Showing 87001 words to 90000 words out of 128353 words

Chapter 30 - IBTISAM COMPLETE

11 Nov 2026

22

ita ne yake faruwa.

“Koma me kikai Allah na tare damu, yanzu tashi ki hada kayanki, na tabbatar kinada magungunan da kikesan boyewa in kuma kin ban dama inje ni in hada mik

i kayan.”

Hajiya ta kalli Aminu, tace “Aminu?”

Kallan Ummy yai wacce ta nunamai yatsa tare da tamke fuska sosai tace “Wallahi ka kuskura kasa baki ka shirya daina amsa gaisuwata har nabar duniya.”

Idanunsa ya runtse baice komai ba sai kawar dakai dayai

kawai ya fito daga gidan cikin kumar zuciya.

A waje yaga Ibty ta dan hade hannayenta biyu alamar tana addu’a, kallansa tai tare da sauke hannu, matsowa yai ya sa karfi ya riko hannunta sosai, zafin matsar taji idanunta na hawaye tace “Yaya hannuna.”

“Ha

nnunki? Ni kinsan halin da kika jefani? Ke ko kunyar munafircin da kika hada bakiji ba?”

Ta daure tana dan motsi da hannunta dake zafi tace “Komai laifinane kenan?”

Yace “Yanzu fadamin laifin waye? Haka kawai ina zaune zaman zamana daga auranki kina nema

n ruguzamin farinciki.”

“Ka tabbatar da can a farinciki kake?” Tambayar datamai kenan ita kanta batasan dalili ba.

Jikin bango ya dan karasa da ita haryanzu hannunsa na rike da nata, idanunsa sunyi jaa sosai yace “Me kike nufi?”

Kai tadan girgiza tadan

sauke kai kasa saboda azabar ciwo da kanta yakeyi, dago habarta yai da karfi yace “Tambayarki nake?”

Tace “Na tabbatar sanda na aureka ba fara’a a fuskarka, ba jin dadi na kwanciyar hankali, aiki kawai kake sai kula da abinda ya zama dole.”

Yarfe hannun

sa yai yace “Yanzu fa? A kallanda ina aiki cikin kwanciyar hankali yanzu fa? Kin ruguzamin rayuwa.”

Idanu tadan runtse kadan tace “Daga baya zaka fahimci ban taba neman ruguza maka rayuwa ba.”

Sauke hannunta yai cikin karfi ya juya ya fita daga gidan,

a waje ya tsaya ya kira Baffa ya sanar dashi abinda ke faruwa yana rokarsa akan yawa Ummy magana, Baffa yace “Shi dakanshi zai karaso a tattara Hajiya dan ya tabbatar Ummy tanada kwakwaran hujja.”

Jin wannan kalamai yasa zuciyarsa ta sake tafasa, cikin ba

cin rai ya shiga gida ya bude motarsa ya zauna yana tunanin abinyi.

Ummy kam tana tsaye akan Hajiya duk yanda Hajiya taso ta sa kwalli ta kasa, haka ta hada kaya da niyyar wallahi goben nan zata dawo dan bataga mai korarta ba.

Haka Ummy ta sata gaba suk

a fito, Hajiya yau kam ji take wannan ranar tafi kowace rana bakin ciki, lalai in ta tashi yiwa Ummy magana wanda yafi ko wane muni zata aikata mata.

****

Suna fitowa waje Ummy taga Ibtisam, Hajiya ta kalleta wato itace ta sanar da Ummy abinda ya faru ke

nan? Wani murmushi tai a ranta tace “Kema ki shirya ganin bala’i da masifa.”

A waje sukaga Aminu da mota, Ummy ta kalleshi tace “Ina zaka?”

“Zan kai Hajiya hotel din dazata kwana.”

Tai wani murmushi tace “Bansaka ba ni da kaina zan kaita, kace Mamman d

a Ainah su fito mu tafi.”

Takaici ne ya kara kamashi ya zabgawa Ibty wani kallo yace “Ita kuma yaushe zata barmin gida?”

Wannan karka damu, zan zo na dauke abata goben nan, ai dai bakabar yaranka ba kowa bako? Xan zo na dauketa na kuma dauke jikokina kai

sai kai zamanka kai kadai.”

Ciki ya juya cikin kunar rai, Ummy ta kalli Ibty tadan dafa kafadarta a hankali tace “Karki damu, yau ranar farinciki ce a rayuwata sannan ba wanda zai rabaki da gidanki.”

Ta kalli Hajiya tace “Duk tsubun mutum Allah yana ta

re damu, kuma ke da Aminu mutu ka raba, kafin wani abu ya faru insha Allahu sharrin wacan mara imani da tsoron Allahn ya karye, kedai kiyi kokarin ci gaba da addu’a sannan kija mijiki a jiki.”

Kanta ta sunkunyar tare da daga kai, cikin sanyin murya tace “

Ummy sai yanzu na tuna tunda ta bashi kunu ya tafi office dashi ya canza halayensa.”

Murmushin takaici tai tace “Ai ni ina kallan d’ana nasan ba kalau yake ba, Aminu ko ya tsani mutum baya nunawa kiri kiri haka.”

Kallan Hajiya tai tace “Yau ko zaki mutu

kin bar gidan nan kenan, addu’ar shekara biyar bata fadi ba.”

Hajiya ta kallesu zuciyarta na wani tunzura, lalai ko zata koma a sake kusantarta koma ta ina ne sai taga bayan mutanen nan guda biyu.

{Nace Hajiya ko na d’auko ragowar tsiren ki tafi dashi?

🤭🏃🏻

‍♀

️

tunda ba’asan sanda za’a sake gamuwa ba

🤭

?}

[3/19, 10:39 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

(.........In Between)

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Bat

ch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA* *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004

2083371244

Zenith Bankima

36

Hajiya gaba daya ta kasa yin wani, duka ya kamata tawa Ummy ta koma ciki? In tai haka kuma

ai ta kara lalata alakarta da Aminu, ‘yar iskan yarinyarcan wai harta samu baki tana fadawa Ummy ta ba Akinu abu, lalai dole ta tozarta yarinyar nan.

Ummy ce ta kalleta tace “Ke banda ma dai ba kunya a harkarki ki hau adaidaita ki bar nan mana? Ko gidan

d’anki ne?”

Hajiya ta kafe Ummy da ido tana mata wani kallo, Ummy tai dan karamin tsaki tace “Yau baki samu damar yimin maganin ba? Ko kuwa wanda kikai da ne ya karye?

Hajiya takai makura, Ummy ta kalli Ibtisam tace “Ki koma ciki ki kwanta a gidan mijin

ki, gidanki, in zaki wuce kicewa Bala yazo ya siyomin kwado dan dakaina zan rufe gidan da kuma kaina zan tafi da makulin saboda irin wadannan mutanen da basa tsoron Allah bakasan me zasu aikata ba.”

Ibtisam duk da ciwon dake damunta hamdalla da sake addu’

a kawai take akan Allah yasa matarnan tabar gidan kenan har abada.

Tana kokarin wucewa taji an jawo rigarta ta baya iya karfi, wanda yasata yin kakari.

Ummy ta kalli Hajiya wacce ta jawo Ibty gabanta kafin suyi wani yunkuri Hajiya ta tsinkawa Ibtisam wa

ni gigitacen mari, da alama neman inda zata huce takeyi dama.

Ummy a fusace ta matso ta rike hannunta data rike rigar Ibty tace “Malama kanki daya kuwa?”

Hajiya ta daga hannu tana neman sake zuba mata Ummy ta hankadeta da karfi, Ibty mamaki ya rufeta g

a wani azabar zafi da kuncinta yakeyi, ai Hajiya kamar jira take nan fa ta balle, “Allah idan har yarinyarnan bata bani hakurin abinda ta aikatamin ba ta shirya fuskantar bala’i da masifa.”

Ummy ta bude baki zatai magana kawai taji Ibtisam tace “Allah na

tare dani, kuma duk wanda ke neman d’an uwanshi da sharri to ya shirya fuskantar wannan sharrin a kansa.”

Baki Hajiya ta bude tace “Ni kike fadawa haka?” Ta nufo Ibty kamar wata bijima, kofar gate aka bude nan suka maida kallansu kan kofa, me zasu juyo su

gani? Hajiya ce yashe a kasa tana kuka.

Ummy ta kalleta ta kauda kai dan ko batai magana ba tasan sharri take shirin yi, Ibty kam mamaki ne ya rufeta tace “Lafiya?”

Ai Hajiya bata kulata ba sai kuka kawai da take tana sa hannu akai, Aminu cikin sauri ya

nufi har yana neman yin tuntube, ya karaso yace “Hajiya? Meke faruwa?”

Ta girgiza kai tana kuka tace “Aminu matarka da mahaifiyarka ne suka hadu suka dakeni, daga nace da Na’imah na duniyar nan na tabbatar baza’a tozartani haka ba, Aminu banda kowa a dun

iyar nan sai kai to dama Na’imah ce ta hadamu gashi yau sun ra……..” ta kwace da kuka, ai Aminu a zabure ya dago yana neman shararawa Ibty wani marin, cikin tsawa yaji ance “Kana sauke hannu a fuskar nan wallahi zai kayi dana sani mai karfi.”

Ibtisam ta k

alleshi kawai ta juya ta wuce tare da sanar da Bala sakon Ummy na kwado, nan ya taho ya amshi kudi ya wuce siyowa.

Aminu nan fa ya tsuguna yana lalashi Hajiya ita Ummy abin ma dariya yaso bata, suna nan tsaye itadai Ainah tana tsaye tana kallan ikon Allah

.

Bala ne ya dawo da kwado, Ummy da kanta ta datse gidan tasa kwado daya a ciki daya a gate, sannan ta kalli Hajiya tace “Ko mantuwa kikai ki sanar dani zan zo na aika miki kauyenku.

Suna kokarin shiga mota sai ga Baffa ya iso, da sauri Aminu ya karasa

kamar wani zarare yana rokar Baffa akan ya taimaka ya ba Ummy hakuri, ai Baffa hannu kawai ya dagamai bai tsaya mai magana ba ya nufi gun Ummy.

Murmushi tai tace “Yallabai an taso ka?”

Ya kalli Hajiya yace “Ina zata da daren nan?”

Kafada ta daga tace “

Dama hotel nake tunanin nema mata ta kwana gobe ta tattara ta nufi inda ya dace.”

Kai Baffa ya daga yace “Hakan yayi, mu wuce?”

Ta girgiza kai alamar a’a tace “Ina bukatar mu wuce dasu Islam ne daga gida su dinga zuwa makaranta, na sati biyu, sannan inda

hali Ainah kicewa kanwar Ibtisam ta biyomu mu wuce tare gobe zan sa a maidata gida.

Baffa bai nemi jin dalilinta ba dan ya tabbatar tanada hujja, haka suna nan a tsaye Hajiya tun tana kokan karya har ta fara zuge jaka tana neman kwalli ko turare.

Hankal

in Ummy ne yakai kan abinda take, Ummy ta kalli Ainah tace “Kwashe kayan kisa a bayan mota.

Hajiya ji take kamar ta shake Ummy dan takaici, haka suna tsaye aka kwashe suka jira har aka hado kayan su Islam itama Iman ta hado nata suka shiga motar Baffa, it

a kuma Ummy daga ita sai Hajiya suka shiga motar Mamman.

Haka Ibty na jikin gate har suka wuce, addu’a ta sakeyi sannan ta kalli Aminu wanda ya dafa goshinsa gaba daya kana kallansa kasan yau ankaishi makura gashi bashi da wata mafita.

Waigowa yai fitili

n gaban gidan suka haske mai Ibtisam wata irin tsana ta kara kamashi, juyawa tai ta koma ciki ba tare da ta tankamai ba.

Shigowa yai a fusace, yana neman tarar mata, kafin ya karaso ta wuce falanta, nan ya nufi falanta yana neman ta ganin batanan ya nufi

daki, yana hankade kofa ya ganta zaune da Al-qur’ani tana karatu, to kodai bashi da imani ai bazai je ya finciko ta tana karatu ba, ya kuma tabbatar munafirci ne yasata daukan qur’ani a wannan lokacin, da karfi ya banko kofar kai kace ballata zaiyi.

**

***

Sukam su Ummy suna tafe Hajiya tana zazzagawa Ummy magana “Yanda kika tozartani kema sai Allah ya tozartaki dama batun yau ba nasan kin tsaneni amma ban dauka tsanarki takai ki tattaroni cikin dare da mutuncina da kimata ba, wato Na’imah ta mutu bakwa

ganina da daraja, ai ko baku daukeni a bakin komai ba kwa duba jikokin dake tsakaninmu.”

Ummy tana jinta ta kwantar dakai tare da lumshe ido tana godiya ga Allah daya nuna mata wannan rana.

Hajiya ganin da gaske fa Ummy take ta waigo ta kalleta tace “Na

ji na bar gidan yanzu ku kamamin gidan da tunda kukai niyya, badai kusa da Aminu bane bakwaso na zauna? To na hakura ku nemamin wani gun……”

Ummy duk yanda taso ta daure batasan sanda ta kwashe da dariya ba, ta bude ido tace “Gida? Yanzu? Sanda nake rokark

i ki zo mu baki wani gun kin kula mu? Yanzu kuwa ai korar kare muka so yi miki akuma dalilin me zamu baki gun zama?”

Hajiya ta juyo tace “In baku bani ba ina kuke so na zauna? Ni ba kudi ba?”

“Wannan damuwa tace? Ki wuce can kauyenku a taimaka a baki gun

zama ko da can ba’a kauyen kike ba?”

Hajiya gaba daya zufa ce ta fara karyo mata, tunowa tai da dubu darin da Aminu ya bata harta cinye dubu biyar, yanzu me ta ba mai magani sannan ina zata samu gun kwana na kwana biyu kafin ta dawo gidan ta? Dan ko za’a

mutu bamai rabata da gidanta.

Ummy bata ko bi takanta ba sai da suka isa wani dan karamin hotel wanda kana gani kasan na wanda yake da dan rufin asiri ne.

Wani kallan kyama tawa hotel din tace “Badai anan zaki ajiyeni bako?”

Ummy balle jakarta ta cir

o dubu goma, ta mika mata tace “kwana daya dubu biyar ne, ragowar kyaci abinci kiyi kudin mota. Sannan zan kara sanar dake makulin gida na gurina kuma goben nan zan sa mutane a cikin gidan, in ma kina tunanin zuwa gun Aminu ne dan ya taimaka miki ki har wa

halar da kanki.”

Huci kawai Hajiya takeyi, Ummy ta dan mika hannu tace “Kawo wayarki nasa miki sabuwar numberta ko zaki kira ki fadamin kin isa riga?”

Kamar bazata bada ba sai dai gwara ta bada yanda in boka ya nemi wani abin zatai amfani dashi.

Tana mi

kowa taga Ummy ta balle bayan waya ai nan Hajiya ta fusata ta fara kokarin kwace wayarta, Ummy ta cire sim din kamar masu kokarin dambe ta cila jakarta ta sa a kasa sannan ta mika mata wayarta, Hajiya ta hau zage zage tana tsinewa Ummy akan wallahi sai tag

a bayansu yanda suka mata itama sai ta ninka musu abinda suka aikata mata.

Nan ta fito ta kalli dan iskan hotel din kawai tahau adaidaita tabat gun dan ko za’a mutu bazata kwana anan ba.

Ina zata? Ko ta koma gidan Aminu? Kai ta girgiza da sauri in har

tai hakan me Aminu zai dauketa? Ko ba shiba ina zata zauna bayan tsinaniyarnan ta rufe mata gida? Ai gwara taje ai magani a rufe bakin Ummy ko a haukatata yanda zata dawo da karfinta.

******

Ibty ce ta fito daga daki dan yunwa ta fara cinta dayawa ha

r bata gani sosai, ga mari da tashin hankalin data fuskanta yau kala kala, ga tun ruwan zafin safe ne a cikinta.

Mamaki ne ya kamata ganin Aminu zaune a falanta ya hade kafa daya kan daya, fuskarsa ba annuri sam, kai ta dauke kawai ta fara yin hanyar kit

chen.

“Bakiga jiranki nake ba?”

Kallansa tai kamar zatai magana sai kuma ta nufoshi, karasowa tai ta zauna daga dan gefen kujera, cikin muryar mara lafiya tace “Gani.”

Kallanta yai sannan ya kawar dakai saboda rashin san ganinta dayake, “Wato ke munafuk

a ko? Yanzu hankalinki ya kwanta?”

Ibty takai makura duk hakurinta ta rasa me tai, kallansa tai kawai yaga ta daga kai.

Yace “Eh?”

Ta sake daga kai tare da dan kauda kai, hannu yasa ya rikota tare da jawota kusa dashi, dayake ba jiki ne da itaba daga a

nsa karfi sai kaga ana fincikota, balle yau da ba karfi sam a jikinta, yanda ya jawota ne yasa ta fada jikinsa, kokarin dagata ya farayi zafin jikinta ne ya ji a jikinsa, kallanta yai tausayinta na ratsatsi sai dai sam bayasan ganinta.

Dagata yai ta mike

zaune tana dan maida numfashi kadan, kanta na wani irin ciwo ga jiri dake dibanta a zaune.

“Meye hakan kike?” Yai tambayar ganin tana wani langwabe kai.

“Banasan iskanci da munafirci, magana nake miki ko? Ko kuwa rashin kunyar kikesan nunamin?”

Bata ta

nka mai ba dan sam batada karfin magana, kwantar da kanta tai jikin kujera tanadan fitarda numfashi kadan kadan.

A fusace ya mike yabar gun saboda takaicin yanda kasan zuciyarsa ke tsananin tausayinta.

Bangarensa ya nufa sai dai sam ya kasa zama, yawo

ya shiga yi yana tuno zafin da yaji a jikinta da kuma yanda tai luuu, karfa yarinyar mutane ta mutu a gida daga shi sai ita?

******

Hajiya hotel hudu tana shiga daga taji uban kudi sai ta fito, dan kudin nata da ba yawa ne dasu ba bazata karar dasu a k

wana daya ba.

Haka nan taja uban kayanta ta nufi inda Ummy ta ajiyeta asali, kamar zatai kuka haka ta shiga ciki, babban tashin hankali bai kara afkuwar mata ba sai da taga an dauke wuta wai an kuna solar amma wai ba fanka ba Ac haske kawai solar din take

badawa, ga uban sauro dan ma lokacin sanyi ne.

Tagumi ta baza lalai bata taba tunanin za’aci zarafinta haka ba, ta dauka yau rana ce mafi farinciki a rayuwarta amma an juya mata ita zuwa bakin ciki. Dole gobe da asuba ta nufi gun boka dan bazata iya jira

ba.

Kanta tadan dafa ta tuno fadan da sukai dashi, haka nan zanje na bashi hakuri ya zanyi?

**

[3/22, 10:41 PM] Hauwa Galadima:

💫

IBTISAM......

💫

      (.........In Between)

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*ŋą Ä̤

ʏʊ

ֆ

ɦɛʀ



ʍʊ

ɦɖ

🏌🏻

‍♀

️

*

*Top Ten! Takun Haske Batch A*

Ki hanzarta ki mallaki naki

🤸🏻

‍♀

️

*TURA 500 TA*  *Ka samu rahusar novel bakwai tare da shirye shirye*

+447894142004

2083371244

Zenith Bank

37*

Aminu gaba daya baccin sa na ranar ragage ne kuma mat

a dadi, zuwansa sama da bakwai bangaren Ibty sai dai haryanzu tana nan a kwance a falo, daga ya nemi ya karasa gunta sai yaji sam bayasan ganinta sai ya juya, haka ya dinga zirga-zirga daya ya kwanta tunaninta zai hanashi bacci ya mike, sai yazo yaji ya ka

sa karasawa ya juya. A haka har asuba tai itakam wanni baccin wahala take mai cike da yunwa da rashin karfin jiki sai dai tayi bacci sosai.

Mikewa tai dakyar ta nufi toilet dakyar dan har wani jiri takeji, alwala tai ta tada sallah a dakinta, kawai datak

ai sujjada ta fashe da wani irin kuka tana rokar Allah ya daidaita tsakaninsu da mijinta, kuka take sosai tana rokar Allah….

Shikam Aminu bacci sai wajen asuba ya kamashi, a firgice ya tashibyai alwala sannan ya fito zai tafi masallaci, jiki a sanyaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login