Showing 39001 words to 42000 words out of 128353 words

Chapter 14 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

48

bake ta tare gado da suna hotel, to me take anan?”

Tsugunawa yai yasa yadan tabata gadan, hannun tadan ja tana neman ta dan rike hannun dan ta mike zaune, dayake a tsugune yake tana ja ta sa ya runkufo kanta, wayarsa ce ta haska saman dakin, numfashinta

ne ya tsaya cak nadan wucin gadi, ta kura mai ido. Tsayawa yai yana kallanta kafin yace “Yaushe zaki sakeni na tashi?”

“Kaine fa ka dane ni.”

Hannunta ya kalla data rikeshi yace “ Ko?”

Ido ta zaro sannan ta sakeshi da sauri, bata jira ya tashi ba kawa

i ta miko taba san tashi saboda kunya, ji kake gum ta nake goshinsa, zafi ne ya ziyarci goshinsu a lokaci daya, tasa hannu da sauri tana sosa gun, tana neman yin ‘yar karamar kara yasa hannu da sauri ya toshe bakinta tare da nuna mata su Islam.

Itakam me

ke damunta?

Mikewa yai ya kalleta sannan ya zare hannunsa daga kan bakinta ya dan girgiza kai sannan ya fita daga dakin.

Kafafunta ta bubuga a kasa tare da sa kanta cikin cinyoyinta saboda jin haushin kanta datai.

Aminu kam yana fita yasa hannu a s

aman goshinsa tare dayin dan runtse ido dan gaskiya yaji zafi sosai, bayasan ta rainashi ne shiyasa ya nuna kamar ma baiji zafin abin ba. Haka ya wuce bangarensa yana mulmula gun a ransa yace “Anya bama da saninta ta makeni ba? Kila tana san rama abinda na

mata jiya akan su Islam?”

*****

Ibty kam ta dade tana murza gun dan ta bugu sosai, kafin ta mike ta fito daga dakin, alwala tai bayan tayi sallah ta dade tana addu’a wacce rabinta akan Yayarta Bilkisu takeyi, kafin ta mike ta koma dakin su Islam.



Tana kwance tana dadana wayarta bacci yadan sake daukanta, kamar a mafarki cikin bacci taji muryar Islam tace “Ilham me takeyi anan?”

“Nima bansani ba, badai ta fara abin bako?”

Islam cikin rashin jin dadi tace “Ina santa lokacin tana kawar Aunty amma y

anzu bana santa tana matar Dady.”

“Nima haka.” Abinda taji Ilham tace kenan, bata bude idanunta ba tace “ Islam? Ilham? Da kawar da kake tare da ita shekara sama da biyar da wanda kansani a kwana uku wane yafi matsayi?”

Kallan juna sukai Islam tace “shek

ara biyar?”

Ibty ta bude ido ta zauna tana kallansu tace, “kwana dari uku da sittinda biyar ne a shekara kunsan yawansu?”

Ilham tace “Dayawa kenan”

Ibty tace, “To haka sau biyar kunga yafi kwana dubu ko?”

Suka daga kai a tare, tace “Dady dinku dana ke

tare dashi na…”tadan bude yatsun hannunta alamar uku “Na kwana uku, wane yafi yawa?”

Cikin sauri sukace “Na Kawar Aunty.”

Ta jinjina kai tana musu tafi tace “to kungani? Ni yanzu kawar Aunty ce ko matar Dady?”

Shiru sukai suna tunani, Ilham tace “Amma

duk da haka ke matar Dady ce ko?”

Ta daga kai alamar eh kafin tace “Amma nafi dadewa a kawar Aunty Ainah, sannan a kawar Aunty na sanku ba a gidan Dady ba ko?”

Yanzun ma alamar tunani sukai kafin su daga kai alamar eh, ta dan daga hannu tace “Yanzu muy

i musabaha a matsayinmu na kawayen Aunty Ainah ko?”

Nan Islam ta sauko da sauri itama Ilham ta sauko sukai musabaha, dadi ne ya kamata nan suka mike ta musu wanka anayi Islam nata bata labarin islamiyarsu, kaya iri daya suka dauko ta saka musu sannan suk

a fito falo wani irin dadi takeji dan jiya sam bataji dadin yanda suka juya mata baya ba.

Falo suka zauna tace “Kuje ku gaida Dady bari na hado muku tea kusha.”

Nan sukai bangaren Dady da sauri suna wasan guje guje. Wanka tai itama tasaka atamfa riga da

skirt, ita dama ba wani jiki ba ga kayan sun zauna mata, mayafi ta yafa babba sannan ta fito ta shiga Kitchen “Dandai tarewarta anyita ne ba shiri amma ai da ya kamata ta taho da gara, sai yanzu ta fahimci hakan nada amfani, ruwan zafi ta dora kamar daga

sama taji ana kwankwasa kofa.

Zuciyarta daya tai tunanin ko mai gadi ne? Kila Ya Aminu ne ya aikeshi.

Sai datazo daf da kofar sannan tace “Wanene?”

Sam bata zata ba sai jitai ance “Nice.”

Gabanta ne yai wani irin faduwa, a hankali ta bude kofar, tar

e da kallanta.

Hajiya ta saki murmushi tare da mika mata tire din hannunta dake dauke da kuloli biyu da flask, dakyar tasa hannu ta amsa sannan ta gaisheta.

Hajiya tai murmushi tace “Amarya kin tashi lafiya?”

“Lafiya kalau.”

Murmushi ta sake tace “Nasa

n ana shan amarci ba damar tashi ayi abinci, sannan na saba yin girki dasu shiyasa. Ke dai ki huta abinki zan dinga yi muku girki ina aikowa dashi.”

Tsananin mamakin kalamanta ne yasa Ibty ta kasa ko furta kalma daya dan bata taba tunanin jin wannan magan

ar ba.

Hajiya ta dan kalli ciki tace “Su Islam nagun Aminu ne?”

Bakinta nadan rawa tace “Eh.” Bata sake zata ba taji hannunta a saman kanta, “Allah ya miki albarka ya baku zaman lafiya.”

Sam ta kasa cewa Ameen saboda yanda taji zuciyarta na bugawa da s

auri da sauri, juyawa Hajiya tai ta bi bayanta da kallo.

Dakyar ta iya shiga ta ajiye abincin a kitchen kawai ta zubawa kwanukan kallo ko budesu ta kasa yi, kalamanta ne suke sake dawo mata, itakam gaba daya ta rasa dalili tsoron matar ma takeyi, haka ta

kwashi tiren ta kai bangaren Aminu.

Yana zaune yana aiki a laptop dinsa su kuma su Islam suna kallan cartoon a tv. Ajiyewa tai akan dinning dinsa dake gefen falan sannan ta bude flask din.

Soyayyen dankali ne da kwai sai dayan kular farfesun kaza, flask

din kuma kunu ne a ciki.

Idanunta ne suka danyi raurau, kafin ta shigo cikin falan.

Gaisheda Aminu tai ya dago ya kalleta, goshinta ya kallan wanda haryanzu da alamar buguwar dazu, itama nashi goshin ta kalla wanda haryanzu shima bai baje ba.

Amsawa

yai sannan ya maida kansa yana cigaba da abinda yake, kallansu Islam tai tace “Ilham a kashe kallan azo aci abinci.”

Ganin yanda suka taho da murna yasa ya dago ya kallesu, kamar jiya ba sune suka nuna basasan zuwa gunta ba. Tadan bi bayansu tana cewa “Wa

nda ke san yasha tea ya fadamin.”

Hannu Islam ta daga tace “Kawar Aunty ni, Ilham da Dady kullum sai shan kunu.”

Murmushi tai sannan suka karasa, sai da suka zauna ta sa musu a plate sannan ta fara hadawa Islam tea, yunwar dayaji tadan motsoshi ne yasa

yadan yi gyaran murya tare da ajiye computer dinsa, “Anya tace yazo ma yaci abinci kuwa? Kamar gaisuwa kawai sukai.” Tunanin me yace me kuma tace bayan sun gaisa yadanyi sai dai gani yai ya kasa tunawa gashi yunwa yakeji.

Mikewa yai yasa hannu a aljihu y

a nufi dinning din, zama yai sannan yadanyi gyaran murya yace “Kunu zansha amma karkisamin sugar.”

Kallansa tai kafin tace “to” haushin abinda Hajiya ta mata ne yasa kawai taji batasan yimai magana, yanzu dayaga abinci bai kamata ya mata bayani ba? To ya

ce me? Ibty karfa idanki ya rufe saboda jin haushin wata.

Abinda zuciyarta ta raya mata kenan, nan sukaci abinci itakam tea kawai ta hada ta dau bread ta tafi falanta taci dan bataji zata iya cin abincin.

Bayan ta gama ta dawo falo ta kwashe kwanuka, ka

llansa tai tace “Ya Aminu ko zamuje mu siyo abubuwan gida? Na abinci?”

Ya mike yace “Eh gwara muje mu dawo ma da wuri dan inasan fita.”

Hamdala tai a ranta tunda dai ya amince, haka kawai ba haukar da zata sakata ta amince da uwar matarsa ta dinga kawo

musu abinci, duk rashin wayanta bai kai nan ba.

Su Islam suka hau tsale suka dauko hijab dinsu suka saka, a tare suka fito hannunta rike da hannunsu.

Gaban Hajiya ne ya fadi dan dama tun bayan ta dawo take leke ta katangar da sauran kadan a karasata, g

anin ta gaji yasa ta koma falo, yanzu kam muryarsu Islam kadai dataji yasa ta fito da sauri.

Ranta yakai kololuwa gun tashi ganin hannunta a cikin nasu Islam suna tafe suna dariya, huci ta fara tana kallan muzurai, ko ba komai ai ta fara aikin ta a cikin

abinci, sannan jiya tasa mata laya a kasan katifa, kwafa tai ta koma ciki ranta a matukar bace, ta zauna a falo ta daura kafa daya kan daya tana girgizawa. Bata taba tunanin Aminu zai fara daukarta da yaransa su fita ba daga aure.

********

Baya suk

a shiga ta shiga gaba, Aminu na kokarin shiga sai ga mai gadi ya taho da sauri, “Alhaji! Hajiya tayi bako.”

Bako? Yai tambayar cikin mamaki, ya dan sake sukunyo na girmamawa yace “Yayanta ne jiya da shekaran jiya dashi aka wuni ana aiki kayan daki, yanzu

yazo wai yazo kawo mata abu.”

Ba tare da ya kawo komai ba yace “Ya shigo mana.”

Nan ya juya ya tafi kiransa, Umar kam wanda ya samu leda ya cikota da littatafan dayasa Bilkisu ta sa Iman ta dauko na Ibty, sannan ya rubuta mata waskila akan lalai lalai y

au karfw goma na dare ta san yanda tai ta fito waje zaiso su wuce Sokoto, karta damu ya tattaro kudin da zasuyi tafiya.

Shigowa yai, kallan gate tai ganin Aminu shima yana jiran ganin shigowarsa.

Wata muguwar faduwar gaba ce ta fadi mata, da sauri ta fa

ra addu’a duk jitai ta rikice.

Idanunta ta kauda daga kallansa ta juya tana kallansu Islam.

Batai zata ba sai ji tai an kwankwasa glass din window dinta.

Inda Aminu yake ta kalla cikin firgice da tsoro, hannunta na rawa ta zuge glass din.

Umar ya zuba

mata ido cikin tsananin kishi, ya dauka yanda ya birkice saboda rashinta itama tana nan tana rashinsa? Lalai yau ya tabbatar yarinyarnan munafuka ce, ba sanshi take ba. Sai dai wlh ko tana sansa ko bata sansa sai ta zauna zaman aure na har karshen rayuwa d

ashi.

Cikin rawar murya yaji tace “Ya Umar?”

Idanunsa yai jaa sosai ta danyi yake, tana kallan Aminu daya zagayo ya mikawa Umar hannu, kallan hannunsa Umar yai sannan ya kalli Ibty, bai mika mai hannu sunyi musabaha ba kawai yadan ce “Ina kwanan mu?”

Am

inu ya maida hannunsa aljihu yace “ Ashe kaine, ko ba mijin yayarta bane?”

Wani abu ne ya tokare mai makoshi ya zabgawa Ibty wani kallo sannan ya kalli Aminu da jajayen idanunsa.

Aminu ya kalli Ibty yace “ki fito ku gaisa.”

Daga zaune tace “Ina kwana?”

Umar mamaki ya kara kamashi wato fitowarce bazatai ba?”

Aminu ganin yanda Umar ke kallansa yasa ya shiga mota ya zauna, Umar idanunsa nakan Ibty ya a zuba mata wani mugun kallo, itakam ta kasa sake kallansa sai rawa da jikinta keyi daga ciki.

Aminu na

shigowa ta samu kanta da rike hannunsa da sauri.

Mamaki ne ya kamashi ya kalleta, kallansa tai tare da yin yake. Yanda jikinta ke dan rawa ya kalla, tabbas akwai abinda ke faruwa.

Umar kam ji yake kamar wanda ake hurashi a cikin wuta, zuro ledar yai b

aice komai ba ya zabgawa yaran Aminu harara sannan ya juya ya fita.

Islam ta kalli Ilham tace “Wannan sai yai kama da irin mugayen nan ko?”

Ilham tace “Nima tsoro ya bani.”

Haryanzu Ibty bata sake hannun Aminu ba, kallanta kawai yake yanda haryanzu jiki

nta bai dawo daidai ba.

“Mu wuce?” Abinda ya tambayeta kenan, ta daga kai alamar eh.

Ya kalleta sannan ya kalli hannunsa, da sauri ta sakeshi sannan ta zauna, nan ya tada mota suka fito.

Daga waje sukaga Umar, Aminu yadan tsaya ganin yana tafiya da kaf

a yace “Ko zamu rage ma hanya?”

Ai Ibty gaba daya ta sake rikicewa, Umar ya mai wani kallan tsana yace “Da sayyadata.”

Aminu yasa hannu a aljihu ya dauko kudi yana neman mikamai, da sauri Ibty ta rike hannunsa dan tafi kowa sanin Umar ya tsani a rainashi

, balle akanta. Yanzu saboda kudin nan batasan me zai aikata ba.

Maidawa Aminu yai sannan yace “To ka gaida su Umma.”

Umar kam hannun Aminu data sake rikewa kawai yake kallo lalai zai iya yin kisa da akwai wuka a jikinsa, tab.

Gaba sukai tadan juyo ta

kalleshi ta madubin mota, Aminu kam mamakin yanda haryanzu tai shiru ta takure a gefe yake, ance gida daya suka taso, meyasa take shakkarsa haka?

Umar kasa motsi yai ya tsaya kawai yana kallan motarsu harta kule, lalai duk wanda yake da hannu a cikin abin

nan ya shirya fuskantar bala’i da masifa, ai ko bayan ya dauke Ibty wallahi sai ya dau fansar rike hannun Aminu datai.

{Nikam Ayusher kasa ko magana nai, anya mutumin nan nasa man kai?}

🏌🏻

‍♀

️

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Betwee

n)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ya samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

A

isha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

17

🤸🏻

‍♀

️

Har suka isa Jifatu muryar Islam da Ilham ce kawai ke tashi, sam ko magana ta kasayi, duk wannan abinda take yana lure da ita, tabbas akwai abinda ke

faruwa a gidansu. Baisan ko menene ba amma da alama shine dalilin dayasa mahaifinta ya kawota ba ranar da suka tsara ba.

Parking yai sannan taji muryar Islam tana cewa “Kawar Aunty mun iso.”

Firgigit tai tare da kallan gun, sannan ta kalli Aminu wanda

shima yake kallanta yana ganin zata juyo ya dauke kai tare da kallan gefe.

Fitowa tai sannan ta budewa su Ilham, nan suka fito ta rike hannunsu.

Kallan cikin motar tai bataga alamar yanada shirin fitowa ba. Dan sako kanta tai saitin glass din motar ta

ce “Ya Aminu muje?”

Ya kalleta sannan ya kalli shagon yace “Kece me siyayya ki shiga kafin ki gama daukan abinda kikeso zan shigo.”

Mamaki ne ya kamata tace “Yanzu ni kadai zan shiga ga yara ga siyayya?”

Kallansu Islam yai kamar zaiyi magana sai kuma

taga ya sake daurewa, ya gyara zaman farin glasses din dake fuskarsa sannan ya fito.

Da gusu Ilham ta kamo hannunsa sannan ta jashi kusa da inda su Islam suke. A tare suka shiga cikin shagon, kallansa tai tace “Ya Aminu cart din da zamu zuba kaya.”

Wa

ni kallo ya mata yace “Hannunki fa?”

Ta kalleshi ta nuna jakarta da hannun Islam datake rike dashi, aransa yace “Lalai yarinyarnan, wannan fa in na kyaleta da alama aiki ma sani zatai.”

Ya dago yace “Bazai iya ba intaga dama ta turo” kawai yaga bata gun

. Can yadan hangota harta fara daukan abu tana nunawa Islam suna dariya.

Wata kwafa yai sannan yaja cart din kai kace shine ya batamai rai. Takaici duk ya ishehi, banda ta rainashi ina zai dingabin mace zagagai zagagai tana siyan kaya shi kuma yana tura

mata kayan? Dazun nan ya gama tausayinta ashe zata wulakantashi. Yanzu in wani ya ganshi ai ta gama zubarmai da girma.

Ibty kam batasan ma yanayi ba, Ilham ta dawo kusa da ita suna tafe suna daukan kaya intaga abin zagin yayi yawa tace a’a.

Haka suka g

ama siyayyarsu ya biya sannan suka koma mota, a zuciye ya fizgi mota suka hau kan titi.

Wayartace ta fara kara, ta dauko tare da yin sallama cikin girmamawa tace “Ummy ina wuni?” Jin ta ambaci Ummy yasa yadan rage gudun tare dadan kasa kune yaji me zatac

e.

Ummy bayan sun gaisa tace “Ibtisam ina Aminu? Na kira wayarsa bansamu ba.”

Tadan kalleshi kadan tace “Gamu tare mun fita siyayya.” Kunya ce ta kama Aminu ji yake kamar ya fizge wayar, shikam yarinyarnan yau ta shirya kaskantar dashi.

Ji yai ta kar

amai wayarta a kunne, dan gyaran murya yai sannan ya gaida Ummy.

Cikin jin dadin da kanajin maganarta zaka gane tace “Aminu ko zaku biyo ta gida tunda kun fito?”

“Ummy inada aiki wlh”

Tace “In ka koma kayi, sannan ai ba dadewa zakuyi ba, dama naso zuwa

ganin gida ne amma tunda kun fito ku karaso dan Allah.”

To kawai yace ta kashe wayar cikin jin dadi, dan dama hankalinta ne sam yaki kwanciya tun jiya shiyasa ta yanke shawarar zuwa dan dole ta yiwa Ibtisam gargadi dan sakacinsu ne yaja musu gashinan mat

a tafi karfinsu.

******

Murna da tsale su Islam suka fara sai da ya kallesu sannan suka zauna, Ibty tai shiru tana kallan wayarta, so take taji muryar mahaifiyarta, da ‘yan uwanta amma ba dama, itakam wannan bala’i dame yai kama?

Gun parking na cikin

gidan ya tsaya, tunda suka shigo ta hango Ainah a tsaye a harabar gun tana rike da kugu tana girgiza ta turo dankwali gaba irin ture kaga tsiya din nan, dariya ce ta kusa kwacewa Ibty.

Aminu na fitowa ya kalli Ainah, ai tana ganinshi ta ruga ciki a guje

, dakinta ta shige tace “Sam na manta dashi ina jiran masifa.”

Ibty tana kallan sanda ta ruga ciki, dariya ce tadan sake zuwa, ido suka hada da Aminu tadan maze, kai ya girgiza sannan ya wuce ciki.

Islam ma a guje suka shiga ciki, itakam sai data kara

gyara zaman mayafinta ya rufe kanta sosai sannan ta fito.

Ainah tana leke ta kofa tana ganin Aminu ya wuce bangaren Ummy ta fito da sauri, Ibty na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login