

Murmushi yai yace “Nima kiyi hakuri kinji.”

Ta daga kai cikin jin dadi……..

(

🤧

Bilkisu)

*******

Su Islam na islamiyar Tahfiz saboda yau asabar ta wuce kitchen tana hada musu

abincin rana.

Aminu ne ya shigo kitchen din yana kallan kitchen din kamar mai neman abu, cocumber din da take yankawa na salad ta ajiye ta kalleshi, shima kallanta yake hannunsa a baya yace “Naji ance mata suna so a dinga dubasu in suna aiki ne.”

Murmus

hi tai tace “Bawai a duba muba a tayamu muke so.”

Ido yadan ware yace “Me?”

Ta juye cocumber din ta dauko lettuce tace “Ehen.”

Ya koma jikin kofa yace “Shikenan sai mu cigaba da zaman mu basai mun leko mun duba ku ba.”

Tadan turo baki tace “Na yafe tay

in ko lekowar a dingayi.”

Takowa yai yazo ta bayanta yadansa hannu ya zagayo dashi ta cikinta ya kansa akan wuyanta wani abu ne yadan ratsata tadan lumshe ido kadan, cikin dan rada yace “Haka kawai an sani karatu bayan na gama skul.”

Karatu? Ta tambayesh

i cikin mamaki.

Yadan gyara kansa yace “Eh ni kaina bansan ya akai na dage da karatu haka ba.”

Juyowa tai tana mai kallan mamaki, ya dan rungumeta kadan yace “Bakyajin kunya in babban namiji kamar ni yana abu kamar yaro?”

Ido tadan jujuya tace “A’a!”

Y

a saketa yana murmushi kadan kadan, tadan riko hannunsa tace “Ni banga yaushe kai abu kamar yaro ba.”

“Kalleni fa a kitchen? Gani inata nemab janki a jikina.”

Wasa da hannunta ta fara cikin kunya tace “Ni hakan ai dadi yakemin.”

Ya dan sauke ajiyar zuci

ya yace “Ya zanyi? Tunda dai inaso in dauke hankalinki akan kowa sai ni? Gashi ina tsoron kar kiga da yaro kika aura da yafi kula dake?”

Duk yanda taso kartai dariya kasawa tai, ganin yanda take dariya yasa yace “especially wannan kidahumin saurayin naki.

”

Ya juya kamar zai fita daga kitchen din, da gudu ta taho ta tsaya jikin kofar tana dariya haryanzu.

Fuskarsa cike da mamaki yace “Wai wannan ma abin dariya ne?”

Ta girgiza kai tana hadiye dariyarta tace “Farin ciki ne ya sani dariyar ba komai ba.”

Ka

llo mai dauke da tambaya ya mata, tace “Wannan alama ce ta kana sona.”

Ya tako ya dan rike kuncinta yace “Ke sai yanzu kika sani?”

Tana murmushin jin dadi tace “Tunda kake karatu akan yanda zaka kula dani kenan kafi sona akan……”

Sai kuma tai shiru, hann

u yasa a aljihu yace “sai ma kin hada?”

Mamakin kalamansa ne ya kamata ta kalleshi cikin wani yanayi, mai kalamansa yake nufi?

Tana tunani taji yace “I can’t remember yanda naso ta sai dai yanda nakeji yanzu abu ne daban taba ji ba a rayuwata, hankalinki

ya kwanta?”

Hannu tasa da sauri ta rufe fuskarta, sumbatar hannunta yai ya fito daga kitchen din yana shafar fuskarsa.

Lalai Aminu lamarinka ya fara karfi, yaushe ka zama haka? Ya sake shafar sajensa lalai anyi girman kwabo. So ba ruwansa da girma.

Ya

fada a fili yana murmushi.

Itakam gaba daya aiki take tana murmushi kamar wata wawiya, hannu tasa bayan ta gama miya tanaso ta dandana taji ko komai yaji, tana kaiwa bakinta taji tana neman yin amai, dan kirjinta ta bubuga lalai tsabar yanayin da ta shi

ga ne har taji batasan kamshi da dandanon abincin? Tabbas yau ita kadai tasan dadin da takeji saboda kalamansa

Ayusher

🏌

️

‍♂

️

[5/12, 10:10 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝

e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye TA*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*mg's skincare*

Shin Ina matan suke

🗣

️

🗣

️

🗣

️

maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi

😃🤩

Hakika tabbas

duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaranjiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg's orga

nic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum

👌

hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg's b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasaur

an mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar

❣

️

Shin kinafama da

Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?

Shin f

atanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki

😫

Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi'iznillah sister's duk Wanda yayi using mg's sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear

Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy

🤗

ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind

Bridal kit:18k

Beauty kit:11k

Stu

dent package:7k

Herbal whitening soap:3k

Chat

08062991549

07046881166

07067210195

Call 08064532391

Facebook: mg's skincare

Instagram:glow_with_mgs

Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg's babushi akasuwa

🤝

Do you guys wan

na achieve that milky skin that turns head wherever you go

🤩

Then @mgs skincare gat you covered

💯

Now is time to glow

😍

Pamper ur skin

🦵

Shine like bride

👰🏻

‍♀

Glow

🧖

‍♀

️

💯

tested nd trusted

🤝

Guarantee

*49*

Bayan ta kammala duk abinda ya

kamata tayi a kitchen, taje ta shirya table sannan ta nufi daki. Wani irin yanayi takejin kanta a cike wanda tasan na farin cikin Aminu ya fada tarkon santa ne. Sakarwa jikinta shower tayi tana sake rintsa ido sakamakon dadi da takeji. Sabulu ta janyo ta

fara gogawa a jikinta, kamshinsa ya sake sanyata cikin nutsuwa samun kanta da shinshinashi tai, tai ta wanke jikinta tana sake lumshe ido hakan yasa ta dade bata fito ba.

Daure da towel ta fito tana maida gashinta da yake a jike baya, sam bata kula da ka

n gado ba, idanunta ne suka sauka akan gadanta.

Aminu ta gani a zaune bakin gado yana ta danna waya, ita kuma tana tsaye sai bude hanci take tana shinshino kamshin dakin, kafin ta sake daga kafa taji wani irin amai yana shirin fitowa, da gudu ta koma band

akin, da kyar takai kanta saboda neman kwace mata dayai.

Aminu na zaune yaji kakarin amai, shi da yana zaune irin ya basar din nan yana san yaga me zatai? Jin ta a bandaki yasa ya dan sauke ajiyar zuciya badai kunyarshi take ba? Da sauri ya mike tsaye han

kali a tashe Aminu ya mike yabita bandaki yana tambayar lafiya? Gabaki daya sai da ibty ta amayar da dan abincin cikinta dataci da safe, tsugunowa yai ya riko kafadunta yana mata sannu sannan a hankali ya shiga dan bubuga bayanta.

"Baki da lafiya ne?"

Mi

kewa tai bayan ta gama ta kuskure bakinta sannan ta kalleshi idanunta yayi ja saboda wahalar datasha.

"Wallahi ban sani ba, kawai naji bana san kamshin dakin." Aminu ya zaro ido.

"Subahanallahi! Haka kawai?”

Ta daga kai adan galabaice ta kasa cewa komai

, ya taimaka mata ta sake wanke baki yasa hannu ya wanke mata fuskarta dakanshi, sannan ya kamota zai maida ita daki tace.

"Habiby wait please." Aminu ya tsaya, gani yai ta koma bandakin ta dakko sabulu tana shinshinawa.

"Menene hakan?"

"Ƙamshin nake so

, Allah ji nake kamar na gutsira naci." Zaro ido ya kuma yi.

"Sabulun zakici?" Ba musu tace.

"Eh." Kwacewa yai ya mayar dashi inda yake sannan ya sake fito da ita. Bakin gado ya ajiyeta ya nufi wardrobe dinta. Yana neman kayan da zai dakko mata yaji ta k

uma yinkurin aman, ta ruga bandaki yabi bayanta cike da tashin hankali.

"Bazai yiwu ba gaskiya, asibiti zamuje yanzu." Ya fada yana sake rike ta.

"Habiby dazu fa lafiyata kalau ciwo ko awa biyu baiyi ba yana neman illatani? Nikam inaji mutuwa zan..." Da

sauri Aminu ya toshe mata baki da bakinsa, jikinsa har tsuma yake saboda karta furta a bakin mala'iku.

Ya dago fuska a dan hade yace “Banasan irin wannan furucin, kibar kaddara tayi aikinta, ki dena gaya min irin wannan kalmar saboda zuciya ta zata gaza j

urewa. Murmushi tadanyi ganin yanda yai, ya dagota yace “Cuta ba mutuwa bace, zaki warke Insha Allahu. Muna nan tare harsai kin haifa mana baby mun aurar dasu tare da Ilham."

IBTISAM ta shiga raba idanuwa, tunani ya fara zagaye kwakwalwarta kalamansa suka

sanyata cikin hasashe, yau sati uku kenan tana jiran period dinta, sam bata damu ba saboda yanda suke ta kokarin nunawa junansu kulawa itada Aminu, akoda yaushe kowa kokarin faranta ran dan uwansa yakeyi shiyasa ma sam bata tsayawa yin tunanin kananan abu

irin wannan.

Kan gado ya kwantar da ita ya mike dan komawa ya dauko mata kaya yaji ta riko hannun rigarsa. Aminu ya durkusa shi kansa jiyayi yana mata biyayya ba tare da yasan hakan tana faruwa ba.

"Habiby mekake cewa ne?" Ta tambaya tana kallan cikin i

danunsa.

Yadanyi shiru alamar nazari kafin yace “Ohh nufina nai ki samarwa su Islam baby." Ibtisam ta ritsa ido.

"Aa dan koma baya ka fadi abinda kace." Ya sake gyara zama yana rike da hannunta yace.

"Zancen baby da aurar dasu danai?” Da sauri ta sake r

ike rigarsa hakan yasa ya kalleta sannan ya kalli hannun rigarsa.

"Habiby I think……” sai kuma tadanyi ajiyar zuciya tace “Shine ma saboda wasu da irin wannan yanayin yake farawa. Kuma nima…..”

Katseta yai alamar tambaya yace “You think me?”

Tadan shagwa

be fuska tare da turo baku kamar kai shirin kuka tace “Shi dai.”

Yace “Shi me? Badai aljanu ba?”

Haushi yadan kamata kadan tai raurau da ido cikin dan bacin rai tace “Wani aljanu kuma? Ciki fa na……”

Yanda ya kalleta ne yasa ta juya baya da sauri tare da

sa kanta cikin pillow.

Shiru yai yana nazarin kalamanta har ta fara tunanin wani abin, sai kuma taji ya rungumeta ya kwanta sosai a bayanta ya jawota jikinsa sosai yana sumbatar duk inda ya samu, da yake towel ne a jikinta ya warwareshi tare da matseta c

ikin kirjinsa yana cewa.

"Allah yasa, Allahumma amin Habibty zata haifa min baby."

Hannu tasa tare da rungume shi itama, sai dai takan rintsa ido sakamakon tashin zuciya da yake kuma addabarta. Cikin murya mai tsananin sanyi tace.

"Dan Allah Habiby ka

dakko min sabulun, ji nake kamar zan mutu idan banjishi kusa dani ba."

Aminu ya dago ya kalleta, ta bashi tausayi sosai, ya tashi ya dakko mata ta karba da sauri takai kusa da hancin tare da jan numfashi da karfi. Mikewa tsaye yai yana cewa.

"Wannan Baby

din da alama mai sabu mukai? To ko mu binciko ko company din sabulun sunyi turarenshi?”

Bata iya kulashi ba ita kadai tasan ya takeji dan haka Kota fada ba ganewa za'a yi ba. Ya taimaka mata tasa kaya ya nemo hijab ya bata sannan shima yaje ya shiryo suk

a tafi asibiti.

Ana gwadata ya tabbata ciki gareta, gyaran murya yai irinta manya yana danne abinda ke ransa ya mikawa doctor din hannu suka sake musabaha yana mai congratulation, Murmushi yai yace “Mu zamu koma.”

Doctor din cikin rada yace “To ko na ba

ku guri ne kafin ku karasa mota?”

Hannu yasa a aljihu ya dan daure fuska yace “Kaifa dadina dakai neman magana, ce maka akai ni yaro ne wanda zai nuna zumudinsa a fili?

Ya dan jinjina kai yace “Zancen yarinta da rashinsa ai babu tunda dai ga baby nan.”

Gyaran murya yai yana mai wani kallo, doctor ya guntse dariyarsa ya kalli Ibtisam yace “bari na amso abu.” Bai jira mai zata ce ba ya fita.

Yana fita Aminu ya dagota ya rungumeta a jikinsa kenan dr ya bude kofa yana cewa “Bari na dau waya…..”

Da sauri Am

inu yadan saketa yana sake yin gyaran murya itama ta koma ta zauna tana dan kallan gefe da gefe.

Komawa dr din yai ya rufe yana cewa “A’a ku cigaba na dau wayar daga baya.l

kunya duk tabi ta kamata har ta kasa bari su hada ido dashi.

Ai ba shiri ya kal

leta yace “Tashi mu bar nan.”

Ta kalleshi tace “Kaima Yaya wayasaka a asibitu?”

Ya dan kalli kofa yace “Zan gamu dashi sannan dadinta mamata na rungume ko?”

Baki tadan bude ta daga kai tana dariya kasa-kasa.

Suna fita daga cikin asibitin suna hanyar gi

da tai bacci hakan yasa batasan meke faruwa ba har suka isa gida. Koda ya gama parking bata farka ba shi kuma be tashe ta ba sai kujera da yaja baya ya jingina shima ya shiga danna waya.

Shigowar su Islam daga islamiya hayaniyarsu tasa ta tashi, kallan ju

na sukai ita da Aminu ya sakar mata murmushi tare da cewa.

"Ya zanyi tunda zuciyata ta kasa tashinki? Habibty kin shammaceni wallahi, gabaki daya kin hanani sukuni."

"Ni kuma mena sakeyi?" Tai maganar cike da shagwaba. Ya kai bakinsa ya sumbaci gefen kum

atunta.

“Bansan me ke damuna ba akanki, bana iya boye yanayin da nakeji……."

Jin ana kwankwasa gilashin motar ne yasa shi saurin budewa, ya kalli yaran tare da mika musu hannuwanshi suka kama.

"Andawo?"

"Eh." Suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login