Showing 57001 words to 60000 words out of 128353 words

Chapter 20 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

35



kansa yana jin haushin abinda yai, yanada zafi sai dai bai iya rufe mutum da fada haka ba, sannan wasu kalamai daya mata sun sa yaji haushin kansa.

Ibty kam ta dade tana kuka kafin ta mike, abincinsa ta dauka takai mai, tana kokarin fitowa ya fito daga d

aki sanye da doguwar riga, idanunsu ne suka hadu da juna, idanunta duk sun kumbura.

Kai yadan kawar da kansa sannan ya karaso, zama yai ta zubamai abinci sannan ta fito daga falan gaba daya jikinta ba karfi.

Haka yaci abincin gaba daya shima zuciyarsa b

a dadi, komawa yai ya zauna yadan kunna tv.

Ibty ta dawo ta fara daukan kwanuka, sai datazo na karshe sannan ta kalleshi, haka kawai taji wasu hawayen sun zubo mata.

*****

Gaba daya ba abinda ya sake hadasu harsu Islam sukai bacci, ji take kamar karta

kwana a dakinsa sai dai alkawari ta dauka ba yanda zatai.

Dakinsa ta nufa bayan tayi wanka tasa kayan bacci, idanunta haryanzu a kumbure suke, sallama kawai tai sannan ta wuce ta kwanta.

Dakin yayi shiru sai kara keyboard na laptop dinsa dake tashi, duk

yanda taso tai bacci ta kasa saboda kalaman Aminu dake dawo mata.

Juyowa tai saitinsa tana hawaye tace “Yaya a matsayinka na babba bai kamata ka fara bincika taba kafin ka dau hukunci akaina?”

Jikinsa ne yai sanyi, sai dai baisan me zai ce ba. Ta dan s

hare kwallarta tace “Bansan tsakaninku da Hajiya ba bankuma san shakuwarku ba sai dai a kalla nima a bani hakkina aji ta bakina, bansan laifin danai ba ka rufeni da fada.”

Kallanta yai yanzun ma baisan me zaice ba, juyawa tai kawai ta cigaba da share kwa

llarta.

Hannu yasa ya dauko tissue din dake gefensa ya dan taba bayanta, juyowa tai ta kalleshi. Nan ya mika mata tissue din yace “Kukan ya isa haka nan.”

Amsa tai ta dau biyu ta ajiye ragowar sannan ta share fuskarta.

Shiru tai can taji yace “Rainane

ya baci bansan ya akai ba na rufeki da fada ba tare da jin ta bakinki ba, sai dai inaso ki sani banasan zuwanki ya zama silar rugujewar farincikin gidan nan, bance sai kinyi komai daidai ba but banasan ki takurawa tsohuwar da batada kowa sai ni, wacce bata

da lafiya take neman mai kula da ita.”

Shiru Ibty tai lalai itakam taga ta kanta, har tana murna zamansu ya fara dadi sun fara fahimtar juna yanzu shine matar nan zata fara yi mata sharri.

Sunyi shiru jiki a sanyaye tace “Kayi hakuri”

Harta dauka baza

iyi magana ba sai taji yace “Kema.”

Haka ta kwana da bacin ran abinda matarnan ta aikata mata, gashi batasan yanda zatai ta huce takaicinta ba.

Ayusher

🏌🏻

‍♀

️

[2/19, 11:34 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s

̝

k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

*22*

Aminu sam baccin ranar baimai dadi ba, ya rasa yanda zaiyi ya amshi laifinsa, da asuba kam mikewa tai kawai ta fito daga dakin dan ko sallah ba’a dakin tai ba. Yana dawow

a daga masallaci ya dauka zai juyo karatunta yanda ya saba yaji shiru, dakin ya nufa bata ciki, hakan ya tabbatar mai bama anan tai sallah ba, nan ya zauna bakin gado tare da dan murza saman goshinsa, baisan meke damunsa ba, tabbas yasan bai kyauta mata ba

sai dai baisan ta yanda zai bata hakuri ba.

Bayan ta shirya yara ta kawo abinci, kallanta yai sanye take da riga da skirt na lace, ya mata kyau sosai “Ina kwana?” Abinda kawai tace kenan ta zauna suna magana dasu Islam, yanayinta ya kalla, haka yaci abi

ncin duk jikinsa a sanyaye, nan suka fito ta rakosu har mota sannan ta koma ciki. Da kallo yabita harta shiga ciki sannan yaja mota suka bar gidan.

Ibty kam gyaran gida ta gama ta zauna tai shiru a falo tana tunanin kalaman Aminu, tabbas an dade ba’a fad

a mata munanen kalamai irin haka ba, hawayenta ta share, sannan kalaman Ummy suka fara dawo mata, lalai inhar ta bar abin nan batasan nan gaba me matarnan zatace ma Aminu akanta ba, “matsoraciya!” Kalaman Aminu ne suka daki dodan kunnuwanta, kwanciya tai t

ana tunanin mafita, ganin damuwa da takaicin abin sunki barinta kawai ta mike ta nufi kitchen, kwanukan Hajiya ta kwaso ta zubar da abincin sannan ta wanke, awarar indomie datai da safe wanda yai ragowa ta zuba a daya daga cikin kular sannan ta dau leda ta

zuba kulolin a ciki ta dau wayarta ta kira Aminu.

Yana zaune yana duba wasu takardu yaga kiranta, cikin dan hanzari ya daga tare da yin gyaran murya, sallama tai yana amsawa tace “Zan shiga naba Hajiya hakuri akan abinda ya faru.”

Cikin sanyin jiki yac

e “Karki damu komai ya wuce ai.”

Kai tadan girgiza kamar yana ganinta tace “Yanda rankanya baci jiya ina ganin gwara na bata hakuri da kaina.”

To kawai yace dan baisan abinda zaice ba, tunanin abinda zaice ya fara kawai yaji an kashe wayar, lalai yarinya

rnan dan taga baiji dadin abinda yai ba shine take mai abinda taga dama?

Ibty kam hijab dinta ta zura kawai ta fito, duk da tsoro da fargaba dake damunta sai dai wannan karan bazata bari a maidata wawiya ba, Umar ya koya mata hankali, ita kadai tasan wah

alar datasha agunsa.

Dayake gate dinta ba rufewa take ba, turawa kawai tai ya bude, bakin kofar shiga ta tsaya ta dade tana addu’oi kafin ta kwankwasa kofa.

Hajiya tana zaune ta baje akan kujera tana kallan tashar arewa, gefe kuma ga cincin nan da fant

a ta kwalba, tana jin wani nishadi, yanzu ma tunanin abinda ya kamata tayiwa Amarya takeyi, murmushi tai ganin ta gama hada abinda zata mata wanda ta tabbatar Aminu sai ya kusa marinta.

Kwankwasa kofa taji, mikewa tai ta bude dan tayi tunanin almajirin d

atake aika ne, yanda ta zabura kadai ya tabbatarwa Ibty tayi mamakin ganinta.

Cikin dauriya tace “Amarya?”

Ibty ta gaisheta, nan fa suka fara kallan juna, Hajiya ta daure tace “Shigo mana.”

Sallama tai ta shiga ciki ta zauna a kasa, sannan ta sake gai

sheta.

Hajiya ta amsa tana dan yake ta amsa, Ibty ta miko mata ledar kwanuka tace “Dama kwanukanki na kawo miki, sai abin kwalama danai da safe.”

Wani kallo ta mata, aranta tace “Badai nima maganin ta samin ba?”

Ganin yanda take kallan Ibty yasa tai d

an kasa dakai tace “Kiyi hakuri bansan ranki ya baci ba, sannan jiya nidai Bala cemin yai dankalin daga gidan Ummy yake.”

Sam ta manta da wannan karyar datai, dariya tai tana washe baki tare da kokarin boye karyar datai tace “Kinsan Bala wani sa’in akwai

shiririta, cemai nai ya kaiwa su Islam kila can ya tafi yana tunanin shirme.”

Ibty tai murmushi tace “nima nayi tunanin haka, sannan farfesun mata da kika kawo abinda yasa bansha ba, banasan abubuwan mata daga aurena, a gida ma da aka bani bansha ba, am

ma tunda bakiji dadi ba kiyi hakuri.”

Hajiya tadan canza murya tace “Aminu dai sai a barshi, nifa sam bancemai naji haushi ba, sannan ni danake gidana ta ina zansan baki ci ba, muna hira ne fa zancen ya ratsa.”

Ibty kanta na kasa dan ta kula inta hada id

o da ita bata iya maida murtani yanda ya kamata, tace “Allah sarki, amma dai duk da haka nasan ke kika mai zancen dan shi baima san kin kawo abincin ba, kinga maganin mata dama bai kamata ya sani ba, sannan na jiya kuma da aka kai ance Ummy balle yasan dag

a nan ne”

Hajiya tadan yi dariya sosai tace “Kinsan kn girma ya kama mutum sai yai ta maganar shirme, ni banmasan ya akai muka fara maganar ba.”

Itama Ibty tai murmushi tace “Nayi tunanin haka dama dan nasan haka kawai bazaki hadamu fada dashi ba, tunda

dai ke a matsayin uwa muka daukeki.”

Hajiya rasa abin cewa tai wato lalai yarinyar nan ba kanwar lasa bace, lalai sai ta tashi tsaye ta ci kwal uban yarinyar nan.

Ibty ta mike tare sa yi mata sallama ta fito, da wata muguwar harara tabi Ibty, lalai wa

nnan tsinaniyar yarinyar wuyanta yayi kwari.

Kallan kwanon tai a fusace ta wuce kitchen ta zuba abincin a shara, tace “ta rasa abinda zata jefenk dashi ma sai awara? Da alama maganine a tsakiyar waken suyan.”

Ibty kam tana fita ta kama bango dan jitai

kafafunta na rawa, ajiyar zuciya tai sannan ta koma gida, ko ba komai ta rage takaicin dake ranta sannan inma da biyu take kawo mata abinci itama yanzu zata dinga kai mata sai taga me zai faru.

*******

Umar ne ya kalli wani dalibin da ya fito daga m

akarantar yace “kenan sai wani satin za’a fara registration?”

Saurayin yace “Eh gaskiya.”

Shiru yai sannan yai dan kwafa ya wuce gida ransa a matukar bace.

Takaici ne ya kamashi ganin Bilkisu a kwance akan kujera tana kokarin mikewa, wata muguwar tsana

da takaici ne ya rufeshi, babban burinsa bai wuce ya shigo gidan auransa yaga Ibty ta taho da gudu ta rungumeshi ba, yanzu wace banzar rayuwa yakeyi?

Bakinta na rawa tace “Yaya ka dawo? Sannu da dawowa.”

“Bandawo ba, tunda aljani kika gani bani ba, ni

wai dan Allah kwakwalwar dakikai gareki ko me? Wace irin ‘yar iskar tambayace wannan? Wai Ka dawo? Ban dawo ba ina waje.” Yaja tsaki sannan ya zauna akan kujera ya dau remote ya kuna music, jiki a sanyaye ta hau kan kujerarta, batada lafiya tun jiya take

fama, abinci ta daukomai ta ajiye a gabanshi.

Wani kallo ya watsa mata yace “dan Allah inkin ajiye ki matsa daga nan, sam banasan ganinki.”

A hankali taja kekenta ta wuce daki, ya kara zabga wani tsakin sannan ya lumshe idanunsa, fuskar Ibty yake hangow

a tana mai murmushi, hannunsa ya dunkule ya dan naushi kujera, wallahi sai Allah ya sakamai, kuma dole ne ya dawo da Ibty gunsa.

*******

Bayan yara sun tafi islamiya wajen karfe biyar da kwata Aminu ya dawo, hannunsa dauke da manyan ledoji na fruits,

yaba Bala karamar ledar yace yakai bangaren Hajiya sannan ya wuce ciki.

Tunda ya shiga yake juyo kamshin turare, lumshe ido yai dan tabbas yanasan kamshin nan, bangarenta ya nufa, bakowa a cikin falan, kitchen ya wuce ya ajiye ledar sannan yadan kalli da

kinta.

Kamar zai wuce sai kuma ya nufi dakin, sam a rayuwarsa bayasan shiga hakkin mutum shiyasa tun jiya abin ke damunsa.

Knocking yai, ba’a amsa ba hakan yasa yadan tura kofar dakin, Ibty ta gama wanka kenan saboda jinin al’ada daya zo mata dazu, dat

aji kwankwasawa yasa ta daura towel ta fito tana mamakin har lokacin tashinsu Islam yayi ne?

Fitowa tai sanye da towel din ta iya gwiwa, turus ta tsaya shima ya kalleta, haka kawai yau baisan dalili ba yaji wani abu yadan tsirgamai.

Ibty kamar zata koma

toilet din sai kuma ta dake tace “Sannu da dawowa.”

Gyaran murya yai sannan yace “Na shigo naji shiru ashe wanka kike.”

Kai ta daga kawai batace komai ba, juyawa yai yana tunanin da alama da saninta take mai wulakanci, tun jiya inya mata magana sainta

dinga amsamai kamar bataso, ya dauka ya bata hakuri? Ita tace kayi hakuri shima yace kema. Wannan bai isheta ba take nufi ko me? Shifa ya tsani a dinga neman juyashi.

Ibty kam kaya ta saka sannan ta danyi kwalliya sama sama, sai yanzu take fahimtar meyas

a mata suke zama ‘yan duniya a gidajensu, wato wasu mazan sai su dinga nuna kallo ma baka ishesu ba, bawai so take ya sadu da ita a dole ba amma a kalla mijinka ya nuna maka kaima macece.

Lalai ko saboda Hajiya dole ne ta shawo kan Aminu yasota, dan ta t

abbatar da yana santa bazai rufeta da fada jiya ba tare da bincike ba.

🏌🏻

‍♀

️

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

2083371244

Zenith Bank

Aisha M.Salis

+447894142004

Ko kati a 07043079282

*Shaidar biya ta wannan* 07065283730

23

⛹

🏻

‍♀

️

Su Islam an

dawo bayan sunci abinci sunyi sallah ta zauna dasu ta koya musu homework, suna zaune tana dubawa ko sunyi daidai ya leko falan, dan yana zaune a falanshi yaji shirunsu yayi yawa. Shine ya leko yaga ko harsun kwanta ne.

Ganinta zaune tana dudubawa tana sa

ke musu gyara yasa yai shiru tare da dan jingina da bango yana kallansu, shifa ko homework in sukace anbasu ce musu yake bashida lokaci suje suyi da kansu, shiyasa shi sam baisan ma me suke a skul ba, sai jarabawa tazo in aka kawo result basuyi kokari ba y

a hausu da fada. Kallansu yake sosai cikin tsananin sha'awa abinda ya sake birgeshi sam babu alamar bacin rai a fuskarta in bash gane ba sake koya musu take.

Jin kamar ana kallansu yasa tadan juyo, ganin tana kokarin juyowa yasa yai saurin dagawa daga ji

kin bangon yana neman wayancewa, hannayensa yadan harde tare dayin gyaran murya yace "ku cigaba, dama naji shiru ne na leko inga ko sun kwanta ne."

Bata amsa ba sai dai idanunta na kanshi, haka kawai ta kasa yakice kalaman daya fada mata a ranta.

Islam

cikin jin dadi ta dau book dinta ta nufeshi tace "Dady kalla kagani, wannan ne kawai banyi daidai ba shima yanzun nan zan gyara." Tai maganar cikin tsananin farinciki.

Murmushi yai tare da shafan saman kanta yace "Lalai Aunty ta iya koyarwa ko?"

Kai ta

daga cikin jin dadi, yace "wannan kokarin dole nayi kyauta, tunda akwai sauran time kafin ai bacci ko muje dominos?" Ai nan Ilham ma ta taso tana tsalle, suka hau murna suna eh Dady.

Kallan Ibty yai yace "In a shirye kike muje?"

Cikin mamaki tace "Hard

a ni?"

Yace "Keda kikai koyarwa ai dole harda ke."

Dan murmushi tai sannan ta mike ta shiga daki, fuskarta ta gyara ta daura dankwali sannan ta sa mayafi, kayan lefenta ta dauko wani akwati ta dinga duba turaruka, jin kamshin wani yafi wanda take amfan

i dashi yasa ta dauko ta fefesa, dan dole ko kadan kadan ne ta fara jawo hankalin mijinta kanta.

Tare suka fito sun rike hannunta, bayan mota ta bude musu suka shiga sannan ta shiga gaba itama ta zauna. Kamshin turaren ta sosai yamai dadi, wanda harsai d

aya dan kalleta. Zama tai fuskarta haryanzu ba a sake kamar yanda ta saba ba, yana jinsu tanata hira dasu Islam shidai yai shiru dan ko wannan fitar saboda ita yayishi, yana fatan zai wanke laifinsa ta haka, shifa raini ne bayaso da alama ta kula yana nema

n bata hakuri ne shiyasa take dadaga mai kai.

Sun isa ya kalleta bayan yayi parking ganin bata da alamar fitowa, kallansu Islam yai yace "Muje?"

Nan suka fito suna murna, Ibty kam datake jira yace suje kawai taga sun fara tafiya, badai ta wuce gona da i

ri ba?

Fitowa tai itama tabi bayansu, ita datake neman karkato hankalinsa kanta in tun yanzu aka bangare ai ansamu matsala.

A ciki sai daya fara order sannan ya juyo yace "Akwai abinda kikeso?" Murmushi tadanyi tace "Kome aka siya yayi." A zahiri bata

taba zuwa shagon ba, batasan ya abinsu yake ba, kartaje garin salo ta kwafsa shiyasa ma bata soma iyayi ba, dan Abba haka kawai bazai kawo su nan ya kashe kudinsa ba.

Sai da aka gama hada musu suka hada da ice cream sannan suka fito, inka gansu abin sha'

awa, haka suka shiga mota suka koma gida.

*****

Hajiya kam tunda taji alamun fitar motarsu take leke ta gate, ina suka je bayan magriban nan? Bakin cikin duniya ya isheta da ta dauka shi kadai ne ya fita sai dai data tambayi Bala yace mata dukansu ne, sa

i suntiri take a tsakar gidan, jitai gwiwowinta sun fara amsawa, jingina tai da jikin gate din tana dan sake lekawa, jin alamun Bala zai bude gate yasa ta dan leko kanta tana lekensu.

Ibty dake zaune gaban mota ne idanunta yakai jikin gate din, mamaki n

e ya kamata ganin ta hango kan mutum yana leke saboda fitilar motar daya kuna. Lalai matarnan takai makura gun sa ido, kauda kai tai kamar bata ganta ba ta juyo tanawa su Islam magana.

Hajiya ta koma ciki tai kwafa cikin tsananin kunar rai, wato Aminu ba

iji abinda tacemai ba kenan ko? Lalai yarinyarnan anyi tsinaniya tunda har ta iya wanke laifinta a kwana daya, sai dai intasan wata batasan wata ba, ta tabbatar da abinda malam yace mata inhar ta bari yarinyar nan ta shiga ran Aminu to fa ta shirya barin g

idan, yanzu kam taga alama sarai, tunda dai gashi kiri kiri ta sanar dashi abu amma a kwana daya ya canza.

Komawa ciki tai hankalinta duk ya tashi, hangota take a cikin rumbum abinci tana kwance tana kyarmar sanyi.

A zabure ta mike tsaye tabbas bazata

taba sabuwa ba.

*******

A falan Dady suka zauna,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login